Showing 63001 words to 66000 words out of 89400 words
Bayan sun koma Nigeria, Mai martaba ne ya shiga gidan Chief ɗaya daga cikin sojoji wani ya kaishi har ciki da mota, ita kuma Aunty Yolash tana daga waje a cikin mota taƙi shiga gidan domin ba ƙaramin ɓata mata rai Abbah yayi ba,
Mai martaba ne yake zaune a falon Abbah shima Abbah ɗin yana nan anyi dace yau bai fita ba, bayan sun gaisa ne Mai martaba ya ce "a gaggauce nazo domin a yau nake son komawa Jidder..."
Abbah cikin nuna farin ciki ya ce "Tinda kuwa hakane nasan kaima akwai abinda ya kawo ka..."
Mai martaba ya ce "sosai ma kuwa shiyasa ka ganni nayi zuwan bazata ai..."
Murmushi Abbah yayi sannan ya ce "Yolash taje ƙasar da kake ko? nasan ƙarata takai kaima kazo kayi mun maganar wancan matar da yanzu ji nake kamar na hallakata ko ....?
Mai martaba ya ce "duk abinda haƙuri bai baka ba rashin sa ba yanda za'ayi ya baka, duk abinda yayi tsanani a rayuwa haƙuri shine maganinsa, kuma ita gaskiya ba'a faɗa da ita, bai kamata ace duk wanda zai gaya maka gaskiya kayi faɗa da shi ba, kuma duk wanda zai yi maka nasiha akan abinda zai fissheka to kayi haƙurin zama dashi koda baka jin daɗin zama da shi ɗin, Ni nazo ne akan na baka shawarwarin da zai taimake ka a rayuwa a mazannina na ɗan uwanka bawai don na kai bane, ita wannan matar da kake gani tayi abubuwa da dama a rayuwa na rashin tunani amma yanzu da rayuwa ta sauyata mai ya kamata ayi mata? sai a yafe mata sannan a cigaba da zama da ita tinda ta gyara kurkuren da ta aikata..."
Bai ƙarasa iddasa maganarsa ba Abbah ya dakatar da shi da cewa "shin na tambaye ka mana...?"
Mai martaba ya ce "inajinka Chief.."
Abbah ya ce "shin ba'a mutuwar Aure ne?..."
Mai martaba ya ce "Anayi mana amma a dole badan ana so ba..."
Abbah ya ce "to kuwa tinda na rabu da ita har abada bazan ƙara kallon yanda take ba balle tayi tunanin zan maido ta, kuma wallahi zanje na sameta ta fita shirgi na, ta daina bibiya mun ƴan uwa idan ba haka ba zan yi mata abinda batayi tunani ba, kuma da kuke cewa saboda ƴaƴanta na dawo da ita shin a tsirara kuka ga ƴaƴanta? ko kuma barinsu nayi da yunwa? to ko su yaran su ɗauka cewa uwarsu ta mutu domin baza su ƙara kusantar yanda take ba kada ta shafa musu baƙin hali da dabbanci, na rantse da sarkin dake busa mun numfashi duk wanda ya ƙara mun maganar na dawo da Kilishi wallahi sai nayi shara'a da shi domin bana son harkar shishshigi, kuma ko kaine idan na sake jin kayi mun maganar na dawo da ita wallahi zan yanke alaƙata da kai har abada..."
Mai martaba cike da mamaki yake kallon Abbah ya ce "Subhanallahi abun bai kai ga haka ba, Allah ya huci zuciyarka Ni zan koma yanda na fito, na barka lafiya..."
Mai martaba fita yayi yana fita ya tarar da Ummy a tsugune sai faman kuka take, tsugunawa yayi tare da ɗago kanta yana faɗin "Uwar masu gida ki kwantar da hankalin ki insha Allahu mamanki zata dawo..."
Ta bayansu Abba ne ya fito yana faɗin "sai dai su haɗu a lahira domin ita da mahaifiyarta sai a mafarki, duk photunan Kilishi nasa an fitar mun da su a cikin gidan nan, a duniyar nan babu macen da ta sa hannu ta mareni sai ita na tsane ta..."
