Showing 51001 words to 54000 words out of 89400 words
ganin bazai iya kyale ta haka ba yasa shi buɗe murfin motar sa ya nufi part ɗin Roshan..
Baiwar ALLAH bayan shigar ta cikin falonta zama tayi a kujerar falon tana sabinta kukan ta, tana cikin wannan halin ta soma jin ana knocking ƙofar falon, da sauri ta share hawayen tayi tunanin Roshan ne bata so ta nuna masa damuwarta saboda kar ya ƙara samun Abbah da maganar, buɗe ƙofar tayi kwatsam ta tarar da Razhdeen a tsaye a bakin ƙofar yana mata wani irin kallo na ƙasƙanci wato kallon up and down...
Kutsawa yayi ya shige ciki a yayin da ita kuma take ja da baya domin ba ƙaramin ƙwarjini yake mata ba,
ma ta nuni yayi da ta zauna a kujera ba musu haka ta zauna eyes ɗinta akansa shima jawo glass table yayi ya zauna a front ɗinta suna fuskantar juna, fuska a haɗe ya ce "ki kalli cikin eyes ɗina kiga shin nayi kala da abokin wasan ki?..."
Shuru tayi bata bashi amsa ba sai kallonsa da take ko ƙibta idon bata yi, cikin fushi ya cabki wuyanta ya riƙe sosai yana zazzaro mata manyan eyes ɗinsa tare da faɗin "ke ko a ƴar aikin matata bazan ɗauke ki ba domin bakiyi kala da wacce zata zauna a gidan da nake ba balle na haɗa jinsi da ke, kinyi kuskure sosai da kika nuna kina sona domin ciwon haukarki ne yake rinjayarki, naso baki janye ƙudirin ki ba wallahi tallahi nayi niyar nasa hannu na murɗe miki wuya har sai kin bar duniyan nan, bana sonki! na tsane ki, ki janye jikinki daga gare ni sannan ki kawar da idanuwanki daga yanda nake idan ba haka ba zan kashe ki ne har lahira, nonsense girl ƙazama marar hankali, wawiya dabbiya..."
Baiwar ALLAH ƙirjinta ne yake wani irin bugawa da sauri ta kawar da fuskarta gefe tana rufe da eyes ɗinta taji zagi kala-kala da cin mutuncin amma babu cin mutuncin da yafi ƙona mata rai kamar na Razhdeen, jin yanda yake ta faɗa mata maganganu yasa zuciyarta hargutsa a gigice ta cabki kwalar rigarsa tare da miƙe wa tsaye tana kuka ta ce "Uncle Deen don ina sonka bashi zai sa na tsaya kana faɗa mun maganganu son ranka ba har kana sako iyayena a ciki waɗanda basu san a wani hali nake ciki ba shin sun mutu ko suna raye Allahu A'alamu, dan ALLAH kaji tsoron Allah ka dai na azabtar da zuciyar da ta amince da kai, don ina sonka bashi zai sa ka wulakanta ni ba..."
Razhdeen ganin yanda take riƙe da kwalar rigarsa wanda tinda yake mace bata taɓa sa hannu da niyar riƙe gaban rigar sa ba hatta namiji balle mace a fusace yasa bayan tafin hannunsa ya zabga mata mari rai a ɓace,
A gigice ta faɗa kan kujera tare da sakin wata ƴar ƙara, tana riƙe da gefen fuska wani irin kuka take ta cin rai da takaici a fusace ta juyo tare da kai hannu zata rama yayi saurin riƙo hannun ta cike da mamaki ya ce "whattttt? Ni zaki mara? ni ne zan bari hannun mace ya sauƙa akan fuskata da niyar mari ? impossible..."
ya ƙarisa maganar tare da wurgata kan kujera ya cabko sumar gashinta yana murmushin takaici
ya ce "idan akwai macen da nafi tsana a rayuwata to bazai wuce ke ba, you are my enemy..."
