Showing 6001 words to 9000 words out of 89400 words
gajiya da kalar wulaƙancin da Maamie take mata acikin gidan nan,
baki ta buɗe cikin sassanyar murya tace "Aunty Maamie duk zuriya ta sun wuce ace musu mayunwata, domin kin san asalina da tushe na, daga gidan sarauta na fito sannan na ƙara shiga gidan sarauta Kinga kuwa gaba da baya Arziƙi ne ke bibiyata..."
Maamie sake baki tayi tana mata kallon mamaki, tasa hannu a saitin haɓarta tana faɗin "iyyeeee! Lallai matar nan, yanzu har kina da bakin da zaki gaya mun magana? Ahh lallai wuyanki ya isa yanka, tabbas saina ƙara miƙewa tsaye a kanki ƴar banza..."
INDO kallonta kawai take cikin rashin fahimtar abinda take nufi,
Abinda Maamie take nufi shine akwai sihirinda tayi mata kuma yana shirin karyewa dole sai ta sake zuwa gurin bokan ta...
Ramlat ganin bazata iya tsaya sauraronsu ba yasa tayi saurin ficewa zata nufi masauƙin su Razhdeen.....
A ɓangaren su Razhdeen kuwa suna zaune akan dadduma a ƙasin gadonsu suna tsare-tsaren yanda bikin Roshan zai kasance,
Jin sallama yasa Roshan ɗogowa tareda amsa sallamar shi kuwa Razhdeen daman ko ɗagowa baiyi ba yana rubuce-rubuce,
Ramlat durƙusawa tayi tana gaishe su tareda ajiye musu kulolin abinci, kafin kace mai ƙamshin turaren jikinta har ya hargutsa ɗakin gaba ɗaya,
Roshan idonsa yakai kan Ramlat yana yamutsa fuska tareda faɗin "wannan wani irin turare ne babu daɗin ji..."
Itama ɗagowa tayi tana kallonsa ido a zazzare tsananin tsoro ne a bayyane kan fuskarta, dasauri takai idonta kan Razhdeen wanda tinda kansa yake ƙasi ko ɗagowa bai samu daman yi ba,
Ganin har zuwa yanzu bai ko motsa ba yasa jikinta yin sanyi domin da sunansa akayi amfanin haɗa turaren,
Razhdeen ganin shima turaren ya ishe shi da wari yasa ya ɗago a fusace yana wurga mata harara cikin tsawa yace "You'll get out inside our room or u want me to remove u by myself..."
A tsorace tayi firgit ta miƙe tsaye ba shiri tayi waje da gudu,
dogon tsuka yaja tareda faɗin "non sense girl..."
hakan na nufin tsafin baiyi aiki ba tinda so ake yaji ƙamshi shi kuma wari yaji, an samu matsala kenam...
Haka ta shige Falo tana kuka, kai tsaye bedroom ɗin Maamie ta wuce ganin bata tarar da ita a falon ba,
Maamie tana ganinta a cikin wannan halin tayi saurin dafe ƙirjinta tareda faɗin "na shiga uku kar dai kice an samu matsala..."
tana kuka tace "naga korata yayi cikin fushi, Ni Maamie nace miki mu rabu da Uncle Deen ɗin nan babu wani tsafin da zai kama shi...."
kafin ta rufe baki Maamie tayi saurin katseta da cewa "yi mun shuru dallah! ai wannan tsoron nakin ne zai jawo mana matsala, zakiyi abu amma bazaki sake jiki kiyi ba ƴar Banza kawai..."
Ramlat tace "toh Maamie ya zanyi, yanzun meye mafita? gashi gobe asubanci zasu yi su koma Nigeria..."
Maamie tace "wa? ai ƙafarki ƙafarsu dake zasu tafi kuma dole Abbansa nasan saiya tilasta shi akan ya Aureki tinda yana jin maganar mahaifinsa..."
Ramlat tace "toh shikenam yanzun naje na fara shiri kenam?..."
Maamie tace "eh mana, kuma da daddare inaso kije ki kusance shi da waɗannan ƙananun kayanki nan masu bayyanar da surar jiki, amma ki tabbatar Roshan baya ɗakin..."
Zaro ido Ramlat tayi tareda dafa ƙirjinta tace "nashiga uku Maamie wallahi kasheni zaiyi, ke baki san halin Uncle Deen ba koh?..."
Maamie a fusace tace "Dan buro ubansa idan yafi ƙarfin kowa ai baifi ƙarfin makircin mace da surar jikinta ba..."
Ramlat shuru tayi tana kallon Maamie cikin kalar tausayi...
Maamie ta kuma cewa "kiyi duk abinda nace, kai inta kama kiyi tsindir a gabansa..."
