Showing 66001 words to 69000 words out of 89400 words

Chapter 23 - MY ENEMY BOOK 2 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

2524

zamana har ƙarshen rayuwata ita zan rinƙa kusan ta, saboda haka kiyi nesa da abinda zai sa mu fake wuri ɗaya, zan cigaba da shan lemon tsami na har Allah yasa mu rabu,
Da fatan dai ban ɓata miki rai ba ko?..."

Baiwar ALLAH ganin bazata iya juran kalaman Roshan ba yasa ta tashi tare da fashewa da matsanancin kuka ta bar ɗakin da gudu, kai tsaye part ɗinta ta nufa.

Shima Roshan bai san lokacin da hawaye ya fara masa go slow ba domin ba ƙaramin ƙaunar Baiwar ALLAH yake ba, ya kasa cire ta a ransa kodan yana ganinta koda yaushe ne...


★★★★★★


Bayan isar su Abbah garin Suleja gidan da aka masa kwatance nan yayi parking a ƙofar gidan, gidan ne kana gani kasan gidan haya ne amma kowa da part ɗinsa,
Har Ummy ta sauƙa daga cikin motar tayi gaba zata kutsa ciki Abbah yayi saurin riƙo ta yana faɗin "baki da hankali ne? daga ganin gida zaki shiga idan ba nan ne gidan kuma fa?..."
Ummy tsayawa tayi domin a halin yanzu bata da wani buri da ya wuce taga mahaifiyarta..

Wani magidanci ne ya fito daga gidan da duk kan alamu shima a gidan yake da iyalansa, Abbah ne yayi masa magana yana faɗin
"Dan ALLAH bawan Allah nan ne gidan da Kilishi take?..."

Mutumin ya ce "eh dake part-part ne gidan ban san a wani ƙofa take ba, kuma akwai mata da yawa a gidan duk bansan sunayen su ba..."

Abbah ya ce "okay matan duk bazaware ne ko matan Aure?..."

Mutumin ya ce "duk matan Aure ne bazawara ɗaya ce ɓangarenta daban ita kaɗai..."

Abbah ya ce "okay to wurin bazawarar muka zo..."

Mutumin ya ce "nasan ƙofar da take muje na kai ku..."

Abbah ya ce "a'ah kayi mana sallama da ita muna waje daga nan zamu wuce ne..."

Mutumin ya ce "okay..." Sannan ya shige ciki, can ya fito ya sanar da cewa "tana fito wa..."

Bayan wasu ƴan mintuna sai ga Hajiya Kilishi ta fito tana sanye da hijab ɗinta sai faman leƙe leƙe take tana son ganin wanda yazo mata sam bata lura da su Abbah ba,
Sai ji tayi an rungume ta sosai, zaro ido tayi tana kallon Ummy wacce ganin ta yasa ta tafo da gudu ta rungume ta,
A ruɗe Hajiya Kilishi ta furta "Ummy..." cike da mamaki take binta da kallo, Ummy tana kuka ta ce "Mommy yau gamu mun zo gare ki..." tayi maganar cikin nuna farin ciki,
sai ga Ƴar tinny itama ta rungume ta, cikin farin ciki Hajiya Kilishi tasa hannu ta ɗaga ƴar tinny tana hawaye tare da faɗin "Nagode muku sosai yara na, kamar daman kun san ina cikin damuwa na rashin ganin ku a kusa da ni..."

Ummy fashewa tayi da kuka tana faɗin "Mommy ki ga duk kin rame kin zamo ƴar ƙarama, Mommy baki da ƙashin wuya amma ki ga yanzu yayi miki sauƙa, meyasa zaki zauna cikin wahala Mommy..."

Hajiya Kilishi tana kuka ta ce "to ya zan yi Ummy dole na zauna cikin wahala kinga fa kowa ya guje ni, Ni kaɗai nake zaune ba mai taimaka mun, sai yanzu da Auntyn ku Yolash take turo mun kuɗi, ita take biya mun gidan hayan da nake ciki yanzu..."

