Showing 87001 words to 89400 words out of 89400 words

Chapter 30 - MY ENEMY BOOK 2 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

2529

da abun a raina domin ina jinya ma da abun nake kwana kuma take tashi, kuma nayi miki alƙawarin sai Razhdeen ya dawo kuma Alhamdulillah ranar ta zo, yau zan sauƙe nauyin dake kai na dalilin da yasa na nemi yin Aure kenam, zan rabu da matar da bata sona sannan zan Auri wacce take sona kuma take son kasancewa dani har ƙarshen rayuwar ta,
Kiyi haƙuri Ammata sakamakon ɓata miki lokaci da nayi yanzu dai ganan takardar sakin ki da kike nema...."

Ya zaro wata farar takarda ya miƙa mata,
wani irin yawu Baiwar ALLAH ta haɗiya kamar wacce zata haɗiyi ranta, zuciyar ta wani irin ƙuna yake kamar wanda aka dasa mata garwashi, lokaci guda hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba..

Roshan ya ce "karɓi mana akwai ayyuka a gabana kinsan next week Aure na, ina buƙatar yin wasu shirye-shirye..."

Baiwar Allah juyowa tayi tana kallon takardar hannun sa ga hawaye yaƙi tsayuwa mata,
Hannu tasa ta karɓa ta ɗago tana kallonsa shima kallonta yake, idan ta akansa haka ta saita tsakiyar takardar ta ɓe ra shi gida biyu sannan ta ƙara yaga wa, haka ta yayyaga takardar idonta yayi jawur...

Kallonta yake cike da mamaki, bayan ta kammala tayi saurin shige wa tsakiyar sa ta rungume shi sosai tana kuka tare da faɗin "Yaya Roshan bai kamata ka ɗaukar mun wannan hukunci ba, wallahi bazan taɓa saku wa ba ina nan tare da kai, tin kafin a kawo wannan lokacin nake nuna maka irin son da nake maka amma ka kasa fahimta ta, na koyi shiga ɗakin ka ina maka gyara saboda na nuna maka soyayyata amma ka dakatar da ni, duk wasu abubuwan da ya kamata ace ka fahimci ina sonka amma ka kasa fahimta, wallahi ina sonka Yaya Roshan har cikin zuciyata...
ta ƙarasa maganar tare da fashewa da matsanancin kuka,

Shima Roshan rungumar ta yayi sosai a jikinsa yana kuka domin ya fahimci halin da take ciki yanzu, shima ba son rabuwa yake da ita ba, gaba ɗaya kuka suke babu mai rarrashin kowa, sai daga baya Roshan ya ɗago ta yana faɗin "it's okay, yanzu na fahimce ki, amma meyasa kika kasa sanar mun tin lokacin, har kika cutar da zuciyar ki da kuma tawa? zurfin ciki ko? Ammata ina sonki sosai..."

Itama ta ce "Nima haka Yaya Roshan..."

Murmushi ya yi sannan ya ce "to maganar Aure na fa? zan iya dakatar wa tinda muradin raina ta dawo gare Ni...".

Baiwar ALLAH ta ce "Yaya Roshan kowa yasan zakayi Aure, kuma Abbah da Uncle mai martaba sun tsayar da maganar bai kamata lokaci guda a watsa musu ƙasa a ido ba tinda kai ka buƙaci yin Auren..."

Roshan ya ce "to ai bana so nayi miki kishiya...".

Baiwar ALLAH ta ce "Abokiyar zama dai, baka ga Mommy da Ammy yanda suke zaman lafiya ba, kullum Abbah a cikin farin ciki yake sun haɗe kansu..."

Roshan ya ce "shikenam amma kinsan dai kwanan nan zan koma ƙasar Egyph da aiki shekara biyun da aka yanke mun yayi zan koma, zan tafi da ɗaya daga cikin ku amma son samu ace ke kaɗai ce dani,
gaskiya Ammata banji daɗin ƙin sanar mun da kika yi ba, har sai da na nemi Aure tukun zaki sanar mun abinda ke ranki why?..."

Baiwar Allah ta ce "kayi haƙuri mijina nayi laifi sannan na aikata kuskure a yafe mun dan Allah..."

Roshan ya ce "na yafe miki Ammata nah...." ya ƙarasa tare da ja mata hanci suka sake rungumar juna....


