Showing 36001 words to 39000 words out of 89400 words

Chapter 13 - MY ENEMY BOOK 2 HAUSA NOVEL

asmeetah   

20 May 2025

2531

kurmance ne?..."

Baiwar ALLAH cewa tayi "ai naga baki yi sallama ba ne..."
A fusace Minal ta ce "saboda nan ɗin gidan Ubanki ne? ke ki dakata kiji saboda Abban mu ne yasa muke respecting ɗinki Albarkacin kina Auran Ɗan uwan mu amma wallahi baki isa ki gaya mun maganar banza ba, saboda ko ba komai nasan na girme ki sosai..."

Baiwar ALLAH dai shuru tayi bata ce mata komai ba sai cigaba da kallonta da ta yi, Minal tsabar ƙololuwar baƙin ciki bata san lokacin da ta fincikota ƙasin carpet ba tare da faɗin "ba magana nake miki ba dan ubanki, aikin banza kawai idan baya nan ki sanar mun mana..."

Baiwar ALLAH ɗagowa tayi tana kallon ta dai-dai lokacin da Roshan ya fito daga part ɗinsa dake cikin falon gaba ɗaya,
Idonsa ne ya sauƙa akan Baiwar ALLAH wacce take baje a ƙasin, ƙaraso wa yayi dab da ita tare da miƙa mata hannu zai ɗago da ita, ba tare da ta miƙa masa ba ta tashi da gudu tana kuka ta wuce part ɗinta...

Roshan kallon Minal yayi sannan ya ce "mai kika mata ne?..."
Minal tana yamutsa fuska ta ce " Yarinyar ce tana da raini wallahi, na shugo ina mata magana tayi wani banza da ni..."

Roshan ya ce "Minal kin dai san mata ta ce ko? kamar yanda kike respecting ɗina ya zama dole itama kiyi mata, idan kika raina ta toh kamar ni kika raina ne, so be careful..."

Maganganun Roshan ba ƙaramin ƙona mata rai ya yi ba, kamar zata yi kuka ta ce "Sorry in ba dan uzuri ne ya kawo ni ba babu abinda zan zo yi ɓangaren ta tinda ita batada mutunci..."

Roshan ya ce "okay zaki iya tafiya Minal..."
Cike da mamaki take bin sa da kallo ta ce "wurin da zamu je fa?..."

Juyawa ya yi zai koma ciki ya ce "babu ruwa na da lamuran ki, kije kiyi duk abinda kika ga dama..."

bata san lokacin da ta fara kuka ba tana faɗin "Yaya Roshan dan ALLAH kayi haƙuri wallahi in har bada taimakon ka ba babu yanda zanyi na samu Marshall, Abbah yana shirin haɗani da wani Abokinsa kaima kasan da haka, ya hanani fita ko ina koda wurin aiki ne, sojojin gidan suna nan koda yaushe babu halin fita ba tare da kai ba, wallahi ina son Marshall inaji a jikina bazan iya rayuwa ba tare da shi ba, shekaru na sunata ja ina buƙatar yin Aure ga wanda nake so, ka taimaka..."

Roshan tsayawa yayi yana sauraron ta daga bisani ya ce "Okay kije ki bata haƙuri tukun..."
Tana kuka ta ce "bazan iya ba Yaya Roshan..."
Tana share hawaye tayi ficewar ta..
Shi kuwa girgiza kai ya yi yana faɗin "girman kan ki Minal shi yake azabtar da ke..."
Shima wuce wa yayi ya nufi room ɗin Baiwar ALLAH yana zuwa ya samu ƙofar a ƙarƙame yayi bugawar duniya amma taƙi buɗe wa haka ya haƙura ya wuce room ɗinsa...

Minal tana fita daga part ɗin Roshan kai tsaye wurin swimming pool ta nufa tana kuka..

Tana zuwa ta jefar da handbag ɗinta a gefe tare da mayafin ta, tazo dab da bakin ruwan zata faɗa ciki taji anyi saurin dakatar da ita,
Da sauri ta waiwaya tana bin Roshan da kallo wanda ya biyo bayanta bayan yayi tunanin halin da zata iya shiga,
Ƙaraso wa wurin ta yayi tare da faɗin "meye kike shirin aikata wa? Minal daman zaki iya hallaka kan ki akan soyayyar ki?..."

Tana kuka ta ce "Yaya Roshan babu wanda ya damu da damuwa ta, ina cikin wani halin da ba kowa ne zai fahimce ni ba, kai ma da kake son taimaka mun yau kana shirin juya mun baya saboda matar ka..."
Nan ta fashe da kuka sosai,
Riƙota yayi yana faɗin "lolz my bloody bai kamata ki yanke wannan hukunci a kanki ba, kiyi haƙuri ina tare da ke, yanzun muje mu tafi ko..."

Rufe bakin ta tayi da hannaye biyu tana dariyar farin ciki, cikin nuna farin ciki ta ce "Nagode sosai Yayana..."