yana iddasa maganarsa ya juya zai tafi har ya isa bakin ƙofa yaji ta furta wata kalma wanda ya dakatar da shi,
ƙara maimaitawa tayi ta ce "yes me too I hate you, sam baka daraja mata especially wacce ta nuna damuwarta akan ka kafi wulakanta ta, amma ka sani duk abunda kayi kaima sai an mata, kamar yanda ka ƙuntata mun kaima wata rana sai kayi kuka cir da idanuwanka, wata rana saika durƙusa a gaban mace kana bata haƙuri a yayin da ita kuma take wulaƙantaka, wallahi ina maka wannan fatan kuma ka rubuta ka ajiye domin maganata a rubuce take, Razhdeen ko kaɗan bana jin tsoronka kaje bana son ƙara ganin fuskar, na gama maka komai tinda na Auri ɗan uwanka..."
Wani irin ƙololuwar baƙin ciki ne yake ziyartar cikin zuciyar Razhdeen, a yanda yake jin kansa ji yake kamar yaje ya murɗe mata wuya cikin zafin rai ya nufi yanda take a zaune bai iya aikata mata komai ba sai dunƙule hannunsa da yayi da ƙarfin gaske ya doka akan glass table na tsakiyar falor har sai da table ɗin ya dagargaje, hannunsa ne ya tsatstsage sai zubar da jini yake cikin zafin nama ya saito da gwala-gwalan eyes ɗinsa sai tin nata, a zabure ta ƙara mannewa da jikin kujera cikin tsoro da fargaban yanda ta gànshi lokaci guda ya canza kamar horror fuska yayi jawur tsabar ransa yayi matuƙar ɓaci, cikin dirarriyar murya ya ce "me kike taƙama da shi? saboda kina da ɗaurin gindi a wurin Abbah shine zaki rinƙa yin abubuwa kamar wacce kike da alaƙa da mu, ki kama kanki domin zan iya yi miki rauni a yanda nake jin kaina yanzu..."
wani dogon tsuka yaja sannan ya fice daga falon gaba ɗaya,
har ya fice Baiwar ALLAH bata daina ganin bakin ƙofar ba domin ba ƙaramin razana tayi ba ganin irin bugun da yakai wa glass table ɗinta har sai da ya dagargaje..
Allah yaso akwai abun bugu a wurin da a ita zai kai bugun nan..
Wani irin haɗiyar yawu tayi sannan ta ƙara fashewa da wani irin matsanancin kuka a haukace ta soma wurgi da filillikan kujerun falon tana kuka tana faɗin "Nima bana sonka na tsane ka wallahi, you bastard, you are crazy and you are my enemy, you broke my heart Razhdeen why? why? why???...."
Na ta ƙara fashewa da kuka, da iya ƙarfinta ta ɗauki glass table wanda yake a fashe ta wurga saitin plasman dai-dai lokacin da Roshan ya shugo da sallama a bakinsa ganin yanda plasman ya faɗo ƙasi a fashe yasa shi cewa "subhanallahi me zan gani haka?..."
bin falo yake da ido ganin yanda tayi kaca-kaca da falon, Baiwar ALLAH da gudu ta wuce bedroom ɗinta tana kuka,
Bin ta yake da kallo a tunaninsa rashin son zama da shi ne duk ya jawo haka, girgiza kai yayi tare da sauƙar da nannauyar numfashi ya ce "daman nasan baki haƙura da ƙudirinki ba Ammata, kinyi haka ne saboda ki faranta wa Abbah amma ba'a son ranki ba, amma Insha Allahu zan kawo miki good idea wanda zaki samu Dawwamammiyar farin ciki mai ɗorewa indai rabuwa da nine zai kawo miki farin cikin ki kar ki damu..."
Shima Razhdeen a fusace ya fizgi motar sa yabar gidan gaba ɗaya...
