Showing 54001 words to 57000 words out of 89400 words
yake tambayarsa cewa "ina dai babu wata damuwa a tattare da zamantakewar ku na Aure?..."
Da murmushi akan fuskar Roshan ya ce "babu komai Abbah muna zaune cikin ƙoshin lafiya..."
Ya ƙarasa maganar yana kallon Baiwar ALLAH wacce itama shi ɗin take kallo domin yasan tana cikin damuwa na rashin son zama da shi wanda ba hakane a ranta ba, Baiwar ALLAH ta kasance mace ce mai zurfin ciki sai dai abu yaita damunta a ranta amma bazata iya sanarwa ba, ita a ranta tana son Roshan ya kasance da ita a matsayin matarsa ta Aure, burinta shine su zauna su cigaba da soyayyarsu kamar yanda ma'aurata suke kowa a cikin farin ciki,
Roshan ganinta a cikin damuwa hakan na nuna masa cewa haƙurin zama da shi kawai take, especially idan ya tuno cewa twins ɗinsa take so, cije lips ɗinsa yayi yana kukan zuci domin yana da kishi sosai wanda bazai iya cigaba da zama da ita a haka ba, shi har yanzu baya ɗaukar kansa a matsayin mai Aure domin duk abinda ake samu a cikin Aure har yanzu bai same shi ba...
Ko wannen su da abinda yake tunani a ransa, ita Baiwar ALLAH tana tunanin neman mafita yanda zata nasar masa cewa tana masifar son sa, shi kuma yana tunanin lokaci yayi kawai ya rabu da ita...
Bayan nan Roshan ne ya tashi tare da faɗin "Abbah zan wuce wurin aiki na sai na dawo..."
Abbah ya amsa masa cikin kulawa da cewa "Allah ya kiyaye a dawo lafiya..."
Shima Abbah tashi yayi yabar musu falon suka cigaba da hirar su, ita dai Baiwar ALLAH a dole take iya yin magana...
____________________________________
Aunty Yolash ce take zaune a wantalelen falon ta dake garin Bauchi tana tare da wata ƙawarta wacce ta kawo mata ziyara,
Knocking ƙofar falo aka shiga yi murya ciki-ciki Aunty Yolash ta ce "waye?"
Daga waje ne Mai gadinta ya ce "Hajiya kin yi baƙuwa ne..."
ta ce "daga ina?..."
Mai gadi ya ce "wallahi ban sani ba Hajiya..."
ta ce "ok ka ce ta shugo..."
Mai gadi ya amsa mata tare da komawa bakin gate..
Aunty Yolash suna zazzaune suka ji an turo ƙofa da sallama a bakin matar da ta shugo, cike da mamaki Aunty Yolash ta miƙe tsaye baki ya gagara rufuwa ta ce "wa nake gani kamar Hajiya Kilishi..."
Hajiya Kilishi murmushi tayi tana faɗin "wallahi Ni ce, kinyi mamakin gani na a garin Bauchi ko?..."
Aunty Yolash ta ce "gaskiya kam saboda naga baki taɓa taka ƙafarki kinzo mun ba, nasan yanzun ma uzurinki ne ya kawo ki..."
Hajiya Kilishi ta ce "ai ko ba uzuri zan iya zuwa miki ai..."
Aunty Yolash taɓe fuska tayi ta ce "Banga alama ba saboda tin ana tare ma baki zo ba balle yanzu da ba'a tare..."
Hajiya Kilishi sunkuyar da kanta ƙasi tayi tana shirin zubda ƙwallah,
Ƙawar Aunty Yolash Hamdiyya ta ce "haba ke kuma Yolash ba'a haka bai kamata ba sam, mata ta taso daga yanda take tazo wurinki ki tsaya kina gaya mata magana ko wurin zama baki bata ba balle kayan drinks..."
Aunty Yolash ta ce "ai nasan uzurinta ne ya kawo ta Bauchin..."
Hamdiyya ta ce "to ko uzurinta ne ya kawo ta ai ta mutuntaki ne yasa ta zo har yanda kike, inda wata ce ai tafiyar ta zata yi baza ma ta kalli hanyar gidan ki ba...".
Aunty Yolash kallon Hajiya Kilishi tayi sannan ta ce "ko dai kin yi bazawari ne anan Bauchi shiyasa kika kawo masa ziyara..."
