Showing 81001 words to 84000 words out of 89400 words

Chapter 28 - MY ENEMY BOOK 2 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

2533

tana nuna Baiwar ALLAH cikin ɓacin rai,

Baiwar ALLAH damuwar da yake kanta ma ya ishe ta haka take zubda hawaye ba ƙaƙƙautawa...

Hajiya Kilishi idonta akan Pinky ta ce "kina ganin halin da take ciki amma kina gaya mata cewa ita ta jawo? mijinta ne fa taya zatayi sanadiyar mutuwar sa, haba Balkisu ki koyi iya magana dan ALLAH...."

Pinky ta ce "to naga bata sonsa wai Uncle Deen take so shine take son hallaka shi..."

Ummy ta ce "innalillahi wai meyasa hakane Aunty Pinky dan Allah ki bar mu da abinda yake damun mu..."

Hajiya Kilishi ta ce "muyi Addu'a Allah ya bashi lafiya shine kawai, a yanzu dai babu wanda yasan gaibu sai ALLAH..."

Suna cikin wannan halin sai ga Ammy ta fito daga part ɗinta tana sanye da hijab har ƙasi da carbi a hannunta, jin motsin mutane ne yasa ta fito domin ganin su waye ne saboda tasan gidan shuru yake ba kowa...

Ƴar tinny ganin Ammy yasa ta rufa da gudu tana faɗin "Ammy nahh..."

Ammy ta rungumi Ƴar tinny tana dariya, tayi matuƙar farin cikin ganin yaran gidan sosai.

Ta ce "Auta ki ka gudu kika barni ko..."

Ƴar tinny ta ce "Ammy wurin Mommyna naje.."

Ammy ta ce "Ayyah fatan kin samu Mommy cikin ƙoshin lafiya ko?.."

Ƴar tinny ta ce "ai tare muka zo da ita, gata can..."
ta nuna ta da yatsa.

Ammy bata yi tunanin har da uwar aka dawo ba domin bata lura da ita ba,
haɗa ido suka yi Ammy tasau murmushi tare da nufan wurin tana riƙe da hannun Ƴar tinny,
tana zuwa wurin ta durƙusa a gaban Hajiya Kilishi tana gaishe ta
Ta ce "ina wuni Aunty, fatan kin iso lafiya..."

Hajiya Kilishi fuska a sake ta ce "lafiya ƙalau Amaryar mu, nagode sosai kin riƙe mun yara cikin mutunci..."

Ammy ta ce "ba komai wallahi, ai ƴaƴa na kowa ne..."
ta cigaba da cewa "ashe kun zo Ni ban san yau zaku dawo ba ai da anyi muku tanadi na musamman..."

Pinky tana farfara ido ta ce "an maida Auren Mommy da Abbah yanzu ta dawo gidan mijin ta..."

Ammy cikin nuna farin ciki ta ce "Masha Allah, Allah mun gode maka, wallahi naji daɗin hakan sosai, duk da bai gaya mun ba amma nayi farin ciki..."

Pinky ta ce "ai ba dole ne sai an gaya miki ba..."

Hajiya Kilishi wani irin harara ta wurga wa Pinky tana faɗin "bana son iskanci fa, abokiyar ki ce ko kuma dake take maganar ta..."

Pinky kawar da kanta gefe tayi tana tura baki...

Hajiya Kilishi ta kalli Ammy tana murmushi ta ce "wallahi kuwa mu ma bazata akayi mana, ban san da Auren ba sai bayan an ɗaura..."

Ammy ta ce "naso ya sanar mun dawowar ku ai, da an shirya muku girke-girke na musamman..."

Hajiya Kilishi ta ce "ayya kar ki damu, mun zo mun tarar da wani tashin hankali, Roshan ba lafiya yanzu haka sun nufi hospital ciwon zuciyarsa ta tashi..."

Ammy dafe ƙirji tayi tana faɗin "subhanallahi wallahi ban sani ba..."
sai yanzu ta lura da Baiwar Allah dake ta kuka fuska tayi jawur,

Ammy tayo kanta tana faɗin "Allah sarki kiyi haƙuri Daughter Insha Allahu zai samu sauƙi..."

Wayar Ummy ce ta fara ringing tana duba wa taga Uncle Deen ne, ɗagawa tayi tare da yin sallama,
Daga ɓangaren Razhdeen cewa yayi "wai meyasa Abbah baya picking call ɗina ne sannan ina ƙira Roshan shima baya ɗaga wa why?..."

Ummy tana kuka ta ce "Uncle Deen su Abbah suna hospital ciwon heart ɗin Yaya Roshan ne ya tashi, sun tafi ko motsi baya iya yi sai aman jini yake..."

Razhdeen cikin tashin hankali ya ce "whattt?..."
daga nan ya katse wayar...

Hajiya Kilishi ce ta ce "anya bamu bisu asibiti ba? muje mu gano ya ake ciki..."

