Showing 27001 words to 30000 words out of 89400 words

Chapter 10 - MY ENEMY BOOK 2 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

2512

"Dota! Dota!! ke Dota ki buɗe eyes ɗinki kin san abinda kike faɗi kuwa?..."

Muryar Abbah suka jiyo tare da wasu mutanen sun nufo ɗakin da aka ƙwantar da Baiwar ALLAH,
Razhdeen fargaba da tsoro ne suka bayyana akan fuskar sa jin abubuwan da Baiwar ALLAH ke faɗi kuma ga su Abba suna shirin shugo wa, domin sun ji labarin Amarya tana kwance a gadon hospital ba lafiya,
Da sauri Razhdeen ya yi saurin fice wa kafin a tarar da shi ga kuma bakin ta ya gagara rufuwa..."

Da ƙer Aunty Yolash ta samu ta farkar da ita, dai dai lokacin da su Abbah suka shugo da Roshan da wasu...

Razhdeen ta wata hanya ya bi domin baya so a san shima yazo hospital kuma ita Aunty Yolash tayi alkawarin baza ta sanar cewa jinin Razhdeen ba ne, shima Doctor ya yi wannan alƙawarin,
Doctor a iya Baiwar ALLAH ya sanar lokacin da zai ɗaura mata jini na biyu domin a lokacin ta farfaɗo daga bisani ta wuce da yin bacci sakamakon Allurar baccin da akayi mata.....





*DAN ALLAH FAN'S KUYI HAƘURI 🙏 INA CIKIN BUSY NE SHIYASA BAN SAMU LOKACIN YI MUKU UPDATE BA...*
*SANNAN INA MAI SANAR MUKU CEWA AN KUSAN KAWO ƘARSHEN FREE BOOK A CIKIN STEP TWO ƊIN NAN*
*MY ENEMY BOOK YANZU NE WASAN FARKO DOMIN DUK WANI CHAKWAKIYAR YANA CIKIN PAID BAZAN GUDANAR A CIKIN FREE BOOK BA...*

*MY ENEMY PAID 300₦*
*MY ENEMY PAID 300₦*
*MY ENEMY PAID 300₦*

*BA ƘARI☝️BA KUMA RAGI✌️*
*BAN TSAWWALA BA DUK WACCE ZATA BIYA ƘOFA A BUƊE TAKE ITA ZATA NISHAƊARTU SANNAN TA FAƊAKARTU TA KUMA ILMANTU DA SANIN HALIN RAYUWA DA KUMA SOYAYYA...*

*FREE BOOK YA KUSAN ƘARE WA🙏*
*WACCE TAKE JIN DAƊIN LITTAFIN TO BIYAN KUƊIN LITTAFIN BAZAI MATA WUYA BA, 300₦*

*ALLAH YA BADA IKON BIYA🙏🙏🙏*


asmeetah writer ✍️


🤦‍♀️ *MAƘIYI_NAH*🤦‍♀️


*MY ENEMY _*

🫦 مقىينا 🫦


Mallakin
أسماء محمد أولا 🥳

Asmeetah (giaɗe writer)



https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

STEP TWO
👇
*13_ TO_14*


Roshan a firgice ya yo kan Baiwar ALLAH dake kwance, zama yayi gefen gadon tare da sa hannu yana shafar sumar kan ta, cikin sassanyar murya yake faɗin "Ammata meya faru da ke? har da laidar jini?..."

Kallonsa tayi tare da tsiyayar da ruwan hawaye, ta kai idon ta kan Abbah wanda yake ta ambatar sunanta yana gaishe ta da jiki, ga Aunty Yolash itama a zaune gefe guda tana cike da mamakin kalaman Baiwar ALLAH akan Razhdeen..

A ranar aka sallame su kuma a ranar da daddare aka kai Baiwar ALLAH ɗakin mijinta, anyi niyar yin party amma sakamakon rashin lafiyar ta yasa aka dakatar.

Gidan Roshan a cikin gidan Abbah yake, shima ɓangarensa daban,
Roshan yaso ya koma gefe can da Amaryarsa amma Abbah sam yaƙi sakamakon baya son ya rinƙa barinta ita kaɗai saboda zai fara zuwa wurin aiki tin daga safe har yamma,
kafin kaje part ɗin Roshan sai ka wuce na Abbah kafin ka iske ƙaton gate mai launin golden, part ɗin sa ba ƙaramin tsaruwa ya yi ba, sai dai ma sha ALLAH...

Misalin ƙarfe 10 na dare kowa ya watse daga part ɗin Amarya sai iya ita kaɗai ce ta rage a tsakiyar fantamemen gadonta na alhurma, tana rufe da mayafi akan ta sai sharar kuka take gaba ɗaya eyes ɗinta ya yi jawur,
Tana cikin wannan halin sai taji an turo ƙofar ɗakin tare da yin sallama, wasu irin ƙamshin turaruka ne yake dukan hancin ta kala-kala alamun ba mutum ɗaya bane,
Abokanan Ango ne suka rako Ango ɗakin Amaryarsa a ciki har da Razhdeen, wani daga ciki ne ya fara ƙirarin "Amarya bakya laifi ko kin daki hancin twins ɗin Ango..."