Ya ce "don't worry let's go..."
Anan ta ɗauki mayafinta da jakar ta suka tafi tare,
Already sunyi sallama Ammy Amaryar Abbah da Abbah cewa zasu je shopping, sai bayan sun dawo zasu sanar da duk abinda ya faru...

Iya su biyu suka shiga mota ba tare da security ba Roshan shi yake driving, sojojin bakin gate ganin Roshan ne yasa suka buɗe masa gate,
Kai tsaye wurin da za'aje a ɗaura Auren suka nufa, Mohandas kuma Roshan ya tura masa da Address yanda suke saboda in har yaje gidan Razhdeen ɗaukar sa za'a samu matsala sakamako sojojin da suke gidan Razhdeen zasu iya sanar wa Abbah halin da ake ciki...

Mohandas shima fita yayi da motarsa ba tare da Razhdeen ya sani ba..

Wasu manya-manyan malamai Roshan ya tara a wani office na ƴancin kai, ba ƙaramin manyan kuɗaɗe aka basu ba amma sai dai shaidun basu fi su goma ba,
A ranar ne aka ɗaura Auren Minal da Mohandas ga Roshan wanda yake tsaye shima aka yi amma hankalinsa gaba ɗaya ba'a jikinsa yake ba, tunaninsa taya zai fara tunkarar Abbah da wannan maganar...

A wannan ranar kwata-kwata Roshan bai rintsa ba, kuma bai sanar wa Abbah halin da ake ciki ba, a yayin da Minal take cikin farin ciki, tana kwance a ɗakinta da waya a hannu alamar video call take bada kowa ba sai da mijinta Mohandas, shima yana cikin farin ciki ta wani ɓangaren kuma yana tunanin kalar hukuncin da Abbah zai ɗauka idan yaji wannan batun, gaba ɗaya a tsorace yake, ita kuma Minal bata tunanin komai kuma bata jin komai a ranta, abu ɗaya ne yake damunta shine rashin kasancewar ta tare da mijinta...

Roshan sai da yayi kwana uku yana inda-indar sanar wa Abbah, sai a yau ya cire fargaba ya gayyato Mohandas zuwa gidan su a yau za'a sanar wa Abbah dake yau ranar hutunsa ne babu fita aiki...

Mohandas yana zuwa Sojojin suka buɗe masa gate ya shige already Roshan ya sanar musu cewa Mohandas zai zo ba tare da Abbah ya sani ba,
Roshan ne tsaye a wurin parking yana jiran isowar Mohandas cikin lokaci ƙanƙani sai gashi ya iso, a tare suka nufi babban falon gidan suna shiga suka tarar da Ummy uwar masu gida ita da Ammy da kuma Baiwar ALLAH zaune suna karatun wani ɗan littafin hadisi, da dukkan alamun Ammy ce take koya musu wasu abubuwa a cikin littafin, jin sallama yasa duk suka ɗago tare da amsa sallamar.

Ummy zaro ido waje tayi ganin Mohandas ɗan maƙiyin Abbah kuma shima maƙiyin ne tinda yana neman ɗiyarsa,
Ammy kuma dake bata san Mohandas ba yasa ta fara sakin murmushi tana faɗin "babban baƙo mukayi ne? sannu da zuwa Roshan ga wuri ku zazzauna..."

Hakan kuwa akayi duk zama suka yi, Ammy kuma tashi tayi ta shige kitchen zata haɗo musu abin taɓawa, Uwar masu gida kuma itama tashi tayi da haura saman upstairs da gudu zata je ta sanar wa Minal cewa ga Mohandas a gidan su, sai ya rage iya Baiwar ALLAH a falon, idonta akan Mohandas sau ɗaya ta taɓa ganinsa ran da suka je gidan Razhdeen nan ma bata ƙare shi da kallo ba sai yau, haka kawai take jin tsinkar jikinta yana tashi ga wani irin bugun zuciya, ta rasa meye dalilin faruwar wannan al'amarin, shima Mohandas ɗin kallon ta yake ya dai san itace Amaryar Roshan amma bai gaba saninta ba sai yau shima yana jin wani abu sosai a kanta,
Idon Baiwar ALLAH ne suka sauƙa akan wani ɗan sarƙar dake ɗaure a hannunsa shigen irin nata, sai dai ita a wuyanta yake ɗaure kuma akwai mayafi a kan ta balle ta sake ganin kalar natan, ƙirjinta ne yake wani irin bugawa sosai,
A lokacin ne Abbah ya fito daga part ɗinsa wayar sa a ɗore kan kunne sai muryarsa kake ji yana ta waya,
da haka ya gama sauƙowa daga upstairs idonsa ne suka sauƙa akan Mohandas kamar wanda aka ɗauke masa wuta haka ya tsaya cakk.

Itama Minal fitowa tayi da gudu ita da Ummy suka sauƙo falo, Ammy ce ta jejjera musu kayan abinci akan table ɗin falo saitin gaban Mohandas,
Abbah ne ya sanar a wanda yake waya dashi cewa "Please I'll call you back, cut the phone..."
Still idonsa akan Mohandas, shima Abbah zama yayi yana fuskantar su ba tare da ya ce komai ba..

