Showing 42001 words to 45000 words out of 89400 words
Abbah miƙewa yayi akan zasu tafi yaga har yanzu Ammy tana nan a durƙushe bata motsa ba, murmushi yayi domin yasan halin ta indai ba shi ya bata umarnin ta tashi ba to sai dai ta kwana a wurin..
Gyaran murya yayi mata tare da faɗin "toh Mar'atussaliha zaki iya tashi ko..."
Murmushi tayi sai a lokacin ta motsa itama ta miƙe tsaye suka bar falon...
Motar Razhdeen ne ta parker a wurin parking dake gidan sa, fitowa yayi da ƙasaitarsa ga ya sha black glass ba ƙaramin kyau yayi ba, order part shima Roshan ne ya fito fuska ɗauke da murmushi shima yana sanye da white glass daman shi ya saba sakawa koda yaushe shima yayi matuƙar yin kyau sosai, ya biyo Razhdeen ne saboda yazo ya ga Ƴar Amana da comedy ta domin Ƴar Amana tanada abun ban dariya dan ma tana takaicin rashin sumar kanta...
Tin shugowar su gidan suke jin ƙarar sound na kiɗa an ƙura volume sosai,
Razhdeen kallon Roshan yayi jin ƙarar waƙa a gidan, Roshan da bakinsa ya gagara yin shuru ya ce "waye ya kunna waƙa kuma? na farko dai Sarah kurmiya ce bata jin sound balle....."
ya gagara ƙarisa maganar ganin Razhdeen ya wuce ya bashi wuri domin shi ya rigada yasan ita ce...
Roshan dai shuru yayi ya bi bayansa ba tare da ya ƙarasa maganar ba,
Suna shiga falo ai kuwa sai suka tarar da Ƴar Amana sai ɗirkar rawa take tayi ita kaɗai, har suka shugo bata san sun dawo ba, shi dai Roshan zama yayi sai dariya yake ta mata,
Razhdeen ne ya ɗauki remote ya kashe waƙar, da sauri ta juyo tana kallonsa gira a haɗe kamar zata fashe da kuka...
Roshan ya ce "ai da ka bar mata waƙar tinda nata so, domin idan tana cikin nishaɗi zata rage wasu damuwar..."
Razhdeen idonsa a kanta ya ce "bata da wani damuwa sai na rashin sumar kanta...".
Ƴar Amana cikin fushi ta wuce da gudu ta nufi part ɗinta can falo na biyu saman upstairs ga hula tum a kai irin hular sanyin nan...
Razhdeen idonsa akan hanyar da tabi fuskar sa a sake ya ce "nafi so ta rinƙa kaɗa jitar ta, hakan yasa na siyo mata..."
Roshan ya ce "to banda abinka ai dole zata haɗa duk biyun tinda duk ta same su, amma na fahimci tana son kiɗe-kiɗe da rawa duk da kurmiya ce amma tana jin komai da komai mayar wa ne kawai bazata iya ba, shawara ɗaya tinda tana son hakan mai zai hana a shigar ta makarantar koyan rawa? kaɗa jita kuwa sai dai ta koyawa wasu..."
Razhdeen shuru yayi na ɗan wasu lokuta daga bisani ya ce "idan na tafi wa zai rinƙa kula mun da ita? bazan bar ta ita kaɗai a gidan nan ba..."
Roshan ya ce "to ka bayyanar da ita mana kaga saika ajiye ta a can gidan mu..."
Girgiza kai Razhdeen yayi tare da faɗin "nop! saina dawo ko hakan zata faru, bana so ta takura tafi son zama ba tare da mutane ba..."
Roshan ya ce "to ka kaita Bauchi wurin Aunty Yolash tinda ita kaɗai ce..."
Nan ma Razhdeen ya ce "ba haka ba, shawara ɗaya ya yanke cewa zai kawo wata ta taya ta zama a gidan nan, akwai security da zai rinƙa kaita school ya kuma dawo da ita ba tare da kowa ya sani ba har ya dawo..."
Roshan ya ce "okay amma waye zaka ajiye a gidan wanda zai rinƙa kula da ita?..."
Razhdeen ya ce "akwai wata Christal Madam Blessing zan dawo da ita gidan nan ta cigaba da kula da Sarah har na dawo, zan rinƙa biyanta salary duk wata, sannan kaima zaka rinƙa zuwa kana duba ta..."
Roshan ya amsa da cewa "toh shikenam Allah ya bamu ikon kula da ita yanda ya kamata..."
Suna cikin hirar su kwatsam suka jiyo sautin jitar Ƴar Amana daga saman ɗakin ta.
Razhdeen miƙe wa yayi ya nufi yanda ɗakinta yake domin indai yaji sautin jitar nan gaba ɗaya hankalinsa tashi yake, zuwa yake ya zauna dab da ita yana sauraron sautin,
A falo ya bar Roshan shi kuwa tashi yayi ya tafi domin yasan dalilin ruɗewar twins ɗinsa...