Suka kalli Razhdeen dake tsaye a wurin bakin ƙofa su kuwa duk suka kwashe da dariya, Roshan zama yayi a bakin gado yana bin Baiwar ALLAH da kallo dake lulluɓe da mayafi,
Sai da Angwaye suka gama musu nasiha da shawarwari tare da musu fatan alkhairi, kallon Razhdeen suka yi tare da faɗin "Major kai ba abinda zaka ce ne?.."

Baiwar ALLAH jin an ambaci sunan Major yasa ta ɗan ɗago da kanta ta cikin mayafi take binsu da kallo har eyes ɗinta suka sauƙa akan Razhdeen wanda yake takowa a hankali ya nufo wurin Roshan tare da ajiye masa wani ƙaton laida wanda yake ɗauke da naman chicken da su eggs har da su kayan fruit da laimuka kala-kala, ya ɗauki hannu ya ɗora akan kafaɗar Roshan yana jijjiga shi,
Shima Roshan ɗago wa yayi yana sau masa ƙayataccen murmushi, shima Razhdeen sake masa nasa murmushin ya yi a haka suka yi sallama,
Duk fice wa suka yi aka bar Ango da Amaryarsa, ita kuwa Baiwar ALLAH wani sabon kuka ne ya sake kuɓuto mata,
Roshan ne ya kulle ɗaki tare da yo wa kan Amarya yana faɗin "Ammata na an zamo Amarya yanzu kuma sauran ki zamo maman Baby.."
Ya ƙarasa maganar tare da ɗage mata mayafin kan fuskar ta, abinda ya tarar ne ya ji sam bai ji daɗi ba ganin yanda take ta sharar kuka,
Murya ciki-ciki ya soma faɗin "Ammata what's wrong with you? please kiyi haƙuri ki sanar mun matsalar ki, kinsan yanzu a hannu na kike duk wani matsalarki da issues ɗinki duk suna rataye a wuya na ne,
ki taimaka ki sanar mun..."

Girgiza kai tayi tare da faɗin "babu komai..."

Ya ce "Okay kina kukan Amarci ne? ki kwantar da hankalin ki ai kina tare da ƴan uwanki tinda duk a gida ɗaya kuke, kuma Uwar masu gida zata na zuwa taya ki hira kinji koh?..."
Shuru tayi ba tare da ta bashi amsa ba domin ita abinda yake ranta daban yake, kuma kukan da take shima akwai dalilai daban,
na farko anyi Auren ta ba tare da iyayenta ba sannan kuma wanda take so ba shi ta Aura ba..."

Roshan riƙo hannun ta yayi yana shirin ɗago ta tare da faɗin "tashi muje muyi alwala muyi sallah ko ƴar lelen mijin ta..."
Zamar da hannun ta tayi fuska a ɗaure ta ce "kaje ka fara yi mana..."
Ya ce "Okay bari toh naje nayi tinda Allah ya haɗa ni da mata mai alkunya..."
Baiwar Allah ko ɗagowa tayi ta kalle shi ma bata yi ba.
Shi kuwa tashi yayi ya shiga bathroom bayan wasu mintuna sai ga shi ya fito, itama tashi tayi ta shiga ta ɗauro alwala sannan ta fito suka tsayar da sallah a tare, bayan sun idar suka ci suka sha cikin ƙoshin lafiya ba tare da ɓacin rai ba,
Bayan kammalawa cikin kulawa da dabara Roshan yakai hannunsa kan hannunta yana wasa da hannun natan tare da jan ta da hirar soyayya, a hankali yake matsawa dab da ita cikin wayancewa yake faɗin "Ammata nah ke fa ba matar Alaramma bace ki cire wannan hijab ɗin mana..."
ya ƙarasa maganar tare da sa hannu ya zamar da hijab ɗin,
A zabure Baiwar ALLAH ta miƙe tsaye fuska a ɗaure tana kallon gefe,
Shima tashi yayi tsaye tare da kamo hannun ta yana faɗin "lafiya kuwa Ammata? ya naga kamar bakya cikin farin ciki..."

Ganin yana shirin takura mata yasa ta cewa "Please Yaya Roshan ka ƙyale ni nikam..."

Cikin sassanyar murya ya ce "why?.."

Cikin ɗaga murya ta ce "Ni dai kawai ka barni.."

Ya ce "Okay muje to ki cire kayanki sai ki sanya sleeping dress ko.."

Ba tare da ta yadda sun haɗa ido ba ta ce "nan ɗin ɗakin waye?..."

Ya ce "Ɗakin ki ne mana, Ni baƙunta nazo miki..."

Juyar da eyes ɗinta tayi tare da faɗin "Okay zaka iya fitar mu a ɗaki yanzu..."

Roshan cike da mamaki ya ce "what kinsan me kike cewa kuwa ?..."