Ammy ta ce "gaskiya kam..."

Har sun miƙe zasu fita sai ga ƙiran wayan Abbah ta wayar Ummy nan ma ɗagawa tayi tana faɗin "Abbah gamu nan zuwa..."

Abbah ya ce "No ku zauna domin ko kun zo ba samun mu zaku yi ba, yanzu haka muna airport zamu fita ƙasar waje domin sai anyi masa aiki..."

yana kaiwa nan shima ya katsar da ƙiran...

Ummy ta ce "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un ciwon Yaya Roshan yayi tsanani dole sai anyi masa operation a heart ɗinsa, yanzu haka suna airport zasu fita ƙasar waje...."

Baiwar ALLAH tana jin haka data fashe da wani irin marayan kuka ai kawai ta nufi bakin ƙofa da gudu ta fice..

Duk bayanta suka bi suna faɗin "ki dawo Daughter ina zaki je kuma..."

Gudu na gaske take ta buɗe gate ɗin farko ta fice, tana zuwa gate na biyu nan ma ta buɗe ta wuce security da gudu, bayan ta suka bi suma suna faɗin "lafiya kuwa me yake faruwa ne..."

ai kuwa nan da nan ta iso gate na uku wato babban gate nan ne bazata iya buɗe wa da kanta ba haka take bubbugawa tana ihu, har sauran security suka tarar da ita, sai ga su Hajiya Kilishi da Ammy da sauran suma sun iso ta,
Sojojin dake waje jin yanda ake ta bubbuga gate yasa su buɗe wa suna faɗin "who's here?..."

Ganin mutanen gidan ne yasa su cewa "meyasa ku ka fito?..."
suka yi magana fuska a haɗe ba alamun annuri ga jajayen idanuwa...

Ai kuwa Baiwar Allah bata tsaya sauraronsu ba ta zille ta tsakiyar su ta wuce, gudu take bana wasa ba, suma haka sojojin suka bita suna faɗin ta dakata amma ko sauraronsu bata yi ba, ai kuwa tana cikin wannan halin sai ta ƙara tarar da asalin babban gate ɗin gidan gaba ɗaya wanda daga shi shikenam sai outside, anan kuma sojojin dake wurin sun fi goma banda waɗanda suke ta waje,
Baiwar Allah ganin bata da wata mafita kawai ta durƙusa gwiwowinta a wurin ta fara zabga uwar ihu, duk sojojin suka kewaye ta suna tambayar ta meke faruwa amma ta kasa yin magana sai cewa take
"Ku barni naje na gano mijina dan Allah, inason ganawa da shi kafin su shiga jirgi, mijina nake son gani..."

Wani soja ne ya ce mata "kiyi haƙuri ki koma ciki domin jirginsu har ya tashi sun tafi..."

Su Hajiya Kilishi da Ammy kam tin a gate na biyu suka dakata domin ba ƙaramin gajiya sukayi ba, daƙer su Ummy suka ƙaraso wurin gate na huɗun yanda Baiwar Allah ta dakata suma ɗin ba ƙaramin gajiya suka sha ba..

Daƙer aka rarrashi Baiwar Allah ta haƙura suna shiga mota aka komar dasu can cikin gidan amma ta kasa dakatar da kukan....

A haka suka wuni har zuwa dare kowa a cikin damuwa yake,
Misalin ƙarfe 9 na dare duk suna zazzaune a babban falo sai suka ji an turo ƙofar falo da ƙarfi, a matuƙar tsorace duk suka miƙe tsaye idonsu akan bakin ƙofa ganin mutum sangamgam gashi a kwance saman bayansa sai haki yake domin a ruɗe ya iso, kana ganinsa kasan ba'a cikin hayyacinsa yake ba,
Ummy ce ta ƙaraso yanda yake tana faɗin "Uncle Deen..." ta ƙarasa tana kuka...

Duk suma suka nufi yanda yake a tsaye suna ambatar sunansa, banda Baiwar Allah dake zaune tayi tagumi ko kallon yanda suke bata yi ba...

Razhdeen ya ce "wani hospital suke?..."

Ammy ta ce "sun fita ƙasar waje sai anyi masa aik..."

Cikin tashin hankali Razhdeen ya ce "which country?..."

Ammy ta kalli Ummy ta ce "wani ƙasar waje Abban ku ya ce miki sun je?.."

Ummy ta ce "wallahi bai gaya mun ba..."

Hajiya Kilishi ta ce "Razhdeen ka jira zuwa nan da kwana biyu zasu dawo...."
bata ƙarasa maganar ba ya katse ta da cewa "i can't wait..."

