Showing 1 words to 3000 words out of 98004 words
********************** ⬇ **************************
************* Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************
[3/18, 22:22] Hafsat Rano: *SAUYIN K'ADDARA*
SHAFI NA DAYA (1)
©HAFSAT RANO
HASKE WRITERS ASSOCIATION 💡
✨✨✨💫💫
Zaune suke a karkashin bishiyar dake tsakiyar harabar makarantar, zaman jiran siwes supervisor suke tun kimanin awannin biyu da suka wuce, yau ce rana ta uku da suke irin wannan zaman jiran ba tare da sun sami ganin sa ba. Hira suke ɗan taba wa sama-sama har zuwa lokacin da matasan samarin guda biyu suka nufo su, daga nesa Asmy ta hango su tayi saurin tabo Maryam
"Gafa mutanen nan su tawo."
"Suwa?" Tace tana gyara zaman glasses din idon ta, kafin Asmy tayi magana har sun ƙaraso, a tsakiya suka sasu Khamil ya zauna a bangaren Asmy shi kuma Saddi ya zauna ta bangaren Maryam
"Babes kuna nan ashe?"
"Muna nan Khamil, mun zo ganin Malam Bahahuddin ne, kaga tun dazu muke zaman jiran sa."
"Ai wannan malamin bashi da mutunci wallahi, haka fa ranar mukayi ta zaman jiran sa muma sai daga baya yazo."
"Haka fa yake yi."
"Saddi manyan ƙasa." Asmy ta zuba mishi ido tana murmushi, a dakile yace
"An gaishe ki."
Cikin kallon kasa-kasa ya furta
"Yah... Maryam me glass ba magana ne wai?"
Yadda yayi maganar yana kashe ido daya irin na yan duniya, yasa ta kara hade fuskar ta sosai, ta sunkuyar da kanta ƙasa tana jin haushin sasu a tsakiyar da sukayi ga wata shigar banza kamar wasu y'ay'an arna, askin Saddi kamar zakayi amai, banza tayi kamar bata ji ba sai da Asmy ta dan jungureta, daidai lokacin Malam Buhahuddin ya ƙaraso a wata yar kurkurar motar sa golf ja, da sauri ta mike
"Gashi ma ya zo taso kar ya yi wani wajen kuma dan Allah."
Da sauri Asmy ta miƙe ta kalli su Saddi,
"Guys bari mu wuce sai next time."
"Owk take care."
Shafa dan siririn gemun sa ya shiga yi me kama da na dan zakara, kallon bayan su yake har suka haura saman barandar da zata sadaka da ofishin malamai. A hankali ya mai da kallon sa wajen Khamil yana wani shu'umin murmushi,
"Yah ne?" Ya tambaya yana mik'ewa.
"Guy yarinyar nan fa yar rainin wayo ce, ji yadda ta yarfa ka."
Dage kafad'a yayi yana taɓe baki yace;
"Zata shigo hannu ne soon, muje wajen Zuhra tana can albarka tana jiran mu."
"At toh mu fasa kawai, Allah sa tare suke da Soffy kaga nima sai na rage time."
"Shegen sama, haske ne dai tarwai balle kace zaka lalubi yar mutane."
Tafawa sukayi suka bar wajen, duk in da sukayi sai kaji ana musu kirari irin na manyan yara, wasu su amsa wasu su wuce kawai.
***
A kofar office ɗin suka tsaya suna jiran ya basu izinin shiga, Asmy ce ta bata rai tana kallon Maryam kafin ta daure tace
"Gaskiya abinda kike bak'ya kyautawa, ji fa yadda Saddi ke binki kina wulakanta shi, bayan kinsan irin su ba ababen wulakanta wa bane wallahi, ji yadda matan school ɗin nan ke binsa amman ke kina wani sha masa kamshi."
"Na faɗa miki be yi min ba, beside ba ma tsara na bane yanayi na da nasa bazai taba zama daya ba kin gane?"
"Amma.. "
"Naji, a bar maganar dan Allah "
"Shikenan, ke kika sani."
Buɗe kofar yayi suka shiga da sauri, daga gefe suka tsaya sai da ya gama yauƙi da yanga sannan ya ciro form guda biyu ya mika musu,
"Gashi nan ku dawo dashi bayan kwana biyu." Ya dora
"Sai dai bana son private waje ba wani koyan aiki ake ba."
