Showing 15001 words to 18000 words out of 89400 words

Chapter 6 - MY ENEMY BOOK 2 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

2514

zama yayi ya kasa kunne yana sauraron Abbah,

Baiwar ALLAH haka kawai sai satar kallon Razhdeen take tayi...
Abbah ya cigaba da cewa "naji mai martaba ya fara mun wata magana ne dangane da ƙanwar matarsa Maamie, akan cewa za'a haɗa Auren ka dana Roshan itace wacce zaka Aura..."
Dasauri Razhdeen ya ɗago yana kallon Abbah fuska a murtuƙe babu alamun Annuri a fuskar,
Aunty Yolash itama da sauri ta furta "whattttt!..."

Yaran gidan kuwa gaba ɗaya haɗa baki sukayi wurin cewa "Ramlatttt!..."

Baiwar ALLAH kuwa kanta ne yayi wani irin sarawa da ƙarfin gaske kamar wanda aka doka mata Gatari, dasauri ta sunkuyar da kanta ƙasi tana dafe dashi....

Aunty Yolash tace "wai Yaya kana nufin kace Ramlah ƙanwar MAAMIE? Impossible wallahi, kaima kasan cewa Hajia Maamie ta shure Hajia Kilishi matarka wulaƙanci da rashin mutunci Koh? shin baka san cewa Hajia Maamie ita take iko da mai martaba ba koh? toh idan baka saniba yau zan sanar maka, duk abinda hajia Maamie tace ayi a masarautar nan shi akeyi idan tace bata son abu TOH kuwa mai martaba bai iya yayi ba, itace hakima mai mulkar masarautar...."

Abbah yace "ehh king ya sanar mun amma nace ya bari sai sunzo zamu tattauna akan batun tinda duk zasu zo Auren nan, amma ita yarinyar batada matsala ai koh?..."

Aunty Yolash tace "hakane amma kuma tana ɗaukar zugar Yayarta Hajia Maamie, nipah gaskiya Yaya bazaiyu a rinƙa tara mana mata marasa tarbiyya a gida ba, Hajia Kilishi ma ya muka ƙare da ita kuma du a ƙara kawo mana wata, itama Hajia Maamie za'a ɗau hukunci akanta ai....."

wani irin harara Pinky ta wurga wa Aunty Yolash dai-dain lokacin da suka haɗa ido da Aunty Yolash,
Aunty Yolash ce ta ɗauki pillow ta wurga mata tare da faɗin "kin ci ubanki Balkisu! Ni sa'arki ce ko kuma ina wasa dake? aikin banza kawai shin ƙarya nayi ne Uwarki tayi abun arziƙine a gidan nan ? tin kafin a haife ku ake shan gwagwarmaya da ita, gaskiya kuma dole a faɗe ta..."

murguɗa baki pinky tayi tana gunaguni tace "Uwata bata gidan ma amma baza'a barta tasha iska ba..."

Aunty Yolash tace "ita data sha iska kuwa har abada domin ko mutuwa tayi dole a faɗi halayarta na Arziƙi ko akasin haka,
ke nifa ba abokiyar yinki bane, Uwarki ce sa'ar yina domin ko Auntynki Minal bata isheni kallo ba tinda a gabana duk aka haife ku..."

ƙara wurga mata harara Pinky tayi tare da murguɗa baki tace "to kiyi dani ɗin mana..."

dasauri Rukky ta tashi daga cinyarta tana Binta da kallo cike da mamakin yanda Pinky ta tsaya tana yiwa Aunty Yolash ƙanwar Abbansu rashin kunya,
Pinky bata ankara ba taji Abbah ya zabga mata mari tare da jefota ƙasin carpet yana cankinta,
Abbah cikin zafin rai yake tattaka ta yana faɗin "ƴar uwar tawan kike wa rashin kunya dan ubanki, itama mahaifiya ce a wurinku, ashe rashin tarbiyar takun har takai haka?..."