A wannan ranar basu rabu da juna ba a haka suka kwana ɗaki ɗaya sannan gado ɗaya amma kuma basu raya sunnah ba sakamakon wani ɗan matsala da aka samu, a wannan ranar Baiwar Allah ta tashi da period ɗinta, amma ba haka aka so ba..

Bayan kwana biyu biki yana ta matso wa Roshan kuma da Baiwar Allah soyayya tana ta ƙaruwa...
Rana yata yau da sassafe Baiwar ALLAH tana shirya dinning shi kuma Roshan yana shan baccin safen sa bai samu tashi ba,
Sai taji an yi knocking ƙofar falo, ɗaga kai tayi taga agogo yanzu ƙarfe 6 ne na safe a ranta ta ce "waye da sassafen nan..."

zuwa tayi ta buɗe bayan taji an ɗan dakata da yin knocking, tana buɗe wa bata ga kowa ba sai wani baƙin leda da ta gani an ajiye a ƙasin ƙofar, lelleƙa ko ina tayi bata ga kowa ba daga baya ta ɗauki ledar ta koma ciki tare da rufe ƙofar...

Pinky da Rukky ne suka ɓuya suna leƙenta har ta koma ciki bayan sun tabbatar ta ɗauki ledar amma ba haka suka so ba, sun so shi Roshan ne ya fito ya ɗauka, haka suka bar part ɗin suka koma can part ɗin su ....

Baiwar Allah room ɗinta ta shiga ta zauna a bakin gado ta ciro abun leda taga wani ƙaton gift ata baya an rubuta "from Baiwar ALLAH..."

Abun kuma sai ya ɗaure mata kai cike da mamaki take faɗin "Ni kuma?..."

tana buɗe ledar jikin gift ɗin taga wani danƙareren abaya mai sheƙin gaske ga kuma wata takarda ta faɗo, cikin da mamaki ta ɗauka tareda buɗe takardar ta soma karanta wa kamar haka "Amincin Allah ya tabbata a gareki gimbiyar mata, kiyi haƙuri a bisa abubuwan da nake miki a cikin mutane nake nuna bana sonki, kema kinsan ina matuƙar ƙaunar ki domin bazan iya ɗanɗanar zuman ki na barki haka kawai ba, kina da zaƙin da ba ko wata mace ce take da shi ba, please haɗuwar mu a hotel ina jiranki da yamma, tinda Roshan ya dawo dole sai a hotel zamuna haɗuwa, kar ki bar Roshan ya sani domin ni da kaina zan zo na ɗauke ki ba tare da kowa ya sani ba, sannan ga saƙon Abayar da kika ce na kawo miki, ki kula mun da kan ki, *DAGA MASOYINKI RAZHDEEN TWINS ƊIN MIJINKI....* "

A zabure Baiwar ALLAH ta miƙe tsaye hawaye duk ya wanke takardar domin tinda ta fara karanta wa take zubar da hawaye tsabar takaicin sharrin da aka ƙulla mata saboda a rabata da mijinta,
cikin kuka take furta "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un na shiga uku wannan wani irin ƙalubale nake fuskanta a rayuwa ta ce, haba Razhdeen ka rasa wani irin sharri zaka yi mun sai na zina? Ƙiyayyar da kai haka daman wayyo Allah nahh..."

Da gudu ta shige toilet ta yayyaga takardar sannan ta sa a toilet tayi floshing ɗinsa, ta fito tana kuka ta ɗauki rigar da ledar gift ɗin ta zura a cikin baƙar ledar tana ciki,
Ba shiri ta ɗauki mayafinta ta fice, ta yanke cewa zata je har gidan Razhdeen ta same shi, yau sai ya faɗa mata dalilin da yasa ya yi mata irin wannan sharrin sannan ta bashi rigar sa, har ta tsara irin cin mutuncin da zata yi masa, sai kuma yanzu take jin takaicin yaga takardar da tayi domin shi zai zamo mata shaida amma tayi hakan ne saboda gudun kar wani ya gani especially Roshan, duk da tasan Razhdeen yayi hakane saboda Roshan ya gani ya raba Auren su,
wani irin ƙololuwar baƙin ciki ne a ranta, bata taɓa jin tsanar Razhdeen ba sai yau, zata je gidan Razhdeen ne ta dawo kafin Roshan ya farka daga bacci,
Zuwa tayi ta samu Security ɗaya ta sanar masa cewa Roshan ne ya aike ta gidan twins ɗinsa ya kaita da mota, security jin yanda ta tsara masa zance yasa shi yadda ya ɗauke ta a mota suka tafi...

