Showing 75001 words to 78000 words out of 89400 words

Chapter 26 - MY ENEMY BOOK 2 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

2530

"ai daman nace kar ki sanar wa Abbah ki kayi kunnen uwar shegu..."

Abbah ne ya zaro ƙaramar bindigar sa daga aljihu tare da kunna kunamar bindigar ya sai ta su.

Pinky da Rukky gaba ɗayan su baya suka ja suna zazzaro ido waje a tsorace,
Abbah ya ce "ko ku sanar mun gaskiya ko kuma yanzu na aika ku lahira kuje can ku cigaba da shirmen ku domin ba'a gabana zaku yi wannan ta'addanci ba..."

Rukky kamar zatayi kuka ta ce "Abbah wallahi zan faɗi gaskiya..."

Abbah ya ce "to inajinku..."

Pinky ta ce "Abbah ai baka faɗi maganar da zamu faɗi gaskiyar ba..."

Abbah ya ce "ku faɗa mun gaskiya magana ɗaya shin kuna maɗigo? wallahi idan naji ƙarya daga bakin ɗayan ku saina harbe ta..."

Rukky ta dafe ƙirjinta tare da faɗin "wallahi tallahi na rantse da mahalicci na bamu taɓa aikata irin haka ba tinda muka zo duniya, maganar gaskiya kenam..."

Itama Pinky ta ce "Abbah me zai sa mu aikata wannan abun, mun san dai sai anyi Aure akayi..."

Abbah ya ce "maɗigo ɗin dan ubanki?..."

Da sauri ta girgiza kai cikin nuna tsoro..

Suna cikin wannan halin sai ga Ammy ta shugo tana murmushi tazo har yanda suke ta ɗago su idonta akan Abbah ta ce "kayi haƙuri Abban yara irin wannan a hankali ake binsa, ka ciro bindiga ai tsoro ma bazai barsu su faɗi gaskiyar ba, Ni zan je da su zamu yi magana ta fahimta sannan ayi musu nasiha a ƙara tunatar da su abubuwan da addinin musulunci ya ƙunsa..."

Abbah cikin ɓacin rai ya kawar da kai ko sauraronsu bai yi ba, haka Ammy ta fita da su....


Garin Suleja

Ummy da Ƴar tinny har sun murmure na ɗaukin ganin mahaifiyar su, suna zaune cikin ƙoshin lafiya, ga Aunty Yolash kusan kullum sai tayi musu aike domin ba ƙaramin farin ciki tayi ba jin yara biyu sun dawo wurin mahaifiyar su ko ba komai zasu ɗauke mata kewa kuma zata rage tunanin Abbah....


Bayan wasu kwanaki Pinky da Rukky gaba ɗaya basa jin daɗin zaman gidan domin gidan ya yi shuru kamar ba mutane ga rashin ganin ƴan uwansu ko ba komai zasu ji daɗin zama idan suna kusa da ƴan uwan, Minal ta tafi ga Ummy da ƴar tinny suma sun gudu wurin Maman su, ga Baiwar ALLAH basa shiri balle suje part ɗinta, su kuma baza su iya zama da Ammy suyi hira ba hakan yasa suka yanke shawara suma zasu gudu wurin Mamansu, gashi graduation ɗin da zasu yi ba'ayi ba Abbah ya yaudare su a cewar su..

Ganin ba wata mafita saboda ta ko ina a cikin tsaro yake, shawara ɗaya suka yanke cewa zasu sanar wa Abbah cewa zasu kai wankin kayansu tinda yaƙi kai su wurin Maman nasun.

Kamar yanda suka tsara haka suka samu Abbah cewar zasu kai kayan su gidan wacce take musu wanki,
Abbah ya ce "meyasa ita ɗin bazata zo tayi anan gidan ba sai an kai mata, bana so kayan ku suna fita can wani wuri..."

Pinky ta ce "Abbah wai bata jin daɗin jikinta ne shiyasa zamu kai mata duk sanda ta miƙe zuwa gobe ko jibi sai tayi mana sannan ta goge sai ta kawo mana..."

Abbah ya ce "to kuje Security ɗaya ya kai ku sai ku dawo da wuri..."