Hajiya Kilishi dai kai a sunkuye ta kasa ɗagowa balle ta haɗa ido da Aunty Yolash,
Aunty Yolash ce ta kalli Hamdiyya ta ce "wannan ɗin dai Hajiya Kilishi ce matar Yayana General wanda ya rabu da ita...."
Hamdiyya sake baki tayi tana kallon Kilishi cike da mamaki ta ce "wannan ɗin Hajiya Kilishi ce? Innalillahi naga duk ta rarrame kamar mai HIV ga fuska ta kokkoɗe tayi fiyau, ai ni bangane ta ba wallahi, duk meya faru da ita haka?..."
Aunty Yolash ta ce "Nima ina zan sani, kamata yayi yanzu muga kin ƙara murmurewa kinyi ƙiba sakamakon ba'a takure kike ba, zaki iya fita duk san da kika ga dama ki dawo gida duk lokacin da kike so babu mai takura miki, kinsan General yana takura miki baya barinki kije duk yanda kike so yanzu kuwa kura ta mutu muyi wasa, yanzu kuma naga akasin haka sosai da duk kan alamu kina cikin tashin hankali Hajiya Kilishi,
Kinga duk taƙamarki da izzarki da girman kanki yau ke ce a gaba na kina zubda ƙwallah?..."
Hamdiyya ta ce "Kinga Yolash ki ce ta zauna mana tin shugowar ta take tsaye babu daɗi, ko ba komai ai an haɗu tunda akwai yara a tsakani..."
Aunty Yolash ta ce "Ok ki shigo ki zauna..."
Hajiya Kilishi ce ta ƙarasa shigo wa ciki ta zauna a ƙasin carpet,
Aunty Yolash ta ce "a'ah tashi ki zauna akan kujera, ni bana wulakanta mutum duk wanda yazo gidana zan karɓe shi hannu bibbiyu yawwa..."
Hajiya Kilishi ta tashi ta zauna akan kujerar falo ba tare da ta ce komai ba.
Hamdiyya ce ta tashi tana faɗin "Ni zan koma gidana na bar yara su kaɗai..."
Suka yi sallama Hamdiyya ta tafi tana mamakin ganin Hajiya Kilishi a cikin wannan halin...
Aunty Yolash ce ta ƙwalla ƙiran ƴan aikin gidanta tare da sanar musu cewa su kawo wa baƙuwarta abinci da kayan drinks,
Bayan ƴan mintuna sai ga su da kayan abinci da su fruit da drinks sun ajiye akan table ɗin tsakiyar falo tare da jan yo shi gaban Hajiya Kilishi, sai da Hajiya Kilishi ta gama cin abinci da sauran kayayyaki tukun ta fuskanci Aunty Yolash,
Itama Aunty Yolash kallonta take tana son jin mai ke tafe da ita...
Bayan Hajiya Kilishi ta ci tayi nak sai kawai ta fashe da kuka,
Aunty Yolash ta ce "ha'a lafiya kuwa?..."
Durƙusawa Hajiya Kilishi tayi da gwiwowinta tare da haɗe hannayenta biyu tana roƙon Aunty Yolash da cewa "Dan girman Allah Auntyn yara inaso ki mun wani taimako ba dan hali na ba, kamar yanda Allah ya rufa miki asiri dan ALLAH nima ki taimake ni ki rufa mun nawa asirin..."
Aunty Yolash ta ce "kema Allah ya rufa miki asiri sai dai kece kika tona wa kanki asirin, abun ya ban mamaki shin wani irin taimako ne kike so nayi miki har da durƙusawarki wanda tunda kike baki taɓa yin gigin yin haka ba..."
Hajiya Kilishi tana kuka ta ce "dan Allah kiyi haƙuri akan abubuwan da na aikata miki, nasan ban kyauta miki ba amma ki gafarce ni..."
Aunty Yolash murmushi tayi tare da faɗin "nasan ba wai neman gafarata kika zo yi ba, akwai abinda ke tafe dake, Ni indai nine za'a zauna lafiya ƙalau ba tare da ɓacin rai ba don haka komai ya wuce a wuri na, shin wani taimako kike so nayi miki indai baifi ƙarfi na ba zan taimaka miki,
Sannan ki tashi ki zauna akan kujerar bana son durƙusawarkin Nan..."
