Showing 69001 words to 72000 words out of 89400 words
ce "ban sani ba Nima, haka na same ta a sume..."
Roshan duba ta yayi sosai ya ga jini ya ɓata farin wandon ta, girgiza kai ya yi sannan ya ce "ba sai an kaita asibiti ba ta fara period ne..."
Yasa hannu ya karɓe ta tare da yi mata ɗaukar luɗa ya nufi ɗakinta, yana haurawa ya kwantar da ita akan gado sannan ya sanar wa Madam Blessing cewa "ki canza mata kaya sannan ki shirya ta, fatan dai kuna da pad?..."
Madam Blessing ta ɗaga kai tare da faɗin "eh akwai pad..."
Ya ce "to kisa mata, zan je na kawo alluran da za'ayi mata ta dawo setting, sannan tana buƙatar ledar ruwa domin naga ba ƙaramin jikkata tayi ba..."
Yana ƙarasa maganar sai ga ƙira ya shugo masa waya, dubawa yayi yaga Razhdeen ne ya ɗauka yana sakin murmushi, kafin buɗe baki Razhdeen ya katsar da shi da cewa "ka je ka dubo mun Sarah meya faru da ita..."
Roshan sake baki yayi yana jinsa yana mamakin taya yasan bata da lafiya,
Roshan ne ya ce "kai da kake can taya kasan wani abu ya faru da ita?..."
Razhdeen ya ce "haka kawai zuciyata take bugawa da kowani harafi na sunanta, gaba ɗaya na kasa kwantar da hakalina..."
Roshan cike da mamaki ya ce "to pah, kwantar da hankalin ka yanzu haka ina gidan, ciwon mara take fama da shi na period, yanzu haka zan fita naje na kawo wasu magungunan da zata na sha da allurar da za'ayi mata..."
Razhdeen ya ce "i known, daman nasan akwai abinda ya faru da ita, ba haka kawai zuciyata take bugawa ba kuma sannan na ƙira wayan Blessing yafi sau nawa she didn't answered dole zan damu, please you should better take care about her because she's my partner of mind, please bana so ta raunana sosai..."
Roshan jinjina kai yayi sannan ya ce "okay don't worry the father of lover not soldier in dis time..."
Razhdeen ne ya katse shi da cewa "who told you? kar kayi tunanin kawo mun maganar soyayya domin she is a younger girl how comes zan yi soyayya da ita, but ba ƙaramin raina mun wayo kayi ba twins..."
Roshan yana dariya ya ce "Ni ne ma ka ke raina mun wayo ai my Man, ka mayar ni yaro ƙarami..."
Razhdeen ya ce "Please ka dakatar da wannan shirmen nakan kayi mata video ka tura mun inason ganin a wani hali take..."
Roshan kamar yanda Razhdeen ya ce hakan ya yi daga baya ya tura masa, a yayin da Roshan ya fice zai je nemo maganunnuwa, ta wani bangaren kuma zuciyar sa na kuka ganin yanda Razhdeen yake nuna matuƙar kulawa akan Ƴar Amana amma sam baya maganar Baiwar ALLAH, ita kuma shine a zuciyar ta, ganin son maso wani take kuma bata son zama a gidan mijin da Allah ya zaɓa mata yasa yake jin takaici....
Da wannan takaicin ya fice.
Ata ɓangaren Razhdeen kuma ganin video yasa shi miƙewa tsaye daga zaune, ganin irin girman da Ƴar Amana tayi ta zama cikakkiyar mace, yarinyar da yake raina shekarun ta gashi har tafi wata mai shekara 25 cikar jiki, da breast da hips haɗe da ƙugu duk a cike, wani irin haɗiyar yawu yayi yana ƙareta da kallo kamar wanda yake gaban ta, girman yarinyar yarinyar ba ƙaramin mamaki ta bashi ba,
yana cikin wannan tunanin yaji an masa magana ta baya, switch ɗin wayar yayi tare da juya wa ganin Madam Parveen ce ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da try ɗin kayan Abinci tana ƙoƙarin jera su akan dinning, cikin yaren turanci take faɗin "M.G Razhdeen meya faru ne naga ka miƙe tsaye..."
