Showing 9001 words to 12000 words out of 89400 words

Chapter 4 - MY ENEMY BOOK 2 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

2510

gwara Abar maganar nan saboda banason damuwa, kasan halin Razhdeen nima haƙuri nake dashi, kuma ba kowace mace ce zata iya zama dashi ba in har ba sonta yake ba, domin ita zata sha wahala Ni kuma hakan ne banaso..."

Mai martaba dogon numfashi yaja tareda faɗin "toh maganar gaskiya dai Hajiya Maamie ce take son haɗin nan amma shi Razhdeen baya so domin jiya ma Saida suka samu matsala har Saida Razhdeen ya mareta a take ta sume a wurin..."

Abbah yace "whattt! Ita yarinyar ya mara ?..."

Mai martaba yace "a'ah ita kanta Uwar yarinyar, kasan Razhdeen bashida haƙuri kuma baya son raini ita kuma Maamie rashin kunya da wulaƙanci..."

Abbah yace "kana nufin kace matarka Razhdeen yasa hannu ya mara?..."

Mai martaba yace "No bawai na gaya maka saboda ranka ya ɓaci bane i just tell you that haɗin Auren bazai yu bane tinda ba son yarinyar yake ba..."

Abbah numfashi ya sauƙe yana faɗin "ba abun mamaki bane domin Razhdeen zai Aikata, shiyasa banason tura shi baƙunta wani wuri amma zanyi maganin shi, Please King kayi haƙuri Razhdeen Sam bai kyauta ba..."

Mai martaba yace "wallahi ko a jikina Yaya, kadai san zaman haƙuri kawai nake da ita, ta zamo mun ƙarfen ƙafa..."

Abbah yace "kayi haƙuri idan kuka zo gaba ɗaya za'a san yanda za'ayi..."

Mai martaba yace "TOH shikenam ba damuwa,
Amma Yaya ita kuma Minal fa ya za'ayi da ita yakamata a Aurar da ita tinda ta kammala karatunta..."

Abbah yace "bata da manemi shiyasa..."

mai martaba yace "naji tace tanada wanda take so ai..."

Abbah yace "Arne take so kuma ko zata mutu bazata Auri jinin Christal ba..."

Mai martaba yace "inda zai musulunta sai kawai a Aura mata shi..."

Abbah ya kuma cewa "Da nayi tunanin nan amma yanzu na sauya ra'ayina koda ya musulunta ma ƴata bazata Auri jininsu ba, yanda ta fito a cikin Musulunci haka jininta zai cigaba da gudana a cikin Musulunci, banason jikokina su kasance sunada family christoci..."

Mai martaba yace "Yaya wannan hukunci yayi......."
bai ƙarasa maganar ba yaji Abbah ya katse shi da cewa "nafa gama maganata babu sauyi kuma,
idan Roshan yana kusa ka bashi wayar...."

Mai martaba babu yanda ya iya haka ya miƙawa Roshan wayar,
Roshan hannu na kakkarwa ya karɓa tareda karawa a kunne da sallama a bakinsa,
Abbah yace "ina Razhdeen?..."

Roshan yace "na barshi a ɗakin kwanan mu..."

Abbah yace "kaje ka same shi kace ya taho Nigeria yanzu yanzu inason ganinsa..."

Roshan yace "TOH Abbah.."

Kafin Abbah ya katse ya kuma cewa "inaso zanyi video call da Minal kaje ka same ta yanzun nan..."

Saida ƙirjin Roshan ya buga jin abinda Abbah ya faɗa,
A birkice ya tsaya yana kallon screen ɗin wayar,
bai ankara ba yaga Abbah ya juyar da ƙiran zuwa video call, sai gwala-gwalan idon Roshan ne suka sauƙa akan Fuskar Abbah dake cikin wayar, nan suka fara kallon juna, Abbah ne ya katse shi da cewa "meye kake kallona haka, kaje ka bata wayar ina kallonka..."

Shima mai martaba Saida ya jinjinawa Abbah Sarkin wayo...

Roshan tashi yayi ya fara tafiya da haka yabar falon mai martaba ya fice kai tsaye ɗakinsu ya nufa yana zuwa ya buɗe ƙofa ya shige,
samun Razhdeen yayi yana zaune a bakin gado ya shirya tsab cikin ƙananun kaya ga yanda ƙamshin turare yake tashi,
Roshan yana zuwa ya juyar da wayar saitin fuskar Razhdeen,
wani irin kallo ya watsawa Roshan ganin yanda ya saita masa fuskar waya a tunaninsa photo zaiyi masa ne, sai ji yayi daga cikin wayan ance "Minal nace ka haɗani da ita ba wannan mai kama da mutuwa ba fuska ba annuri...."

