Showing 39001 words to 42000 words out of 89400 words

Chapter 14 - MY ENEMY BOOK 2 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

2517

Bayan su Abbah sun haura Roshan da gudu yabi bayansu, yana haurawa can part ɗin da suke, jawo ƙofar room ɗinsu yayi tare da murɗa key yabar key ɗin a jikin ƙofar sannan ya dawo yana ce musu "Marshall ka kama matarka ku tafi duk yanda ya kamata, kada ka bari kowa yasan yanda kuke domin Abbah zai iya sawa a nemo ku a duk yanda kuke, daga nan ka wuce airport ku bar ƙasar..."
Girgiza kai Mohandas yayi alamun bazai iya ba,
Minal ta ce "Dan ALLAH Mohandas kazo mu tafi kafin Sojojin gidan su ankara kaga yanzu basu san halin da ake ciki ba..."
Jin haka yasa Mohandas riƙo hannun Minal suka fice, Roshan ne yabi bayansu saboda yana so ya fita dasu kar Sojoji su fahimci wani abu,
Hakan kuwa akayi motar Mohandas suka shiga, Mohandas shine mai driving sai Roshan a gefen sa, Minal kuma tana ta back seat da haka suka fice a gidan gaba ɗaya kai tsaye airport suka wuce...

Abbah da Ammy suna cikin bedroom ɗinsu sai ji sukayi an ƙarƙame su, ga bindiga a hannun Abbah yayi ƙolon duniya akan azo a buɗe mishi ƙofa amma babu wanda ya nufi wurin, ga wayar sa ya barta a falo balle ya ƙira sojojin gidan gaba ɗaya Abbah ya rasa mai yake masa ciwo, ita kuwa Ammy alwalarta tayo tazo ta tsaida sallah domin a halin yanzu Abbah ba sauraronta zai yi ba,
Baiwar ALLAH tana so taje ta buɗe musu ƙofar jin yanda Abbah yake ta ƙiraye-ƙirayen sunayen su especially sunan Uwar masu gida yafi ƙiran ta akan taje ta buɗe amma Ummy fur taƙi zuwa sannan tana riƙe da hannun Baiwar ALLAH taƙi sakin ta,
Ummy tana kuka ta ce "haba Aunty Dota har yaushe za'a kawo karshen wannan bala'in ƙiyayyar Abbah da su familyn Yaya Mohandas? Aunty Minal da Yaya Mohandas suna matuƙar ƙaunar junan su hakan yasa bazata iya Auran kowa ba kuma kinsan a halin da take ciki, ita fa ba ƙaramar yarinya ba ce, tanada matsalar matsinancin sha'awa amma Abbah ya kasa ganewa, Yaya Mohandas saboda soyayyar Aunty Minal ya musulunta fa, ai abun alfahari ne wallahi, don haka baza'a buɗe ƙofar nan ba sai har Yaya Roshan ya dawo tukun..."

Baiwar ALLAH gaba ɗaya ta rasa mai zata ce a wannan al'amarin gashi bata san meya haɗa ƙiyayyar ba, amma itama tana mungun tausaya musu sosai...
Ganin bazata iya juran ƙiraye-ƙirayen sunayen da Abbah yake yi ba yasa ta fice a falon gaba ɗaya, kai tsaye can part ɗinta ta nufa zuciyarta a jagulgule...

Itama Ummy haurawa upstairs tayi can room ɗinta,
Roshan bai tashi dawowa ba sai da ya tabbatar jirginsu ya tashi tukun, wuce wa part ɗinsa yayi cike da fargaba domin bai san wani irin hukunci Abbah zai ɗaukar masa ba...

Dab da mangariba sai ga motar da ake kai Ƴar tinny school kuma a dawo da ita, a falo ta tsaya tare da jefar da jakar ta anan taci karo da wayar Abbah akan kujera, ɗauka tayi tana faɗin "Yaaa wayan Abbah..."

Da gudu ta haura upstairs ta nufi room ɗin su Abbah, buga ƙofar ta soma yi tana ƙiran sunan Abbah tare da faɗin "Abbah ganan wayay ka..."

Daga ciki Abbah ya ce "yawwa Auta duba mun akwai key a jikin ƙofar?.."