Ummy cikin ɓacin rai ta taso tana kuka ta ce "wallahi Abbah banda sai a lahira kam, mahaifiyar mu tana raye amma ka haramta mana ganinta? duk ƙiyayya ai bazai sa ka raba mu da ita ba, idan kai baka sonta ai mu muna sonta tinda har ta shayar damu ruwan nonon jikinta..."
Abbah a fusace yayo kanta zai dake ta Mai martaba yayi saurin riƙo shi yana faɗin "a'a banda dukan uwar masu gida domin daga baya zakayi nadama..."
Ummy da gudu ta koma cikin babban falon gidan tana kuka, Ammy tayi rarrashin duniyan nan amma taƙi daina wa..
Abbah a fusace ya shugo yana balbala masifa ya kalli yanda Ummy take ya ce "ina kema kin koyi rashin kunya irin na yayunki dana uwarki ko? to kar ma ki fara domin karya ki zanyi a cikin gidan nan, ke har nawa kike? Uwar ki ce bazaki ƙara sakata a idonki ba na gaya miki..."
Bayan ya gama surutansa ya haura part ɗinsa, Ammy ce ta cigaba da rarrashinta...
Mai martaba bayan ya fita motar Aunty Yolash ya shiga rai a ɓace, Aunty Yolash murmushi tayi domin tasan matsalar shiyasa bata shiga ciki ba domin zata iya yiwa Abbah rashin kunya..
Airport suka nufa anan ta sauƙe Mai martaba kafin ya shiga jirgi ya kalli Aunty Yolash ya ce "zaku daɗe baku ganni anan Nigeria ba..."
yana kaiwa ya shige jirgi, ita kuma Aunty Yolash wuce wa tayi kai tsaye Suleja taje daga nan ta wuce Bauchi...
★★★★★★
Bayan Aunty Yolash ta samu Hajiya Kilishi a garin Suleja zama sukayi suka tattauna akan maganar Abbah,
Aunty Yolash kamar zatayi kuka ta ce "Hajiya Kilishi shawaran da zan baki shine ki cire Abban yara a ranki domin bazai taɓa mai dake gidansa ba, ki duba kika irin wulaƙanci da yayi mana Ni da mai martaba abun ba daɗi, kuma ya rantse cewa bazai taɓa kusantar yanda kike ba to kuwa kinga babu amfanin kiyi ta bibiyansa yana wulaƙanta ki, shi kaɗai ne namiji? ko shi ɗin ɗan gwal ne, to bari kiji inda nice wallahi ko ɗan gwal ne bazan kalli yanda yake ba balle ya samu damar wulaƙanta Ni, Ni mamaki ma kike bani har kina bibiyansa kina roƙonsa cab aini namiji baka isa ka samu wannan damar ba, bazan taɓa roƙon namiji abu shi kuma ya tsaya yana mun Rashin kunya ba.....
asmeetah writer ✍️
🤦♀️ *MAƘIYI_NAH*🤦♀️
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء محمد أولا 🥳
Asmeetah (giaɗe writer)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
STEP TWO
👇
*41_ TO_45*
Aunty Yolash ta cigaba da cewa "duk da nasan ke kike da laifi Amma ai yanzu kin shiryu kuma kinyi alƙawarin bazaki ƙara maimaita kuskuren ba, ya kamata Chief ya dubi halin da kike ciki yayi haƙuri amma tinda bashida yafiya sai ki sharar da shi, dan Allah Kilishi ki zamo mai kamun kai, ki daina bibiyansa haka, ni duk abinda kike so ki ƙira wayata zaki same ni zan dauke miki duk ɗawainiyar ki kar ki damu, ki cigaba da addu'a komai mai wucewa ne, ki kwantar da hankalinki, ni yanzu zan koma bauchi domin ayyukana na bari nazo gurin da aka wulakanta ni, na tafi saina ji ki..."