Suka amsa sannan suka fita daga falon sa..

Already sun ciccire kayansu daga akwati sun maida su cikin babbar jaka wuri ɗaya yanda baza'a gano su ba.

Security ne ya ɗauke a mota ya kai su har ƙofar gidan mai musu wanki, a ƙofar gidan yayi parking da mota su kuma suka shige gidan, ba tare da matar gidan tasan da zuwan su ba haka suka bi wata ɓoyayyar hanya dake cikin gidan suka fita ta can suka gudu...

Security dai waran awan sa uku yana tsaye jiran fitowar su amma shuru, ganin zaman yayi yawa yasa ya fara kwaɗa sallama dake matar tana da miji...

Matar ce ta fito tana sanye da hijab ɗinta har ƙasi ganin ɗaya daga cikin security gidan Chief ne yasa ta durƙusawa har ƙasi tana gaishe shi, ya amsa mata a mutunce sannan ya ce "wai waɗannan yaran sun manta dani a waje ne?..."

Matar ta ce "wasu yaran?.."

Security ya ce "ha'a su Pinky yaran Chief tin ɗazu na kawo su da jakar kayan wankin su...".

Matar ta ce "ai ni basa kawo mun wanki sai dai naje har gida nayi musu saboda tsaron da Chief yake basu, amma ya akayi yau ɗin aka barsu su kawo wanki, kuma Ni ina gidan banji motsin kowa ba innalillahi..."

Security ya ce "na shiga uku yau sun jawo mun tashin hankali..."

Matar ta ce "amma tin yaushe suka shiga?..."

Security ya ce "yanzu waran awa huɗu fa duk ina tsaye zaman jiran su..."

Suna cikin wannan halin sai ga mijinta ya dawo nan ta kwashe ta sanar masa halin da ake ciki,
Mijin ya sanar wa security cewa "ka shigo Mu dudduba ciki ko sun ɓuya ne, domin akwai matsala in ka koma ba tare da yaran nan ba..."

Haka suka shiga ko ina sai da suka dudduba amma ba motsin su, sai daga baya aka gano cewa ta ƙofar baya suka fice ganin wani ɗan ƙaramin ƙofa a buɗe.

Security hannu ya ɗora a kai tare da faɗin "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un yau mai zan ce wa Chief..."

Matar ma haka take ta salati tana jero Addu'o'i domin abun ba ƙaramin bata mamaki yayi ba, tana tunanin taya suka san da wannan ƙofa alhalin basu taɓa ganin wurin ba...

Mijin matar ne ya dafa kafaɗarsa Security sannan ya ce "ka kwantar da hankalin ka kaje ka sanar masa yanda al'amarin ya faru, ai ba laifinka bane tinda ba daga hannunka suka fece ba, idan suka dawo su kuma zasu yi bayanin yanda suka je...."

Security ya ce "shikenam ba damuwa amma ina neman alfarma ɗaya ina so na tafi daku domin ku zamo mun shaida..."

Suka ce ba damuwa haka suka shiga mota suka tafi...


★★★★★★


Pinky da Rukky kuwa har sun isa garin Suleja, sai da suka isa tukun suka nemi wayar Ummy domin Mommyn su ta chanza sim, Ummy tayi farin ciki sosai jin labarin su Pinky sun zo, haka Hajiya Kilishi ta rinƙa tunani a ranta cewa "anya da sanin Abban su suka zo? amma kuma akwai security mai kai su ko ina zai yi wuya su tafo ba tare da sanin kowa ba..." haka take wannan tunanin a ranta.

Bayan sun zo har suka shiga gidan da Ummy ta kotanta musu domin yanzu tasan duk wani lungu da saƙo na unguwar yanzu a free take...

Pinky da Rukky suna shiga gidan bayan sun je part ɗin da Mommyn su take suna ganin ta haka suka rufa da gudu suka rungume ta suna farin cikin ganin mahaifiyar su, sunyi matuƙar kewar juna sosai haka rayuwa ta dawo musu kamar sabuwa...