Ba tare da ya furta komai ba ya koma ya zauna yana hasasho ƴar Amana,
Madam Parveen ce ta ƙaraso cikin falon ta zauna a ɗayan kujera tana facing ɗin Razhdeen kamar zata yi kuka take faɗin "yanzu kaima zaka ce baka san yanda Mohandas ya shiga ba?..."
Razhdeen ya ce "tinda har ya aiko muku letter cewar yayi Aure sannan babu wanda zai san a yanda suke ai shikenam sai kuyi haƙuri ku jira bayyanowar su, duk da nasan ba son ƙanwata Minal kuke ba kuma most especially ya musulunta ba tare da sanin ku ba, duk wannan abubuwan da ya aikata ban san da su ba, ban san ya musulunta ba sannan ban san yayi Auren sirri da Minal ba sai labarin tafiyar su naji..."
Madam Parveen hawaye ne yake gangaro mata ta ce "shikenam yanzu a cikin yara uku bana tare da guda biyu? iya ɗaya nake da shi yanzu, Rakesh nake gani naji daɗi, Amreesh na rasa ta tin tana yarinya, yanzu kuma Mohandas shima ya guje ni, Ni in har zai dawo gare Ni na amince ya zauna da matar sa sannan ya zauna cikin musuluncin da ya zaɓa...."
Ta bayanta taji an katse ta da cewa "impossible, Mohandas tinda ya musulunta to yabar family na, sannan tinda har yayi Auren sirri hakan ma da ƴar maƙiyi na to ya aikata babban laifi saboda haka na sallame shi, don haka ko da shi ko ba shi we are completed family..."
Duk wannan maganganun Daddyn su ne ya fito daga part ɗinsa yake faɗin haka wato
"Chief Of Defence Staff" shugaban sojojin ƙasar U.S ya ƙarasa maganar tare da zama shima akan kujera.
Madam Parveen kallonsa tayi tare da faɗin "we are not complete, Mohandas he's my first born bazan taɓa cire shi a raina ba ina kan son sa har gobe, sannan my last born na rasa ta since how comes zaka ce we are completed? why? tell me your reason..."
Daddy ya gyara zamansa sannan ya ce "You want me to tell you my reason abi, okay the firstly my daughter Amreesh she has already passed, ta mutu kuma bamu isa mu dawo da ita ba sai dai mu tuna ta sannan muyi mata addu'a, shi kuma Mohandas ya bijire mana yayi tafiyar sa that means yanzu baya buƙatar mu tinda mun gama masa komai, munyi sanadiyar kawo shi duniya sannan mun masa gata yanzu kuma mun gama masa amfani,
Na fitar da shi daga cikin ƴaƴan da na haifa..."
Rakesh ne ya shugo shima jikinsa a sanyaye jin abinda Daddynsu yake faɗi, dawowar sa daga wurin aiki kenam gashi sanye da kakin soja a jikinsa,
Gaishe su yayi zai zauna kenam Madam Parveen ta dakatar da shi da cewa "your welcome my Son but kaje ka rage kayan jikinka sai kazo mu je dinning..."
Ko ƙara kula Daddy bata yi ba saboda yanzu zaiyi abinda zai sa suyi faɗa, kowa yana ji da aikin ɗamarar sa.
Daddy ne ya kalli Razhdeen tare da sakin murmushi ya ce "M.G my best soldier naga aikin da kayi jiya ya burge ni sosai, kayi ƙoƙari..."
Razhdeen ya ce "thank you Dad..."
Razhdeen ne ya kuma yin magana yana faɗin "Dad Please i want to ask you something..."
Daddy ya ce "okay go ahead..."
Razhdeen ya fara magana da cewa "meyasa kake gava da mahaifina sannan baka son haɗa jinsi da shi amma kuma Ni ka ɗauke ni tamkar ɗan ka, ko kaɗan baka son ɓacin raina, a koda yaushe ja na kake a jikinka kuma nasan iya Ni kaɗai kake so acikin yaran mahaifina i don't know why...."
