Showing 30001 words to 33000 words out of 89400 words
bisani aka farkar da shi,
A ruɗe ya tashi yana fitar da numfashi sama-sama kamar wanda aka ɗage masa numfashi, gaba ɗaya ya yi jirib da gumi duk da sanyin A.C da ke cikin room ɗin,
Idanuwansa ne suka sauƙa akan Ƴar Amana dake tsaye a gabansa da wannan kan natan da babu sumar gashi ko ɗaya yanda kasan madubi,
ta zuba masa ido babu alamar annuri a fuskar,
Zaro eyes ɗinsa shima yayi yana binta da kallo lips na motsi a hankali yake jera Addu'o'i,
Ji yayi an dafa kafaɗarsa ana faɗin "what are you looking for? kayi mummunar mafarki Koh?...."
Sai a lokacin idanuwansa suka fara ganin dai-dai ashe Marshall Mohandas ne ya shugo ɗakin shi kuma sai yake kallon Ƴar Amana a madadin sa..."
Razhdeen lips na motsi a hankali yake furta "Sarah! Sarah!! Sarah!!!..."
Mohandas ya ce "shin ka gano a yanda take ne?..."
Girgiza kai Razhdeen ya yi tare da faɗin
"Naga a yanda take but I can't find a way, wurin is too far forest..."
Mohandas sauƙe numfashi yayi tare da goya hannayensa kan ƙirji.
Da sauri Razhdeen yakai eyes ɗinsa kan wayarsa sai yanzu ya tuna da message ɗin da aka turo masa, a gaggauce yasa hannu ya ɗauki wayarsa ko message ɗin yana da alaƙa da ita,
Ai kuwa cikin sa'a yana buɗe wa yaci karo da Address ɗin yanda Ƴar Amana take can cikin daji ne, ana ƙiran dajin da suna dajin dutse, da kuma lokacin da za'a aikata ƙiyama...
Zaro ido waje Razhdeen ya yi yana kallon wayar,
Mohandas karɓar wayar yayi shima yana dubawa ganin yanda Razhdeen ya ƙame a wurin,
Da sauri Mohandas ya ɗaga kai sama yana kallon agogo yaga ƙarfe 5 ne yanzu na asuba, cikin ɗaga murya ya ce "Major bamu da isasshen lokaci remain 1 hour ...."
Razhdeen a firgice ya ce "Okay.."
Ya tashi ya nufi hanyar fita, Mohandas ya riƙo shi yana faɗin "wait Major ka tsaya kayi sallar asuba, bari na ƙira sojojin nan su tanadar mana da elekwabta da kuma sojojin da zamu tafi da su domin bamu san mai zamu tarar ba..."
Yanda Mohandas yace haka Razhdeen ya yi, shiga toilet yayi tare da ɗauro alwala ya fito wannan lokacin kam a gida ya yi sallar asuban sa, bai tsaya wata-wata ba ya yi shirinsa cikin kakin soja irin na ƙasar U.S, ya fito a Major General Razhdeen ɗinsa, ya ɗaure sumar kansa da wani jan ƙyalle mai zanen gum a jiki, kayan sojojin nan ba ƙaramin masa kyau suka yi ba duk da a birkice yake,
Shima Mohandas yayi shirinsa na kakin soja shima na ƙasar U.S duk suka ɗauki bindigun su already an kawo musu jirgin da zai kai su cikin dajin domin sun shigar da bayanai sosai duk da basu tabbatar ba tukun...
Da sassafe an fito da kowa kamar yanda aka saba kullum sai an kashe mutum biyu to haka yau ma, yau kuma akan Ƴar Amana za'a fara sai wata daga ciki itama,
A wannan ranar Guess shima yana wurin, ga kuma Yallaɓai a zaune akan kujera,
Yallaɓai ya kalli Guess sannan ya ce "You Guess a wancan lokacin na baka ajiyar wannan yarinyar amma ka barta ta gudu, toh yau kuma kai da hannunka zaka yanke mata maƙogaro a filin nan kowa yana kallo..."
Guess yana tsaye da baƙar hula a fuska daman shi koda yaushe fuskarsa a rufe take, babu wanda yasan kamannun sa,
Yallaɓai tashi yayi ya nufi wurin da Ƴar Amana take a durƙushe, ya ɗagota sannan ya since mata igiyoyin da aka ɗaure ta da shi, yana faɗin "Allah sarki kurmiyar Allah yau za'a wuce ƙiyama, idan kinje kice ina gaida su mutanen mu da kuma sabuwar Shugabar ku mace da aka kawo wato Madam Aliya wacce nayi silar mutuwarta ta hanyar doke motar ta da trailer, da kaina nake tuƙin babbar mota trailer nayi fushhhh na doke motar ta, domin ta maye mun gurbin shugabanci nah a gidan marayu, Ni kuwa bazan juri ganin haka ba, ohhhh ashe dai ke baki santa ba lokacin nasa an sace ki sorry! sorry!! sorry!!!, ki dai gaishe ta kinji ko?..."