Razhdeen shigarsa cikin room ɗinta ya tarar da ita a tsakiyar gadon ta ga hawaye shaɓe-shaɓa kwance saman fuskar ta,
Sam bai ji daɗin ganin ta acikin wannan halin ba, ya saba ganinta a cikin farin ciki idan tana kaɗa jita a wannan lokacin kuma kuka take.
Shima haurawa saman gadon yayi domin ganin hawayenta dai-dai yake da ciran duk wani fata na jikinsa saboda shi yake jin zafin haka, ya rasa gane mai yake ji akan ta shin tausayinta yake yi ko kuma so ko kuma burgewa ? amsa ɗaya zuciyarsa ta ba da shine tausayin ta yake yi..
A ruɗe ya kai hannu kanta yana faɗin "Please ki dakatar da wannan kukan Sarah, it's okay bazan ƙara miki laifi ba, yanzu ma ki je ki kunna waƙar ki kinji ko..."
Juya masa ƙeya tayi tana turo baki, jawota yayi tsakiyar faɗaɗɗen ƙirjinsa yana rarrashinta, ita kuwa ƙoƙarin ɗagowa take tana tutture shi ita a dole tayi fushi...
Ganin bazata iya ƙwacewa ba yasa ta fara kai masa duka har da su cizo a kan dantsen sa, ko kaɗan bai ji zafin cizon ba sai cewa yake "Sarah are you mad? da girman ki kike cizo?..."
Asan tashi tabar wurin ne hular kanta ya cire gaba ɗaya, zama tayi ta kafa masa ido jin hular ya cire, ji tayi kamar ta haɗiyi ranta tsabar takaicin cirewar hular domin ko zata yi wanka bata cire wa,
Razhdeen ne ya kafa nashi idon akan ta, yana so yayi magana amma ya kasa tsabar mamakin yanda sumar kanta ya dawo kamar yanda yake, ita kuwa a tunanin ta har yanzu kanta a gwigwiye yake, fashewa tayi da wani sabon kuka ta tashi da gudu zata bar ɗakin yayi saurin riƙo ta tare da juyar da ita saitin gaban mirror,
Ƴar Amana zaro ido tayi waje sosai kamar zasu faɗo ganin yanda sumar kanta ya dawo kamar ba'a Aske ba.
Hannayenta biyu tasa a kan sumar tana cakwarkwayawa taga dai gashin ta ne da gaske, shima Razhdeen hannu yasa yana murza zirin gashin cike da mamakin ganin ikon ALLAH.
Cikin wata uku gashi ya dawo yanda yake ba tare da kowa ya sani ba, kanta sanye da hula amma bata san an maido mata da gashi ba..
Ƴar Amana wani irin farin ciki ne ya wanzu mata lokaci ƙanƙani a ruɗe ta juya ta rungumi Razhdeen sosai tana tsallen farin ciki, shima kan shi Razhdeen ɗin abun ya nishaɗartar da shi domin a halin yanzu ganin Ƴar Amana a cikin farin ciki tamkar anyi masa bushara da gidan Aljanna ne, shima bai san lokacin da ya tsinci kan shi acikin murmushi ba, rungumar ta yayi yana shafar sumar kanta mai murɗi-murɗi kamar yanda yake a baya...
A wannan ranar a tare suka kasance babu wanda ya motsa ko ina a cikinsu,
Uncle Deen ne zaune a saman gado a yayin da ita kuma Ƴar Amana ta ɗora pillow akan cinyarsa tare da ɗora kanta akai, yana wasa da gashin kanta har bacci yayi awun gaba da ita dake yanzu dare ne already sun ci sun sha ba tare da wata matsala ba, yanzu misalin ƙarfe 10 ne na dare, Razhdeen sai da ya fahimci tayi nisa sosai a baccin ta tukun ya gyara mata kwanciya ya rufe ta da mayafi daga bisani ya kashe hasken ɗakin shima ya fice a ɗakin tare da kulle room ɗin da key ya nufi part ɗinsa...
🌝🌝🌝
"Wallahi tallahi bazai yu ina fama da kaina ki baro gidan mijin ki kizo ki ɗora mun wahala ba, ke wato ƴar hutu ko? to bari kiji ni ba boyi-boyin ki ba ce da har kina kwance sai dai na dafa ki ci ba, sai dai ki bar mun gida ehen..."
Hajia Kilishi tana kuka ta ce "haba Uma Saratu ke fah ƙanwar mahaifiyata ce, shin idan baki riƙe ni ba wazai riƙe ni, mijina ya ƙi karɓa ta ko ina naje gudu na ake, ga a wurin aiki an kore ni..."
ta ƙarasa maganar tare da fashewa da kuka..
Uma Saratu tana tsaye sai faman zabga mata harara take ta sau ajiyar zuciya tare da faɗin "kin san dalilin da yasa ake ƙin ki?..."
Hajia Kilishi ta girgiza kai alamar tana son sanin dalili..