Haɗiyar yawu Ramlat tayi tareda cewa "tam! I'll try my best..."
Misalin ƙarfe 9 na dare Roshan da Razhdeen sun kammala cin abincin dare kenam saiga Mai martaba ya shugo musu ɗakin da sallama a bakinsa,
Da fara'a akan fuskar Roshan ya amsa sallamar tareda faɗin "Uncle kaine a room ɗin mu..."
Mai martaba yace "ina Razhdeen?..."
Roshan yace "ya shiga bathroom yanzu ina tunanin wanka yake yi..."
Mai martaba yace "Roshan yanzu Abbanku yake cemun tareda Minal ku ka taho, ina kuka barta?..."
Saida ƙirjin Roshan ya buga jin asirinsa ya tonu, baiyi tunanin Abbah zai sanar wa Uncle ba,
Cikin ƙinƙina Roshan yake faɗin "Am daman Uncle..."
hannunsa akan sumar kansa ta wurin ƙeya yana sosawa gaba ɗaya ya rasa mai zai ce.
Mai martaba kallon ƙurilla yake masa yace "ina jinka banason rashin gaskiya fah..."
Roshan yace "Uncle damun koma can falonka sai mu tattauna..."
Mai martaba yace "tattaunawa akan meye?..."
Roshan yace "Please Uncle maganar tanada muhimmanci sosai..."
Mai martaba yace "okay ina jiranka yanzun nan..."
yana ƙarasawa yayi ficewarsa, shima Roshan dasauri yabi bayan Mai martaba....
Suna fita Ramlat tayi saurin shugowa daman ta daɗe tana tsaye tana jiran fitarsu,
tsayawa tayi tana kalle-kalle a ɗakin kamar wani baƙonta, tana sanye da Black net shirt wanda bai rufe mata cibiya ba, duk ana kallon surar jikinta ba tareda tasa ko breziyya ba,
sai wani ɗan gajeren wando wanda ya tsaya a iya cinyarta,
Ga daman tanada dirin jiki...
Saida tayi kusan minti talatin tana tsaye kafin Uncle Deen ya fito daga cikin bathroom ɗaure da white towel a kunkuminsa,
Ganinsa yasa ta zaro ido waje ta ƙame a wurin ganin yanda tsarin surar jikinsa yake, ga gargasa a kwance luf-luf kamar gashin jarirai, yanda kasan ba mutum ba domin Ni kaina bazan iya tsara muku yanda surar jikin Razhdeen yake ba,
Ga farin fata mai ɗauke ido har wani shining yake, tsayi kuwa ba'a magana domin idan ya jeru da Ramlat zata zamana a iya kunkuminsa zata tsaya, bugu da ƙari ma ga ƙira mai kyau haɗi da murɗaɗɗen jiki, ƙirjinsa kuwa sai ya haɗe mata biyu zuwa uku aciki tsabar faɗi kamar tray..
Razhdeen bai ankara da mutum acikin ɗakin ba saida ya waiwaya ya ganta, domin yasan fitar Roshan shi da Mai martaba....
asmeetah writer ✍️
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء محمد أولا 🥳
Asmeetah (giaɗe writer)
STEP TWO
5 and 6
"Roshan ka daina mun ƙin-ƙinda ka fito fili ka sanar mun abinda ke faruwa, kunyi wa Abbanku ƙaryar cewa kun taho da Minal Ni kuma ban ganku da ita ba, shin ina kuka barota?...."
Roshan yana sunkuye da kai ƙasi tinda Mai martaba ya fara magana bai ɗago ba,
Saida mai martaba ya sake ƙiran sunansa ganin ya tafi dogon tunani...
A firgice Roshan ya ɗago yana faɗin "na'am Uncle.."
ya zuba masa ido alamun bai ji duk abinda ya ce ba.
Mai martaba ya kuma cewa "shin ina ku ka baro Minal?..."
Girgiza kai Roshan yayi tareda faɗin "Uncle ana bikin ƙawarta ne shine ta tsaya a wurin kuma itace babbar ƙawar Amarya..."
Jinjina kai Mai martaba yayi yace "duk alamun rashin gaskiya sun bayyana akan fuskarka Roshan, babu gaskiya acikin lamarinka amma ban sanka da wannan halin ba, Roshan baka ƙarya meyasa yanzu?..."
Gaba ɗaya gumi duk ya wanke masa fuska kamar wanda ya fito daga cikin rijiya,
wani irin yawu ya haɗiya wanda ya tokare masa maƙogaro,
tsoronsa idan har Abbah yasan cewa Minal tana tare da Marshall toh kashinsa ya bushe, motsi yake da lips ɗinsa a hankali ya furta cewa
"Uncle ka sanar wa Abbah cewa bada Minal muka zo ba?..."