Bayan sallar isha'i da misalin ƙarfe 9 Baiwar ALLAH ce take zaune a falo idonta akan plasman ɗin jikin bango tana kallo amma sai dai hankalinta baya jikinta domin wani dogon tunani ta zurfafa, bata taɓa jin haushin Razhdeen kamar yau ba, gaba ɗaya taji ya wanke mata a rai especially idan ta tariyo maganganun da ya gaggaya mata, wani irin tsuka taja wanda har ya fito fili a cikin zuciyarta take faɗin "gwara na cigaba da zamana a gidan mijina domin hakan shi yafi mun alkhairi saboda bazamu taɓa dai-daita da Uncle Deen ba...
tana cikin wannan maganar zuci kwatsam taji muryar Roshan yana faɗin "Ammata gimbiyar mata..."
ya ƙarasa maganar tare da zama a kusa da ita idonsa akanta ya kuma cewa "idan ban takura miki ba ina so nayi magana da ke..."
Itama Baiwar ALLAH bin kyakkyawar fuskarsa tayi da kallo, girgiza kai tayi alamar babu matsala.
Gyara zama ya yi yana fuskantarta da murmushi akan fuskarsa ya ce "kiyi haƙuri Ammata nasan ina takura miki sosai, amma nasan amince da zama dani da kika yi a dole ne ba'a son ranki ba, amma na kawo wata mafita kuma nasan zaki ji daɗin haka sosai amma sai dai zaki ɗan ƙara haƙurin zama dani kafin aci nasara..."
Baiwar ALLAH zuba masa ido kawai tayi tana son jin wani irin magana zai furta mata,
Roshan ne ya cigaba da cewa "ba tare da kowa ya sani ba daga ni sai ke zamu tsara, zakiyi haƙuri ki zauna da ni na tsawon shekara biyu ba tare da mun kusanci juna ba duk da nasan ba amince dani zaki yi ba kamar yanda muke zaune a haka, idan har lokacin yayi na tsawon shekara biyu aka ga bakida ciki to za'a fara zargin ko ke bakya haihuwa ko dai ni, zan nuna cewa nine bana haihuwa kinga kuwa Abbah zai yanke cewa na rabu da ke domin kije ki Auri wanda zaki haihu da shi, nima zan goyi bayan haka! Abinda ba yanke kenam amma ki ƙara haƙuri da zama dani kinga zuwa lokacin nasan Razhdeen zai dawo daga U.S tinda shima two years zai yi..."
Baiwar ALLAH jin abinda Roshan ke faɗi ne yasa ta haɗe fuska rai a ɓace ta miƙe tsaye ta bar falo ta koma bedroom ɗinta, ita a halin yanzu bata buƙatar jin sunan Razhdeen duk da har yanzu akwai son sa a cikin zuciyarta amma tayi alƙawarin zata fara cire shi a ranta...
Roshan binta yayi da kallo tare da girgiza kai a fili ya furta "nasan shekara biyu yayi miki nisa tinda a yanzu baki ƙi na rabu da ke ba, amma wannan shine shawara mai kyau ba tare da an zargi wani abu ba..."
Bayan sallar Asuba ne Razhdeen ya gama shirya komai tafiya ƙasar U.S ta kankama, a harabar gidan sa ya tsaya murfin mota a buɗe yana shirin shiga za'a kai shi airport domin su Abbah da Roshan tare da sauran ƴan gidan duk suna airport suna jiran isar sa suyi ban kwana,
Ƴar Amana ce take ta fama kuka tana ƙoƙarin ƙwace wa daga riƙon da Madam Blessing tayi mata tana son bin Razhdeen yanda zai je,
Razhdeen bai so ya tafi yabar Ƴar Amana ba domin ji yake kamar zai rasa ta ne har abada, yana cikin kukan zuci ya shige motarsa security ya yi driving ɗinsa suka tafi...
Ƴar Amana ganin an buɗe gate sun tafi yasa ta fizgewa da ƙarfin gaske daga riƙon da Madam Blessing tayi mana tare da wurgar da bebin robar ta cikin fushi ta koma cikin falo tana hawaye,
tsaya kallon da Madam Blessing tayi domin al'amarin Ƴar Amana sai Allah shima kan shi Razhdeen ɗin a hankali yake bi da ita...