Abbah har numfashinsa ne yake shirin ɗagewa tsabar ɓacin rai dake yanada hawan jini, Aunty Yolash ce ta tashi tana rirriƙe shi tare da bashi haƙuri tana rarrashinsa,

Pinky tana kwance ba abinda take sai kuka, ji nayi an ɗagota da hannu ɗaya ana janta suka nufi hanyar bakin ƙofa za'a fita da ita, idanuwanta ta buɗe tana ƙoƙarin ganin wanda yake shirin fita da ita, naga Razhdeen ne fuska ba annuri, daga nan ta saddaƙar cewa yau ranar mutuwarta ne, Ihu ta fara kurmawa tana ƙiran sunan Mommy, "wayyo Allah nah Mommy kizo ki temake Ni zasu kashe Ni, Mommy nah wayyo, Dan ALLAH Uncle Deen kayi haƙuri ka ƙyaleni, wallahi bazan ƙara baaa...."

Abbah kuwa cewa yake "kaje ka hukuntata tinda itama halin uwarta gareta, ba'a gidan nan za'a mun wannan iskanci ba..."


*ƳAR AMANA*🕊️🕊️🕊️

wani makeken ɗaki ne wanda yake zagaye da wantalelen carpet babu kujera ko ɗaya a ɗakin, fili ne kawai, ga wasu ƴan mata guda 50 duk suna zazzaune a filin ɗakin sun jeru hannayensu a ɗaure ta baya, ƙafafu ma a ɗaure, kana ganin kasan sato su akayi,
aciki kuwa harda ƴar Amana itama anyi mata ɗaurin da akayi wa sauran...

ɗakin duhu ƙirin baka iya ganin abinda ke ciki dake ƙofar a ƙarƙame yake, sai wani ɗan ƙaramin window wanda iska zai rinƙa shiga kaɗan-kaɗan, wannan lokacin kuwa window ma an rufe babu mashigar iska, duk matan nan babu wacce bata rigirta ba, numfashi sama-sama haka suke shaƙa, wata a ciki kuwa har ta mutu tana zaune kai a durƙushe wuya ya rigada ya karye, amma babu wanda yasan ta mutu...
suna cikin wannan halin suka ji motsin mutum yana ƙoƙarin buɗe ƙofa, a hanzarce duk suka ɗaɗɗago suna bin bakin ƙofar da kallo duk da duhu ne wurin basa iya ganin ƙofar ma,
wani irin farin ciki ne ya bayyano musu domin suna muradin shaƙar iskar waje...

Buɗe ƙofa akayi sai ga haske ya haskaka wantalelen ɗakin, wani irin iska ne yake ratsa su, ko wacce sai buɗe kafar hanci take tana shaƙar iska mai daɗin gaske,
Wani gabjejen mutumi ne ya shugo yana huci yayo kansu ya canko wasu ƴan mata biyu da hannu ɗaɗɗaya yayi waje dasu, duk na cikin kuwa kuka suka fara yi suna faɗin "wayyo mun shiga uku, yau ne ranar da za'a kashe mu..."

sai ga wasu mazan suma sun shugo, haka aka rinƙa fita dasu waje, duk aka jejjera su a waje, ga wurin kurmin daji ne babu mutane a dajin sai su, anan suke aikata miyagun ayyukan su, kuma anan suke ƙirƙiran ƙwayoyin maye, anan ake sato ƴan mata a kawo su, wasu a fitar dasu ƙasar waje aje a sayar dasu, wasu kuma yankasu ake acire wasu abubuwa ajikin mace ta hanyar nan suke samun maƙudan kuɗaɗe,
suna zazzaune ga wasu manya-manyan zabga-zabgan maza suna tsaye a kansu, saiga wata ƙatuwar motar baƙa ƙirin har wani sheƙi take, mai taya ta bayan mota, baka iya ganin wanda yake cikin motar, can ba jumawa sai ga wanda yake cikin motar ya buɗe murfin motar a hankali ya fara sauƙar da ƙafarsa ta hagun daga baya ya fito gaba ɗaya,
wani mutumi ne ɗan dattijo dashi, yana sanye da baƙin glass ga gemu ya ɗan sauƙo, mutumin baƙi ne yana sanye da manyan kaya water fruit, zuwa yayi ya tsaya a gaban ƴan matan yana wani irin lanƙwasa yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, cikin dirarren murya yace "wayyo ga ƴan mata zuƙa-zuƙa amma dole na ganku na ƙyale ku saboda banida abun more rayuwa kashhhhhh!!!..."
Yarinyar data rabani da dukiyata inda zan ganta a yau wallahi babu abinda zaisa na yankata a yau..." ya ƙarasa maganar yana bugar ƙafarsa da ƙasa tsabar takaici....