Daga nan Aunty Yolash ta koma Bauchi, ita kuwa Hajiya Kilishi a ranar ko rintsawa bata yi tsabar kuka, ba ƙaramin shiga damuwa tayi ba, ga yanzu ba halin ganin ƴaƴanta balle taji sanyi a ranta, idan taje yanda suke kuma Sojoji hanata shiga ciki suke sakamakon bin umarnin Abbah, ya sanar musu cewa idan suka ƙara barin Kilishi ta shiga masa gida duk saiya hora su...
Ummy uwar masu gida itama ba ƙaramin shiga damuwa tayi ba na rashin ganin mahaifiyar ta tsawon shekara guda, ta samu Abbah akan tana son zuwa yanda take amma yaƙi barin ta, hakan yasa yanzu ko zuwa wurin da Abbah yake bata yi kullum a cikin kuke take, ga yanzu kwana biyun nan ta ƙi saka komai a cikin ta haka take zaune ba ci ba sha, ganin halin da Ummy take ciki ne yasa itama ƴar tinny ciki damuwa, yanzu a ɗakin Ummy take bata zuwa wurin Ammy ma balle shi kan shi Abbah, duk sun ƙaurace masa,
Ammy ta yi magana wa Abbah yabar yaran su je suga mahaifiyar su amma Abbah ya dakatar da ita akan cewa babu ruwanta kada ta ƙara shiga cikin maganar,
Roshan ganin halin da Ummy da ƴar tinny suke shima ya samu Abbah, yana faɗin "Abbah ka bari na kaisu idan sun gana da juna saina dawo da su..."
Nan ma Abbah ya ce "bai yarda ba sai dai su mutu..."
Kowa har yayi ya gaji.
Wata rana Ummy ta fito falo kana ganinta kasan bata da lafiya ga duk ta rame tsabar jikinta babu ƙwari haka ta yanki jiki ta faɗi sumammiya, Ammy dake shirya abinci akan dinning tana hangota ta tafo da gudu tana ƙiran sunanta, dai dai lokacin da Abbah ya shugo, ganin Uwar masu gida a cikin wannan halin yasa yayo kanta a ruɗe, haka yasa hannu ya ɗago ta yayi waje da ita sai asibiti...
Ummy Saida ta sha ledar jini da ruwa domin ba ƙaramin wahala take sha ba, sai da suka kwana tukun ta farfaɗo tana kuka tare da faɗin "ni ku kaini wurin mommy, nasan tana cikin mawuyancin halin, bana so na mutu ban ganta ba dan Allah, mommy na an rabani da ita kenan? ba zan taɓa yafe wa duk wanda ya rabani da Mahaifiyata ba wallahi...."
tana kaiwa ƙarshe ta fashe da matsanancin kuka...
Abbah yana tsaye yana jin duk maganganun da take faɗi ga kuma Ammy a zaune a gefen gadon da take sai Baiwar ALLAH itama tazo duba ta.
Suna cikin wannan halin sai ga Doctor ya shugo Abbah ne ya ce "shin za'a iya sallame mu yanzu?..."
Doctor ya ce "eh duk abubuwan da ya kamata ayi mata munyi yanzu komai normal..."
Abbah ya ce "good, kinga uwar masu gida tashi muje ki shirya na kai ku wurin uwatta kun tinda kun fi sonta akan Ni..."
ya kalli Ammy ya ce "ina Auta ta?..."
Ammy ta ce "ta fita da Roshan ina tunanin gida suka nufa..."
Ya ce "Okay zan kai su amma bazan bar yarana a hannunta ba domin da mutuncin su..."
Ammy ta ce "kenam kana nufin kace ita uwar tasun batada mutuncin ne?..."
Abbah ya ce "ko kaɗan babu..."
Ammy shuru tayi tana gudun kar ta fusata shi domin yanzun ma a dole zai kai su ba dan yana so ba...
