Showing 12001 words to 15000 words out of 89400 words
da suke zazzaune a wurin, Razhdeen yana zaune a back seat eyes ɗinsa kawai yake ta wurgawa, cije lips ɗinsa yayi sannan yayi magana ciki-ciki yace "let's go..."
Jan motar driver yayi suka miƙi hanya, haka sauran motar ma suka bi bayan motar su Razhdeen,
mabaratan ganin motocin sojoji ne yasa babu wacce tayi motsin tashi balle suzo yin Bara, sai gani sukayi wani soja ya dirƙo daga kan mota ya nufi yanda suke fuska ba annuri ga bindiga a rataye a kafaɗa,
ko wacce jikinta ne ya fara kakkarwa ganin sojan yayo kansu, tsayawa yayi ya zuge jakar hannunsa sannan ya Ciro wasu maƙudan kuɗaɗe duk ya rarraba musu, lokaci guda suka fara washe hakwara sai faman zabga masa godiya suke tare da Addu'o'i, ko amsa musu baiyi ba ya juya yaje ya shiga cikin motar daya rage iya shi kaɗai ne a wurin,
yana shiga kamar walƙiya suka bar wurin, daman Razhdeen ne yasa a raba musu ta hanyar tura musu saƙo ta waya....
Isar su keda wuya duk falon an hallaru ana jiran shugowar Uncle Deen, Ummy gaba ɗaya ta kasa zama tsabar farin ciki da zumuɗin ganin Uncle Deen, tayi matuƙar farin ciki sosai da Abbah ya dawo dashi cikin Ahali da temakon Aunty Yolash wacce take zaune itama a two seater sai faman pressing phone ɗinta take,
Pinky da Rukky suma suna zaune a five seater Rukky ce take kwance kanta a saman cinyar Pinky tana ɗan lumshe ido kamar mai jin bacci, a yayinda Pinky take ta danna wayar hannunta alamar charting take, duk abubuwan da ke faruwa a gidan tana sanarwa mommy wato Hajia Kilishi, yanzu ma charting take da ita...
Baiwar ALLAH kuma tana can cikin ɗakinta a kwance saman katafaren gadonta kamar mai yin Bacci, sai dai ba baccin take ba, amma idonta a lumshe suke,
Ga wata ƙatuwar waya ƙiran iPhone 15S, ƙira ake tayi ba ƙaƙƙautawa daga wannan ƙiran ya yanke sai wani ƙiran ya sake shugowa anyi ƙiran yafi sau 15 a lokaci guda kuma duk mutum ɗaya ne mai wannan ƙiran,
Baiwar ALLAH tana ji amma taƙi ɗaukar ƙiran domin ta rigada tasan cewar Roshan ne mai wannan damun,
wani ƙiran ne ya sake shugowa Once takai ƙwayar eyes ɗinta kan screen ɗin wayar ganin ROSH a rubuce kan screen yasa taja dogon tsuka tareda tashi zaune tana hararar wayar cikin ɓacin rai ta soma magana tana faɗin
"Mttssww! aikin banza wai dan saboda kai ka sayi wayar shine zaka takura Ni? I hate dis nonsense wallahi, banason mutum mai nacin tsiya, takurawarka ne yasa nake ƙara tsanarka wallahi Roshan....."
a fizge tasa hannu ta ɗauki wayar ganin bazai daina ƙiran ba,
ɗaukar ƙiran tayi ta kara a kunne tayi shuru tana hararar gefe, magana yake ta cikin wayar yana ambaton sunanta "Ammata! Hello Ammata!! Assalamu alaikum bakya jina ne? Ammata nah Dan ALLAH kiyi magana mana...."
