Showing 57001 words to 60000 words out of 89400 words

Chapter 20 - MY ENEMY BOOK 2 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

2532

Hajiya Kilishi bata san lokacin da ta washe baki ba na farin ciki ta ce "Nagode sosai Auntyn yara Allah ya saka da ALKHAIRI..."

Aunty Yolash ta ce "kar ki damu, a rayuwata na tsani ganin uwa ta fita tabar ƴaƴanta a gida ina jin takaicin haka, amma sai dai ƙaddara ta riga fata, za'a san yanda za'ayi Insha ALLAHU...."

Hajiya Kilishi cikin nuna farin ciki ta miƙe tare da faɗin "shikenam Auntyn yara Ni zan koma suleja..."

Aunty Yolash ta ce "ok muje na sauƙe ki a airport to..."

Hajiya Kilishi ta ce "a'ahh bani da kuɗin hawa jirgi, zanje na shiga mota..."

Aunty Yolash gani ɗaya tayi wa Hajiya Kilishi tasan bata da kuɗin motar ma kawai tayi iya kuɗin zuwa ne,
Ta ce "shin kina da na motar ne?..."

Hajiya Kilishi sunkuyar da kanta tayi ƙasi tare da girgiza kai,
Aunty Yolash ta ce "Ok kar ki damu, idan kika ce mota zaki shiga zaki yi dare ne, muje kawai na biya miki na jirgin..."

Aunty Yolash ta haura saman upstairs yanda room ɗinta yake taje ta ɗauko wasu maƙudan kuɗaɗe a cikin baƙar laida ta sauƙo tare da miƙawa Hajiya Kilishi tana faɗin "ga wannan kije ki biya duk kan buƙatunki da su, ki biya kuɗin haya sannan ki sayi kayayyakin abinci da dai sauran abubuwan da kike buƙata..."

Cikin nuna farin ciki Hajiya Kilishi ta karɓa tana godiya haɗi da cewa "wannan ai zan daɗe ina amfana da su.."

Aunty Yolash ta ce "to muje na biya miki kuɗin jirgi ..."

A tare suka fita Aunty Yolash ta ja su a mota sai airport....


___________________________________


A bangaren Ƴar Amana kuwa har zuwa wannan lokutan fushi take da Razhdeen saboda ya tafi ya barta, ma sha ALLAH sai haɓaka take tayi, a shekara ɗaya ta zankaɗe tayi tsayi ga dirin jiki kamar wacce ake hura mata iska, fatar jikinta kuwa kamar zaka taɓa jini ya fito tsabar farin da tayi ba ƙaramin kyau tayi ba, ga gashin kanta a baje kamar wanda ake ƙara jansa sai tsayi yake yana tafe da murɗi-murɗinsa, ta ko ina a jikinta ya ciko hatta breast ɗinta sun fito sun cicciko, ƙugunta kuwa ba'a magana daman kuma can Ƴar Amana ba siririya bace da ɗan dirinta balle yanzu ta haɗa da cikar budurci, hips ɗinta irin mai shape ɗin kifi ne.

Tana zaune a falo tana kallo kwatsam taji Madam Blessing ta zauna kusa da ita tana shirin miƙa mata wayar hannunta, da sauri Ƴar Amana ta ture wayar tare da miƙe wa tabar falon ta koma room ɗinta domin tasan Razhdeen ne yake son yin video call da ita, tinda Razhdeen ya tafi tsawon shekara guda Ƴar Amana bata taɓa yadda sunyi video call ba shi kuwa kullum sai ya ƙira madam blessing akan ta haɗa shi video da Saararsa amma fur Ƴar Amana taƙi yadda hatta photo bata taɓa yadda tayi ba tinda Razhdeen ya tafi saboda tasan indai ta ɗauka sai madam blessing ta tura masa, kullum sai yayi complain akan a turo masa photon Saarah amma Ƴar Amana taƙi, har takai ta kawo yanzu indai taga waya a hannun madam blessing bata yadda ta zauna a kusa da ita saboda kar ta ɗauke ta a photo, a tunanin ta indai yaji zafin haka zai dawo.