Duk tsaya kallonsa suka tsaya yi,

wani daga cikin yaransa ne yace "Ogah ɗaya daga cikinsu ta sheƙa pah..."

Yallaɓai yace "ina gawarta..."

cikin ƙanƙanin lokaci suka ɗaukota,
yace "okay kuje ku cire abinda ake buƙata ajikinta saiku bisineta...."
hakan kuwa akayi...


saiji sukayi yace "kai ina yarinyar dana ce ku nemo mun ita a duk inda take a doron ƙasa ?...."
yayi maganar a ɗaya daga cikin yaransa, wani ne yazo yanda Ƴar Amana take zaune yasa hannu ya janyo ta har gaban Yallaɓai...
Ƴar Amana tin lokacin data gashi taji gabanta yanata faman yankewa domin tasan mutumin asalin mungune bashida imani,
Yallaɓai kallon ƴar Amana yayi tare da tintsirewa da wata mahaukaciyar dariya harda tafa hannayensa, yana faɗin "shegiyar yarinya ashe tana wurin tana jin ina cikiyarta tayi luƙusss,..."
ya durƙusa a gabanta tareda kamo sumar gashinta ya kuma cewa "yau gaki a fadata, nine Sarkin wannan yankin, a wancan lokacin nasa an kamo ki a gidan marayu kin kuɓuce kin gudu, TOH yau kam babu ƙafar guduwa idan kuma kikace zaki ƙara tsere mun wallahi tallahi saina yanke miki ƙafafu Kinga kuwa ke kurmiya sannan gurguwa, shin ina ƴar Uwarki Baiwar ALLAH? tana ina? Hhhhh naji cewar tana gidan General koh? akwai tsaro sosai a gidan shiyasa banyi gigin zuwa yanda take ba, ke da ita kunyi bankwana har abada daga nan sai ƙiyamar da ba dawowa...."
Ƴar Amana sunkuyar da kai tayi ƙasi ko ɗagowa tayi ta kalleshi bata yi ba...

hannu yasa ya ƙara ɗago ta kanta suna kallon juna yace "munafuka ko irin hawayen nan bata yi, ke wai jaruma ko? to yau zan nuna miki tsoro a cikin idanuwanki..."

ya miƙe tare da ja da baya yana faɗin "duk ku Aske musu sumar kansu domin waɗannan babu wacce za'a sayar da ita da ranta, idan aka musu yankan rago zasu fi Albarka, yau za'a yanka mutum biyu gobe ma mutum biyu da haka har su ƙare, kullum mutum bibbiyu, da zarar sun ƙare sai a ƙara sato wasu ƴan matan kuma du, bamason talauci ya wanzu mana, indai akan kuɗi ne zamuyi abinda yafi haka..."

Duk matan wurin babu wacce bata tsorita ba,
wata a ciki tana kuka tace "Allah sarki Babana da Mamana basu taɓa haihuwa ba sai a kaina kuma ni ɗaya ce tilo, bayan Ni Allah bai ƙara basu haihuwa ba, gashi yau Nima zasu rasani, a hanyar zuwa makaranta aka sace Niii...."
ta face da matsanancin kuka mai cin rai....

Wata ma ta amsa da cewa "Ni ƴar talakawa ce Babana makaho ne Ni da Mamana muke buga-buga muciyar da kanmu, Ni a wurin tallah suka sato Ni..."
itama ta fashe da kuka...