Yana ƙarisawa ya hankaɗata gaban Guess sannan ya wulla masa wuƙa yana faɗin "yanzun nan ba tare da ɓata lokaci ba ka yanke mata maƙogaro..."
Guess yanjo ta yayi tare da ɗora mata wuƙar akan wuya ya ɗaga mata haɓar ta sama,
Yallaɓai wani irin murɗaɗɗen murmushi yayi ya ce "ehen gurza mata wuƙar..."
Guess dai ya kasa ai watar wa wuƙar kawai ya ɗora mata amma ya kasa gurzawa,
Yallaɓai ganin Guess bazai yanka ba yasa ya fitar da ƙaramin bindigar sa ya saita kan Guess yana faɗin "Guess kafin na ƙirga 1 zuwa 5 ka yanke mata maƙogaro in ba haka ba saina fasa maka kai sannan itama na kashe ta, ta tabbata kenam kai ka barta ta gudu ko?..."
Shuru Guess ya kasa aiwatar wa, Yallaɓai ne ya fara ƙirge kamar haka
"I, 2, 3..."
Guess ganin Yallaɓai da gaske yake kuma yana matuƙar tsoron mutuwa a hankali ya fara danna wuƙar yana shiga a hankali, nan jini ya fara zubowa sakamakon shigarta da wuƙar ya fara yi...
Yallaɓai ganin haka yasa ya dakatar da ƙirgen still bindigar tana hannun sa.....
Ɓangaren su Roshan da Baiwar ALLAH sa har zuwa wannan lokacin bata bashi haɗin kai ba, ko kaɗan bata son haɗa ɗaki ɗaya da shi...
Tana kitchen taji shugowar mutum da sauri ta waiwaya ganin Roshan ne yasa ta haɗe rai tare da juyawa ta cigaba da aikin ta,
A hankali ya furta "good morning Ammata..."
Bata kula shi ba ta cigaba da aikin ta, ya ce "dan ALLAH zan iya sanin laifi na? ki sanar mun a yanzu zan iya durƙusa miki na baki haƙuri, amma kina azabtar dani Ammata, shin yaushe zaki bani lokaci na ne a matsayina na mijinki?..."
Juyowa tayi tana kallonsa fuska a haɗe ta ce "babu rana, bare wata bare kuma shekara, tunda har ka Aure Ni a haka sai kuma ka cigaba da zama dani a haka har sai ran da ka gaji da zama dani..."
tana kaiwa nan tayi ficewar ta, ta bar shi a kitchen shi kaɗai....
asmeetah writer ✍️
🤦♀️ *MAƘIYI_NAH*🤦♀️
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء محمد أولا 🥳
Asmeetah (giaɗe writer)
https://chat.whatsapp.com/ERHR7h6oEY76fTvAQFZauw
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
STEP TWO
👇
*15_ TO_16*
Ƴar Amana har ta fara shiɗewa sakamakon wuƙar da ya ke shigar ta a hankali, ga jini har ya wanke gaban rigar ta.
Yallaɓai yana riƙe da bindiga a saitin kan Guess kwatsam yaji bullet ya shigar masa hannun da yake riƙe da gum ɗin, a firgice ya jefar da bindigar hannunsa yana kallon yanda aka harbo bullet, gani yayi Elekwabtan Sojoji yana shirin sauƙa har guda biyu kuma duk a cike da Sojoji, Yallaɓai ganin haka yasa ya yi gudu ya shige cikin daji yana riƙe da hannunsa da aka harba, shima Guess jefar da wuƙar hannunsa ya yi tare da tserewa, haka duk yaran Yallaɓai suka fara guduwa suma Sojojin dirƙowa suka rinƙa yi suna bin bayan su, iya Razhdeen da Mohandas ne kawai suke tsaye a wurin.
Razhdeen ido ya zaro sosai ganin halin da Ƴar Amana take ciki domin kallo ɗaya yayi mata ya gane ta dake ba kowa ne zai iya gane ta ba saboda Askin da aka mata babu alamun gashi..