Madam Blessing bayan Ƴar Amana tabar falon girgiza kai tayi ta cigaba da magana da Razhdeen tana faɗin "Yallaɓai indai kana son ganin Saarah gwara ka ware lokaci ɗaya kazo ka koma, nake gaya maka in kaga yanda yarinyar nan ta girma saika kama baki, ba ƙaramin girma tayi ba amma sai dai har yanzu bata fara period ba, amma tana dab da farawa saboda ta cika sosai, amma Yallaɓai a tunaninka zata yi shakara nawa?..."

Daga ɓangaren Razhdeen wanda yasa computer a gaba domin da shi yake video call ya ce "ina tunanin bazata wuce 17 years or 18 ba,
Madam!
Sarah yarinya ce ƙarama just girman jiki ne kawai..."

Madam Blessing ta ce "okay zan fara sa mata ido saboda tana dab da farawa ai lokacin ta yayi..."

Shima Razhdeen cewa ya yi "ki kula mun da ita sosai, ki fara gwada mata yanda zata yi kafin ta ankara da shi domin zata iya tsorita duk lokacin da abun yazo..."

Madam ta ce "okay kar ka damu tinda tana jin abinda ake ce mata mayar wa ne bazata iya ba ai da sauƙi..."

Razhdeen ya ce "about her school ina tana gane karatu?..."

Madam Blessing ta ce "sosai ma, wallahi nake gaya maka inda ace yarinyar nan tana magana ba ƙaramar yarinya mai ilimi da fahimta za'ayi ba, yanzu ma tin daga kan note ɗinta zaka gane tanada ilimi..."

Razhdeen murmushi yayi ba ƙaramin jin daɗin hakan yayi ba, ya ce "good..."
Madam Blessing ta kuma cewa "Yallaɓai zan maka rainonta yanda ya kamata, gashi kun dace sosai, miskilancin ku ɗaya da kuma zafin rai..."

Razhdeen ya ce "me kike nufi?..."

Ta ce "tana gama school kawai ka Aure ta tin kafin a rigaka..."

Tsuka ya ja tare da faɗin "You're very stupid Madam Blessing, this younger girl kike mun maganar Auren ta? look ina kiwatata ne saboda na ɗauke ta a matsayin ƴata..."

Madam Blessing zaro ido waje tayi tare da faɗin "ƴarka dai? No don't said that, me laifin kace ƙanwarka amma ƴa ai babu Aure a tsakani kenam..."

Razhdeen ya ce "look wai waye ya ce Auranta zan yi ne? Nigeria people kuna da matsala sosai,
Ni akwai wacce nake son Aura anan ƙasar U.S kuma Soja ce..."

Madam Blessing ta ce "Yallaɓai Are You serious?..."

Kafin ta ƙara cewa wani abu Razhdeen yayi saurin katse wayar,
Madam Blessing girgiza kai tayi tana murmushi domin tasan Razhdeen ba wata budurwar da yake da shi kawai ya faɗa ne...


Washe gari da safe Ƴar Amana ta sauƙo falo cikin shirin kayan uniform da jakarta a goye a baya, tayi gyaran gashin ta tayi rolling donut da gashin, ga ta gaban gashin ta gyara da Gel daman su school ɗinsu ba'a saka hijab ko hula ko kuma gyale haka nan ake barin gashi a waje, shiyasa ko wacce take ƙoƙarin gyara gashin ta, da masu tsara kitso da kuma masu saloon su gyara gashin, ita ƴar Amana bata kitso sai dai Madam Blessing ta kaita wurin saloon a gyara gashin,
Style ɗin uniform ɗinsu kuma doguwar riga ne zuwa gwiwa baya sauƙa ƙasi sai sapa da thorns mai tudu, makarantar akwai gasar fashion dake private school ne na ƴaƴan masu kuɗi,
Ƴar Amana bayan ta gama shirinta zuwa tayi ta zauna akan dinning table daman an haɗa mata abinci kala-kala masu kyau da gyaran jiki shiyasa take ta haɓaka kamar yeast, madam Blessing ba ƙaramin gyara Ƴar Amana take ba kamar ƴar cikinta haka take ji da ita, bayan ta kammala breakfast goya jakarta tayi mai bala'in tsada sannan ta ɗauki lunch bag ɗinta wanda a ciki haɗin abinci ne masu rai da lafiya da kayan fruits,