Shiru Maryam tayi don ita burin ta ta kai nan wajen dake gaba kaɗan da gidan su saboda matsalar yau da kullum,
"Malam..."
"Ina jinki."
"Dan Allah Malam ka barni na kai Arkel Poultry Farm."
"A ah gaskiya, ban yarda ba."
"Malam dan Allah."
Ta cigaba da magiya saboda nan ne kaɗai tasan zai fi mata sauki ko saboda kudin mota ma, a kafa zata taka kamar yadda take takowa zuwa makaranta, idan yace sai waje me nisa zai iya zama karshen karatun nata, ba zata so hakan ba saboda ta zo gangara level 3 suke, faɗi tashin da aka sha kafin azo in da ake yanzu ba kaɗan bane.
Ganin yadda ta nace ne yasa shi cewa
"Kije ki kai musu mu gani, ba lallai ma su yarda ba nasan."
"Nagode, Nagode malam."
"Karku manta ƙwana biyu na baku."
"Mun gode malam."
Suka haɗa baki suka faɗa sannan suka masa sallama suka tafi.
Daga nan gate suka nufo tun da dama abinda ya kawo su kenan, Asmy ta hau napep ta wuce ita kuma ta shiga takawa a kafa, kallon gaban ta take har ta gangara gefen titin ta shiga lungun da take bi kullum da zai kai ta unguwar su, tana tafiya cikin nutsuwa zuciyar ta gaba daya ta tafi wajen da take son kai form d'in kar su ƙi karba su jaza mata.
Yadda ta lula da tunani yasa har bata ji sautin takun tafiyar su ba har sai da suka cimmata, da sauri ta waigo jin kamar an taba bayan ta, Saddi ne shi da su Khamil sai Sameer da Adnan su hudu fuskar nan tasu dauke da murmushi cike da wani irin kallo. Ras gaban ta ya fad'i jikin ta ya soma rawa ganin layin babu kowa, waige-waige ta shiga yi tana neman hanyar gudawa, dariya suka kwashe a tare Saddi ya damko hijab din ta yana ƙoƙarin manna ta a jikin sa, kici-kicin kwacewa ta hau yi ta saka kuka tana magiya, fisge hijabin jikin nata yayi doguwar rigar atamfa leda ta bayyana a jikin ta, dam ta kamata tayi mata d'as a jikin ta,
"Wow..."
Suka haɗa baki suka furta a tare. Hannu Saddi ya kai zai taba ta yaji an bigi hannun nasa, ihu ya saka cikin jin zafi, tsaye yake fuskar sa a daure tamau yana faman huci, ido suka zuba masa cike da mamakin kokarin sa
"Waye kai?"
Khamil ya tambaya yana kallon yadda Saddi yake yarfe hannu, wani banzan kallo ya watsa masa yana mika hannun sa wajen Saddi
"Bata hijab d'in ta."
"Ba zan bayar ba, uban waye kai da zaka dake ni? Kasan waye ni?"
Be tanka mishi ba ya matso kawai yasa hannu ya fizge hijab din ya wurga mata yana d'auke kai, da sauri ta chafe tayi saurin sawa har lokacin kukan take, hanya ya nuna mata alamar ta wuce ta tafi, tsayawa tayi zatayi masa godiya ya daka mata tsawa
"Dalla leave.!"
Da sauri sauri ta bar wajen tana jiyo hayaniyar su Saddi suna zagin sa da maganganu mara dadi, juyawa yayi ya bar wajen bayan yayi making duk fuskokin su.
A wajen wani me kayan miya ya tsaya ya ciro Naira dari sai da ya miƙar da ita saboda duk taji jiki sannan ya mik'a masa
"Baba ga kudin kayan jiya da Inna ta karba, mun gode Allah saka da Alkhairi."
"Nima nagode Hafizu, ga gaida mutanen gidan."
"Zasuji."
***
A zauren gidan su ta tsaya ta share hawayen ta kafin ta shiga, umma tayi wa sannu da gida tayi saurin wucewa daki, ciro komai tayi ta ajiye ta daura zani ta fito waje bayan ta ɗora hijab a saman zanin, bokiti ta dauka ta buɗe in da suke zuba ruwa, dan kuntun ruwa ne a ciki gashi yau ba ƙaramin rana ta kwaso ba so take ta dan watsa ko taji dadin jikin ta
"Umma ba ruwa fa a gidan."