Ta ce "Yes i known what am tooking about, please can you pack your self and get out inside my room?..."

Dogon numfashi ya ja tare da faɗin "Ammata daman nasan bakya so na, amma meyasa kika gagara sanar mun dan ALLAH?..."

Tsuka ta ɗan ja tare da ɗaukar pillow tana faɗin "zan je parlor na kwanta nake ga zai fi mun wannan dogon jawabin nakan..."

Har ta juya zata fice yayi saurin riƙo hannun ta tare da girgiza mata kai ya ce "dan ALLAH Ammata kar ki mun haka, zaki cutar da ni ne domin ba ƙaramin tsumi aka mun ba, ki taimaki rayuwata da kuma halin da zan shiga a cikin daren nan..."

Numfashi ta sake tare da faɗin "wannan damuwar ka ce, ka sake mun hannu nikam..."

Roshan kamar zai yi kuka haka yake riƙe da hannunta ya kasa sake wa,
Sai da tayi magana sau uku akan ya sakar mata hannu amma fur ya ƙi,
Cikin zafin nama ta fizgar da hannunta tare da ɗaukar wani ɗan ƙaramin wuƙa na yankan fruit ta ɗora a saitin maƙogaron ta ido a lumshe take faɗin "Yaya Roshan wallahi tallahi idan ka cigaba da tsayuwa mun a ɗaki saina ja wuƙar nan ta yanke mun wuya in yaso kowa ma ya huta da ni...."

Lokaci guda Roshan ya birkice eyes ɗin nan suka yi jawur yana kar kaɗa mata hannu murya ta ƙi fito wa a haka yabar ɗakin a gaggauce,
Jin shuru yasa ta buɗe eyes ɗinta taga baya nan tukun ta ajiye wuƙar ta taho da sauri ta danna key a ƙofar ɗakin,
Wani ruɗaɗɗen kuka ne ya zo mata ba shiri, haka ta doku saman gadon tana rera kukan ta...

Roshan shima ɗakin sa ya nufa hankali a tashe, zuciyarsa ce take masa zafi, kai tsaye bathroom ya shige tare da kunna ruwa a kansa domin sam ba'a cikin hayyacinsa yake ba...

Bayan kwana biyu An kawo Amaryar Abbah itama cikin ƙoshin lafiya, kowa ya watse daga matar gida sai yaran gida sai kuma Roshan dake can part ɗinsa shima da Amaryarsa,
Pinky da Rukky sun shirya tsab zasu koma karatu ƙasar London, Aunty Yolash ma ta koma Bauchi wurin Aikin ta, daga Ummy sai Ƴar tiny da Babbar Auntyn su Minal, sai kuma Amaryar Abbah Ummu Salamah wacce suke ƙiranta da Ammy,
Itama Ramlat tana nan bata tafi ba tana so ta ɗan ƙara hutawa kafin ta koma...

*AFTER ONE WEEK...*

Cikin Daren Juma'a da misalin karfe 2:00 AM,
Wayar Razhdeen ne ya yi ƙara alamar shugowar message a yayin da shi kuma yake kan sallaya ya idar da sallar dare, eyes ɗinsa yakai kan wayar dake kan drower, a lokacin bai saurari wayar ba sai kawai ya cigaba da lazuminsa, daga baya ya tashi ya cire jallabiyarsa already ya yi wankan sa tsab, daga shi sai Three quarter da singlet mai kakin soja, feshe jikinsa yayi da turare mai shegen ƙamshi kafin ya faɗa saman katafaren gadonsa tare da jan mayafi, gaba ɗaya ya mance da saƙon da aka turo mishi, lokaci guda bacci ɓarawo yayi awun gaba da shi...

Ta ɓangaren Ƴar Amana kuwa a cikin daren nan ko rimtsawa batayi ba, ga sauran yanda duk bacci ya ɗauke su gaba ɗaya an rarrage mutanen su waɗanda aka kamo ta hanyar kashe su,
A washe garin Jumma'a ne za'a kashe Ƴar Amana da misalin ƙarfe 6:00 na asuba, sumar kanta kuwa har yanzu bai fara tofowa ba,
A wannan lokacin har ta saddaƙar cewa babu wanda zai zo ya cecesu daga halin da suke ciki, tayi kukan har ta gaji,
Dab da asuba ƙarfe 4 Yar Amana bata san lokacin da bacci ya ɗauke ta a zaune ba,
Lokaci guda wani farin haske ya bayyano kan goshinta kafin ƙibtawar ido har hasken ya ɓace kamar walƙiya, hasken bai sauƙa a ko ina ba sai a kan goshin Razhdeen dake kwance yana ta shan baccin sa, a lokacin ne ya fara wani irin mafarki akan Ƴar Amana,
A cikin mafarkin aka bayyana masa halin da Ƴar Amana take ciki, abu kamar video haka yake gani a cikin mafarkin tin daga farkon al'amarin har zuwa yanzu da kuma yanka ta da za'ayi a gobe juma'a,
Ya juma yana wannan mafarkin mai birkitar wa kafin daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login