Madam Blessing rakata tayi har harabar gidan yanda security yake jiran fitowar ta,
Ƴar Amana babu a wanda tayi wa alamar magana kai tsaye mota ta shige ta zauna a back seat ta ci boom kamar wacce ba'a halicce ta da fara'a ba, haka security ya ja mota suka fi ce...

Madam Blessing ɗaga mata hannu take tana mata fatan alkhairi amma Ƴar Amana ko kallon yanda take bata yi ba, Razhdeen yasa tana fushi da kowa daman can ba'a taɓa ta ba yata ƙare balle an tsokano ta....


Abbah kuwa har an sanar masa cewa akwai mutane a gidan da Razhdeen yake kafin ya ankara kuwa Roshan ya sanar masa cewa akwai wacce ta karɓi aron gidan ne zuwa nan da shekara biyu kafin Razhdeen ya dawo..

Abbah ne ya amsa da cewa "okay na fahimta..."

A ranar yau ne Aunty Yolash tazo Abuja zata cika wa Hajiya Kilishi alƙawarin da ta ɗaukar mata na cewa zata same shi...

A falon Meeting ɗin Abbah Aunty Yolash ta same shi zaune yana daddanna computer sa, zama tayi tare da gaishe shi, ya ɗago yana murmushi ya ce "Auntyn yara yau kece a garin Abuja?..."

Tana dariya ta ce "wallahi kuwa Yaya na shiga ciki ai Ammy take sanar mun cewa kana nan falon ka..."

Abbah ya ce "tamm akwai problem kenam tinda har kika kasa jirana a can public falo..."

Aunty Yolash ta ce "ai daman Yaya maganar da zamuyi yana buƙatar sirri ne..."

Abbah ya ce "meya faru ne Auntyn yara?..."

Aunty Yolash har fargaban fara tuntuɓar Abbah take da maganar domin tasan ba ƙaunar jin zance Hajiya Kilishi yake ba,
zuciyarta ne ya fara bugun uku-uku tana haɗiyar yawu ta ce "Daman! Daman!! akan magana mai muhimmanci ne..."

Abbah ya ce "yadai? Ina jinki..."
Aunty Yolash ta fara da cewa "Yayana Allah S.W.A ma muna masa laifi kuma ya yafe mana, mu kasance masu haƙuri a rayuwa, muyi koyi da manzon Allah S.A.W...."

Abbah shafa farin gemunsa ya fara yi yana faɗin "too gama mun wa'azi tukun sai ki gayi abinda ya kawo ki ko..."

Aunty Yolash ta ce "Yaya shin idan mutum yayi maka laifi kuma yazo neman gafarar ka shin zaka haƙura ko kuma ?..."

Abbah kwata-kwata bai kawo maganar Hajiya Kilishi a ransa ba, shi har ya manta da wata Kilishi kuma bayan haka Aunty Yolash bata taɓa masa maganar ta ba balle ya kawo haka a ransa,
Ya ce "indai yayi laifi kuma daga baya ya gano kuskurensa ya nemi a ayafe masa da gaske har cikin ransa mai zai hana a yafe masa, ai akwai laifukan da muke yi wa Ubangijin mu a sanin mu ko ba'a sanin mu ba mu roƙe shi kuma ya yafe mana balle mu marasa tunani, indai akwai zuciyar musulunci zan yafe masa mana..."

Aunty Yolash ta ce "Alhamdulillah haka nake son ji, nasan Yayana akwai tawakkali da yafiya da juriya..."

Abbah ya ce "Ni fa na tsani jan rai idan zaki faɗi magana kin rinƙa jan zance kenam..."