Mai martaba yace "ehh tabbas saboda ban ganta ba.."
Zaro ido waje Roshan yayi yana kallon Mai martaba,
gaba ɗaya jikinsa yayi la'asar kamar ba jini, sai ji yayi mai martaba yace
"Ni ban sanar masa komai ba, yadai gaya mun cewa tareda Minal kuka zo amma ban ce masa bakuzo da ita ba, rashin sanin abinda zan gaya masa ne yasa na katse wayar domin sai naji daga bakin ku tukun na yanke hukunci..."
wani irin sauƙe nannauyar numfashi Roshan yayi yana faɗin "thank God,
sannan yace Uncle zan sanar maka duk halin da ake ciki..."
Mai martaba yace "TOH ina sauraronka..."
Nan Roshan ya sanarwa mai martaba halin da ake ciki na Minal da kuma Mohandas..
Dogon numfashi mai martaba yaja sannan yace "TOH banda abinka Roshan meye zaka iya a wannan lamarin? kadai san halin Mahaifinku idan yace baya son abu TOH kuwa duk duniyan nan bamai sashi yayi, sannan kuma shi Mohandas so kake ya bijirewa iyayensa kenam akan mace?..."
Roshan idonsa akan mai martaba yace "Uncle ina tausaya musu ne, wallahi suna son junansu kuma shima Mohandas ya amince akan zai musulunta, nasan idan ya karɓi musulunci Abbah bazai hanashi Auren Minal ba..."
Murmushi Mai martaba yayi yace "yaro yaro ne, Roshan har yanzu da ƙuruciya akanka, kana nufin kace Abbah zai bawa Mohandas Auren Minal ba tareda iyayensa suna so ba? ko kuma Abbah zai ɗauki yarinya ya bashi ba tareda iyayensa sun sani ba?
TOH bari kaji shi Aure ya wuce yanda kake tunani, ina mai sanar maka cewa Mahaifinku bazai taɓa yadda da wannan al'amarin ba sai dai idan har iyayen Yaron suma sun Aminta nan ne za'ayi abu cikin lumana..."
Roshan Dafe goshinsa yayi yana hura iskar bakinsa tareda jinjina maganganun mai martaba,
Ɗagowa yayi yana faɗin "yanzu ya zamuyi Uncle?..."
Mai martaba yace "ku sake shawara dai..."
Roshan yace "Uncle inason jin daga bakinka duk yanda kace hakan za'ayi..."
Mai martaba yace "sai dai a samu iyayensa ayi magana cikin hankali idan su bazasu musulunta ba to subar yaronsu ya musulunta inyaso sai a Aura masa yarinyar..."
Roshan jinjina kai yayi sannan yace "tabbb! Uncle ai gwara tawa shawarar zai iya yuwa, amma nasan iyayen Mohandas yanda suke riƙe da ƙarfin Addininsu bazasu taɓa yadda ba wallahi...."
Mai martaba ne ya buɗe baki zaiyi magana yaji wayarsa tana ringing,
Dubawa yayi yaga number Abbah ne, Saida ya kalli Roshan tukun yace "shine..."
Zaro ido Roshan yayi ya haɗe hannayensa biyu alamar roƙo kar Mai martaba ya gayawa Abbah halinda ake ciki,
Mai martaba ne yasa wayar a speaker yanda Roshan zaiji duk tattaunawar da zasuyi...
Mai martaba ne yayi sallama tareda faɗin "na gaida mazan pama..."
Abbah yace "yadai muna cikin waya ka katse ƙiran?..."
Mai martaba yace "wallahi naɗanji hayaniya ne shine naje dubowa meke faruwa..."
Abbah yace "okay! yakamata yaran nan su dawo gida yau saboda hidimar bikin da za'ayi yau sauran kwana huɗu..."
Mai martaba yace "yau kuma? sai dai gobe su taso da sassafe, saboda har da matan gidan gaba ɗaya zasu tafo..."
Abbah yace "TOH shikenam kaifah?..."
Mai martaba yace "a'a Ni sai ana gobe ɗaurin Aure zan taho,
Amma Roshan shi kaɗai za'a Aurar ne? mezai hana a haɗa da Razhdeen?..."
Abbah yace "kabar zancen Razhdeen shi da bai tsayar da kowa ba, ai baza'a Aura masa babu ba..."
Mai martaba yace "hakane amma maizai hana a haɗa shi da Ramlat ƙanwar Matata Maamie naga tana sonsa sosai..."
Abbah ne yace "shi ɗin yana sonta ne? In har yana sonta sai a haɗa Auren gaba ɗaya, idan kuma Razhdeen baya ra'ayinta TOH