Showing 3001 words to 6000 words out of 89400 words

Chapter 2 - MY ENEMY BOOK 2 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

2506

adadin dukiyarda nake da shi ba, naji ɗan uwana Razhdeen ya fini yawan dukiya amma inaso ki sani cewa ko a yanzu nace ya bani rabin dukiyarsa ba musu zai bani saboda mu ɗin gudan jini ne, nashi nawa ne haka kuma nawa nashi ne,
Ƙanwarki kuma ki sanar mata cewa koni Roshan bazata samu shiga ba balle my twins da ko ƴar aiki bazai ɗauketa ba balle a matsayin mata..."

Hajiya Maamie kama kunkumi tayi tana kallonsa cike da mamakin maganganun da yake jifarta dasu,

Murmushi tayi tana yatsina fuska tace "Hmmm! Roshan kenam, Ni baka isheni kallo ba, bata kai nake ba ka matsa ka bawa ɗan uwanka wuri mu magantu..."

Roshan ɗaga kafaɗarsa yayi tareda faɗin "okay fine! Idan kikayi dashi tamkar kinyi dani ne..."

Ya ƙarasa maganar tareda komawa gefe,
Razhdeen ne ya maye gurbin da Roshan ya tsaya shima yana fuskarta da hannayensa a goye kan ƙirjinsa, fuska a ɗaure ba Annuri.

Maamie itama kallonsa take fuska a sake sai faman sakin murmushi take tace "Razhdeen inaso muyi magana ta fahimtar juna, kaga yanzu mun zama ɗaya Ramlat tamkar ƴar uwarka ce, kuma ka dubeta ita ɗin marainiya ce bamuda uwa babu uba, dan ALLAH ka temaka ka Aureta ko zata samu farin ciki,
Ni zanyi iya ƙoƙarina naga ka Aureta tinda wannan matsolon Sarkin ya kasa aiwatar da komai...."

Saida ta kammala zantuttukanta tass sannan tayi shuru tana son jin amsar da zai bata, itadai addu'arta shine yace ya amince..."

Sakin nannauyar numfashi yayi sannan yace "kin gama?..."

Tace "kai nake sauraro Razhdeen..."

Kafin ta ƙibta ido har ya kai hannu ya zabga mata wani irin gigitaccen marin da bata san lokacin da ta dungura kan kujera tayi tsalle ta faɗa bayan kujerar ba,

Kaf waran babu wanda bai tsorita da wannan marin ba,
hatta shima mai martaba bai san lokacin daya miƙe tsaye ba, ita kuwa Ramlat bata san ta zamo daga kan kujerar da take ba, ta kafa gwiwowinta a ƙasan carpet,
Itama INDO ja da baya tayi tana zazzaro ido waje hannayenta a toshe da bakinta,
Shima Roshan bai taɓa tunanin Razhdeen zai iya marinta ba, abun yayi matuƙar bashi mamaki sosai kuma ya jinjina wa zafin ransan nan...

Maamie tana kwance a bayan kujera shuru bata ɗago ba har zuwa wannan lokacin,

Mai martaba murya na kakkarwa yace "Razhdeen meka aikata haka? shin bakada hankali ne? Matata ce fah? ka manta yanda nake a wurinka?..."

Cikin ɓacin rai Razhdeen yake kallonsa tareda faɗin "bana juran ganin irin waɗannan dabbobin matan, saboda haka ne yasa bana zama inuwa ɗaya da matar Abbanah saboda nasan wata rana zan iya illata ta, duk da yanzu naji labarin basa tare, don haka itama wannan tabi a hankali kafin nabar ƙasar nan..."

yana kammalawa ya juya zai fita shima Roshan bin bayansa yayi zasu fice a tare,
Juyowa Roshan yayi yana kallon Mai martaba cikin tausayawa yace "Uncle akwai ɗauri a jikin ka Please ka nemi maganin karya asiri domin ba haka aka barka ba, Uncle wanda na sani a baya bakai bane yanzu, duk zafin ran Abbanah baiyi ka ba amma yau kaine nake gani haka mace tafi ƙarfinka? Amma zan tayaka da addu'a karka damu...."

yana kammalawa shima ya fice, kai tsaye part ɗin su suka nufa...

Mai martaba girgiza kai yayi domin al'amarin yana shirin fin ƙarfinsa,
kallon yanda INDO take yayi sannan yace "ki kai musu abinci basu ci komai ba tinda suka zo, sannan ki lallamesu su ci karsu zauna da yunwa..."

Amsa masa tayi cikin girmamawa ta wuce kitchen,

yana tsaye yaji kukan Ramlat tana faɗin "Abul ta mutu kazo ka duba ta bata motsi wayyo Allah nahhhh..."

tana kuka sai faman jijjigata take amma Maamie ko motsi babu, Saida mai martaba ya zagayo bayan kujerar ya tarar da ita kwance ga fuska har ya kumbura,
a hankali ya furta cewa "kije ki ɗauko mun ruwan sanyi.."