Razhdeen idonsa akan wayar ta ciki yake kallon Abbansu, shima Abbah kallonsa yake, daga bisani Abbah yace "kai kuma Razhdeen inaso yanzu ka dawo gida banason dogon zance..."

Kai kawai Razhdeen ya ɗaga masa,
Roshan kuwa kasa ɗage wayar yayi daga saitin fuskar Razhdeen hannu sai kakkarwa yake,
Abbah ne ya kuma cewa "ina Roshan ya haka ne, nagaji da kallon fuskar Razhdeen haka ka kawar mun da wayar kaje ka haɗani da Minal...."

Roshan wayar ya kawo saitin fuskarsa yana kallon Abbah fuska a jagwalgwale kamar zaiyi kuka,
Abbah yace "ha'a Roshan zan saɓa maka fa, ina wasa dakai..."

A hankali yake jan ƙafa zai fice daga ɗakin kwatsam yaji Abbah yana faɗin "dakata! dakata mun!! Ɗaga mun wayar sama saitin fanka naga abu yana lilo kamar mutum..."

Shima Roshan ɗaga kansa sama yayi domin tabbatar da abinda Abbah ke magana akai,
Zaro ido yayi baki a sake ganin Ramlat a ɗaure saman fanka kanta na kallon ƙasi, sawaye kuma a ɗaure da fanka,
Saida ya nannaɗeta da zanin gado kafin ya ɗaureta sannan ya janye ta sama, iya fuskarta ne a waje, bayan ya gama mata dakun sakwara, ba ƙaramin duka yayi mata ba ganan hancinta yanda yake ɗigo da jini,
Dasauri Roshan ya sauƙar da kansa ƙasi yana maida kallonsa kan Razhdeen sai yanzu ya lura da dorinar da yayi kaca-kaca a ɗakin,

Ji sukayi Abbah ya fara salati yana faɗin
"Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Razhdeen Koh? Razhdeen Koh? nasan shi yayi mata haka, wayyo Allah ya zanyi da Razhdeen ɗin nan,
Kai Roshan miƙawa Razhdeen wayar nan..."

Dasauri Roshan yaje ya miƙawa Razhdeen wayar domin yana so Abbah ya manta da batun Minal,
Razhdeen karɓa yayi tareda kawar da fuska gefe domin bazai iya fuskantar Abbah a halin yanzu ba,
yana jin yanda Abbah yake zaginsa game da cewa
"anya kuwa Razhdeen kai mutum ne? Dan ALLAH ka dawo na kai ka bakin ruwa nafi tunanin kai ɗan ruwa ne,
Amma Aljanun nan basu kyauta mun ba, kai kaɗai ne suka canza mun kai, ban saniba ko tin kana cikin uwarka suka ɗauke mun Razhdeen ko kuma tin kana jariri,
Bakin ruwa dole saina kaika domin bazan barka kaita kashe ƴaƴan mutane ba...."

Razhdeen kai a gefe kunne ne kawai yake jiyo maganganun Abbah,

Shi kuwa Roshan ya kama kunkumi kansa a sama yanda yake ta kallon Ramlat yana tunanin ta yanda akayi Razhdeen ya ɗaureta haka, kuma alamun a sume take domin ko motsi bata yi kodai mutuwa,
haka yake ta wannan tunanin,

Abbah yace "Razhdeen na roƙe ka da sunayen Allah ka dawo Nigeria a yanzun nan dan ALLAH,
Ina Roshan?..."

Roshan ne ya karɓi wayar yana faɗin "gani Abbah..."

Abbah yace "kasan yanda zakayi ka since yarinyar nan..."

Roshan yace "TOH Abbah..."

Daga nan ya katse wayar...

Roshan sauƙe numfashi yayi yana faɗin "yanzu ta ina zan fara?..."

Razhdeen kuwa ko kallonsa baiyi ba balle ya furta wani abu,

suna cikin wannan halin sukaji bugun ƙofa,
Roshan ne yayi ƙarfin halin cewa "waye?..."

Hajia Maamie ce tace "Ni ce nazo duba Ramlat ne ko tazo nan..."

Roshan yace "daman kinsan da zuwanta?..."

Hajia Maamie tace "ehh! A'ah!! Eyy!!! A'ahh!!!!! Ehhh tohhh...."

Razhdeen ne ya juyo suka haɗa ido da Roshan,
fuska a haɗe Razhdeen yace "ki shugo ki ɗauke kayanki..."

