Showing 45001 words to 48000 words out of 89400 words
da yake ciki kamar mutuwa zai yi,
Murya na kakkarwa ta ce "mai ya faru da kai Yaya Roshan?..."
Ɗagowa ya yi da rinannun eyes ɗinsa yana binta da kallo daga bisani ya ce "ke ke ce damuwa ta, ke ke ke ce matsala ta, Ammata dan ALLAH ki taimake ni ina cikin mawuyancin halin da bazan iya control kaina ba, mai na miki ne kike azabtar da ni? idan nayi laifi ki sanar mun ko zan samu salama acikin raina, wannan hukuncin yayi mun tsauri da yawa wanda ƙwaƙwalwata baza ta iya ɗauka ba, please Ammata nah..."
Baiwar ALLAH tana tsaye a kansa cike da mamaki ta goya hannayenta a saman ƙirjinta fuska a haɗe ta ce "wai mai kake buƙata ne daga gare ni Roshan?..."
Cikin sassanyar murya ya ce "ke! ke nake buƙata Ammata, da zaki mallaka mun kan ki da kin kawo ƙarshen matsala ta ..."
Wani abu taji ya daki zuciyarta cikin nuna fushi ta ce "Roshan please stay away from me, kana buƙata ta amma ni sam bana ra'ayin hakan, ko ana dole ne? shin ni kake so ko biyan buƙatar ka?..."
Haka lips ɗinsa yake kakkarwa haɗe da teeth ɗinsa kamar mai jin sanyi ya ce "ke ke ke nake so Ammata..."
yana magana murya na ƙaƙƙafewa sakamakon tsananin ciwon cikin da yake fama da shi...
Murmushi tayi sannan ta ce "to indai har da gaske kana sona inaso ka cire wannan batun daga bakin ka, kafin kayi Aure shin neman mata kake yi ne? nasan baka neman mata haka kake haƙuri har tsawon shekaru, to yanzun ma inaso ka cigaba da haƙuri ka zauna da ni a haka idan zaka iya..."
Roshan ya ce "amma mai yasa kika yanke wannan hukuncin?..."
Murya cikin tsawa ta ce "saboda bana sonka Roshan, bana jin sonka a cikin zuciyata, baka san irin raɗaɗin da nake ji a cikin zuciyata ba dana kasance inada igiyar Auren ka,
Roshan idan nace zaka samu farin ciki daga gareni nayi maka ƙarya domin nima an datse mun nawa farin ciki, inaso mu cigaba da zama haka cikin ƙunci nake ga hakan zai fi..."
Roshan ji yayi kamar ana kwaɗa masa guduma a tsakiyar kansa lokaci guda ya fara jin hawaye suna masa go slow a saman kuncin sa, girgiza kai yayi tare da faɗin "kin zalunci kanki da baki sanar mun tin kafin a ɗaura Aure ba, sannan kin zalunce ni da kika kasa furta mun abinda ke ranki har kika bari aka ɗaura Aure, amma dan ALLAH inason sanin dalilin da yasa bakya sona?..."
Baiwar ALLAH ta ce "duk wata hanyar da yakamata na bi don na nuna maka cewa bana sonka na bi hanyar amma ka kasa fahimta, ance labarin zuciya a tambayi fuska amma kai duk da hakan baka gane ba saboda a lokacin ƙwaƙwalwarka a toshe take bata gane farin cikin mutum da kuma baƙin cikin mutum, kai kanka kawai ka sani, farin cikin ka kawai ka sani,
You know what? bari na sanar maka wani abu da baka sani ba, ina damuwata kake son sani ko? to yau zaka sani..."
Ƙarasawa gabansa tayi ta durƙusa da gwiwowinta tana fuskantar sa a yayin da shi kuma yake zaune a bakin gado.
Ta ce "Yaya Roshan kayi haƙuri da abinda zaka ji daga bakina duk da nasan zaka ji ba daɗi amma rashin daɗin nake so kaji kamar yanda nima ba'a cikin daɗin nake ba, tin farko zuciyata da kai ta fara aminta amma daga ƙarshe labari ta sauya zuwa kan Razhdeen..."
