Showing 60001 words to 63000 words out of 89400 words
rajin, wannan kalmar tinda nake a duniyan nan a kuma zaman Aure da nayi ban taɓa jin a furta mun ita ba sai yau, a rayuwata bana fatan dan na samu matsala da mijina na koma gidan mu Allah ya kiyaye mun ganin wannan ranar, ina fatan dana ga wannan ranar gwara Allah ya ɗauki numfashi na, ban taɓa samun matsala da mijina ba balle ya kore ni gidan mu, kuma haka ƴar uwata maman su Razhdeen kaine shaida bata taɓa complain akan matsalar da kuka samu ba balle take gida har ta cika da imana, haka Nima har nayi rayuwa da mijina marigayi bai taɓa korata gida ba,
Amma yanzu ka furta mun wannan kalmar...."
Ta ƙarasa maganar tarar da fashe wa da kuka ta juya da gudu ta koma part ɗinta tana kuka,
Uwar masu gida ganin Aunty Yolash ta fito daga part ɗin Abbah tana kuka yasa hankalin ta tashi yanzu kuma ta sake ganin Ammy tana kuka ta wuce part ɗinta nan ne hankalin ta ya ƙara tashi can sai ga Abbah ya zo ya wuce part ɗin Ammy domin hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba ganin hawayen Mar'atussaliha....
asmeetah writer ✍️
🤦♀️ *MAƘIYI_NAH*🤦♀️
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء محمد أولا 🥳
Asmeetah (giaɗe writer)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
STEP TWO
👇
*36_ TO_40*
Misalin ƙarfe 10 na dare Roshan yana kan sallaya bayan ya kammala sallar lafilfilinsa yana jan carbi a hankali bakinsa motsi, jin knocking ɗakin da yake ne yasa shi ɗago da kansa yana kallon bakin ƙofar, miƙewa yayi cikin farar jallabiyar sa ba tare da ya tambaya ba ya buɗe ƙofa, ganin Baiwar ALLAH yasa shi mamaki domin tinda take a cikin gidan nan bata taɓa zuwa ta buga masa ɗaki ba ko hanyar wurin bata yi, cike da mamaki ya ce "Am lafiya kuwa yau na ganki a part ɗina?..."
Baiwar ALLAH ba tare da ta bashi amsa ba ta ƙarasa shugo wa ciki, kamar zatayi kuka haka take bin sa da kallo ta ƙudurta a ranta cewa yau kam zata sanar masa gaskiyar abinda ke ranta domin bazata iya cigaba da zama a haka ba, ko ganin yanda su Abbah suke shan soyayyarsu da Matarsa abun yana bata sha'awa,
Zuwa yayi ya tsaya a gabanta yana mata kallon ƙurilla ya ce "meya faru ne?..."
Yamutsa fuska tayi tare da faɗin "sai wani abu ya faru tukun da na zo ɗakin ka?..."
Ya ce "to ai naga baki taɓa zuwa bane shiyasa dole abun zai ban mamaki tsawon shekara guda ana tare..."
Tana son sanar masa amma sai dai bazata iya ba kawai sai ta fake da cewa "daman, daman naji motsi ne a ɗakin da nake Ni kuma ina jin tsoro..."
A ruɗe ya ce "motsi kuma? muje na duba miki..."
Haka ya riƙe hannunta suka nufi waje kai tsaye part ɗinta suka nufa, yana zuwa ya soma Dube-dube amma bai ga alamar motsi ba.
Ita kuwa zama tayi a bakin gadonta ta wani zuwa masa ido sai sakin murmushi take, wani irin kallon so da ƙauna take masa wanda ita kanta bata san tana masa ba,
Juyowar da zai yi yaga ta zuba masa ido sai kallonsa take ba ƙaƙƙautawa, kaɗa mata yatsunsa yayi a sai tin idonta, a firgice ta dawo hayyacinta tana sauƙe nannauyar numfashi, ya ce "Are You Okay?..."