Abbah yana jingine a jikin motarsa ganin koke-koken ya ƙi ƙarewa yasa shi cewa "kinga Madam kar ki raunana mun zuciyar ƴaƴa Please, muna son komawa..."

Hajiya Kilishi sai yanzu ta lura da Abbah, kallon yanda yake tayi tare da faɗin "kayi haƙuri ku shugo ciki mana ku ci abinci..."

Abbah ya ce "look ba wai zuwa muka yi mu zauna ba, just na kawosu su ganki, yanzu kuwa tinda kunga juna su zo mu tafi kawai..."

Ummy ta ce "Abbah inason cin girkin Mommy..."

Abbah cikin takaici ya ce "daman tinda kike kin taɓa cin girkin ta ne? tin da kika zo duniya kin taɓa ganinta a kitchen?..."

Ummy ta ce "yanzu ina son cin abincin da ta girka da kanta..."

Abbah ganin Ummy zata bijire masa yasa shi cewa "ok kuje ina jiran ku yanzu..."

Hajiya Kilishi ta ce "kai ma ka shugo mana..."

Abbah ya ce "kinga ba wurin ki nazo ba, na dai kawo yarana ne, amma mu shiga daman inason miki last warning akan bibiyan yanda ƴan uwana suke..."

Hajiya Kilishi ta ce "tam..."
tana ɗauke da ƴar tinny ta riƙe hannu Ummy suka shiga, Abbah shima bin bayan su yayi...


Bayan isar su ciki Hajiya Kilishi ce ta jido girkin da tayi a flask tuwon shinkafa ne da miyan Alaiyahu yasha gyaɗa har da nama a ciki kamar wacce tasan da zuwan su, kuma dake yanzu Aunty Yolash tana turo mata kuɗi sosai,

Ummy tana kallon Kilishi ta ce "Mommy ke fa zaki yi feeding ɗin mu..."

Hajiya Kilishi ta ce "to rabin Rainah..."

Ta wanke hannunta sannan ta soma basu abinci a baki duk su biyun da haka ta kammala basu suka ci suka ƙoshi, ta basu ruwa suka sha...

Ummy ta ce "Mommy daman haka kika iya girki shine bakya mana..."
Hajiya Kilishi murmushi tayi ta ce "kuyi haƙuri nayi kuskure a gafarce Ni yara na...".

Ummy itama murmushi tayi ta rungumi mommynta tana faɗin "kar ki damu Mommy muna tare da ke..."

Hajiya Kilishi ta ce "kuna jin labarin su twins ɗina kuwa?..."

Ummy ta ce "su Aunty Pinky ai sun kusan dawowa, kwanan nan zasu yi graduation 🎓 na gama deegre..."

Hajiya Kilishi ta ce "ma sha ALLAH, ina su Roshan da matar sa?..."

Ummy ta ce "duk suna nan, Uncle Deen kam ya koma U.S..."

Hajiya Kilishi kamar zatayi kuka ta ce "bakwa jin labarin Minal ko?..."

Jan numfashi Ummy tayi sannan ta ce "tana can tare da mijinta nasan tana cikin ƙoshin lafiya tinda Marshall yana matuƙar ƙaunar ta..."

Hajiya Kilishi ce ta kalli Abbah ganin yanda yake ta haɗa rai yana fushi,

Abbah kuwa idonsa a gefe guda yana tunani a ransa cewa "anya kuwa wannan Kilishi ce? gaskiya rayuwa tana bugan ta kuma ina so ta ƙara bugarta da kyau, kuma naga ta sauya sosai kamar ba Kilishi ba..."

Daga baya ganin tunanin ba shida wani amfani yasa shi yin gyaran murya yana kallon Kilishi ya ce "kalli Nam..."