Cikin rashin fahimta Roshan yake binta da kallo ya ce "bangane mai kike nufi ba..."
Ta ce "Razhdeen ya saye mun zuciyata, shi nake so, kuma nake son kasancewa tare da shi, har yau har gobe son sa bai ragu a cikin zuciyata ba..."
Roshan wani irin zazzaɓi ne yake shirin rufan sa murya na kakkarwa ya ce "amma meyasa baki sanar tin da wuri ba? mai yasa zaki cutar da zuciyarki? kina son Ɗan uwana amma kin kasa sanar wa kowa why? hatta shi kan shi bai sani ba, inda kin sanar mun wallahi bazan bari ayi Auren da ni ba, ina sonki har cikin zuciyata amma jin irin son da kike wa twins ɗina yasa na ƙara sonki, Ammata bazan bari zuciyarki ta cigaba da azabtuwa ba, zan sama miki mafita, ki kwantar da hankalinki Okay..."
Lokaci guda taji wani irin matsanancin kuka ya yanko mata, kwantar da kanta tayi kan cinyarsa tana kuka, shima za mo wa yayi ƙasi ya ɗago da fuskarta suna fuskantar juna ya ce "kukan mai kike? ba nace ki kwantar da hankalin ki ba, ina dai Razhdeen kike so? to ki yi haƙuri zaki same shi..."
Ya ƙarasa maganar tare da fashe wa da kuka shima ya rungumota jikinsa duk kukan suke babu mai rarrashin kowa a cikin su...
Bayan kwana biyu da faruwar haka Roshan yana zaune a falon Meeting ɗin Abbah da shi Abbah ɗin, Roshan ne yake son sanar wa Abbah halin da Baiwar ALLAH take ciki na tsananin son Razhdeen da kuma yana son sanar wa Abbah cewa zai haƙura da ita domin sama mata farin cikin ta,
tunani ya zurfafa daga bisani Abbah ya katsar da shi da cewa "mai yake faruwa ne Roshan?..."
Roshan cikin tsananin damuwa ya ce "Abbah daman ina so zan yi magana da kai ne..."
Abbah ya ce "ina jinka Roshan! naga kamar kana cikin damuwa please tell me my Son..."
Lokaci guda sai ga hawaye shaɓe-shaɓa akan fuskar sa kamar wanda yake jira ayi masa magana, kuma daman yana maƙale da hawayen..
Abbah ya ce "Subhanallahi Roshan kuka kuma? kai ɗin? dan ALLAH ka taimaka ka sanar mun bana so ka rinƙa jefa kan ka cikin damuwa kasan kana da matsalar heart, ka duba kamar marar lafiyan da yayi shekara a kwance duk ka bi ka rarrame..."
A hankali Roshan yake motsa lips ɗinsa waɗanda suke ta faman kakkarwa kamar mai jin zunzurutun sanyi, da ƙer ya iya cewa "A A A Abbbah, please help me my heart so pain........!!!"
lokaci guda ya fashe da wani irin raunannen kuka har sai da ya za me ƙasin carpet, ya kifar da kansa a ƙasi ba abinda yake sai kuka..
Jikin Abbah ne ya fara ɓari gaba ɗaya ya tsorita da ganin Roshan acikin wannan hali, cike da mamaki ya nufo wurin da yake shima ya durƙusa yasa hannu yana ƙoƙarin ɗago shi.
Abbah Ya ce "shin Daughter ce ta mutu? ko kuma tana kwance ne a gadon asibiti? ka sanar mun mana..."
Roshan rungumar Abbah yayi jikinsa duk ya ɗau zafi murya na kakkarwa yake faɗin "Abbah Ammata bani take so ba, gaba ɗayan mu babu mai kwanciya hankali, ni bana cikin farin ciki itama haka, ina matuƙar ƙaunar Ammata amma ita sam ba ni ne a gaban ta ba, tinda muka yi Aure tsawon wata uku zuwa huɗu yanzu bamu taɓa raya sunnah ba please Abbah inaso na bar duniyan nan, am really tired of this would, wannan duniyar cike take da ruɗani da tashin hankali Abbah, ina da abubuwan more rayuwa amma bani da kwanciyar hankali Abbah..."