Madam Parveen ce ta kalli Chief domin ta daɗe tana bashi haƙuri akan yaje su sasanta kansu ko dan saboda Razhdeen,
Razhdeen bai taɓa masa wannan tambayar ba sai yau,
Shi kuma Chief Of Defence ya ce "bazai taɓa zuwa yanda Chief Of Army's Nigeria yake ba sai dai idan shine ya fara zuwa yanda yake domin a cewar sa ai shine sama da shi...
Daddy ya kalli Razhdeen sannan ya ce "idan a tsakanin kai da Rakesh ku ka samu matsala a wurin aikin soja shin acikin ku wa ya kamata wani ya gurfar da kai ya nemi yafiya?...."
Razhdeen jin a wurin aiki suka samu matsala yasa shi cewa "Rakesh ne ya kamata ya fara neman maslaha domin Ni ne sama da shi, kuma bugu da ƙari a wurin aikin ne ba'a ordinary place ba..."
Daddy ya ce "Good my best, to shi Abbah ku yayi laifi amma girman kai yasa ya kasa neman sulhu tin tsawon shekaru domin tin ina Nigeria da zama yanzu shekara 23 kenam, i swear to God in har ya zo ya nemi sulhu zan yafe masa tunda a ƙasa na yake..."
Jinjina kai Razhdeen yayi sannan ya ce "but meya haɗa ku?..."
Daddy ya ce "tin a Nigeria nine Ogansa, sun fita aiki yaje ya jefar da bindigarsa, ganin ina mutunci sosai da shi kuma a lokacin abokai muke sai dai igiyar mu ba ɗaya ba yasa na ce sai dai yayi abu biyu na ɓatan gun a wurinsa, zaɓi biyu ko yasa hannu a takardar Apologize letter ya bada haƙuri kenam albarkacin ina tare da shi, inda ace wani ne daban dole sai ya biya ko kuma a kulle shi, sannan nace ko ya biya kuɗin gun in yaso ya biya rabin kuɗin ni kuma saina taya shi biyan rabin shin banyi masa halacci ba ? to a lokacin sai ya ɗauki takardar bada haƙuri ya yage a gaba na sannan ya sanar mun cewa wai ina so na tozarta shi ne yasa na bashi takardar saka hannu, sannan ya ce ba zai biya kuɗin ba tinda wurin yaƙi yake kuma a lokacin anji masa rauni a ƙafa daƙer yake iya tafiya a lokacin, mahaifinku ya gama mun rashin kunya sannan ya fice a office ɗina yana ganin bazan iya koransa daga aikin soja ba amma kada ya manta nima fa inada Oganni, bayan kwana biyu ban san ya akayi ba ashe sauran shuwagabannin sunji labarin abinda ya faru na ɓatan gun mai bala'in tsada hakan yasa suka sa aka kamo mahaifin ku suka kulle shi na tsawon wata uku, hakan ma Ni nayi shige da fice nasa aka fito da shi daƙer domin tsawon zaman da zai yi a kulle tsawon shekara uku ne amma saboda jajircewar da nayi yasa na fito da shi a cikin wata uku, a lokacin ba ƙaramin kashe kuɗi nayi ba, dukiyata haka na ɗauka ina zubar da su duk a saboda mahaifinku ya fito daga uƙubar da yake,
Ashe shi a tunaninsa nine nasa aka kulle shi, amma bai san Ni nayi ƙoƙari na fito da shi ba domin hanawa nayi a sanar da shi har yau bai sani ba, kuma wallahi Ni babu yanda za'ayi nasa a kulle shi duk girman laifin da ya mun domin tin muna primary muke tare, muka yi Junior tare har muka yi secondary, daga nan muka rabu na je nayi deegre da master ɗina a anan ƙasar U.S na soldier,