Hajiya Kilishi kallonsa take tana son jin wani irin warning za'ayi mata,

Abbah ya ce "last warning da zan miki shine kar ki sake bibiya mun ƴan uwa da abokaina akan maganar komar dake gidana domin bazan taɓa mayar ki ba, kin fita kin fita kenam ba komawa, domin bazan kije ki sawa matata damuwa ba, nafi son na rinƙa ganinta ita kaɗai a gidana tana walwala, don haka ki dakatar da wannan shirmen nakin, idan ba haka ba wallahi tallahi kotu ce zata rabamu, a saboda ke na ɓata da abokaina da yawa da ƴan uwana, wacce nake ji da ita a raina ƙanwata Yolash kinsa na samu matsala da ita, a saboda ke Ɗan uwana ya taso daga wani country yazo wuri na amma rabuwar ba daɗi muka yi duk saboda ke, meyasa kike son shiga mun rayuwata kam? shin ana zaman Aure dole ne? nace banaso ana dole kam? Ni fa ba ƙaramin yaro bane da za'a zo ana damu na da maganar ki, to na rantse idan kika ƙara turo mun wani sai na ɗauki mataki na gaya miki...."

Ya ƙarasa maganar yana zazzaro mata ido,

Hajiya Kilishi tana hawaye ta ce "Chief...."

Kafin ta cigaba ya katse ta da cewa "Chief ya mutu wani ne a madadin sa wato Ni ..."

Hajiya Kilishi ta ce "to ai kai ɗin nake nufi Abban yara,
tin daga lokacin dana tura Aunty Yolash shin na tura wani ne ko wata? daga ita ban ƙara tura kowa ba na kai kuka na zuwa ga mahalicci, ko shi Mai martaba Aunty Yolash ce ta tura shi ba Ni ba, idan kayi shara'a dani ai dole cewa za'ayi da uwar ƴaƴanka kayi shara'a, wannan sunan bazai gogu ba na cewa Ni uwar ƴaƴanka ce, kafin ka fara sharia da ni ka fara goge wannan sunan tukun, ka nema wa ƴaƴanka wata uwar a daina cewa ni uwar ƴaƴanka ce..."

Abbah ya ce "tin tinin na goge wannan sunan domin na nema wa ƴaƴana uwa ta gari wacce ta fi uwar su, tana can ƴar aljanna kenam, tana bawa ƴaƴana kulawar da basu samu a wurin Uwar tasun ba..."
ya ƙarasa maganar yana hararar ta, sannan ya maida idonsa kan Ummy yana faɗin "ku tashi mu tafi..."

Ummy ƙara narkewa tayi a jikin Hajiya Kilishi ko ɗagowa ta kalli Abbah bata yi ba..."

Abbah ya ce "ina miki magana kina jina..."

Ummy ta ce "Abbah nafi son zama a wurin uwata ba'a wurin Uwar wani ba, duk uwar da za'a kawo mun baza tafi uwata ba kuma itama uwar tawan ƴar Aljanna ce da yardar Ubangiji..."

Abbah ya ce "Uwar masu gida Ni kike gaya wa haka?..."

Ummy ta ce "Uwar masu gida ta mutu wata ce a madadin ta wato Ni..."

Abbah ya ce "ki tashi muje na ce..."

Ummy ta ce "Abbah wallahi bazan tafi nabar Mahaifiyata ba, idan kana so na tafi sai dai mu tafi gaba ɗaya da ita, amma in har babu ita to Nima babu ni..."

Abbah ya ce "to shikenam ki cigaba da zama a wurin natan, ke Auta taso ki bi Abbanki ma za..."

Ƴar tinny babbar yatsar ta tasa a baki idonta akan Abbah itama ta kwanta akan Hajiya Kilishi tana faɗin "Oh -ohhh..."

Abbah ya ce "ta so ma za zan siya miki yogurt..."

Ƴar tinny ta ce "Oh -ohhh...."

Abbah ya ce "Dan ubanki yau ɗin baza ki mun magana ba ne?
Yau bakyaso ki kwana da Ammyn ki Koh?..."

Ƴar tinny ta ce "eh ɗin yau da Mommy na zan kwana, Oh -ohhh..."

Abbah ya ce "shikenam kun kyauta, yana kaiwa nan yayi ficewar sa, a fusace ya shige motar sa sai Abuja...."

Ummy farin ciki kamar bazata mutu ba, daman shirin ta kenam inta samu tazo wurin mommynta ba koma wa kuma gashi shirin ta yayi kyau, Abbah yayi zuciya ya tafi, daman haka take so..."