Haka Abbah ya riƙo hannun Ummy ya ɗago da ita duk suka tashi suka fice,
Bayan sun koma gida duk shirya wa sukayi har ƴar tinny Ammy ta shiryata, sai a lokacin hankalin Ummy ya dawo jikinta domin a halin yanzu tana muradin sanya mahaifiyar ta a idonta, kuma taji labarin tana shan wahalar rayuwa kowa ya guje ta..
Abbah shi da kansa zai kai su har garin Suleja...
★★★★★★★
Baiwar ALLAH ce a ɗakin Roshan tana gyara masa gadon kwanciyar sa, yanzu kwana biyun nan ita take masa komai, kullum sai ta je part ɗinsa ta gyara tare da wanke masa bathroom ta feffeshe ko ina da turare, sannan tayi girki ta shirya su akan dinning su ci tare, a baya kuwa sai dai ta ɗauki nata ta shiga room ɗinta ta ci acan shi kuma ya zauna a dinning ya ci shi kaɗai, yanzu kuwa zama take su ci tare,
Abun ba ƙaramin mamaki yake bashi ba, a ransa yake faɗin "shin mai take nufi ne?..."
A yanzun ma ta gama gyara masa gado ta juya zata fita kwatsam ta gànshi yana tsaye a bakin ƙofa ya goya hannayensa saman ƙirjinsa yana mata wani irin kallo na rashin fahimta,
Itama tsaya kallonsa take daga bisani ya ƙarasa shugo wa ya zauna a bakin gado sannan ya kalle ta ya ce "ki zauna mana..."
Itama taje ta zauna a wurin da ya nuna mata a kusa da shi,
zama tayi jiki a sanyaye..
Roshan idonsa na kallon gabansa ya ce "naga kwana biyun nan kin canza shin meye a cikin zuciyar ki? tsawon shekara muna zaune ko da wasa baki taɓa zuwa part ɗina ba amma yanzu a kwana biyun nan meyasa? kinsan dole zan yi tunanin wani abu a raina, domin duk wanda ya ce baya sonka da safe babu wanda za'ayi da daddare ya komo yace yana sonka wannan ƙarya ne, saboda haka tin a baya kin nuna bakya sona ɗan uwana kike so kuma nasan har yanzu hakane a cikin zuciyar ki, kiyi haƙuri nasan na cutar da ke dana riƙe ki har zuwa tsawon wannan lokacin kinyi haƙurin zama dani a gida ɗaya, inda ace tin farko baki nuna cewa zaki zauna dani ba da yanzu kinada yaron ki jinin ɗan uwana Razhdeen domin a lokacin ya nuna ya amince kika kwabsa, gashi muna zaune zaman ba daɗi Ni ba ɗa kema haka ko kusantar junan mu bamu taɓa yi ba wai hakan muna zaman Aure,
Insha Allahu sauran ɗan watanni kaɗan Razhdeen ya dawo da zaran ya dawo zan damƙa masa ke domin yanzu haka takardar sakin ki na nan a ajiye lokaci kawai nake jira...."
ya ƙarasa maganar yana sharar hawayen da ya zubo masa,
Itama Baiwar ALLAH kukan take jin maganganun da yake faɗa mata kuma alhalin yanzu ba haka bane a cikin zuciyarta,
Cigaba da cewa yayi "zan roƙe ki wata alfarma shin zaki iya mun?..."
Yayi maganar yana kallonta, itama kallonsa take tare da ɗaga masa kai,
Jinjina kai yayi sannan ya ce "inaso ki daina shugo mun room, ki tsaya a yanda kike a baya, girki ne idan kika yi zan ci idan kina so zamu zauna a dinning muci kamar yanda muke yanzu, amma fake wa wuri ɗaya ne banaso domin nasan kaina banida juriya, kina cuta na sosai idan naga mun fake Ni kuma bazan iya aikata komai dake ba saboda nasan wata rana ke matar twins ɗina ne, bana so ya karɓi saura na, nafi so ya ɓare ki sabuwa a leda zan fi jin daɗin haka sosai, inaso idan na kusanci mace to ya