Ƴar Amana itama a tsaye take idonta na kallon dishi-dishi amma da haka ta iya gane Razhdeen, kafa masa shanyayyun idanuwanta tayi waɗanda suke shirin rufe wa, ga kuma wuya yanda aka fara yanka wa, ganin idanuwanta ba ƙarya suke gane mata ba shi ɗin ne Razhdeen yasa ta fara takawa da gudu tana yowa kansa, duk da a halin da take ciki amma bai hanata gudu ba ga wani irin hajijiyar da take ji, har tayi kusan zuwa dab da shi aka harbo mata kibiya ta baya, ido ta zaro waje jin an soketa ta baya, tangal-tangal ta fara yi zata faɗi ƙasi Razhdeen ya yi saurin riƙo ta a ruɗe, rungumarta yayi sosai idonsa akan kibiyar dake soke a bayanta, gani yayi kamar an ƙara jefo da kibiyar a karo na biyu ya yi saurin juyar da ita ya kasance shine a gurbin ta, ai kuwa kibiyar bata sauƙa a ko ina ba sai a bayan Razhdeen yana rungume da ita, sake jefo da wata kibiyar akayi a karo na uku nan ma ya sake sokar Razhdeen ko motsa wa baiyi ba ya rungume Ƴar Amana sosai idanuwansa a lumshe domin kibiyoyin ba ƙaramin sokarsa suka yi ba,
A wannan lokacin ne Mohandas ya saita yanda ake harbo da kibiyar da bindigarsa nan take ya harbe saitin goshin wanda yake harbowa, ba kowa bane illa Yallaɓai, daga nan Yallaɓai bai ƙara shurawa ba domin goshin sa aka samu da bullet,
Mohandas ne ya ja Razhdeen tare da Ƴar Amana cikin Elekwabta tare da yara ƴan matan da suke wurin duk aka sassaka su da sauran Sojojin duk suka shiga jirgin ya tashi suka tafi, ɗayan Elekwabta kuma masu laifin da aka kamo duk ɗinsu ne aka sassaka su a ciki har da Guess suma suka tafi, bayan sun je sama sosai Sojojin suka jefo da bom gaba ɗaya wurin ya tashi duk abubuwan su suka tarwatse...
Razhdeen da Ƴar Amana ba ƙaramin jikkata suka yi ba domin kibiyar yana da dafi sosai dafin har ya ratsa jikinsu, especially Ƴar Amana ita daman ga wuyan ta da aka fara yanka wa,
Cikin lokaci ƙanƙani suka isa cikin gari, Razhdeen ne ya yi musu alama da hannu cewa kada su tsaya a ko ina sai gidansa baya buƙatar zuwa hospital, hakan kuwa akayi sauran ƴan mata kuwa da masu laifukan duk headquarters aka wuce da su.
Mohandas ne ya shiga da Razhdeen wani soja kuma ya shigo da Ƴar Amana, kai tsaye part ɗin Razhdeen aka wuce da Ƴar Amana dake can cikin falo na biyu, shi kuma Razhdeen sai aka shigar da shi bedroom dake falo na farko, shi ya bada umarnin haka domin baza'a rasa masu zuwa duba shi ba kuma baya so asan Ƴar Amana tana nan, ya sanar wa Mohandas shima cewa baya son kowa yasa Ƴar Amana tana hannun sa...
A lokacin yasa aka ƙira masa wani Abokin sa babban Doctor yazo shi kaɗai da kayan aiki domin an sanar masa cewa Razhdeen ne ya samu hatsari kuma ba'a buƙatar zuwa hospital, bayan wasu mintuna sai ga Doctor ya zo da akwatin kayan aiki a hannun sa, da sauri ya yo kan Razhdeen zai duba shi bayan ya isko shi a bedroom.
Razhdeen yana kife akan gado babu riga a jikin sa ga kibiyoyi guda biyu da Mohandas ya cire masa akan drower, Razhdeen ido a lumshe murya ciki-ciki ya ce "kuje ku fara duba Yarinyar tana cikin mawuyancin hali..."
Doctor da Mohandas ne suka fice da sauri kai tsaye ɗakin da aka ƙwantar da Ƴar Amana suka nufa domin tafi jikkata sosai wanda a halin yanzu ba'a sani ba ko tana raye ko kuma ta mutu..
Doctor yana samun ta a wannan yanayin shi kansa sai da ya tsorita ganin ana shirin yanka mata wuya ga kibiya yanda aka cire mata a baya, babu alamar numfashi a tattare da ita.
Girgiza kai Doctor ya yi sannan ya ce "wannan aiki ai sai hospital bana aikin gida bane domin akwai abubuwan da ake buƙatar yi mata a hospital..."
Mohandas ya ce "aikin ba zai yu a gida bane?..."
Doctor ya ce "zai yu mana amma zai fi kyau a kaita hospital..."
Mohandas ya ce "to in har zai yu kayi abinda Major ya ce kawai, jinyar ana so ayi shi cikin sirri ne ba tare da kowa ya sani ba, hakan yasa muka ƙira ka ai mun san da hospital muka ƙira ka, ka dai san halin mutumin nakan kawai kayi aikin da ya dace..."
Doctor ya ce "okay ai sai ku mun bayani tin farko, insha Allahu zanyi iya ƙoƙari na..."
Daga nan Doctor ya fara cire kayan aikin sa shi kuwa Mohandas fice wa yayi domin ba'a son a tsaya akan majinyaci idan ana masa aiki...
Abinda Doctor ya fara yi shine ɗinke mata wuya sannan ya sanya mata bandeji ya ɗaure wuyan, sannan ya juyar da ita ya fara ɗinke mata wurin da aka soke ta da kibiya sai da ya gama treat ɗinta sosai sannan ya buƙaci a ɗaura mata laidar jini domin ta zubda jini sosai..
Bayan an sanar wa Razhdeen sai ya buƙaci a ja nashi jinin, Doctor bai yadda da hakan ba sakamakon shima ya zubda jini