Saiga Maamie ta shugo baki a washe ta ɗauka cewa sun gama fahimtar juna ne data jita tayi shuru a ɗakin,
ta shugo tana faɗin "tana inane? ha'a kodai itace a lulluɓe saman gado, ahhhh Masha Allah tinda bacci take bari na barku karna takura muku Koh....."

Har zata fice Roshan yace "ɗaga kanki sama..."

Maamie tana ɗagawa ta wani sau ƙara tana dafe da ƙirjinta, ƙafafunta har wani rawa suke, lokaci guda gumi har ya wanke mata fuska...."

Sai ga mai martaba shima ya shugo jin ihun MAAMIE yana faɗin "lafiya kuwa meke faruwa?..."

Saiga INDO itama domin ihun ya karaɗe ko ina na gidan,
Ai kuwa duk suka ɗage kayiwansu sama suna kallon ikon ALLAH,.
Mai martaba yace "meye wannan?..."

Maamie tana kuka tace "wani irin tambaya ne wannan kana ganin sun kashe mun ƙanwaaaa...." nan ta fashe da matsanancin kuka harda majina,

Mai martaba yace "meya kawo ta ɗakin nan TOH?..."

Maamie tace "kafin ka gama tambayarka Ni a Ciro mun gawar ta tinda sun kasheta mungwaye kawai azzalumai macuta, Allah ya isana tsakanina daku wallahi...."

ta nufi wurin Roshan tana kai masa duka,
Shi kuwa sai faman kaucewa yake, ita kuwa sai duka ta ko ina...

Mai martaba ne ya rirriƙeta yana faɗin "meye haka kike dukansa shi ba ƙaramin yaro ba, ko ce miki akayi shi yayi mata haka? TOH gashi can kije ki same shi ki dake shi..."

ya nuna mata yanda Razhdeen yake,
kallonsa tayi taga yanda yake wurga mata wani irin kallo kamar idanun zasu faɗo, tin daga lokacin da ta fara kaiwa Roshan duka yaji kamar ya shaƙota kawai yana ganin mutuncin Mai martaba ne, shi dai yasan in har ya miƙe daga zaune to saiya ɗage mata numfashi ne,
kafin a ankara aka nemi Maamie aka rasa harta fice da gudu tana kuka...

Girgiza kai mai martaba yayi yana faɗin "kaga Roshan kayi haƙuri dan ALLAH, yanzu ya za'ayi mu Ciro ta..."

Roshan ya kalli Razhdeen sannan yace "my man ka temaka ka Ciro ta..."

Miƙewa Razhdeen yayi ya nufi yanda Akwatinsa yake tareda faɗin "Impossible..."
ya ɗauko Akwati yana ja zai fice mai martaba yace "ina kuma zaka je?..."

Tsayawa yayi yace "Abbah yana son ganina right now sannan idan na ƙara kwana ɗaya a ƙasar nan wancan matar saina hallakata..."

Mai martaba yace "a'a! ALLAH ya huci zuciyarka Major General Razhdeen Allah ya kiyaye hanya ya tsare rayuwarka..."

Razhdeen amsa masa yayi da Amiin sannan ya fice...
Shima Roshan bin bayansa yayi zai rakashi can airport da motar gidan...

Mai martaba tsayawa yayi ya rasa yanda zai yi duk sun tafi sun barshi,
Saida yasa aka ƙira ma'aikatan mazan gidan kafin suka zo suka Cirota daƙer....

Roshan bai tashi dawowa ba saida yaga jirgin Razhdeen ya tashi kafin shima ya dawo masarautar,
Razhdeen an koma Nigeria.....




*POSTING DAYS*
*SUNDAY*
*TUESDAY*
*THURSDAY*
*FRIDAY*

*A SATI SAU HUƊU ZA'ANA POSTING*
*GA RANAKUN YIN POSTING...*

*ALLAH YA BANI IKON BIN TSARIN YANDA YA KAMATA*

*SANNAN A DAGE DA COMMENTS DOMIN SHI ZAISA A RINƘA YAWAN MUKU POSTING....*

asmeetah writer ✍️




*MY ENEMY _*

🫦 مقىينا 🫦


Mallakin
أسماء محمد أولا 🥳

Asmeetah (giaɗe writer)


STEP TWO
7 to 8



Bayan Razhdeen ya sauƙa a airport already akwai sojojin da suka zo ɗaukarsa,
Saida yasa suka miƙi hanyar mabarata yanda zai ga Ƴar Amana,
cikin rashin Sa'a ya zuba ido yaga babu alamar ta sai tarin tsofin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login