Da gudu Ramlat ta miƙe taje frig ta ɗauko jug mai ruwan sanyi ta kawo,
ana watsa mata kuwa ta farfaɗo tana sauƙe numfashi sama-sama,
tareda faɗin "aina nake? ina ne Nam? gida nake son zuwa.."

Daƙer mai martaba ya ɗagota sannan ya wuce da ita bedroom ɗinta tana sumbatu cikin rashin hankali domin ji take kanta yana juyawa bata san a yanda hankalinta yake ba, da haka aka shige da ita ciki...




*A TANTANCE MUN*
*SHIN DA HAJIYA MAAMIE DA KUMA HAJIYA KILISHI WACCE TAFI WULAƘANCI????*


asmeetah writer ✍️




*MY ENEMY _*

🫦 مقىينا 🫦


Mallakin
أسماء محمد أولا 🥳

Asmeetah (giaɗe writer)


STEP TWO

sorry for the mistake a farkon step two nasa 51 to 52 maɗorin ƙarshen step one neh, naga wasu suna mun complain akan anyi musu nisa sosai a step two, toh ba haka bane farkon ne, but yanzu zamu cigaba akan page 3 and 4 na step two

*Chapter* 3 and 4






Mamie kamar wata zautacciya haka ta rikice bata san yanda kanta yake ba,
lalume ta fara yi tareda faɗin "ina Ramlat? Ramlat kina ina bana gani dai..."

Ramlat ce ta zauna gefenta a bakin gado ta riƙo hannayenta tana faɗin "Aunty gani nan dai..."

Maamie tana kuka tana cewa "duba mun akwai fuska a jikina?.."
Ramlat tace "akwai fuska mana"
Maamie ta kuma cewa "ki duba da kyau shin ba'a rabe mun kaina da gangan jikina ba? yanzu haka kina kallon fuskata? naga duhu nake gani sannan banji alamun kai a jikina ba..."

Ramlat tace "haba Maamie ai duk ke kika jawo haka, gashi kema Uncle Deen bai barki ba balle Ni,
shin har yanzu kina kan bakarki ne? gashi kinyi mun biyu babu shima Yaya Roshan ɗin yana shirin kuɓuce mun..."

Maamie tace "kina nufin kice ba Razhdeen zaki Aura ba? toh wallahi tallafi ko naman jikina yake yanke wa kullum saina sa ya Aureki dolensa..."

"Hmmm! kece a wahalai nidai zanbi tawa hanya yanda bazan jawo a illatani ba...". a cewar Ramlat.

Maamie cewa tayi "au ina nema miki gidan daɗi ke kuma kina mai watsa mun ƙasa a ido?..."
cikin ɓacin rai Ramlah tace "shikenam Aunty Maamie kiyi duk yanda kika ga ya dace..."
tana kaiwa nan tayi ficewarta,

Maamie cikin ɗaga murya tace "Ai kuwa zanyi abinda ya dace idan naje wurin Boka matsagwal, wallahi sai Razhdeen yazo yana binki har da tsuguno..."
ta ƙarasa tana jan numfashi sama-sama ga fuska yanda ya kumbura suntum har shatin photon hannunsa ake gani akan fuskar...


🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️

ƳAR AMANA tana zaune a yanda suka saba hallaruwa tana riƙe da jitar ta sai kaɗawa take,
Dake duk mutanen wurin ba wanda baya jin daɗin sautin jitarta,
tana cikin wannan halin sai ga wata danƙararriyar mota baƙa ƙatuwa wasu matasa ne su biyu suka fito suna rufe da fuskokinsu da baƙar hula suka yo kan Ƴar Amana dake zaune,
duk waran babu wanda bai tsorita da ganinsu ba domin har da masu riƙe da bindiga, ɗagowa tayi tana binsu da kallo kafin ta ankara har sun finciko hannunta, sun ɗagata sama tana bubbugan bayansu haɗe da shure-shure amma ba bakin yin ihun,
kafin kace mai tsofin wurin sun haɗe waran da kururuwan "wayyo ɓarayi mun shiga uku, akawo mana ɗauki ƴan fashi...."
Nan danan suka ja motarsu a ɗari suka bar wurin,
daman sun juma suna target ɗinta tin barinta a hannunsu ogansu ya hura musu wuta akan sai sun nemota sai yau Allah ya bada sa'ar kamata...

Cikin Daji aka nufa da ita already sun rufe mata fuska da baƙin ƙyalle..