kuma na riga mahaifinku shiga soja bayan wasu shekaru shima ya shiga, bayan ya fito daga maƙarƙama ya same ni anan ma ba ƙaramin matsala muka samu ba abunda yasa na biye masa kuma shine ya ƙirani da Arnen banza kuma ina mazannin Ogansa, daga lokacin na fusata munyi faɗa sosai daƙer aka raba mu, har an bashi takardar barin aiki saboda yayi faɗa da Ogansa nasa aka dawo da shi wurin aikinsa, kuma matakin da yake yanzu na chief Of Army's shine matakin da nake a lokacin, bari na nigeria bayan an ƙara mun matsayi aka dawo dani nan ƙasar Austrolia a wani za'a bada matsayi na a nigeria nasa aka bawa mahaifinku duk zaman gavan da muke, amma har yau bai sani ba,
Sannan kai kuma a lokacin da za'a ɗauki sojoji anan ƙasar na bada sunanka aka aika maka can Nigeria nasan har yau mahaifinka bai san cewa ni ne na ɗauke ka ba, sannan na kai ka matsayin da a lokacin baka kai kaje ba, kuma sai akayi sa'a kana aikin da ya kamata, na kuma ɗauke ka tamƙar ɗan dana haifa, nake jan ka a jiki har muka shaƙu sosai ka kuma ɗauki nan gidan tamkar gidanku,
Kuma dake daman tin kuna yara kai da twins ɗinka Roshan kuka shiga zuciyata, ina masifar son twins a rayuwata, ko zan yi gava da mahaifinku da kuma sauran to ku kai da Roshan bazan taɓa ɗaukar ku a haka ba,
Daga lokacin nasan cewa Christal sun fi musulmi haƙuri da juriya da kuma tawakkali duk da nasan a cikin musulman ba duk haka bane, to kaji dalilin samu matsala ta da mahaifinku...."
Jinjina kai Razhdeen yayi domin a halin yanzu bashi da bakin magana tinda kowa yasan Abbah ne bashi da gaskiya, kuma Chief Of Defence yayi musu ƙoƙari sosai ya yi halacci ba ɗan kaɗan ba....
Duk maganganun da Chief yayi ashe Razhdeen yana yin recording domin tin kafin nan ma yasan Abbah ne da laifi, yayi recording ne saboda akwai lokacin da zai kunna wa Abbah ya ji irin alkhairi da Abokin gavan sa yayi musu a lokacin da yake cikin gava da shi, domin Razhdeen ba lallai ya iya bayyanar da wannan bayani ba hakan yasa yayi recording...
Madam Parveen ta ce "Allah ya dai-dai ta tsakanin ku tinda yanzu kun fara haɗa zuriya ɗaya..."
Daddy ya ce "damuwa ta bawai Auran yarinyar da Mohandas yayi ba ne, babban damuwar shine guduwar da yayi kuma Ni har cikin zuciyata bana son musulunci..."
Madam Parveen ta ce "Ohhhh ka manta ranar abunda kace?..."
Daddy ya ce "what?..."
Ta ce "ka ce inda ace Daughter ka Amreesh tana nan da ka Aurar da ita a Razhdeen,
shin ba haka kace ba?..."
Rakesh yana zaune ya ce "ey tabbas duk muna nan har shi kan shi M.G Razh..."
Razhdeen dai girgiza kai yayi yana ƙwaƙulo murmushi domin tin lokacin da aka haifi Amreesh Chief yayi alƙawarin ta a Razhdeen, kuma shima Razhdeen yaso Amreesh tin tana yarinyar ta, saboda ita kullum yake zuwa gidan su tin suna Nigeria kafin Abbah da Daddy su samu matsala,
Amreesh ba ƙaramin shiga cikin zuciyar Razhdeen tayi ba, tin daga lokacin yayi alƙawari a kansa cewa babu yarinyar da zai Aura in ba Amreesh ba, ya ɗau alƙawarin zai jira ta har ta girma, yana da ƙwarin gwiwa sosai akanta domin Daddynta shima ya sanar cewa yayi Alƙawari idan Amreesh ta girma zai sa ta musulunta sannan ya Aura mata Razhdeen ya kuma cewa da sharaɗi ɗaya,
A lokacin kowa yana son jin wani irin sharaɗi ne wannan kuma har Abbah mahaifin