Showing 48001 words to 51000 words out of 89400 words
Abunda ya faru shine a lokacin da ta bugu da get tayi baya a ruɗe zata faɗi ƙasi shi da kansa Razhdeen ya kauce mata ko sauraronta bai yi ba balle ya yi gaggawar riƙo ta, kafin faruwar haka kuwa Roshan daman ya fito bakin get ɗin ganin yanda take ta kallon Razhdeen ne yasa ya tsaya cakk yana binsu da kallo, ganin tana shirin kaiwa ƙasi ne yasa ya taho da gudu yayi mata ɗaukar luɗa kafin taje ƙasi, shi kuma Razhdeen ko kallon yanda suke bai tsaya yi ba ya buɗe get ya shige ciki...
Baiwar ALLAH tsaya wa tayi tana tariyo abinda ya faru, bayan da tayi zata faɗi da akan Razhdeen zata faɗa shi kuwa yayi saurin kauce mata yabi ta gefen ta, tabbas in ba dan Roshan ba Razhdeen bazai taɓa tallafa mata ba,
rufe eyes ɗinta tayi sosai tsananin kunya ne ya ishe ta, sai yanzu ta fara jin ciwon kai sakamakon buguwar da tayi, kama kanta tayi tana faɗin "wayyo kai na..."
Roshan ne ya ce "na ɗauke ki ne?..."
ta ce "no I have leg, I'll walk by myself..."
Murmushi ya yi tare da faɗin "okay fine..."
Tayi gaba yana binta a baya da haka suka shige, a falo suka tarar da su Abbah da Razhdeen yana zaune sai pressing phone ɗin sa yake,
Roshan ne shima ya zaune dab da Razhdeen, itama Baiwar ALLAH zama tayi a kusa da Uwar masu gida...
Abbah ne ya soma magana yana faɗin "ba komai ne yasa duk na tara ku ba sai dan na sama wa iyalai na Dawwamammiyar farin ciki na har abada, akwai wani labari da naji wanda yayi matuƙar ƙona mun rai ya kuma saka ni cikin ƙunci, na shiga tashin hankali matuƙa dana ji kalar rayuwar da ma'aurata biyu suke yi na rashin wanzuwar farin ciki da zaman lafiya..."
Ƙirjin Baiwar ALLAH ne ya yi wani irin bugawa da ƙarfin gaske jin wannan batun tasan da su Abbah yake,
Uwar masu gida ne ta kalli Baiwar ALLAH domin ta fahimci babu zaman lafiya a tsakaninta da Yaya Roshan kuma tasan Roshan bashi da damuwa sai dai matsalar daga wurin ta ya fito...
Razhdeen dai yana zaune ya kasa fahimtar komai game da abinda Abbah yake faɗi..
Abbah ne ya kalli Baiwar ALLAH sannan ya ce "Daughter Roshan ya sanar mun duk halin da kuke ciki, ya buƙaci rabuwa da ke domin ya sama miki farin cikin da kike nema..."
Nan Abbah ya kwashe duk maganganun da Roshan ya sanar masa ya faɗe su yana kallon Baiwar ALLAH ya ƙarisa maganar da cewa "Shin duk maganar da ya faɗa gaskiya ne?..."
Zaro ido Baiwar ALLAH tayi tana ƙoƙarin haɗiye ranta tsabar tsananin fargaba da tsoro ga yanda Abbah ya fito mata da sirrin da take ɓoye wa a gaban mutanen gidan...
Razhdeen wani irin ƙololuwar baƙin ciki ne ya ziyarci cikin zuciyar sa jin yanda Baiwar ALLAH take wulaƙanta masa twins sannan har take furta cewa bata son shi, jin yanda ta furta wa Roshan cewa shi take so yasa gaba ɗaya yaji ya tsani yarinyar, sai kuma ya tuno da maganganun da take ta furtawa a gadon asibiti...
Abbah ne ya ce "bazan takura miki akan dole sai kin zauna da Roshan ba amma ina mai sanar miki cewa duk wanda ya nuna yana sonki tsakani da ALLAH to shine Abokin rayuwa, amma indai ke kike so kuma ba'a son ki to rayuwarki tana yawo a tsalallakun gajumare ne,
yanzu ina so ki furta da bakin ki kina son Razhdeen..."
Da sauri ta ɗago tana kallon Abbah ido sunyi jawur tsabar kuka, ta kalli Roshan taga shima kallon ta yake sannan ta maida idonta kan Razhdeen a yayin da shi kuma Razhdeen idonsa suke kan Abbah jin tambayar da yake mata...
Abbah ne ya sake maimaita wa da cewa "kina son Razhdeen ne kamar yanda kika faɗa ko kuma?..."
Girgiza kai tayi tana shaƙar numfashi da ƙer cikin kuka ta ce "zan cigaba da zama a gidan mijina..."