🤏Baiwar ALLAH tin da Aunty Yolash tazo take faman gyarata irin gyaran Amare duk da bata son Auren ko kaɗa, har ila yau fuskar Razhdeen ne yake mata gizo, wani sa'in sai taji kamar ta fita taje ta nemo Razhdeen ta roƙe shi akan ya Aureta,
kwata-kwata batada wani sukuni, ba wai bata son Roshan bane Ita dai zuciyarta Razhdeen ya zaɓa mata kuma shi yafi dacewa da ita amma babu yanda ta iya...

Minal kuma tana can gidan Razhdeen ita da Mohandas ita take masa girki duk da bata iya sosai ba sai ya saka mata hannu, wani sa'in kuma shi yake yi da kansa,
Soyayya iya soyayya suna shanta sun fahimci juna sosai domin har Mohandas ya amince akan cewa bayan bikin Roshan shima zai musulunta sannan a ɗaura musu Aure a ɓoye in har Abbah bai amince ba....


Misalin ƙarfe 2 na dare Roshan ya yi sujjada yana sallar lafula, shi kuwa Razhdeen yana saman gadonsu yana karanta karatun Alkur'ani mai girma.

Hajiya Maamie kuwa ta rigada ta ziyarci Bokanta akan maganar Auren Razhdeen da Ramlat, ya amsa mata da cewa komai zai iya yuwa da zaran tabi duk dokokin da ya sharɗanta mata,
ya bata wani ɗan ƙaramin turare wanda Ramlat zata shafa sannan ta nufin wurin Razhdeen, da zaran ya shaƙi wannan ƙamshin turaren shikenam aikin gama ya gama kuma da sunansa akayi amfani,
Hajiya Maamie tayi matuƙar yin farin ciki sosai saboda wannan ƙaramin al'amari ne,
tana murna tace "shikenam da zaran ya shaƙa zai rinƙa bin Ramlat kenam? kamar irin wanda ka bani nayi amfani dashi waran toshe bakin mai martaba Koh?.."
Boka yace "dokar wannan turaren shine muddin ya shaƙi ƙamshi toh asiri yayi dai dai, in kuma wari ya shaƙa toh al'amari ya ɓaci domin babu wani tsafin da zai shafe shi, tashi kije.."
ta tashi cikin zumuɗi ta tafi,

Washe gari da sassafe Hajiya Maamie taje ɗakin Ramlat ta tashe ta daga bacci tareda faɗin
"Ke dallah tashi mun samu abun ƙaruwa..."
tayi maganar dai-dain lokacin da take shirin zama a bakin gado,
Ramlat tashi tayi tana murtuƙe fuska domin ta tsani a tashe ta a bacci indai ba lokacin tashinta ne yayi ba,
tana turo baki tace "wai meye ne Aunty Maamie?..."

Maamie tace "naje wurin Boka ya bani turaren bita zaizai kuma ba makawa asirin nan saiya kamashi domin Boka bai taɓa yin rashin nasara ba..."

Ramlat tsayawa tayi tana kallonta cike da mamaki take girgiza kai sannan tace "wai Aunty Maamie bazaki daina zuwa wurin bokan nan ba koh? meye amfanin haka? toh Ni gaskiya ki daina sakoni a lissafin waɗanda boka zaiyi musu aiki...."
ta ƙarasa maganar tana murguɗa baki...

Maamie ta ƙafeta da kallo tareda riƙe haɓarta tace "iyyeeee! Lallai yarinyar nan kema na kusa nayi aiki akanki indai zakina bijire mun wallahi, kuma dole sai kinyi aikinda Boka yace kiyi aikin banza kawai, wawiya arziƙi na biyoki kina guduwa masa tsabar shirme irin nakin,
dallah malama tashi ki shashshafa turaren ki kai musu abincin breakfast tin kafin wancan matsiyaciyar ta kai musu uwar shishshigi..."

"Toh naji..."
A cewar Ramlat wacce take ƙoƙarin tashi, tayi duk abinda Maamie tasa ta wato turaren nan haka yake tashi yana bada zazzaƙar ƙamshi, haka suka fice a tare kai tsaye kitchen suka nufa, suka tarar an kammala girki an saka musu a kuloli na musamman,
Ɗaukar kayan girki tayi ta nufi Falo tana shirin ficewa, saiga INDO daga upstairs tin kafin ta ƙarasa sauƙowa tace "Ramlat ina zaki da kulolin abinci?..."
Maamie wacce take zaune a kujerar Falo ta ɗora ɗaya akan ɗaya sai wani irin kallo take watsawa INDO, baki a murguɗe tace "yanda kika aiketa uwar shishshigi, kina so a baki ki kaiwa dangi ne? don naga akwai tamowa a jikinsu..."

Sauƙe numfashi INDO tayi domin ta fara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login