Abbah shima idanuwan sa ne suka cicciko da hawaye tsananin tausayin Roshan ne ya ziyarci cikin zuciyar sa, kwantar da kan Roshan ya yi saman ƙirjinsa yana bubbugan bayansa alamar rarrashi tare da faɗin "it's okay my Son, everything will be come easy, know tell me what's going wrong?.."
Roshan kan sa a kwance saman ƙirjin Abbah ya ce "i told you Abbah, Ammata bani take so ba, Auren dole akayi mata..."
Abbah ya ce "shin aina kaji wannan batun, ita ta sanar maka?..."
Roshan ya ce "yess Abbah ta sanar mun duk abinda ya ke ranta, bata sona..."
Abbah ya ce "whattt? to amma ya akayi hakan ta faru, bata sonka kuma akayi Auren? shin waye a ranta har ta kasa karɓar soyayyarka kuma ta kasa baka haɗin kai...".
Ɗago wa yayi daga kwancen da yake akan Abbah, da rinannun eyes ɗinsa yake kallon Abbah sannan ya ce "Razhdeen ne a cikin zuciyar ta, shi take so kuma take muradin ya zamo mijinta uban ƴaƴanta..."
ya ƙarasa maganar yana sakin ƙayataccen murmushin baƙin ciki da kuma farin ciki...
Abbah gaba ɗaya ya gama ruɗe wa, cike da mamaki ya ce "amma shi Razhdeen bai taɓa sanar mun wannan maganar ba, ko a bakin wani ban taɓa jin Razhdeen da Daughter suna soyayya ba...
Roshan ya ce "Abbah ka gane zancen mana, ba soyayya suke ba ita ce take sonsa amma ta kasa nasar masa, ta kasa fitar da abinda yake cikin cikinta da haka har aka ɗaura mana Aure, shi kan shi Razhdeen bai san tana son sa ba..."
Ajiyar zuciya Abbah ya sauƙar yana jinjina kai daga bisani ya ce "Roshan!.."
Roshan ya amsa masa cikin sassanyar murya.
Abbah ya cigaba da cewa "shin wani hukunci kake son ɗauka?..."
Roshan ya ce "Abbah ni na yanke shawarar rabuwa da ita, in yaso sai a Aura mata Razhdeen duk da nasan da wuya ya yarda da hakan, amma zan lallame shi akan ya yarda ya Aure ta, ina son farin cikin ta sosai, a halin yanzu ita ɗin marainiya ce bata da kowa sai mu..."
Jinjina kai Abbah ya yi daga bisani ya ce "shikenam duk yanda ka yanke shine dai-dai, hakan na nufin zakayi sadaukar da soyayyar ka wa ɗan uwanka domin ka sama mata farin ciki, kai baka damu da naka farin ciki ba, shikenam inaso a yanzu kowa ya hallara a babban falon cikin gida, kaje ka ƙira matar takan, nima yanzu zan ƙira Razhdeen yazo yanzun nan..."
Roshan tashi yayi da ƙer yana jan ƙafa da haka ya fice, shima Abbah wayar sa ya ɗau ya danna ƙiran number Razhdeen cikin sa'a kuwa lokacin wayar tana hannunsa ya ɗauka da sallama a bakin sa..
Abbah zuciyarsa a hargutse ya ce "kana ina Razhdeen?..."
Razhdeen ya ce "ina gidana..."
Abbah ya ce "okay I want to see you right now..."
In other side Razhdeen ya ce "but what happen Dad?..."
Abbah ya ce "kar ka damu idan kazo zaka ga komai a idonka..."