Abbah ya ce "a'a Daughter kar ki cuci zuciyar ki da kuma zuciyar wanda yake miki hallaci, nasan tinda kika furta masa cewa bakya son sa to kuwa bakya so ɗin dan haka a yau Roshan zai baki takardar sakin ki, da zaran ki kammala iddar ki za'a Aura miki Razhdeen, zan dakatar da tafiyar sa ƙasar U.S har sai an ɗaura muku Auren kafin nan..."
Baiwar ALLAH ba abinda take sai kuka domin tasan zai yi wuya Razhdeen ya amince, inda zai yadda to da kuwa tafi kowa farin ciki...
Abbah ne ya kalli Razhdeen sannan ya ce "Razhdeen kana dai jin abinda yake faruwa ko, bana buƙatar zaɓinka domin zaɓin marainiyar nan shine zaɓi na, ko ka so ko kar ka so dole zaka Aure ta tinda har Ɗan uwanka ya goyi bayan haka..."
Da sauri Razhdeen ya miƙe tsaye yana huci kamar wani kuntaccen zaki, har eyes ɗinsa sun rine yana motsi da lips ɗinsa a hankali ya ce "God forbid, that's not comp...."
Bai ƙarasa furta kalmar da zai fito daga bakin sa ba Abbah yayi saurin daka masa tsawa da cewa "You'll never escape for this choosing, dole ka Aure ta tinda ta nuna kai take so, uban waye ya ce ka rufe junanku a cikin bedroom na tsawon one week? daga kai sai ita, ita mace ce a koda yaushe kai take gani a cikin ƙwayar idanuwanta, idan zata kwanta bacci sai ta fara tozali da fuskar ka haka nan da zaran ta farka fuskar ka shine madubin ta, so know tell me how comes bazata kamu da sonka ba a halin da kuka kasance a tare? wanda nasan kaima ƙarya kake kace baka ji komai akanta ba, Razhdeen don't tell me the lie I known you too u really loving her..."
"Father I don't love her and I'll never love her in my life forever and ever..."
Razhdeen ne ya furta hakan tin kafin Abbah ya ƙarasa iddasa maganarsa.
Abbah ya ce "to amma meyasa ita take sonka?..."
wani irin kallo Razhdeen ya watsa mata mai haɗe da harara kafin ya ce "she losses her mind that's why..."
Cike da mamaki Abbah ya ce "Deen what are you talking about?..."
Tinda Razhdeen yake a wayonsa bai taɓa zubda ƙwallah ba sai yau shi kanshi Abbah sai da ya girgiza idonsa akan sa, shima Roshan miƙewa yayi tsaye ganin hawaye kwance saman fuskar Deen,
Razhdeen ya ce "bana sonta kuma bazan taɓa sonta ba har abada balle na Aure ta, Dad tell her bata samu mijin Aure ba indai ni zata Aura, now I hate her and if you post me to marry her I'll hate myself too..."
Abbah a firgice ya kalli wurin da Baiwar ALLAH take a zaune tana kallon ƙasin carpet ba abinda take sai kuka,
Abbah bazai iya juran ganinta a cikin wannan halin ba haka yasa ya girgiza kai ya maida kallon sa kan Razhdeen tare da faɗin "Deen dole zaka Aure ta, idan kuma ka azabtar da ita ko kuma ka kasa biya mata hakki zan iya tsine maka Albarka..."
A gigice Razhdeen ya ɗago da jajayen idanuwansa waɗanda suka sha kuka yana kallon yanda Abbah yake, jin kalmar da Abbah ya furta yasa kansa ya fara juyawa wani irin hajijiya ne yake shirin ɗaukarsa..
Roshan shima zaro ido yayi yana kallon Abbah cike da mamaki, Uwar masu gida itama a ruɗe ta toshe bakinta da hannayenta biyu tana kukan baƙin ciki, bata taɓa jin haushin wani matuƙa ba sai yau daga Mahaifiyarta sai kuma Baiwar ALLAH...
Ammy ta ce "Amma Abban yara...."
bata ƙarasa maganar ba ya ɗaga mata hannu alamar ta dakata..
Ya ƙasara wurin da Razhdeen yake tsaye domin zama ya gagare shi, tsayawa yayi a gaban sa tare da faɗin "zaka sake bijire wa maganata a karo na biyu ko? Ƴar uwarka Amina ta bijire mun ta bi zaɓinta ta guje ni, kaima you can do that, now choose your's shin zaka bi zaɓin ranka ne ko kuma zaka yi abinda nace? idan har zaɓin ranka ka zaɓa kaje kaima na sallame ka..."
Abbah ya ƙarasa maganar yana zubda ƙwallah shima,
Razhdeen lips ɗinsa ne yake kakkarwa a hankali ya furta "Dad..."
Abbah ya ce "not your Dad har sai ka zaɓi ɗaya a cikin biyun nan, shin zaɓinka ko zaɓi na?..."
Razhdeen yana kuka ya matso dab da Abbah ya riƙe masa hannayensa biyu yana kuka ya ce "Dad you are my life and the something happen to my life I'll even to be leave, na amince zan Aure ta amma zaɓinka ne Abbah is not my chosen..."
Abbah ya ce "Deen are you sure are you going to get engagement with her ?..."