Jin tambayar da yayi mata ne yasa ta dafe goshinta tana faɗin "kai na ciwo..."
tayi haka saboda kar ya gano ta...
Ya ce "ok sorry bari na kawo miki magani..."
yana kai wa nan yayi ficewar sa, can ba jumawa sai gashi da magani haɗi da gorar ruwa yana zuwa ya miƙa mata.
Hannu tasa ta riƙe hannun idonta akan sa, Roshan ganin hannunsa ta riƙe ba gorar ruwan ba yasa shi cewa "kin riƙe mun hannu..."
Sunkuyar da kanta tayi ƙasi tare da faɗin "yi haƙuri..." ta karɓi gorar ruwan da magani..
Ya ce "ki sha maganin ina zuwa yanzu..." ya buɗe ƙofa ya fice da sauri da duk kan alamu yayi mantuwa ne,
Baiwar ALLAH bin bayansa tayi da kallo tare da sakin murmushi, ta ɓaro magani sannan ta miƙe tsaye ta nufi kan mirror ta ɗauki biro a tsakiyar magani ta rubuta farkon harafin sunan Roshan wato ("R") har takai maganin sai tin bakin ta kawai ta dakatar, tunowa tayi shima Razhdeen farkon sunansa kenam, yamutsa fuska tayi tare da sa biro ta ƙara harafin O a gaban R tana nufin ROSHAN kenam tasau murmushi ta kai maganin bakinta tare da korawa da ruwa ta haɗiye.
Roshan ne ya shugo ɗakin yana waya daga ƙarshe ya katsar idonsa akan Baiwar ALLAH wacce itama shi ɗin take kallo, buɗar baki yayi ya ce "shikenam yanzu babu wata matsala ko? Ni zan koma part ɗina..."
Baiwar ALLAH ji tayi zuciyarta ta buga domin bata so yayi nesa da ita, ya juya zai tafi kenam yaji tana kuka tare da faɗin "wayyo kaina ciwo, hajijiya nake ji..."
Juyowa yayi ya kalle ta yaga tana shirin faɗuwa ƙasi da gudu ya nufi yanda take ya rungumota tare da faɗin "sannu ko ina kinsha maganin?..."
Itama riƙe shi tayi sosai tana faɗin "ka taimake ni zan mutu..."
Kwantar da ita yayi akan gado ya ce "ki kwantar da hankalinki babu abinda zai same ki, kiyi bacci kinji ..."
ya rufa mata mayafi sannan ya juya zai tafi yaji ta riƙe masa hannu..
Juyowa yayi yana kallonta kamar zatayi kuka ta ce "ina jin tsoro dan ALLAH yau ka kwana anan..."
Sakin murmushi yayi tare da faɗin "Ok shikenam ba damuwa..."
ya ɗauki pillow daga kan gadon yana faɗin "barin naje na kwanta akan doguwar kujeran can..."
Nan ma ƙara riƙe masa hannu tayi ta ce "can you sleep with me?..."
Cike da mamaki ya ce "whattt?..."
cikin ƙiƙƙina ta ce "ina nufin anan..."
ta nuna masa bakin gadon..
Kaɗa mata kai yayi ya ce "okay..." ya ajiye pillow sannan ya kwanta ata baki-bakin gadon, ita kuma tana ta bayansa murna take yau zata kwana gado ɗaya da Roshan...
Ta ce "Am ka manta baka kashe ligh ba kuma ni bana iya yin bacci da haske..."
Tashi yayi yaje ya kashe ya dawo ya kwanta kamar yanda yake ya juya mata baya...