Ƴar tinny ta ce "ehh akwai..."
Abbah ya ce "kama key ɗin ki murɗa ƙofar zai buɗu..."
Ƴar tinny ita ba tsayi ba haka ta rinƙa ɗigalgal daga bisani ta ce "Nifa woyyayi Abbah cayina baje je ba..."
Abbah ya ce "kiyi iya ƙoƙarin ki Auta zaki iya kinji..."
Ƴar tinny wani dabara ne ya faɗo mata nan ta koma falo da gudu taje ta ɗauko jakar ta tazo ta ajiye a ƙasi ta taka kansa tana ƙoƙarin murɗa key ɗin, da ƙer tayi nasarar buɗe ƙofar sai ga Abbah ya fito da hanzarinsa kai tsaye falo ya nufa, ganin falon wayam ba kowa ne yasa shi haurawa upstairs su Minal, buɗe room ɗinta yayi yaga bata nan, ya komo falo kai tsaye ficewa yayi ya nufi part ɗin Roshan da motar sa saboda da ɗan rata sosai,
Abbah yana zuwa ya fara buga ƙofar falo, Baiwar ALLAH dake tana kusa ita tazo ta buɗe masa daga shi sai jallabiya har ƙasi, jikinta ne ya fara ɓari ganin yanayin Abbah duk ya canza ga eyes ɗinsa har sunyi jawur tsabar ɓacin rai.
Tambayar ta ya soma yi cewa "ina Roshan?..."

Bata ɓoye masa ba ta ce "yana ciki Abbah amma ban sani ba ko yayi bacci..."

Abbah ya ce "Baccin sa na banza da wofi ina ruwana da baccin sa, ko yana baccin kije ki tayar mun da shi yanzun nan..."

Da sauri ta nufi part ɗin Roshan wanda tunda aka kawo ta gidan nan bata taɓa zuwa part ɗinsa ba, duk da bata san ina ne room ɗinsa ba amma da haka ta lalumo ganin shima yana ƙoƙarin fitowa ne,
Jin ƙira daga Abbah ne gasa zuciyarsa bugawa da ƙarfin gaske, babu yanda ya iya domin ya rigada ya san ya yi laifi sosai,
Yana shiga falo ya tarar da Abbah tsaye ya kasa zaune,
Abbah yana ganinsa yaje gaban Roshan ya zabga masa mari, kafin Roshan ya ɗago Abbah ya ƙara zabga masa mari..
.


asmeetah writer ✍️


🤦‍♀️ *MAƘIYI_NAH*🤦‍♀️


*MY ENEMY _*

🫦 مقىينا 🫦


Mallakin
أسماء محمد أولا 🥳

Asmeetah (giaɗe writer)



https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

STEP TWO
👇
*19_ TO_20*


A kwana a tashi yau wata uku kenam da guduwar su Minal,
Abbah ba irin neman duniya da baiyi ba amma an rasa su, yayi bala'in sa har ya haƙura, tsabar baƙin cikin da Abbah yake ciki har ya yanke cewa koda Minal ta dawo bazai amsheta a matsayin ƴa ba, ya furta cewa ya haƙura da ita duniya da lahira har hawan jininsa ya tashi, domin sai da yayi wata guda a kan gadon hospital, amma yanzu Alhamdulillah ya cire Minal a ransa ƙarfi da yaji...

A kwana a tashi sai hantsi, yau da Gobe sai ALLAH Ƴar Amana jiki yayi sauƙi sosai, babu wani ciwo a tattare da ita sakamakon kulawar da ake bata, Roshan shine likitan ta kullum sai ya je ya duba ta, yanzu Ma sha ALLAH!.

Abu ɗaya ne yake damun ta yanzu kuma yake hanata wargi shine rashin sumar kanta, yanzu almost 3 weeks kenam tin lokacin da ta sanya hula a kanta bata taɓa buɗe wa ba koda wanka zata yi saboda ji take kamar ta hallaka kanta in ta ga ƙoƙon kanta ba gashi.
Razhdeen yayi iya dabarar sa akan ta cire hular ya gani ko gashi ya fara tofowa amma furr taƙi yadda...

Yau ranar Sunday Razh da Rosh ne suke zaune a babban falon cikin gidan Abbah a yayin da shima Abbah yake zaune a ɗaya daga cikin jerukan kujerun falon, iya su uku ne da duk kan alamun akwai tattaunawar da suke yi.

Abbah ne ya kalli Razhdeen sannan ya ce "Deen wai yaushe zaka koma wurin aiki ne?..."

Idonsa na kallon gefe ya fara motsi da lips ɗinsa murya ciki-ciki ya ce "Dadd sun turo mun da letter akan na koma zuwa end of this month..."

Abbah ya ce "shine baka sanar mun ba sai da na tambaye ka, yanzun zuwa lokacin zaka tafi?..."

Razhdeen ɗaga masa kai kawai yayi ba tare da ya furta komai ba..

Jinjina kai Abbah yayi sannan ya ce "Deen bana so ka bar ƙasar nan ba tare da ka tsayar da wacce zaka Aura ba, domin in har kasa ƙafa ka tafi ban san ranar dawowar ka ba, zaman ka a haka ba Aure kuma ba son haka nake ba..."

Razhdeen kallon Abbah yayi tare da cizar laɓɓensa na ƙasi kamar mai nazarin wani abu..

