Showing 69001 words to 72000 words out of 87761 words

Chapter 24 - ƘAYAR RUWA Book 1 HAUSA NOVEL

HALIMAHZ   

20 Dec 2024

6116

ina ce masa,"Zan ɗora abinci ne da kai?".

Wani kallo yay min kafin yace,"Da sai kin tambayeni?".

"Yau ɗin kamawa tayi na tambaya".
"Kiyi duk yanda yay miki".

Kafaɗa na ɗaga na fita, kunun tsamiya na ɗora da soyayyar doya babu ƙwai, ina ga ƙwan sun cinye shi daga shekaranjiya zuwa jiya, dama kiret uku ne yay saura yana cewa za'a kawo ba'a kawo ba. Ban ɗora da yawa ba, daidai cikina da na Iyam da na yaran ne, yanda na ke ta abuna kamar ba wadda za'ai wa kishiya ba. na zuba doya a flask ɗin zan kai mata sai ga shi ya shigo kicin ɗin sanye cikin dakakkiyar shadda fara sai uban ƙyalli da ɗaukar ido take yi, an yiwa babbar rigar azababben ɗinki irin na sarakai, fuskarsa sai fidda annuri yake irin na sabbin angwaye masu ɗoki, ƙamshi kuwa la'ila ha'ilallah ban taɓa dai jin ƙamshi me irin wannan daɗin ba.

Kibiyar kishi ta soke ni naji hannayena sun shiga karkarwa, da ƙyar na iya saita kaina. Muryarsa a tausashe yace da ni,"Zamu wuce can wajen ɗaurin auren, a Abuja ne na san kin gani a katin, ban san lokacin da zamu dawo ba amma ba zama zamu yi ba ana ɗaurawa zamu taho. Amarya sai gobe za'a kawota, babu wani abu da kika buƙata zan iya tafiya?".

"Babu komai". Na faɗa a sanyaye.
"Don Allah Sa'ida kar inji wata fitina. ko Iyam ba wani taro zata yi ba duk ƴan uwa ne".

Na ce,"fitina ai sai fitinanne, ni da banda matsala da kowa".
Ya ce,"Na tafi to".

Na ce,"Allah ya kiyaye ya tsare hanya, a dawo lafiya".
Ya amsa da amin kana ya juya ya fita ni kuma na rakashi da ido, babu yacca ban ba hawaye karsu zubo min amma ina marayan kuka na saki ina durƙushewa a kicin ɗin.
Ubangijin da ke da iko da zuciyar kowanne bawa shi kaɗai yasan irin zafi da raɗaɗin da zuciyata ke yi a wannan lokacin. Haka na ci kukana na gode Allah kafin in miƙe da ƙyar in wanke fuskata a cikin sink ɗin kicin, kaina kuwa kamar zai tsage saboda azababben ciwo, ga jikina da ke karkarwa kamar me shirin kwancewa zazzaɓi. Abincin da na gama haɗawa na kwasa, sai da na haɗe har da nawa na juye a ciki don sam bana tunanin a yau dai wani abu shi abinci zai shiga cikina, ai ko yawun bakina jinsa na ke tamkar maɗaci.
Ina shiga ɗakin Iyam na aje mata abincinta, kallo ta bini da shi da mamakinta na ganina fess kamar ba wadda miji ke ƙara aure ba, kuma saboda an fi son ganinka a ƙuntatace har ce take to Allah sa ba mugun abu na ƙulla ba don ita bata taɓa ganin wacca za'a kishiya na harkokin gabanta ba rai fess a ranar biki.
Na fito ina ƙwala kiran su Rumana Iyam ta leƙo tana shaida min ai da su aka tafi jiya, ta faɗa tana ta ƙare min kallo gami da ƙara cika da mamakina, kicin na koma na aje abincin na su kana na koma ɗaki, ina shiga kuwa na tarar da wayata na ƙara da sauri naje na ɗauka sai dai ganin sunan da ke kan screen ɗin yasa ban ɗaga ba.