Fitowar ta kenan daga bayi rike da buta, gefen dan dandamalin dake wajen wanke-wanken su ta zauna sannan tace
"Sai dai ki maida kayan ki ki zagaya gidan Hajiya Mama ki samo ruwan nan, yau miftahu be zo ya debo ruwan ba."
"Gidan Hajiya Mama?"
"Eh."
"Na hakura gaskia, in sun dawo daga islamiyya sun samo me ruwa."
"Ba wankan kike so ba."
"Allah ina so Umma, Hajiyar ce sai a hankali."
Umma bata sake magana ba ta cigaba da abinda takeyi.
Daki ta wuce ta jawo kwanon abincin ta ta zauna ta fara ci, tana ci tana tunanin abinda ya faru a hanya, bata san iskancin su Saddi ya kai haka ba, lallai dole ta sa Asma'u ta fito harkar su wallahi, in bazata iya ba toh gwara ta fita harkar ta kuwa. Tana nan tana tunani har kannenta suka dawo.
***
Wajen karfe goma ta isa, a harabar ta tsaya tana shaƙar iska wajen, a rayuwar ta tana son duk wani abu daya danganci kiwo, ilimi ne sosai a cikin sa, tana kuma son shuke-shuke suna sata nishadi sosai. Sai data gama kallon wajen sannan ta tambayi wani da yazo wucewa office din da zata, nuna mata yayi da hannu ya wuce ita kuma ta nufi office d'in, a bud'e yake mutane biyu maza suna zaune a ciki, shiga tayi Salim na ganin ta ya fadada fara'ar sa kamar ya santa
"Sannu da zuwa Hajiya."
"Ina wuni?" Ta gaishe shi tana dan rissinawa, hakan ya kayatar dashi ya tattare aikin da yake ya bata hankalin sa
"Siwes student ce Sir daga Buk."
"Siwes... Siwes...?"
"Eh sir Siwes."
"Ko dai IT?" Anas ya tambaya
"Yes shi."
"Ohh... IT zaki ce ai, irin yan attachment ne daga makaranta, kuna karbar yan IT anan kuwa?"
Ya tambaya yana kallon Salim da baki daya hankalin sa na kanta, wurga masa biro Anas yayi yana hararar sa, dariya yayi yana sosa keya yace;
"Sai a karba mana, kawo takardar muga."
Mika masa tayi daga gefe ya duba,
"Tirkashi, gashi dole sai oga ya sa hannu anan, shine matsalar."
"Toh, baya nan ogan?" Ta tambaya cikin zulumi.
"Gaskia baya nan, bansan kuma yaushe zai zo ba."
"Ah tsaya..." Ya jawo wayar sa yana dubawa
"Alhamdulillah, zai shigo gobe na tuna yayi min text jiya, kin ga ki dawo gobe kawai da wuri kamar takwas tayi miki anan, sai kawai yasa hannu a gaban ki ma ki tafi da a barki"
"Ok tam, Nagode, sai anjima.
"Sai goben dai."
Murmushi tayi ta wuce suka cigaba da hirar su.
**
Tun wajen karfe shida umma ke tashin ta taki tashi, da k'yar ta samu ta mike lokacin bakwai ma ta kusa, a gurguje ta tube kayan ta ta nufi bayi, nauyin dad'ewar ta a bandaki ne yasa Umma tashin ta tun dazu amman duk da haka sai data bata lokaci. Fitowar ta kenan daga wanka umma ta shigo d'akin rik'e da dan madaidaicin flask, ajiye shi tayi a gefe tana kallon ta baki bud'e ganin sai yanzu take fitowa daga wanka, kwafa tayi ta juya ta fice ba tare da tayi magana ba. A gaggauce ta shirya ta zuba kunun ta nufi kitchen in da take jiyo kamshin kosai da umma ke soyawa, zama tayi akan turmin dake jikin kofar kitchen d'in tana kurbar kunun tana jefa kosai a bakin ta tana bawa Umma labarin makaranta.
"Kina ganin lokaci kuwa? Ko kin tsaya zance."
"Wayyo ashe takwas ta kusa,na tsaya ina ta zuba, bari na tafi Umma."
"Yafi dai, Allah ya bada sa'a."