Uma Saratu ta cigaba da cewa "dalili shine lokacin da kike gidan mijinki duk danginki ƙin su kika yi saboda kin samu abun duniya, idan dangi suka je gidanki sun zamo abun wulaƙantawa kenam a wurinki shiyasa yanzu kowa ya fita sabgar ki, kuma babu mai zuwa yanda kike, kema kuma haka bakya ziyartar ƴan uwanki bare ƴaƴanki kuma ke kike hanasu zuwa saboda bamu da kuɗi da abun more rayuwa, nasan dai Chief mijinki yana son ƴan uwanki amma ke danginsa da danginki duk bakya ƙaunar su, kinfi son ki zauna daga ke sai mijinki da ƴaƴanki bakya son wani ya raɓe ku, yanzu kuma da ALLAH ya tashi jarabtarki sai kika rasa komai naki, babu miji, babu ƴaƴanki sannan babu kuɗi kuma kin rasa aikin ki, daman mijinki ne ya sama miki yanzu kuwa yasa an kore ki sai mu ga ta gadara, ai Allah ne ya taimake ki dana karɓe ki da kuma naji tausayinki, aikin banza aikin wofi nasan inda mahaifiyar ki da mahaifinki suna raye da tinin suma sun yar da ke saboda ke butulu ce mai manta alkhairi, gashi kin jawa kanki abun kunya labari ya baza ko ina cewa kina yawon bin hotel da Auren ki tir da halin ki wallahi, kuma gashi waɗanda kike bin su hotel suma sun gudu sun barki babu mai sauraron ki, hatta ƴaƴan da kika haifa a cikin ki tinda kika dawo gida babu wacce ta zo bare mijinki, ki ma fidda rai akan Chief domin shi ya riga da yayi Auren sa, ya Auro ƙanwar matarsa ta farko mutumiyar kirki,
Idan kin gama kukan ki ga can wanke-wanke da shara suna jiran ki..."
Uma Saratu tana kaiwa nan tayi ficewarta daga cikin ɗakin Hajia Kilishi wanda ya kasance iya katifa ne a shimfiɗe a ƙasi ko ledar ɗaki babu bare carpet....
asmeetah writer ✍️
🤦♀️ *MAƘIYI_NAH*🤦♀️
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء محمد أولا 🥳
Asmeetah (giaɗe writer)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
STEP TWO
👇
*21_ TO_25*
Remain 7 days Razhdeen zai koma U.S.
Ita kuma Ƴar Amana an saka ta a wani tsararren private school da ake koyan komai da komai,
Makaranta ne na koyan karatun boko da Islamic a wani ɓangaren daban kuma ana koyar da rawa da kuma kaɗa jita, akwai waɗanda ake rubuta musu waƙoƙi ta turanci da larabci sai su bada sautin su da irin basirar da Allah ya basu,
Ƴar Amana kasancewar ta bata iya magana balle a rubuta mata waƙa yasa take iya koyan rawa already ta iya kaɗa jitar ta.
Da uniform ɗinsu na musamman tin safe idan security ya kaita school ba'a dawo da ita sai 6:00 na yamma, tana samun tsaro na musamman da kulawa, idan ka ganta kai kace ƴar gidan shugaban ƙasa ne, domin tin daga kalar suturar ta zaka gane cewa ba ƴar ƙananun mutane ba ce.
Razhdeen ba ƙaramin kuɗi yake kashe mata ba,
Ga kuma wacce ya ɗauko wato Madam Blessing mutumiyar kirki ce tana ganin Ƴar Amana taji yarinyar ta shiga ranta sosai, da duk kan alamu ba ƙaramin kulawa zata samu a wurin Madam Blessing ba..
Baiwar ALLAH ce kwance saman katafaren gadonta ido a lumshe kamar mai yin bacci amma sai dai ba baccin take ba, jin ana knocking ƙofar bedroom ɗinta ne yasa ta ɗan buɗe idon tana mamakin waye yazo mata a wannan lokacin.
Ɗaga kanta sama tayi tana kallon agogon da ke manne saman bango, misalin ƙarfe 12 na dare, dasauri ta kalli bakin ƙofar zuciyar ta na bugun uku-uku, a hankali ta tashi ta nufi wurin ƙofar cikin kakkarwar murya ta ce "wa wa ye?..."
Ji tayi an bata amsa da cewa "Ammata ni ne ki buɗe..."
Haɗe rai tayi cikin fushi ta ce "me ya kawo ka ɓangare na?..."
Cikin sassanyar murya ya ce "Please Ammata ki taimaka magana nake so nayi da ke mai muhimmanci..."
Ta ce "shin gari ba zai waye ba ne?..."
Ya ce "Dan ALLAH..."
Jin kamar a cikin damuwa yake yasa ta buɗe masa, ganin a halin da yake ciki ne yasa ta firgita, yana kame da cikin sa da hannu bibbiyu ko miƙe wa baya iya yi, eyes ɗinsa duk sun kaɗa sunyi jawur, yana fitar da numfashi da ƙer, kamar wanda aka hankaɗo shi jiki na ɓari ya shugo cikin bedroom ɗinta, wuri ya samu a bakin gado ya zauna domin idan ya cigaba da tsayuwa zai iya faɗuwa ne...
Baiwar ALLAH gaba ɗaya ta gama tsorita domin a halin