Su kuwa Pinky da Rukky su suka zauna a ɗaki suka shirya rubutunsu saboda suna so su haɗa Roshan da Baiwar ALLAH rigima har su rabu, idan Roshan ya sake ta sun san Razhdeen ba Auranta zai yi ba, su suke kwata-kwata tabar gidan su ta je ta nemi iyayenta...
Sunji haushi sosai da ba Roshan bane ya ɗauka domin in har shine dole zai sanar wa Abbah halin da ake ciki, shi kuwa Abbah zai kori Baiwar Allah ne bayan Roshan ya sake ta, shi kuma Razhdeen sai dai Abbah yayi fushi da shi na wani ɗan lokaci amma bai isa ya kore shi ba, duk abinda suka shirya ba hakan ne ya faru ba, amma zasu sake shirya wani plan ɗin a cewar su .....


Baiwar ALLAH bayan sun isa gidan Razhdeen security gidan ne ya buɗe musu suka shiga bayan yasan motar gidan Chief ne,
A wurin parking aka Parker motar, tana riƙe da ledar tayi saurin fita da cikin motar ta nufi ƙofar babban falon gidan cikin fushi...

Shi kuwa Razhdeen yana zaune a falo yana jiran fitowar Ƴar Amana zai kaita school domin yanzu tinda ya dawo yake kaita da kansa saboda tsaro, yanzu ya ga ba ƙaramar yarinya bace tana buƙatar tsaro domin ko security yanzu bai yadda da ya rinƙa kaita ba, ya kasa yadda shin kishinta yake ne ko kuma duk a cikin tsaro ne....

Ƴar Amana tana can room ɗinta tana ta faman gyare-gyare da shirye-shirye ta kammala saka uniform ɗinta tsab sai kallon mirror take domin tana so koda yaushe ta rinƙa burge Razhdeen, domin taga duk lokacin da suke tare yana rikice wa sosai a kanta ita kuma hakan burgeta yake domin ba ƙaramin jinsa take a ranta ba, wuni guda idan bata gan shi ba ta rinƙa shiga damuwa kenam, yanzu ko a makaranta bata nutsuwa tayi karatu sai fuskarsa ya rinƙa mata gizo, a koda yaushe tunaninsa take, tunani yaƙi ƙarewa ta rasa gane kanta, tana jin wani iri sosai akan sa, ko bacci zata yi sai ta daɗe tana kallon fuskar sa tukun ta iya komawa room ɗinta,
(Baƙuwar lovayya kenam 😁😁)

Tsayawa tayi a gaban mirror bayan ta gama shirinta tsab tana kallon kanta amma sai dai hankalinta ba'a kanta yake ba ta shiga dogon tunani kuma tunanin bazai wuce Razhdeen ɗin ba....


Baiwar ALLAH tsayawa tayi a bakin ƙofa tana bubbuga ƙafar falo da ƙarfin gaske domin a cikin ɓacin rai take bugawa tana zumuɗin yazo ya buɗe ta yi masa wankin babban bargo...

Yana zaune haka yake jin bugun ƙofa kamar za'a ɓalla ƙofar tsabar ƙarfin bugun,
Haka shima ya tashi a fusace yayi bakin ƙofar zai buɗe domin ya ci alwashin kowa waye zai ya zabge shi da mari indai ba Abbah ko Roshan ba.....




*ALHAMDULILLAH*
*ALHAMDULILLAH*
*ALHAMDULILLAH*

*ALHAMDULILLAH ALA KULLI HALI....*

*ALLAH NA GODE MAKA DAKA KAWO MU ƘARSHE BOOK 2 NA LITTAFIN MY ENEMY WATO MAƘIYI NAH...*

*MU HAƊU A LITTAFI NA 3 WATO MY ENEMY TAKUN ƘARSHE...*

*WAƊANDA BASU BIYA KUƊIN BOOK 3 BA KU SAMU KU BIYA TINDA WURI...*


*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL*
*9065443871, OPAY BANK*
*PAYMENT 300₦...*


*MA SHA ALLAH...*


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login