Razhdeen ya ɗaga masa kai tare da faɗin "bazan taɓa bijire maka ba..."
Razhdeen wani irin tsanar Baiwar ALLAH ne ya ziyarci zuciyarsa lokaci guda, ji yake kamar ya murɗe mata wuya tabar duniya, yayi matuƙar dana sanin haɗuwa da ita, tinda yake bai taɓa jin tsanar wani abu ko wani ko wata sai yau akan Baiwar ALLAH,
Abbah rungumarsa yayi yana faɗin "thank you very much my son..."
Shima Razhdeen rungumar Abbah yayi,
Baiwar ALLAH ce ta ɗago da manya-manyan idanuwanta waɗanda suka canza kamannu ta ɗora su akan Razhdeen wanda yake rungume da Abbah, lokaci guda taji zuciyarta yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske ganin irin kallon da Razhdeen yake mata na tsananin tsana...
Razhdeen idonsa akan Baiwar ALLAH yake maganar zuci yana faɗin "this is the first time that you make urself my Enemy, you are my enemy, I hate you and I'll never love you in my life, I hate you..."
Ga yanda ya zazzaro eyes ɗinsa waje sunyi matuƙar canza launin ja ya kasa ƙibta idonsa akan ta,
itama haka take kallonsa ido a zazzare tsananin tsoro ne da fargaba suka bayyana akan fuskarta, wani irin yawu ta haɗiya na tsoro, ba ƙaramin kwarjini ya yi mata ba...
Roshan idonsa akan Razhdeen ganin yanda yake mata kallon tsana da baƙin ciki gaba ɗaya jikinsa ba ƙaramin sanyi ba, dole yasan Baiwar ALLAH zata sha wahala sosai a hannun Razhdeen...
Abbah ne ya raba jikinsa daga na shi yana faɗin "idan ka taimaki marainiya kaima Allah zai taimake ka..."
Ya kalli wurin da Roshan yake sannan ya ce "Roshan kayi haƙuri ka bata takardar sakin ta..."
Shima Roshan ba abinda yake sai kuka yana daga tsaye ya ciro wata farar takarda a cikin aljihunsa ya nufo yanda Baiwar ALLAH take a zaune ya ce "Ammata yau burinki zai cika, ga takardar raba Aurenki da ni..."
Tana kuka ta miƙe tsaye itama tana fuskantar sa tasa hannu ta karɓi takardar idonta akan Roshan sai da ta dai-daici tsakiyar paper ta raba gida biyu, haka ta yayyaga takardar tana kuka ta ce "Yaya Roshan kayi haƙuri zan cigaba da zama da kai..."
Taje gaban Abbah ta durƙusa gwiwowinta ƙasin carpet tana kuka ta ce "Abbah ka gafarce ni, Uncle Deen baya sona bazan iya zama da shi ba, zan cigaba da zama da wanda yake sona har cikin zuciyarsa, zan canza hali na, zan masa biyayya yanda ya kamata..."
Abbah ya ce "kin tabbata har cikin zuciyarki abinda kike faɗi?..."
tana kuka ta ce "da gaske nake Abbah..."
Abbah ya ce "Alhamdulillah shikenam ki kwantar da hankalin ki mahaƙurci mawadaci yanzu wanda zai sama miki farin ciki shine ya dace dake Daughter..."
Jinjina kai tayi tana sauraron Abbah,
Roshan murmushi yayi ganin yanda ta sauya ra'ayi amma yasan ba har cikin zuciyarta ba, tayi hakan ne saboda gudun matsalar da zata shiga nan gaba tinda itama kanta tasan Razhdeen ba sonta yake ba, tsoronsa da fargabansa ne yasa tayi gaggawar janye ƙudirinta...
Razhdeen murmushin gefen baki yayi na mugunta a cikin ransa ya ce "is better for you..."
Razhdeen ya buɗi baki yayi magana yana faɗin "tomorrow early morning I will travel to U.S..."
Abbah ya ce "lokacin yafiyarka bai yi ba naga..."
Ya ce "Yes! zan tafi tin yanzu nayi muku sallama domin ba lallai na dawo ba, da sassafe zan wuce airport..."
yana kaiwa nan ya juya zai tafi, Abbah ya ce "Are you Angry with your Dad?..."
Razhdeen ya ce "no..."
a takaice
Abbah ya ce "okay zan tarar da kai a airport goben.."
Razhdeen ya ce "ok..."
daga nan ya yi tafiyar sa...
asmeetah writer ✍️
🤦♀️ *MAƘIYI_NAH*🤦♀️
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء محمد أولا 🥳
Asmeetah (giaɗe writer)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
STEP TWO
👇
*26_ TO_30*
Razhdeen shigar shigar motarsa yayi ya zauna yana riƙe da sitiarin motar tsabar ƙololuwar baƙin cikin Baiwar ALLAH ne yasa ya kasa jan motar.
Baiwar ALLAH ne itama ta fito tana sharar hawaye ta nufi part ɗinta bata ma lura da Razhdeen na wurin ba, shi kuwa idonsa akanta