Roshan ne ya katsar da su da cewa "Abbah wacce yake nema bata mallaki hankalin kanta ba tukun, a ɗan bashi dama zuwa shekara biyar..."

"Whatt?..."
Abbah ne ya furta haka yana maida kallonsa kan Roshan.
Roshan ne ya kuma cewa "seriously Abbah..." ganin irin kallon da Abbah ke masa..

Abbah ya ce "wace ce yarinyar? kuma aina take? su waye iyayenta? sannan makaranta take yi ne ko kuma meye da dalilin da yasa sai nan da shekara biyar?..."

Roshan da sauri ya sunkuyar da kansa ƙasi yana faman zazzaro da eyes jin irin tambayoyin da Abbah yake jairo masa ba ƙaƙautawa, kuma shi da za'a kashe shi bai san inane asalin yarinyar ba balle ya zayyano...

Razhdeen wani irin kallo yake watsawa Roshan ganin bazai iya kame bakinsa ba,
Da sauri Razhdeen ya rubuta text ta wayarsa ya tura wa Roshan.
Shima Roshan jin saƙo ya shugo masa waya yasa yayi saurin dubawa yaga ashe twins ne,
Abinda ya rubuta shine:
"ka cika surutu twins, yaushe na sanar maka cewa ina son yarinyar? I just pity her because she need help, please twins kar kasa Dad ya bincika yanda yarinyar take banason kowa yasan ina tare da ita i beg.."

Roshan yana gama karantawa shima ya tura masa saƙo da cewa "ok don't worry my Man..."

Abbah kallon Razhdeen yayi sannan ya ce "Deen tell me wace ce yarinyar da kake nema? domin ba ƙaramin farin ciki nayi ba jin wannan albishir, burina shine na ganka da matar ka..."

Razhdeen fuska a ɗaure ya ce "i don't have any lady Dad, kawai ya sanar maka ne batare da ya sani ba shima..."
Abbah ya ce "Please Deen bana son maganar wasa fa..."

Razhdeen ya ce "seriously Dad ban taɓa cewa ina son ko wace mace ba, ban sani ba ko sai zuwa gaba, but ina neman Alfarma a barni sai na dawo daga U.S kafin a fara mun wannan maganar..."

Abbah ya kalli Roshan ya ce "kai meyasa ka koyi ƙarya ne?.."
Roshan ya ce "Sorry Abbah..."

Abbah ya juyar da ganinsa kan Razhdeen sannan ya ce "Deen meyasa bazaka yadda a Aura maka Ƙanwar matar mai martaba ne kam? banga laifin yarinyar ba naga tana da hankali da tarbiyya..."

Razhdeen zuciyarsa ce ta fara ƙuna kamar wanda aka zabure shi ya miƙe yana faɗin "Dad zan tafi gidan da nake idan akwai wani damuwa a tuntuɓe ni..."
yana kaiwa nan yayi ficewar sa daga falon, shima Roshan tashi yayi da sauri ya bi bayansa.
Shi dai Abbah zuba musu ido kawai yayi sakamakon rashin abun cewa...

Abbah yana zaune shi kaɗai a falo yana duba saƙonnin da aka turo masa ta waya, sai ga Ammy ta shugo falon da sallama a bakin ta,
Abbah ya amsa mata cikin fara'a, durƙusa gwiwowinta ƙasin carpet tayi fuska ɗauke da murmushi ta ce "Barka da hutawa Abban yara..."

Abbah ya ce "yawwa Mar'atussaliha barkan ki kema da aiki..."
Ta ce "Nagode sosai, Allah ya yi albarka..."

Cikin jin daɗi ya ce "Amiin ya ALLAH Mar'atussaliha..."
Kai a sunkuye ta ce "daman na kammala girki ne shine nazo tambayarka shin a kawo maka nan ne ko kuma zaka zauna a dinning ne?..."

Sai da ya sauƙe wata nannauyar numfashi na jin daɗi kafin nan ya ce "a'a zan biki muje dinning ɗin, kin san bana so kina wahalar mun da kan ki shiyasa naso a nemo miki ƴan aiki..."

Murmushi tayi tana faman rufe fuska da hannu ta ce "ai ba'a gajiya da neman lada, idan ka kawo mun ƴan aiki ai shikenam nayi banƙwana da fin rabin ladan da nake samu..."

Ya ce "hakane Allah ya miki albarka..."
Ta amsa da Amiin cikin jin daɗin mijinta ya sanya mata albarka..

Abbah idonsa akan ta sai yake tunowa da marigayiya matarsa uwar su Razhdeen sak kalar ɗabi'un ta irin na wannan matarsa, ga kamannun ma iri ɗaya, haka kawai yake jin wani irin farin ciki sai yanzu yayi dacen samun mata ta gari bayan uwar su Razhdeen da Roshan..

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login