A ɓangaren ɗayan gidan kuma duk sun tafi ganawa da Razhdeen banda Baiwar ALLAH wacce ta kasance ita kaɗai a gidan bata je ko ina ba.....
*HIP_HIP_HIP_HURRRRYY*
*DAN ALLAH MASOYA KUYI HAƘURI DA JINKIRIN DA NAKE MUKU NIMA BA'A SON RAINA BA NE,*
*EXAMINATION NAKE RUBUTAWA KUMA INA BUƘATAR NUTSUWA DOMIN KASAN ABUNDA ZAKA RUBUTA A ƊAKIN JARABAWA, KULLUM INA CIKIN KARATU, KULLUM SAI MUN SHIGA EXAM*
*KU MUN UZURI DAN ALLAH KOMAI LOKACI NE KAMAR YANZU ZAN GAMA LITTAFIN GABA ƊAYA NASAN A MATSE KUKA🙏🙏*
*GA SHORT PAGE*
*BANIDA LOKACI AMMA GOBE IN SHA ALLAHU ZAN SAKE YI MUKU UPDATE TINDA BA EXAM..*..
asmeetah writer ✍️
🤦♀️ *MAƘIYI_NAH*🤦♀️
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء محمد أولا 🥳
Asmeetah (giaɗe writer)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
STEP TWO
👇
*31_ TO_35*
_________ONE YEARS AGO_________
Abbah yana zaune a babban falo tare da iyalansa, Ammy da Uwar masu gida da kuma Ƴar tinny dake kwance saman cinyar Ammy matar Abbah domin yanzu har ta fitar da Momminta daga cikin zuciyarta, dake tana samun kulawa sosai a wurin Ammy lokuta da dama tare suke kwana shi kuma Abbah ya koma part ɗinsa,
Suna zaune a falon sai ga Roshan da Baiwar ALLAH sun shugo falo a tare bakin su ɗauke da sallama daman wasu lokuta sukan zo ziyarta su Abbah duk da a gida ɗaya suke...
zama suka yi suma bayan sun gaggaisa da su Abbah, Ammy da murmushi akan fuskarta ta kalli Baiwar ALLAH ta ce "Daughter Abbah meyasa kwana biyu bakya shugo wa ne?..."
Baiwar ALLAH kai a sunkuye ta ce "wallahi Ammy bana jin daɗin jiki na ne shiyasa..."
Ammy ta ce "ayyah ban sani ba ai da zan je na duba ki, kuma naga Ummy tana zuwa part ɗinki amma bata sanar mun ba..."
Baiwar ALLAH ta ce "ai itama bata sani ba..."
Ummy uwar masu gida tana gefen Abbah cikin zolaya ta ce "kodai kodai mun samu ƙaruwa ne..."
Zaro ido waje Baiwar ALLAH tayi
tana faɗin "ƙaruwar mai?..."
Ammy ce ta fara yin dariya ganin kallon da Abbah yake yi wa Uwar masu gida har da taguminsa jin yanda ta taƙarƙare ta zuba zance, girgiza kai yayi tare da faɗin "Allah ya shirya mun ke Mamana..."
Rufe fuska tayi tana dariya domin sai yanzu take jin kunyar abinda ta faɗa...
Ita kuwa Baiwar ALLAH kallon Roshan tayi ta gefen ido tana maganar zuci cewa "taya zan samu ciki alhalin a ƙaurace muke da juna, yau tsawon shekara guda da Auren mu amma ko a gado ɗaya bamu taɓa kwanciya ba, abun yana damu na wallahi, shi ya ce indai bani na neme shi ba bazai taɓa nema na ba, Ni kuma kunyar hakan nake, hmmmm! meye makomata a wurin Ubangiji na? shin laifi nake aikatawa kodai? dole zan nema wa kaina mafita domin a halin yanzu ina matuƙar ƙaunar mijina Roshan, yafi mun duk wani namijin da zan Aura, bazan taɓa rabuwa da kai ba Roshan..."
Shi kuwa Roshan Abbah ne