ɗan tsuka tayi acan ƙasin harshenta tace "wai dan ALLAH meyasa kake son takura mun ne? ko dan saboda kai ka ban wayar shine zaka rinƙa takura mun, Ni gaskiya bana son irin haka..."
ta ƙarisa maganar tareda tura ɗan lips ɗinta kamar wacce take gabansa,
daga ɓangarensa sauƙe nannauyar ajiyar zuciya yayi murya ciki-ciki yace "oh my God, Ammata banida burin daya wuce na rinƙa ganin farin cikin ki akoda yaushe, inasonki wallahi l, ina ƙaunarki har cikin zuciyata, tinda Allah yasa nabar Nigeria ban ji muryarki ba sai yau, ina kan ƙiranki amma bakya ɗauka mun ƙira why?..."
buɗar baki tayi zatayi magana saiga ƴaR tinny ta kutso kai da gudu tare da faɗin "Aunty Dota Ankuy Deen ya dawo..."
tana iddasa maganar ta juya ta fice,
Ita kuwa Baiwar ALLAH ido ta zazzaro waje cike da mamaki take bin bakin ƙofar da kallo, lokaci guda wani irin farin ciki ne ya wanzu mata,
Roshan yanata magana amma shuru ko jinsa bata yi, bata san lokacin da tayi wurgi da wayar ba ta miƙe tare da sauƙar da ƙafarta ƙasin carpet da gudu tayi hanyar bakin ƙofa itama, zata je taga abinda idanuwanta suka daɗe suna muradin gani,
Da gudun gaske ta faɗa Falo, lokaci guda ta danna burki ganin kowa ya hallaru, duk juyowa sukayi suna kallonta ganin kamar wacce aka hankaɗota, itama tsayawa tayi tana binsu da kallo, idanunta ne suka sauƙa akan kayan lefen da aka bazasu a tsakiyar Falo, wasu irin tsararrun akwatina ne guda sha biyu pink colours, ga kayan cikin su kansu basu san adadin kayan lefen ba tsabar yawansu, ga takalma kala-kala kamar wanda za'a buɗe shagon kayayyaki, kayan bacci suma sunfi hamsin, kayan makeup ba'a magana, gyalulluka da hijabai abun ba'a cewa komai, komai da komai akwai su,
ganin kayayyakin yasa gabanta yanke wa domin tasan duk nata ne, a hankali ta ɗago da shanyayyun idanuwanta ta sauƙe su akan Razhdeen wanda shima yana zaune a kujerar da yake facing ɗinta, idonsa akan wayarsa yanata pressing, jikinsa ne ya bashi cewa ana kallonsa, kamar bazai ɗago ba shima a hankali ya ɗago da kansa tare da wurga ƙwayar eyes ɗinsa kan Baiwar ALLAH wacce take tsaye ta ƙura masa ido ko ƙibtawa babu,
shima kallonta ya shiga yi duk suka fara kallon juna, abinda ya fara tunawa shine wankan da yayi mata da kasancewar da sukayi a ɗaki ɗaya..."
Itama dogon tunani ta faɗa abinda take tunowa shine lokacin da tayi ciwon ciki a ɗakinsa da kula da ita da yayi, har wankan da yayi mata,
Kowa da abinda yake tunawa acikin ransa...
Ƴar tinny ce tayo kan Razhdeen tare da faɗawa saman cinyarsa tana faɗin "Ankui Deen wai yauce Mommy nah jata dawo ne?..."
hankalinsa ne ya karkato kan Ƴar tinny murya ciki-ciki yace "Mamana kiyi haƙuri zata dawo coming soon kinji Koh..."
tace "Ni a dawo mun da ita, kullum idan nace Abbah ya dawo da ita sai yace zai dake Ni ...". kamar zata fashe da kuka ta ƙarasa maganar cikin lankwasa murya...