Yana tunanin abubuwa da dama a ransa, yana jin wani abu akan Baiwar ALLAH amma haka yake jure wa, yana maganar zuci ya ce "inasonki Ammata amma haka zan bawa zuciyata haƙurin rashin ki, kina so ki Auri twins ɗina kuma lokaci nake jira na rabu dake kije ki Aure shi, nayi alƙawari a kaina cewa bazan taɓa saninki a matsayin ƴa mace ba domin inada kishin da bazan iya yin sharing ba, bazan iya Auran mata kuma bayan na gama saninta a matsayin ƴa mace daga baya nazo na rabu da ita ba, wani kuma daban yazo ya Aure ta i can't, Ammata indai zaki zauna dani har ƙarshen rayuwar mu wallahi ko a yanzu kika nuna mun buƙatarki a shirye nake dana kusance ki, amma in har ƙudirin ki yana nan na Auran twins a gaskiya ko zamuyi shekara ɗaki a haka bazan iya kusantarki ba, bana son sharing! bana son sharing, bana son sharing..."
Yana cikin wannan surutan a cikin zuciyarsa kwatsam sai ji yayi Baiwar ALLAH ta rungumoshi ta baya, Shuru yayi yana jin yanda ta manno jikinta jikin na shi,
wani irin haɗiyar yawu yayi tare da ƙarƙame idanuwansa baya so ta tayar masa da feeling shi kuma bazai iya kusantarta ba, haka yake cikin wannan halin yana jurewa tare da jero Addu'o'i har bacci ya yi awun gaba da shi.
Ita kuwa Baiwar ALLAH kasa bacci tayi a tunanin ta Roshan zai juyo gareta ne sai kuma taga akasin haka ko ƙwakƙwaran motsi bai yi ba, tayi takaicin haka sosai domin ba haka taso ba, tana rungume da shi tana ta saƙe-saƙe a ranta, jin alamun yayi bacci yasa ta ɗan juyo da shi tana ƙarewa fuskarsa kallo can ta sumbace shi akan goshi, ta ɗago sannan ta ƙara sumbatar sa a gefe da gefen fuskarsa, daga ƙarshe ta ɗora lips ɗinta akan nashi tayi masa wani irin hot kiss wanda sai da ya ɗan motsa yana shirin buɗe eyes ɗinsa, ɗagowa tayi tana kallonsa shi kuwa ya ƙara zarce wa da yin baccin, itama kwantar da kanta tayi kan ƙirjinsa da haka har bacci ya ɗauke ta...
Sys.Out.PrintIn ("WASHE GARI");
}
Aunty Yolash ce a cikin jirgi ta miƙi ƙasar Jidder tana son samun Mai martaba akan maganar Abbah da Hajiya Kilishi ko shi zai iya sauraronsa..
______________________________________
Aunty Yolash ce zaune a babban falon cikin gidan tana tare da INDO second ɗin Mai martaba a yayin da ita kuma Maamie tana can part ɗinta,
Hira suke sosai suna shan dariyar su domin Aunty Yolash da Indo jinin su ya haɗu sosai, suna cikin shan hirar su sai ga MAAMIE ta sauƙo daga upstairs idonta akan Aunty Yolash duk tana wani binsu da harara, sauƙo wa tayi ta nemi wuri ta zauna tare da ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya tana tauna ciwgim,
Aunty Yolash ce ta kalleta tare da sakin murmushi a ranta tana faɗin "mun ga Hajiya Kilishi ma kuma daga ƙarshe abun baiyi mata kyau ba, kowa da ranar sa kema wata rana sai kinyi kuka da idonki kinzo kina neman gafarar mutane..."
ta ƙarasa maganar idonta akan Maamie,
Maamie ce ta zaro mata idanu tana faɗin "lafiya kuwa Malama kike kallona ko dai akwai abinda na tare miki ne..."
Aunty Yolash ta ce "naga kin shugo mana ba sallama ne..."
Maamie ta ce "ke dakata nan fa yanki nane yawwa, gidan mijina gidana bazaki zo ki takura mun ba, ke asu wa har zakiyi magana akan banyi sallama ba..."