Jikin Mohandas ne ya fara rawar sanyi ganin yanda Abbah ya chanza cikin lokaci ƙanƙani,
A fusace Abbah ya ce "meya kawo ka gida na?..."

Mohandas kasa magana yayi sai Roshan ne ya yi ƙarfin halin cewa "Am Abbah daman akwai maganar da muke so muyi ne..."

Abbah ya ce "nasan akan maganar Amina ne ko? wai shin dole sai ɗiyata zai Aura ne? nace bazan taɓa haɗa jini da familyn su ba kuma babu mahalukin da ya isa yasa na haɗi, dan haka ya tashi ya bar mun gida tin kafin na fusata..."

Roshan ya ce "dan ALLAH Abbah ka saurare ni..."

Abbah ya kalli wurin da Mohandas yake a zaune ya ce "saboda kai na hana ƴata zuwa wurin aiki, na hanata fita ko ina, shin me kake yi a Nigeria da har yanzu bazaka koma ƙasar ku ba, na hanaka tarayya da ƴata ka ƙi, to ƴaƴana mazan ma zan hanaka tarayya dasu saboda haka daga yau zamanka a gidan Razhdeen ya ƙare, na datse Abotar ta kun, sannan Roshan ma kada ka sake shiga sabgarsa na gaya maka, in har ba haka ba zanje na samu mahaifinka na ja masa kunne ya dakatar tinda ni ban isa da kai ba, idan ba haka ba gavar da nake da mahaifinka zai ƙara ninkuwa ne kuma wallahi sai mun shiga kotu da ku..."

Abbah tashi yayi zai koma ciki Roshan ya ce "Abbah Please ka bamu lokacin ka..."
Abbah a fusace ya juyo yana faɗin "Roshan ka maida hankalinka na gaya maka, ka fitar mun da wannan ƙabilan a cikin gidan nan..."

Ammy da ta kasance bata san komai ba amma a yanzu ta fahimta domin taji labarin Minal da Mohandas,
Baiwar ALLAH itama tana wurin akayi komai gaba ɗaya hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, ga bata san dalilin da yasa take jin tausayin Mohandas haka kawai ba, Uwar masu gida har da kukan ta.
Abbah har zai motsa ya tafi yaji Minal ta buɗe baki tana kuka ta ce "Abbah wallahi inason Mohandas kuma bazan taɓa rabuwa da shi ba, sai dai kayi haƙuri amma aikin gama ya rigada ya afku tinda akwai Aure a tsakanin mu..."

Ba Abbah ba hatta waɗanda suke wurin babu wanda bai girgiza da jin abinda Minal ta furta ba banda Roshan,
A firgice Abbah ya ce "whattttt!!!???..."
Murmushin takaici yayi ya kalli Roshan ya ce "kaine silar faruwar hakan ko? Minal bata fita ko ina sai da kai saboda na yadda dakai Roshan ashe kaima zaka iya cin Amana ta? Amma ka cuce ni Roshan saboda in ba dan kai ba babu yanda za'ayi Minal tabar gidan nan saboda tsaron da na sa mata, ban sa a raina cewa hakan zata faru ba saboda na yadda da kai, shiyasa duk abinda kace mun nake Amince maka..."

Roshan gaba ɗaya jikinsa ne ya yi sanyi, bai san lokacin da ya fara zubda hawaye ba, sai yanzu ya yi nadamar aikata hakan..."

Abbah kallon Minal yayi tare da faɗin "kin kyauta, amma ki sani cewa bazai bar gidan nan ba tare da ya baki takardar sakin ki ba..."

Tana kuka ta ce "Abbah ya musulunta fa..."
Wani irin gigitaccen tsawa ya daka mata tare da faɗin "ko Alqur'ani ne a jere a kansa bazaki shiga familyn su ba, babu jini na da zai zauna da familyn su nayi Alƙawarin haka..."
Ya maida kallonsa kan Mohandas sannan ya ce "inaso a yanzun nan ka furta kalmar saki wa ƴata a yanzu..."

Ammy ce ta buɗe baki ta ce "Chief indai ya musulunta ka barsu kawai dan ALLAH, kar a toye musu hakki..."

Abbah ya ce "bana chanza magana idan nayi..."

Sai a wannan lokacin Mohandas ya buɗe baki shima wurin cewa "kayi haƙuri Abbah bazan iya sakin ta ba..."
A fusace Abbah ya ce "haka kace ko? to ku jira Ni ina zuwa, yau zan nuna muku zamani na ya ninka naku sau ba adadi..."
ABBAH yana kaiwa nan da sauri ya haura upstairs domin akwai abinda yake son ɗauko wa (kodai gum ɗinsa zai ɗauko 🤣🤣)


Ammy ce ta bi bayansa itama tana so naje tayi roƙo,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login