Shima kansa ta bashi tausayi shafar sumar kanta kawai yayi,
Abbah kallon Baiwar ALLAH yayi yace "Dota ya kike tsaye ne, ki ƙaraso mana..."
haka take jan ƙafa ta ƙaraso cikin falon ta zauna itama a cikin ɗaya daga jerukan kujerun,
Aunty Yolash murmushi tasau tana kallon Baiwar ALLAH tace "Ammatan Roshan an kusan zama Amarya, duk wannan kayayyakin kine, saboda haka ki kwantar da hankalinki Roshan shine mijin da yafi dacewa da rayuwarki, mutum ne mai kyakkyawar zuciya, kuma yana matuƙar ƙaunarki tinda kullum sai ya ƙirani ya bani labarinki, kinsan Roshan in har yana son abu toh haukacewa yake, don haka ki riƙe mana ɗan Amanar mu hannu bibbiyu, idan muka ganshi cikin ƙunci to kece sila, haka kuma idan muka ganshi cikin walwala da farin ciki nan ma kece sila, Ƴar Amana da Ɗan Amana ku kula mana da kan ku dan ALLAH, yanzu dai sauran mana kwana uku ɗaurin Aure, Insha ALLAHU daga gobe zamu fara ganin manya-manyan baƙi daga ƙasashen waje da garurruwa, sannan ƴan uwan mahaifiyarsu daga Saudiyya suma suna nan tafe...."
Baiwar ALLAH hawaye ne kawai yake faman gangaro mata, abu biyu ne suka tada mata da hankali na farko bata son Auren nan sannan kuma taji an ambaci sunan Ƴar Amana, sai kawai taji zuciyarta na bugun uku-uku, maganar zuci ta shiga yi tana faɗin "yanzu a wani hali kike ciki Ƴar uwata, shin kin mutu ne ko kina raye? a cikin haske kike ko a cikin duhu? wayyo Allah Ƴar Amana ina kewarki...."
bata san lokacin da kuka ya kuɓuto mata ba, kuka take na gaske kanta na kallon ƙasi...
Aunty Yolash tana cikin jawabi taji ƙarar kukan Baiwar ALLAH nan ta dakata da maganar tana kallonta,
Shima Abbah hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba, murya a harharɗe yake faɗin "lafiya kuwa Dota? meya sameki kike kukan? shin bakya son Auren ne? ki gaya mun dan ALLAH yanzu a dakatar..."
kowa ya kasa kunne yana son jin abinda Baiwar ALLAH zata ce,
Aunty Yolash ce itama ta tashi ta nufi wurin da take zaune ta zauna tare da rungimarta tace "Dota kiyi haƙuri ki sanar mana abinda yake ranki, Bama son muyi miki dole domin ke ɗin Amana ce a gare mu, shin bakya son Auren ne?..."
Razhdeen idonsa a kanta ya rasa gane meye dalilin kukanta,
Ummy tana zaune kai a ƙasi ƙirjinta na bugun uku-uku tana addu'ar kar Baiwar ALLAH tace bata son Auren, domin Roshan zai iya shiga mungun mawuyancin hali, tsoronta kar ciwon zuciyarsa ta tashi..."
Rukky tana kwance kan cinyar Pinky domin ba lafiya ne gareta ba tana fama da zazzaɓi, murya na kakkarwa alamar jin sanyi tace "Aunty daman fah idan Amarya anayi mata nasiha kuka take, kowace Amarya ma hakane..."
Aunty Yolash tace "a'ah muna son jin daga bakinta ne domin bamu san abinda ke ranta ba, kar mu toye mata hakki..."
Pinky ɗan tsuka taja tare da kawar da fuska gefe daman ita sam bata ƙaunar Auren nan domin a duniyar nan babu mace data fi tsana kamar Baiwar ALLAH, a cewar ta ita tayi sanadiyar rabasu da mahaifiyarsu..."
Aunty Yolash ce ta ƙara tambayarta cewar "Dota bakya son Auren ne?..."
Girgiza kai Baiwar ALLAH tayi alamar a'ah...
Aunty Yolash tace "to meyasa kike kuka?..."
Baiwar ALLAH tace "babu komai kawai lokaci guda naji kukan ban san meyasa ba...."