Abbah bayan yaji wannan mummunan labarin ya firgita sosai sannan zuciyarsa ta sosu matuƙa bayan yayi bincike ya gano cewa yaran guduwa suka yi wurin mahaifiyarsu can garin Suleja, Abbah kamar yayi hauka haka ya shiga ƙuncin rayuwa, haka ya yanke hukuncin cewa bazai taɓa zuwa yanda suke ba tunda sun zaɓi su rabu da shi....


★★★★★★★


Bayan wata guda da wasu kwanaki gaba ɗaya Abbah ya fita hayyacinsa damuwa ya yi masa yawa har sai da ya kwanta rashin lafiya hawan jininsa ya tashi, daga baya ya samu sauƙi sai kuma ya yanke hukuncin zuwa ya gano ƴaƴansa dake garin Suleja idan da hali yana son ɗauko su gaba ɗayansu.

Washe gari da sassafe ya tayar da tafiyarsa zuwa Suleja, misalin ƙarfe 12 zuwa 1 har ya isa, a ƙofar gidan yayi parking sannan ya yi magana a wani yaro yana ƙofar gidan yaron ya yi masa kwatancen yanda part ɗin hajiya kilishi yake, Abbah bai jira wani excuse ba haka ya kutsa ciki, yabi hanyar yanda part ɗin yake ba mistake yana tura ƙofar mashigar part kwatsam sai ya tarar da hajiya kilishi a gaban murhun gawayi ga tukunya akan murhun alamu sun nuna girki take yi ga ba kowa a tsakar gidan sai ita kaɗai.

Ummy uwar masu gida ta tafi ɗiban ruwa acan bakin fanfo amma a cikin gidan yake can wani ɓangare daban,
Pinky da Rukky kuma sun tafi bakin hanya suyo kifin da zasu yi miya da kayan vegetables, ita kuma Ƴar tinny tana cikin ɗaki tana ta shan baccin ta akan katifar da iya ita kaɗai ne a ɗakin sai ledar tsakar ɗaki,
wurin kwanciya duk yaran ne suke haɗuwa akan katifar su kwanta dake ƙatuwa ce katifar ita kuma Hajiya Kilishi shimfiɗi take a ƙasin ledar ɗakin ta kwanta haka suke inganta rayuwar su ba takuri da tsangwama...

Hajiya Kilishi tana zaune ɗaga kanta da zata yi kwatsam sai suka haɗa ido da Abbah, kamar a mafarki a gigice ta miƙe tsaye cike da fargaba da tsoro domin tasan akan yaran yazo, ga su Pinky sun sanar mata cewa gudowa suka yi, tayi dasu akan su koma amma fur sun ƙi da haka ta haƙura ta barsu,

Hajiya Kilishi idanuwanta ne suka cicciko da ƙwallah domin tasan duk laifin akanta zai ɗora wa kuma bata san da wani kalar wulaƙanci yazo ba..

Abbah cikin fushi da haɗe rai ya ce "ina kika kai mun yara?..."

Hajiya Kilishi ƙiƙƙina ta fara yi tana tunanin mai zata fara ce masa alhalin tasan yaran basa fita ko ina acan gidan su balle a aike su,

"Am amm Auta tana bacci a cikin ɗaki..."

Kafin ta iddasa maganar ya katse ta tare da darara mata tsawa yana faɗin "nace ina yarana suke? kada ki kuskura kice mun kin aike su domin ranki zai yi mungun ɓaci a yanzun nan, kin dai san bana aikan yaran, idan wani abu ya faru da yarana kiyi kuka da kanki sannan idan kika kuskura aka sace mun yara wallahi sai kin ƙwammace baki zo duniya ba..."

Hajiya Kilishi hawaye ta soma zubar wa domin tasan yaran aika suka tafi itama ba'a son ranta ba, su suka ƙi barinta tana fita aikan da kanta..

Abbah ya buɗe baki zai yi magana sai yaji sallama ta bayansa, da sauri ya waiwaya domin yasan ɗaya ne daga cikin su, ganin Uwar masu gida da bucket na ruwa a kanta yasa shi zare farin glass ɗin dake kan dararan idanuwan sa, cikin ɓacin rai ya furta "whattt?..."