Haka yake zarya a cikin falon yana trying number Abbah amma baya shiga, duk wasu numbobin da yake tsammanin zai samu labarin su Abbah amma basa tafiya, cikin ɓacin rai da takaici haka yayi wurgi da wayarsa sai tin plasman, nan danan wayar ta fashe, hatta plasman ɗin ma ya samu rauni domin da iya ƙarfinsa ya wurga, durƙusawa yayi da gwiwowinsa yana cakurkuɗa sumar kansa lokaci guda ya zabga wani irin gigitaccen ihu, ai kuwa nan da nan kamar wani mahaukaci ya fara wargaza falon yaje ya janyo plasman yayi wurgi da shi, yaje ya buga glass dinning har sai da shima ya dagargaza shi,

Baiwar Allah ganin zai iya ji mata rauni yasa ta tashi ba shiri taje ta ɓuya a bayan Ammy...

Hajiya Kilishi ce tayi ƙarfin halin zuwa har yanda Razhdeen yake a durƙushe itama taje ta tsuguna tana ambatar sunansa a hankali "Razhdeen! please ka kwantar da hankalinka Roshan zai samu sauƙi, ai cuta ba mutuwa ba ne..."

Razhdeen fuskar nan tayi jawur haɗi da idanuwansa haka ya ɗago su a shanye yana faɗin "ciwon nan yaushe zai warke na har abada? meyasa ciwon bazai dawo kaina ba?...."

A zabure cikin tsawa ya ce "wai shin meye silar faruwar haka? waye yayi sanadiyar tashin ciwon sa? nasan haka kawai ciwon sa baya tashi sai da dalili, who....?..."

Ita kan ta Hajiya Kilishi sai da ta tsorita da tsawar sa nan...

Baiwar Allah haka take cakumar Ammy ta baya tana ɓuya zuciyar ta na harbawa da ƙarfin gaske...

Baiwar ALLAH bata ankara ba taji an jawo ta tare da yin wurgi da ita a tsakiyar falon, a ruɗe ta ɗago tana kallon Razhdeen wanda yayo kanta yana faɗin "me kika aikata masa? nasan bakya ƙaunarsa fatan ki shine ki rabu da shi, kina son kashe mun ɗan uwa ko?..."

ya cabko sumar kanta a fusace tare da ɗago da kanta yana kallon fuskar ta ya ce "kafin ki kashe mun twins wallahi sai kin rigashi tafiya lahira..."

Gwara kanta yayi da jikin kujera ya nufi kitchen cikin ƙanƙanin lokaci ya fito hannunsa riƙe da wuƙa...

Gaba ɗayan su zaro ido suka yi suna kallon Razhdeen, ganin ya fito yana riƙe da wuƙa, yana zuwa ya ɗaga hannunsa zai caka mata wuƙar ta zabga wani irin gigitaccen ihu, dai dai lokacin da Abbah ya shigo a ruɗe ya ambaci sunansa " *RAZHDEEN*" ..

Dasauri ya ɗago tare da kallon yanda yaji an ƙira sunansa domin kunnensa sun jiyo masa sautin muryar Abbah ne..

Ammy kuwa tinda Razhdeen ya ɗaga wuƙa ta ƙanƙame idonta zuciyarta na bugun uku-uku...

Hajiya Kilishi kam ja da baya tayi sauran kaɗan ta faɗi ta baya badan Pinky tayi saurin riƙe ta ba...

Ummy itama ihu ta zabga tare da faɗin "Uncle Deen..."

Abbah a ruɗe ya shigo falon tare da nufan yanda Razhdeen yake yana faɗin "da hankalin ka kuwa Razhdeen? shin ka haukace ne?..."

Baiwar Allah tana kuka ta tashi da gudu ta nufi yanda sauran suke a tsaye Ammy tayi saurin rungumo ta tana rarrashinta...

Abbah ya ce "kawo wuƙar nan, wa ya gaya maka itace silar kwanciyar sa jinya?..."
Abbah ya karɓe wuƙar yana bubbugan kafaɗar sa cikin rarrashi...

Razhdeen kuka ne ya kuɓuto masa Abbah yayi saurin rungumar sa tare da faɗin "ka kwantar da hankalinka Roshan ya farfaɗo cikin yardar Allah, domin har anyi masa aiki anyi treat ɗinsa sosai, kasan asibitin ƙasar Ethiopia muka je, su kuwa aikinsu ba wasa..."

Razhdeen ya ɗago yana kallon Abbah sannan ya ce "yana ina Abbah? inason ganin twins ɗina..."

Abbah ya ce "na baro shi acan cikin kulawa, gobe zan koma Insha Allahu..."

Razhdeen ya ce "inason ganin shi..."

Abbah ya ce "okay don't worry..."
ya ciro wayar sa tare da dialing call wani ma'aikaci daga can hospital....
cikin ƙanƙanin lokaci aka ɗauka daman video call ne, Abbah ya ce "ina buƙatar ganin Roshan..."
daman suna kusa da shi domin sune masu bashi tsaro,
Roshan ne ya bayyana akan fuskar wayar yana kwance kan gado ya na sanye da oxygen,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login