"Amin ya Allah."
Dogon hijab me hannu ta saka har kasa light brown ta rataya jakar ta ta fice da sauri tana duba lokaci. Karfe takwas da minti hudu ta isa wajen, gaisawa sukayi da me gadin in da ta shiga ciki.
A rufe office din yake alamun be zo ba kenan duk sammakon da yace tayi, kallon hadaddiyar motar dake harabar wajen ta tsaya yi baki bud'e dan ba k'aramin burgeta motar tayi ba, matsawa tayi jikin motar ta dan shafa ta tana niyyar ciro wayar ta ta dauka ta nunawa Asma'u don ita ce mayyar mota taji an turo kofar bangaren da take tsaye, da sauri ta matsa gefe, kafafuwan sa ne suka fara saukowa cikin wani hadadden takalmi irin na motsa jiki, kananan kayane a jikin sa na sport Ash da layi layin Green an rubuta ARKEL da manyan baƙi a bayan rigar, cikin tafiyar sa ta kasaita wadda ta zama na nature d'in sa ne ya nufi kofar yasa key ya bud'e ya shiga gami da bugo kofar da karfi. Sai data bari kamar da mintina goma ta yanke shawarar shiga, knocking tayi a hankali ta murd'a kofar ta shiga kanta a kasa, a masife ya d'ago jin bud'e kofar duk a tunanin sa Salim ne, ganin har takwas da rabi babu wanda yazo a cikinsu, ido ya zuba mata yana kallonta har ta k'araso gaban desk d'in cikin inda-inda tace;
"Malam Ina kwana?"
"What did u want?" Yayi magana cikin bacin rai ganin yadda take simi-simi da kai
"Am... Am.. Dama..."
"Get out !!!"
Tsayawa tayi tana zare ido a matukar tsorace kuma taki fita, nuna mata kofa yayi be sake magana ba, saurin tsugunawa tayi kasa tace
"Dan girman Allah kayi hakuri."
"Wai baki da kunne ne? Ko brain dinki bata aiki, get out please."
"I Hate to see girl acting decent, Allah a fili, a zuciya babu."
Yayi maganar kasa, a kunnen ta taji komai, kallon sa tayi ta juya cikin tsananin tashin hankali, a daidai kofar shiga sukayi kichibis da Salim zai shigo, kana ganin shi kasan shima hankalin sa a tashe yake ganin mota a waje, be yi mata magana ba ya wuce ciki da sauri, gefe ta samu ta rakube tana jin zuciyar ta kaman zata bullo ta fito, sama sama take jiyo muryar sa, faɗa yake sosai, sai da ya gama ciwa Salim mutunci tas sannan ya fito, motar sa ya nufa yaja ya bar wajen ba tare da yayi abinda ya kawo shi ba.
Office din ta koma da sauri lokacin Salim na tattare takardun da ya watsar a kasa,
"Ina kwana?" Ta gaishe shi tana kokarin fito da wata takarda daga jakar ta datayi photocopy
"Lafiya lou, sorry kinzo ashe tun d'azu."
"Eh nazo tun 8 d'in da kace."
"Opss, wallahi uzuri ne ya makarar dani."
"Ba komai."
"Sai dai kinyi rashin sa'a..."
"Na'am?" Ta zaro ido tana kallon shi.
"Kinzo kin tarar da oga, gashi form din naki ma dana bashi da wasu takardun ya haɗa ya watsar dasu kin gansu ina kwashewa."
"Innalillah wa inna ilaihi raji'un."
"Kiyi hakuri, dole yanzu sai dai ki jira, yanyin oga ne in kika ci sa'a in ya dawo next time ya duba ya gani, amma dai karki damu in sha Allah zanyi kokari na."
"Toh... Nagode Allah saka da alkhairi, amma dan Allah ka taimaka min, gobe yace wallahi na mayar."
"Zanyi kokari, amma gaskiya sai dai ko jibi ki sake shigowa, goben nan bana jin zai shigo gaskiya."
"Toh... toh.. shikenan nagode."
"Ba komai."
A sanyaye ta ja kafarta ta fita daga office d'in, gefen wani dutse taja ta zauna zuciyar ta tayi rauni, kuka take so tayi sai dai babu hawaye saboda tsabar yadda zuciyarta ta k'ek'ashe, wajen mintuna goma sha biyar ta dauka a zaune a wajen kafin ta bar wajen.