Aunty Yolash ta ce "hakane kamar yanda kike gadarar gidan mijinki ne haka Nima nake gadara da gidan Yayana ne uwa ɗaya uba ɗaya, kuma hasali na fiki iko da gidan domin ke ko a yanzu aka baki takardar saki dole ki bar gidan, kuma mu ƙi maido ki in juninki rashin mutunci ne..."
Maamie ta ce "ai wallahi bari kiji ni da gidan nan Auren zobe ne ba rabuwa sai dai mutuwa, in hassada kike mun ma gwara ki shanye abun ki..."
Suna cikin wannan cacar baki sai ga Mai martaba ya shugo da sallama a bakinsa domin ya gama sallamar baƙin da yayi a falon masarautar,
zama yayi yana fuskantar Aunty Yolash da murmushi akan fuskarsa domin ba ƙaramin farin ciki yayi ganin Autar ɗakinsu ba, gaisawa suka yi sannan ya ce "Yolash mutan boko yau ɗin boko ya barki kin kawo wa ɗan uwanki ziyara kenam..."
Aunty Yolash ta ce "Yaya mai martaba inason zuwa daman amma ɗawainiya sun mun yawa..."
Mai martaba ya ce "yanzun ma nasan akwai abinda ya kawo ki ai tinda ban ganki da akwatin zaman hutu ba..."
Dariya tayi ta ce "wallahi a yau zan koma sai kuma idan na tashi zuwa da akwatin zan zo nayi muku hutu sosai..."
Murmushi yayi tare da faɗin "Allah sarki ƴan uwa daɗi..."
Itama murmushi tayi.
Mai martaba ya ce "fatan dai kinci abinci ko?..."
Ta ce "tin zuwa na Aunty Amarya ta kawo mun ina ci muna shan hira da haka na kammala..."
Ya ce "Masha Allah haka ake so ai, yanzun me yake faruwa ne?..."
Aunty Yolash ta gyara zama ta kwashe duk halin da ake ciki na Abbah da Hajiya Kilishi ta sanar masa, ta cigaba da cewa "Mai martaba ko dan ƴaƴanta a dawo da ita duk da yaran sun mallaki hankalin kansu, itama kanta Kilishi zata fi nutsuwa, a halin da take ciki inta cigaba da zama a haka ba'a san mai zata aikata zuwa gaba ba tinda indai wahala tayi wahala mutum zai fara neman mafita, to mafitan ne ba'a wani iri za'a nema ba, tinda ta nemi yafiyar mutane ta gyara halayenta sai a dawo da ita..."
Mai martaba tayi gyaran murya sannan ya ce "hakane duk naji batun ki Insha Allahu zan je na samu Chief da maganar, sai dai matsala shine ba lallai ya aminta ba, kar yazo yana faɗa mun maganganu ne kinga shine gaba da Ni, kuma waɗanda suka girme shi ma bai fi maganar su ba, baffanun mu sun same shi da maganar amma fur yaƙi to ba lallai ne Ni ɗin ma yaji ba..."
Aunty Yolash ta ce "a'a Yaya mai martaba kar ka karaya kaje ka lallame shi akan batun dan ALLAH..."
Ya ce "toh shikenam idan kin tashi tafiya sai mu tafi tare Nima inaso na dawo a yau saboda inada uzurirruka a gabana sosai..."
Aunty Yolash ta ce "ai Ni yanzu zan tafi..."
Ya ce "to mu tafi tare..." duk suka miƙe akan zasu tafi,
Maamie tana zaune ta ce "shikenam yarinya ƙanwar bayanka tazo zata kwashe ka ku tafi ba irin ɗan bada girman nan...".
Mai martaba ya ce wa Aunty Yolash "ki sharar da ita kawai mu tafi..."
Aunty Yolash bata kulata ba domin tasan inta biye mata zasu kaure da faɗa ne yanzu kuma bata da lokacin ta, haka suka fice Indo ta raka su har wurin parking, suka shiga mota security ya jasu suka tafi airport.....