Hajiya Kilishi tana sharar hawaye ta tashi ta zauna tare da faɗin "bazai ma fi ƙarfin ki ba, nasan kina ɗaya daga cikin waɗanda zasu faɗi magana General ya ɗauka ko shawari haka, kina ransa sosai, yana matuƙar ji dake...."
Aunty Yolash ta katse ta da cewa "duk nasan wannan wa'azin just go ahead..."
Hajiya Kilishi ta cigaba da cewa "Auntyn yara inason komawa gidan mijina, wallahi ina son kasancewa tareda mijina da kuma ƴaƴana, ina shan wahala sosai a gidan da nake, ga bani da kuɗi yanzu abincin da za'a bani ma ƙyashinsa ake wani sa'in ba'a bani, gidan mijina ya fi mun kwanciyar hankali, wallahi nayi nadamar abubuwan da na aikata a baya, nayi kuskure wanda yanzu nake son gyarawa..."
Ajiyar zuciya Aunty Yolash ta sauƙar tare da faɗin "hakane bawa yakan aikata kuskure daga baya yayi nadamar abinda ya aikata, amma ina so ki sani cewa duk wanda ya tuba don wuya ba lada haka tushen hausar take amma tinda har kika gane gaskiyar lamarin duk ba laifi, amma a gaskiya komawa gidan General zai miki wuya domin a halin yanzu Yayana ba macen da yake jin daɗin tarayya da ita sai Amaryarsa, zai yi wuya ya zauna da wata mace bayan ita, kuma shi daman baya son zama da mata biyu kasancewa shi ba mazauni bane, shin a cikin maganar ki taimakon mai kike so nayi miki?...."
Hajiya Kilishi tana kuka ta ce "inaso ki sa baki General ya mai dani gidansa..."
Aunty Yolash ta ce "kai kai kaiiii ai duk yanda nake da General bazai taɓa yadda da wannan batun ba hasali ma ki ja mun baƙin jini a wurin sa, ga nan abokansa kije ki same su mana..."
Hajiya Kilishi ta ce "kab abokansa waɗanda na sani babu wurin wanda banje ba amma ya ƙi sauraronsu akan batun, bansan wani irin zuciya ne da shi ba..."
Sauƙe numfashi Aunty Yolash tayi tare da faɗin "ke ma bakya jin magana Hajiya Kilishi, ke kika jawa kanki komai wallahi duk abinda ya faru laifinki ne, inda ace kin kama kanki da mutuncinki a gidan mijinki da duk hakan bata faru ba, me zaisa kiyi abinda har Aurenki zai mutu? kin dai san General yana da matuƙar haƙuri amma idan aka kai shi maƙura baya taɓa sauƙowa akan abu, kuma idan ya cire abu a ransa baya taɓa maida shi, kin ƙure shi sosai, kinsan babu wanda zai iya riƙe ki mai zai sa ki bar gidan mijinki? kowa yana rufawa kansa asiri amma ke kina ƙara bankaɗawa kanki asiri, Ni a koda yaushe ina baki shawara bawai bana sonki bane amma kika ɗauki ƙiyayya kika ɗora mun, gani kike babu maƙiyiyar ki kamar ni, Ni kuma ina zaune da mutum da zuciya ɗaya ne, kuma wallahi wannan ranar nake guje miki kuma gashi yazo shin meye amfanin haka?..."
Hajiya Kilishi babu abinda take sai kuka ta ce "bayan fitowa ta daga gidan mijina ba ƙaramin wahala nake sha ba, kowa ya kasa riƙe ni, da farko a gidan ƙanwar mahaifiyata nake zaune amma itama daga baya ta kore ni wai bazata iya riƙe ni ba, sai na koma gurin baffana shima matansa sun hanani zama a gidan, duk zuriya babu yanda ban zagaya ba amma an rasa wanda zai riƙe ni daga ƙarshe dai zaman Abuja ya gagare ni saboda babu yanda zan shiga ga tsadar rayuwa ga bani da kuɗi, abincin da zan saya na ci gagara ta yake, yanzu haka ina zaune a garin suleja na kama gidan haya, to kuɗin da zan biya babu kuma watannin biyan kuɗin ya ƙare, bansan da wanne zan ji ba, shin da kuɗin abinci yau da kullum ko kuma kuɗin hayan gidan da nake?..."
Hajiya Kilishi ta ƙarasa tana fashewa da kuka.