Yanayin da ta shiga gidan ne yasa Umma tasan babu nasara, gefen tabarmar da umman ta shinfid'a taje ta zauna bayan ta cire hijab d'inta ta rataye shi a saman igiyar shanyar dake tsakar gidan
"Umma sannu da gida."
"Sannu Maryam, ya na ganki haka sukuku?"
"Ba labari ne umma, ogan wajen na tarar baki ga yadda ya sauken kwadon bala'i a kaina ba, harda cemin kwakwalwata bata aiki, wallahi umma tun da nake ba'a taba wulakanta ni irin yau ba."
"Sai hakuri, haka rayuwar nan take, kasar nan tamu dai sai addu'a kawai."
"Wallahi fa,shikenan kai talaka sai dai ka mutu in baka dashi."
"Allah ya kyauta kawai."
"Amin Umma."
"Su Habubu an tafi makaranta gidan shiru sai ku kad'ai."
"Sarkin rigima ba, ana chan."
Tashi tayi ta shige ciki, ganin rana ta fara zuwa in da umman take zaune yasa itama ta koma cikin falon, hira suke d'an tabawa sama-sama har lokacin dora abincin rana yayi, shinkafa da wake ta dora akan charcoal. Matsala charcoal d'in ya bata ashe ba bushashe bane, har su Habubu suka dawo daga makaranta ba'a gama girkin ba, kukan yunwa ya fara Allah yaso akwai ragowar kunun safe Umma ta bashi sannan aka samu yayi shiru, yana shan kunun Maryam tazo ta dangware masa kai tana tabe baki
"Mutum sai rigimar banza an girma ba'a san an girma ba."
Umma na jin haka tayi saurin amshewa
"Shi kuma mutum ya dinga jan girman sa mana."
"Allah Umma yaron ne tabarar tsiya."
"Yayi d'in."
Walid ne ya karb'e
"Allah nima haushi yake ban abinda yake."
"Yayi d'in wai ina ruwan ku ne, a'ah? Kun fa samun auta a gaba."
Gwalo Habubu yayi wa Walid ta gefen kofin yadda babu wanda zai gani,
"Zan kamaka ne." Walid ya fad'a yana kwafa.
Haka dai sukayi ta hira suna tsokanar juna har lokacin islamiyya yayi suka shirya suka tafi.
***
Kai tsaye gida ya wuce, parking yayi ya fito yana kallon harabar gidan, motar Alhaji da ya gani a fake a wajen yake kallo, fitar da yayi dazu be lura da ita bane ko kuwa bayan fitar tasa ya dawo? Tab'e baki yayi ya wuce ciki. Tana zaune a cikin ɗaya daga cikin jerin luntsuma-luntsuman kujerun da suka zagaye falon, da sauri ta ajiye wayar hannun ta cikin kulawa tace,
"My boy ina kaje da sassafen nan a mota?"
"Naje duba wani aiki ne, goodmorning."
"Morning dear, ka tashi lafiya."
"Normal fa." Yace kawai ya juya ya nufi d'akin, da kallo ta bishi har ya kai kofar d'akin zai bud'e tace
"Alhaji ya dawo fa."
"Ok." Ya sa kai ya shige ciki. Hararar kofar tayi taja d'an k'aramin tsaki ta koma ta zauna.
Kwance take kafafuwan ta zuwa cikin ta lullube da bargo, idonta a rufe alamun barci, a bakin gadon ya tsugunna ya kamo hannun ta cikin nashi, kuka ne ya taso masa ya shiga yi a hankali, sama-sama take jin kukan nasa, a hankali ta bud'e idonta ta dora shi akan sa. Tausayin sa ne ya kamata ganin yadda yake kuka kamar mace, shafa kansa take son yi tana kokarin maida hawayen da taji yana neman zubo mata.
"Ummi..."
Kallo ta bishi dashi, murmushi yayi mata yana sake rik'e hannunta
"Duk wanda ya mai dake haka wallahi tallahi sai na ga bayansa, sai na dau miki fansa bazan taba yafe mishi ba, kowaye shi Ummi wannan Alk'awari na ne."
So take tayi magana amma babu dama, ganin haka yasa shi saurin cewa
"Karki yi
27, January 2025
Rukayya
Good