Aunty Yolash ta ce "sorry Yayana daman inaso ka yafewa Hajiya Kilishi abinda ta aikata maka, ta wakilce Ni akan nazo na baka haƙuri tayi nadama, kuma wallahi Yaya da gaske take kaga yanda ta zama kuwa kalar tausayi, wai tasan idan tazo yanda kake korar ta zakayi shiyasa ta turo Ni..."

Abbah yayi mamakin jin wannan magana daga bakin Aunty Yolash domin yasan ba shiri suke yi ba,
Ya ce "aina kika haɗu da ita?..."

Aunty Yolash ta ce "jiya har Bauchi taje ta same ni da maganar..."

Jinjina kai Abbah yayi tare da faɗin "zan yi maganin wannan matar indai bata daina bin Abokaina da ƴan uwana ba, na ce bazan dawo da ita gidana ba amma sam ƙwaƙwalwarta na kifaye ne, Ni ban iya zama da mata biyu ba, kuma bazan fara ba tunda da yarinta ta banyi ba balle yanzu da tsufa ta soma kamani..."

Aunty Yolash ta ce "Yaya ka yafe mata Please..."

Abbah ya ce "Ni indai nine taje na yafe mata duniya da lahira tin ba yau ba, wallahi na yafe mata, alaƙa ce dai na yanke..."

Aunty Yolash kamar zatayi kuka ta ce "Yaya ka dawo da ita kan Ƴaƴanta..."

Abbah ya ɗaga mata hannu yana faɗin "Kinga Yolash in ba so kike na ci mutuncin ki yanzu ba kibar mun wannan maganar..."

Aunty Yolash ta ce "haba Yaya matar nan baka san irin wahalar da take sha ba, ga babu yaranta a kusa da ita balle taji sanyi a ranta, ka rabata da komai hatta aikinta da take yi tana samun Salaryn ta ka kore ta shin ya kake so tayi ne, tana ta bin duk ƴan uwanka tana neman gafararsu akan abubuwan da tayi musu sannan tana neman alfarmar a baka haƙuri ta dawo, ita ko ya ya ne zata zauna a haka, yanzu wallahi asirinta a bankaɗe yake..."

Kafin takai ƙarshen maganar ta Abbah ya darara mata tsawa da cewa "you're very stupid Khadijah..."

Zaro ido Aunty Yolash tayi tana kallon Abbah wanda ya ambaci asalin sunanta wanda tinda yake bai taɓa ƙiran sunan ba sai yau, cike da mamaki take bin sa da kallo zuciyarta na bugun uku-uku domin ransa ba ƙaramin ɓaci yayi ba...

Abbah ya cigaba da cewa "Na rantse da sarkin dake busa mun numfashi idan ban yanke alaƙata da ke ba ki canza mun suna wallahi tallahi...".

Ba Aunty Yolash ba hatta Ammy wacce shugowarta kenan tana ɗauke da try ɗin lemuka ta kawo musu jin kalmar da Abbah ya furta ne yasa ta sakin try ɗin drinks a ƙasin carpet tsabar firgici..

Abbah ya cigaba da cewa "ki je ki tambayi wasu abokai na duk na fita shirginsu sakamakon yawaita mun maganar Kilishi, nace bana sonta bazan dawo da ita ba ana dole ne?..."

Aunty Yolash miƙe wa tsaye tayi tana faɗin "Allah ya baka haƙuri Ni na tafi..."

Abbah ya ce "ki tafi mana, kar na sake ganin ƙafarki a gidan nan iskancin banza kawai..."

Ammy ranta ya sosu sosai jin abinda Abbah ya ke faɗi kuma duk saboda an kawo masa maganar Hajiya Kilishi,
Ammy ta ce "wai Abban yara shin ba'a yafiya ne? ka dawo da mata kan ƴaƴanta mana ya zaka raba uwa da ƴaƴanta..."

Abbah ya kalle ta a fusace ya ce "kema ko? ke ma ko? ke ma ko to wallahi ke ma kika mun maganar ta zaki koma gidan ku ne..."

Ammy dafe ƙirji tayi ido a zazzare ta ce "subhanallahi, A'uzubillahi Minal shaiɗani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login