Aunty Yolash tace "Ayyah sorry Dota saboda zaki kasance cikin Amarci ne shiyasa, kuma son samu ace iyayenki suma suga ranar Auren ki...."
kafin Aunty Yolash ta ƙarasa maganar taji Baiwar ALLAH ta ƙara fashewa da wani sabon kukan,
rungumarta tayi tana rarrashinta daƙyar ta iya dakatar da kukan..."
Saida Abbah yayi mata nasiha sosai mai ratsa jiki, ya rarrasheta kafin nan zuciyarta tayi sanyi,
Saida suka kammala tattaunawarsu tsab akan batun Auren kafin nan Abbah ya dawo kan Razhdeen,
ya kalle shi sannan yace Razhdeen!.."
Uncle Deen kallon Abbah yayi jin ya ambaci sunansa, shi gaba ɗaya hankalinsa akan Ƴar Amana yake, tunaninta kawai yake sai fuskarta yana masa gizo...
Abbah ya cigaba da cewa "Yakamata duk wannan shirmen da kake ka dena shi Razhdeen, faɗan da nake maka bawai bana sonka bane, bazan taɓa iya cire hannuna daga kanka ba Razhdeen, miskilancinka yayi yawa ka rage koda bazaka iya cire wa gaba ɗaya ba, girman kanka yayi yawa komai naka yayi yawa haba Razhdeen,
wani irin zuciya ne Allah yayi maka, acikin sojojin duniya gaba ɗaya da wuya a samu mai kalar ɗabi'unka na rashin jin magana, amma duk da haka ina mai ƙara godewa Allah yasa kai ba manemin mata bane sannan kai bame shaye-shaye bane, kai ba ɓarawo bane, duk waɗannan Bad behavior zan shaidi ƴaƴana babu maiyinsu, sai rashin jin magana,
Please Major General Razhdeen be careful about all the things that is make me unhappiness..."
Razhdeen idonsa akan carpet ko ɗago da kai baiyi ba, motsi ya fara yi da lips ɗinsa a hankali yake furta "sorry Dad I'll try to make you happy but my behavior's can never change..."
Aunty Yolash kawar da kai gefe tayi tana dariya ciki-ciki domin Razhdeen ba ƙaramin dariya ya bata ba,
daɗinta dashi baya ɓoye maitarsa, koda mutum bazaiji daɗi ba to dole saiya gaya masa abinda ke ransa, baya tsoro kuma baya fargaban abinda zaije ya dawo..."
Abbah cikin kalar tausayi yace "why Razhdeen?..."
Yace "because I don't have a Bad character's, kawai raini ne bana so sannan banason wulaƙanci da rashin tarbiyya,
har yanzu baku fahimci yanda tsarin rayuwata take ba, inada zuciyar da bazan iya ɗaukar duk wani shirme ba, lokaci guda zan ɗauki hukunci akan mutum shiyasa kuke ganin rashin haƙuri na..."
Abbah yace "TOH shi Roshan daka ɗauki hukunci akansa fa? shi da ya gama fahimtar halinka kuma yake kiyaye ɓacin ranka..."
Razhdeen kallon Abbah yayi sannan yace "why tin lokacin baku tambayeni laifin da yayi mun ba sai yanzu? Dad you known banason yawan magana sosai, my headache..."
Abbah yace "it's okay nasan Kanada matsalar nan,
abinda ya wuce ya rigada ya wuce sai dai bama fatan hakan ya sake faruwa, kayi haƙuri da wannan ciwon kan nakan magana nakeso nayi dakai, dole yau zaka ɗan motsa yin magana kafin kaje kaɗan huta Koh..."
haɗe gira yayi tare da faɗin "okay let me go and sleep before..." ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin miƙewa.
Abbah yayi saurin dakatar dashi yana faɗin "Noooo ka saurara kaji kalar tattaunawar da zamuyi mana..."