Ummy ganin Abban su yasa ta wuce shi da sauri ta sauƙe bucket ɗin ruwan taje ta rungumo Mommynsu tana rarrashinta ganin yanda take ta zubar da hawaye..

Abbah ya ce "uwar masu gida shin baki ga Abbanki bane?.."

Ummy ta ce "sannu da zuwa Abbah, amma dan ALLAH kar kaga laifin Mommy domin mu muka zaɓi mu zauna da ita ba wai ita ce ta riƙe mu ba, kar ka sa mana ita kuka tana cikin farin ciki..."

Abbah ya ce "to meyasa ku ka zaɓi ku zauna da mahaifiyar ku akan Ni mahaifinku wanda zanfi baku kulawa sama da ita..."

Ummy ta ce "Abbah kayi haƙuri mahaifiyar mu ita ce sama da kai a wurin mu, domin Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama yana umartar mu da mu bi uwa, mu bi uwa! mu bi uwa!! mu bi uwa!!! har sai da ya maimaita sau uku kafin nan ya ce mu bi uba, don haka zamu fi samun farin ciki mai ɗorewa idan muna tare da mahaifiyar mu..."

Abbah ya ce "hakane uwar masu gida amma ki zauna a gaban mahaifinki shine mutuncinki da darajar ki wanda ko neman Auren ki akazo yi uwa bazata bayar ki ba dole sai da uba ko ƴan uwan mahaifin ki, ke da ƴan uwanki duk wani abun more rayuwa da kuɗi kuna samu daga wurina bana takura muku...."

Ummy ta ce "Abbah ka sani fa inda ace kuɗi suna dawwamar da mutum cikin farin ciki da Babbar Yayar mu bata gudu tabi mijinta ba saboda tasan duk da kuɗin da take da shi bazai taɓa sanya ta cikin farin ciki ba, haka zalika inda kuɗi sune kwanciyar hankalin mutum da baka kasance cikin damuwa da kaɗaici ba to haka mu ma kuɗi bazai taɓa sanya mu cikin farin cikin ba without our mother, because our mother she's our happiness...."

Abbah shuru yayi yana kallon Ummy ya ma rasa mezai ce mata, yana cikin nazari sai ga Pinky da Rukky sun shugo sunata shan hirar su na school da suka baro, idonsu ne ya sauƙa akan Abban su da gudu suka wuce shi suka je duk suka ɓuya a bayan Mommynsu suna faɗin "Please Mom please kar ki bari ya tafi da mu please..."

Hajiya Kilishi kanta na kallon ƙasi ta kasa cewa komai domin yanzu Ummy ta fi su baki gaba ɗayan su,
Su Pinky su kam sai dai masifa da munafurci da rashin mutunci ga kuma tsoro, amma ita Ummy akwai ta da iya zayyano da zance wanda ko mai shekara 40 bazata nuna mata iya magana ba, domin tinin zata saye zuciyar mutum da kalamanta ko masu daɗi ko akasin haka.....


Abbah ya ce "to yanzu mai ku ke so ayi?..."

Ummy ta kalli su Pinky ta ce "kune Auntys shin ya ku ke so ayi?..."

Daga Pinky har Rukky duk kasa yin magana suka yi daga sun haɗa ido da Abbah sai suyi saurin sunkuyar da kansu ƙasi kamar wasu marasa gaskiya,

Ummy ta ce "Abbah akwai yanda za'ayi amma mu shiga cikin ɗakin mana Abbah kana ta tsaye tin ɗazu..."

Abbah ba yanda ya iya haka ya shiga ciki, duk suma suka shige, Ummy ta ce "Abbah ka zauna a bakin katifar mana..."
Nan ma ya zauna yana binsu da kallo.

Ummy ta tsaya tare da kama kunkumi ta ce "kash ga ba'a kammala girki ba ai da an kawo wa Abbah..."

Abbah ya ce "no bana buƙatar komai..."

Ummy ta ce "Abbah to bari a kawo ruwan sha.."
Nan ma ya ce "a'ah..."

Ummy ta ce "tam shikenam Mommy kema zauna domin akwai maganganu masu mahimmanci da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login