Razhdeen amsa masa yayi tare da faɗin "Okay..." ya katse ƙira yana mamakin ƙiran gaggawar da akayi masa kuma da safe yaje ya gaishe da su Abbah, babu yanda ya iya haka ya bar duk abinda yake ya ɗauki key ɗin motar sa zai fita,
A falo ya tarar da Ƴar Amana dake yau ba school ranar hutu ne, ta zuba wa plasman ido tana kallo kai kace ba kurmiya ba ce, bata ankara ba taji an manna mata kiss akan goshi da sauri ta ɗago tana bin sa da kallo, murmushi ya sakar mata tare da faɗin "take care my Beb, I'll be back..."
Itama murmushi ta sau idonta akan sa, ga gashin kanta yanda ya bazu akan gadon bayan ta...
Kaɗa mata key yayi sannan yasa hannu zai buɗe ƙofa ya fice ya ji Madam Blessing tana faɗin "sai ka dawo Major..."
Ba tare da ya juya ya kalle ta ba ya ce "thank you..."
daga nan ya yi tafiyar sa.
Kowa ya hallaru a babban falon gidan Abbah duk da yanzu basu da yawa a gidan, daga Abbah ne sai Ammy sai uwar masu gida da Ƴar tinny itama yau ba school ga Roshan shima a zaune gefe guda, waɗanda ake jira Razhdeen ne sai Baiwar ALLAH wacce aka ƙira ta tin ɗazu bata samu damar zuwa ba,
Abbah ne ya kalli Roshan sannan ya ce "Roshan kaje ka taho mun da Daughter ina tunanin tasan ƙiran akan maganar ta ne shiyasa ta ƙi zuwa..."
Roshan ya ce "okay tam..." ya tashi zai bar falon.
Razhdeen parking ya yi a gurguje ya buɗe murfin motar sa ya fito dai-dai lokacin da Baiwar ALLAH itama ta iso part ɗin, bakin get ta nufa idonta akan Razhdeen wanda shima wurin ya nufo shima ita yake kallo yana saƙe-saƙe a ransa, a gaba da baya suke ita tana gaban sa a yayin da shi kuma yake ta bayan ta baifi nan da ɗan rata kaɗan ba ya iso ta, tafiya take ba tare da ganin gaban ta ba, idonta akan sa bata san ta iso bakin get ɗin mashigar compound ɗin gidan ba, kawar da kansa yayi daga ganinta yasan ta iso bakin get ɗin amma bai dakatar da ita daga ganin sa ba domin ya daɗe da tabbatar da cewa Baiwar ALLAH taɓaɓɓiya ce ta fara haukacewa tin lokacin da ya kaita hospital.
Kan ta ne yayi wani irin mungun buguwa da ƙofar get mai ƙarfin gaske, wani irin gigitaccen ƙara tayi tare da yo wa baya zata faɗi har ta saddaƙar kwatsam taji an riƙo ta, idonta a ƙarƙame a matuƙar tsorace ta cakume shi sosai jikinta har wani ɓari yake tana sauƙar da numfashi da ƙer,
kallonta ya tsaya yi yana kallon kalar riƙon da yayi mata, caɗaf ya ɗaga ta yayi mata ɗaukar jaririya wanda shima kansa bai san yayi mata irin wannan ɗaukar ba, domin a yanda tayo baya zata faɗi inda bai yi saurin ɗaukar ta ba sai dai a ɗauke ta sumammiya, a hankali take buɗe eyes ɗinta tana so taga a hannun wa take, idanuwanta ne suka sauƙa akan kyakkyawan fuskar Roshan mai ɗauke da ƙayataccen murmushi, zaro ido waje tayi ganin a hannun Roshan take, ƙoƙarin sauƙa daga ɗaukar da yayi mata take, a hankali ya sauƙar da ita, waiwaye ta soma yi tana duba yanda Razhdeen yake domin tasan shine a wurin.
Roshan da ya fahimci Razhdeen take duba wa ya ce "tin tinin ya yi wuce war sa, domin inda Allah bai kawo ni da wuri ba ina tunanin yau sai dai kiyi kwanan hospital...