Itama Hajiya Kilishi tayi farin ciki sosai ganin yaranta a kusa da ita, yau da su zata kwana...


★★★★★★★★★


Ta ƙura volume waƙa a plasman tana kokkoyan rawar da suke, kuma rawar yana mata kyau sosai yanzu ta ƙwarai sosai domin ba rawar da bata iya ba, hatta kaɗa jita ta ƙaro training sosai ba ƙaramin kwarai wa tayi ba,
ta ɓangaren karatu kuwa nan ma ba laifi sai dai tayi rubutu, ta iya na Hausa sannan ta iya na Turanci sosai, ta ɓangaren islamiyya kuma dake makarantar a haɗe take gaba ɗaya, bata iya bada hadda amma tana tattare su a cikin kwakwalwar ta.

Tana cikin rawar sai ga Madam Blessing ta fito daga kitchen daman tasan sana'ar ta kenam hakan yasa ko sauraronta bata yi ba, Ƴar Amana ce taje da gudu ta kamo hannun ta tare da jawo ta gaban plasman tana mata nuni da suyi rawa, ba yanda Madam Blessing ta iya haka ta biye mata sukai ta tiƙar rawa sai da madam Blessing ta gaji ita kuwa Ƴar Amana kamar wacce ake ƙara mata petur, sai da waƙar taje ƙarshe tukun ta haƙura..

Bayan ta ci abincin da aka girka mata na gyaran jiki tashi tayi taje tasa wasu ƙananun kaya riga da wando irin na kwallo amma sai dai wandon gajere ne a iya cinya ya tsaya mata sai rigar wandon marar hannu gata jiki a dire abun ba'a cewa komai, gashin kanta ta tuttuƙe shi tayi donut da shi sannan ta sanya takalmi cover shoe mai igiya irin na ƴan wasan ƙwallo, tana kammala shirin ta kawai ta ɗauki ball ɗinta ta fice, tana wasan basket ball ne idan rana ta kama ranar Saturday da sunday wasu lokuta kuma takan yi wasan kabadi ita da madam Blessing, a filin wasa dake part guda a killace, wani lokaci kuma tasa kayan swimming pool ƴan ƙananu taje tana rayuwar kifaye a cikin ruwan, ko wani sati da kalan wasannin da take yi, sometimes kuma ta fita yawon shakatawa ita da Madam Blessing, suje super market su yo siyayya daga nan su je wurin wasan yara har gidan zoo sai sun gama zagaya wa sannan suke komawa gida.

Madam Blessing ba ƙaramin kuɗi take cabka a wurin Uncle Deen ba hakan yasa take bawa Ƴar Amana kulawa ta musamman...

Bayan sati ɗaya Madam Blessing ce ta haura saman ɗakin Ƴar Amana zata je ta tayata shirin tafiya makaranta domin ta kammala haɗa kayan breakfast..

Shigar ɗakin ke da wuya ta tarar da Ƴar Amana kwance ƙasin carpet ɗin ɗakin tana kame da cikinta ta tukwikwiye guri ɗaya, da gudu Madam Blessing ta ƙarasa gurin ta tana ƙiran sunanta, ai kuwa tana ɗago ta taga bata motsi ga ido a lumshe,
ƙirjin Madam Blessing ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske sai ambaton "Jesus, Jesus take domin bata san me zata ga ya wa Razhdeen ba, kuma tsoron ta kar taje ta mutu, haka ta ɗagota daƙer tayi waje da ita, daƙer ta iya sauƙar da Ƴar Amana ƙasin down stairs domin yanzu tayi cikar da mace bazata iya ɗaukarta ba, madam Blessing niyar ta ta nufi hospital da ita, tana shirin barin falo sai ga Roshan ya shugo falon da sallama a bakinsa, ganin madam Blessing tana riƙe da Ƴar Amana yasa shi yowa kansu da hanzarinsa yake faɗin "me ya faru da Sarah?..."

Cikin ƙiƙƙinar magana tsabar a ruɗe take ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login