Aunty Yolash sarkin tausayi ba ƙaramin tausaya mata tayi ba, ta ce "ke nam babu yanda zaki je ki zauna? abincin da zaki ci gagaranki yake shin ina Alhajan ƙawayenki matan manya-manyan masu kuɗi? shin kina nufin ki ce bakida bazawarai? to ma ina wanda kike bin sa hotel bazai iya taimaka miki bane?..."
Hajiya Kilishi dakatar da yin kukan tayi tana faɗin "yanzu na gane su waye masoyana da kuma maƙiyana, ƙawaye na suna hulɗa dani ne saboda kuɗina da kuɗin mijina, basa kula talakawa idan suka fiskanci bakada komai ka tsiyace daga nan zasu raba hanya da kai duk haka suke, suna ƙawance da wacce take da kuɗi, kuɗi sai kuɗi to ni kuma yanzu banida komai, aikin da nake yi ake biyana maƙudan kuɗaɗe kamfanin General ne kuma ya sallame ni, ko ba kuɗin salary General baya barina ba kuɗi,
Bazawarai kuma su waye zasu zo mun? idan kinga mutum yazo mun to bada niyar Aure yazo ba sai da niyar iskanci, Ni kuma na shiryu bazan iya bada kaina ba saboda kuɗi duk da wahalar da nake sha, duk kowa ya gujeni, wasu sunyi blocking number na wasu kuma idan na ƙira su basa picking, wai daman haka rayuwar take?...."
Ta ƙarisa maganar tana kallon Aunty Yolash,
Aunty Yolash ta ce "yanda kika yi dai haka akayi miki, Allah ya ɗanɗana miki kiji yanda sauran mutanen suke ji da zaran sun zo neman taimakon ki, shin ba haka kike yi ba? idan kina tare da mutum da zaran ya rasa wani abu shikenam zaki nemi hanyar barinsa a cikin ƙunci maimakon ki taimaka masa, hatta ƴan uwanki bakya taimaka musu shiyasa suma yanzu bazasu iya taimaka miki ba, kar ma kiga laifinsu domin ke kika fara ɗanɗana musu raɗaɗin haka, duk wani ɗan uwanki da zaran yazo yanda kike zaki nemi kici masa mutunci sannan ki kore shi, wallahi ban taɓa ganin mata marar wayo ba sai ke, ai inda Ni ce a mazanninki babu wani ɗan uwana da zaiyi kukan talauci, jansu zanyi a jikina suma su ci arziƙi saboda nasan wata rana wani abu zai iya faruwa dani wanda dole sai ƴan uwana ne zasu mun, amma ke daga ke sai ƴaƴanki bakya son wani ya raɓi jikinki, ga shi yanzu kin ci ke kaɗai sannan kina shan wahala ke kaɗai yanzu meye amfanin haka?..."
Hajiya Kilishi ido yayi jawur fuska a kokkoɗe ta ce "nayi nadama bazan ƙara aikata makamancin abinda na aikata a baya ba..."
Aunty Yolash ta ce "tam yanzu dai kin san masu sonki da kuma waɗanda basa sonki..."
Hajiya Kilishi tayi saurin katse ta da cewa "indai ata ɓangaren ƙawaye da kuma abokai babu masu Sona tsakani da ALLAH, ƴan uwana kuma daman haushi na suke ji shiyasa suka kasa taimaka mun..."
Aunty Yolash ta ce "tam yanzu dai idan Allah yasa kika koma gidan General babu ruwanki da wani ɗagun kai da girman kai da wulaƙanci da kuma masifa ki kama kanki, kinga wacce take zaune yanzu babu ruwanta batada tashin hankali, idan wani abu ya ɓullo za'a ce ke ce..."
Hajiya Kilishi ta ce "ai babu abinda zai faru Insha Allahu, zan riƙe abokiyar zamana hannu bibbiyu..."
Aunty Yolash murmushi tayi sannan ta ce "Ni na manta ashe dai kince bakya son zama da kishiya..."
Hajiya Kilishi ta ce "wallahi ruɗin duniya ne amma ni yanzu General ko mata uku ya jera to zanje na zauna ata huɗun..."
Aunty Yolash ta ce "to shikenam gobe Insha Allahu zan shiga jirgi naje Abuja na same shi da maganar duk yanda ake ciki zanje har yanda kike a sulejan na sanar miki..."