Wata ma tana kuka tace "Ni marainiya ce a wurin Kakata nake zaune iyayena sunyi hatsarin mota duk sun rasu, ina kan hanyar dawowa da islamiyya saiga baƙar mota ta tsaya a gabana suka ɗauke Ni ....."

Haka ko wacce take gabatar da kanta wa junansu da yanda akayi aka sato ta, aka zo kan Ƴar Amana bata ce komai ba ita, sai wata ce tace "wannan kamar kurmiya ce Allah sarki, ko wacce da kwanakin ranar da zata mutu..."

Duk Yallaɓai yasa aka Aske musu gashin kansu anyi musu tanƙwal, kayuwa sai sheƙi suke,
Sai a wannan lokacin Ƴar Amana ta fara tsiyayar da hawaye ganin yanda akasa Aska ana yanke mata zara-zaran sumar gashin kanta, ganin yanda sumar gashinta yake zubowa ƙasi yasa ta yanki jiki ta faɗi sumammiya, duk da haka ba'a dena ba saida aka yanke gashin gaba ɗaya kayin yayi tal kamar madubi...

Ko wacce haka akayi mata domin daman in zasuyi yanka sai anyi wa mutum Aski,
Sannan aka zo duk wacce take wurin Saida aka manna mata wani kalanda mai danko ajikin kalandar an rubuta ranar da za'a yanka ka da lokaci,
Ita Ƴar Amana an manna mata ranar Jumma'at ranar 15 ga watan August next week kenam da misalin ƙarfe 7 na safe itada wacce tace ita kaɗai iyayenta suka haifa...
Domin akowace rana za'a yanka mutum biyu ne,
Idan aka yanka abubuwan da ake buƙata sune kamar Nonuwa, ƙwayar idanun, harshe, sai kuma farjin mace,
Duk suna zaune aka kamo waɗanda aka manna musu cewa yau za'a yanka su, duk matan ihu suka fara yi suna kururuwa ganin an janye wasu ƴan uwansu guda biyu,
shigar dasu akayi cikin wani ɗaki a ɗan gefe da dajin, shi kuwa Yallaɓai zama yayi domin shine ogansu shine maisa ayi,
hango Ƴar Amana yayi tana kwance har zuwa yanzu bata farfaɗo ba, murmushin mugunta yayi tare da kawar da fuskarsa gefe,
Can wasu ɗan lokuta sai ga masu yanka sun fito hannayensu riƙe da wuƙaƙe duk jini, ɗaya yana riƙe da ƙaton faranti yanda aka ɗoɗɗora kayan amfanin ƴa mace, har dana wacce ta mutu a ɗakin
zuwa sukayi suka ajiye a gaban Yallaɓai wanda fuskar yake murtuƙe babu kyan gani, Ciro wayarsa yayi ya danna ƙiran wani daga ƙasar waje yana faɗin
"Hello David akwai kayayyakin mata uku sun hallaru, zaku iya turo mun da kuɗin ta Acc, a yau zan tura yarana biyu su kai muku, kuma gobe ma haka daga yau har kullum, daman mata hamsin ne kafin a nemo wasu..."

daga other side suka tambaya cewa "nawa ne zamu baka?..."

Yallaɓai yace "mun gama magana ai! mace ɗaya a 20millions take kaga kuwa mata uku 60millions kenam..."

other side "ok don't worry we'll send you right now, but we need the things Early morning..."

Yallaɓai yace "ai cikin dare zasu tafi..."
Da haka suka katse,
Sannan ya bada umarnin gangan jikin mata biyun a bisine su tinda an ciri abinda ake buƙata already an bisine ɗayar,
sannan ya kuma cewa a maida sauran matan cikin ɗakin duhu zuwa gobe kuma du...
Hakan kuwa akayi.......




Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un
Rayuwa kenam!
Allah ka kawo wa waɗan nan matan ɗauki, ka cecesu🙏🙏
Waɗanda suka tafi kuma Allah ya jiƙansu .....


asmeetah writer ✍️




*MY ENEMY _*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login