_"zan yo hayar ƴan daba mu zo gobe"._
Maganar ta Safiyya a jiya ta haska min cikin kai, don haka kawai na mayar da wayar na ajiye, na sani Safiyya me matuƙar damuwa da damuwa ta ce, tana kira ne don taji a wanne hali na ke, to sai dai raunin da ke tare da ni ba zai iya ɓoye halin da zuciyata ke ciki ba wanda ko da na faɗi akasin hakan don ɓoyewa za'a ƙaryata ni, kuma ina tsoronta da ta ƙara tambayar adireshin gidana don Safiyya na daga cikin mutanen da ke tabbatar da maganarsu idan sun faɗa, ko bata zo da ƴan daba ba to tabbas zuwanta sai ya haifar da rashin daɗi. Sai bayan kiran ma ya katse na ga ashe tun kusan da na fita ne ta ke kira miscalls goma haka ta bar mini, na shiga message ina duba saƙon da ta turo.

_"Beb na kasa yin breakfast, zuciyata taƙi yarda da cewa Nazifi ne zai yi miki kishiya, don Allah ki ɗaga kirana ko ki turo min da address na gidanki, yanzu haka ina shirin baro legos nan da awa ɗaya da mintuna zan shigo kano jirgi zan biyo, kuma don girman Allah ki daina kuka na sanki sarai, am on my way to na zo nayi haukar da zata sa a fasa auren nan yau"._

Girgiza kaina kawai nayi ina sauke numfashi a fili na furta Allah ya sanyaya miki. Ina kwance nayi nisa cikin tunani Ummani ta kira ni, Allah sarki uwa muryarta kawai ya shaida min cikin damuwa take, bayan mun gama gaisawa ta tambayeni babu dai wata matsala ko na ce mata ehh babu komai har ma na shaida mata masu tada hatsaniyar basa gidan jiya Yaya Babba ya zo duk ya kora su sai dai ban sani ba ko sai anjima za su zo amma dai yanzu daga ni sai Iyam ne sai baƙin ƙauye mutum uku da suka zo. Sai sannan naji natsuwa ta samu a muryarta tana aduan Allah yasa ma su tsaya a can gidan su yi bikinsu, haka tayi ta min hira duk dan ta ɗebe min kewa, katin wayarta ma ya ƙare kuma babu jimawa ta ƙara kira wai har ta bayar an siyo mata katin ɗari biyu, haka muka ci gaba da wayarmu na shagaltu a labarin rayuwarta da take bani, har sai da taji an fara yi mata warning kana ta ce to ko ta turo min Hindatu da Sa'adatu su tayani zama zuwa yamma sai su dawo na ce mata a'a kar su zo a sami matsala tunda duk suma zuciyarsu a wuya take. Nan ta shiga nanata min da cewa in ƙara haƙuri da kauda kai cikin maganganunta na kwantar da hankali da sa natsuwa da haka mu ka yi sallama.

Wajen sha biyu na rana gida ya fara cika da mutane, ashe biki sosai Iyam ta shirya matsayinta na uwar ango dan har sai da ta kai an wangale gate, waɗanda su ka fara zuwan duk ƴan  uwa ne irin na nesa sai jama'arta na tsohuwar unguwarsu, kan kace kobo gida ya ɗinke da hayaniyar jama'a kace auren fari ne ko kuma zata aurar da ƴar autarta ne. Da kanta ta zo har ɗakina karon farko tun zamanta a gidan tace na sauko na tayata karɓar baƙi kafin ƴaƴanta su zo, bayan fitarta na daɗa gyara jikina tukunna na fita, tunda na sakko ido yayo kaina ni kuwa na mayar da komai ba komai ba kamar yanda mahaifiyata ta ce da ni, don haka cikin fara'a da mutuntawa muka gaggaisa da mutanen da na samu a falo sannan na wuce ɗakin Iyam, can na sameta sunata hidima ita da muƙarrabanta, na ce mata gani me za'ai, tayi min nuni da kulolin abinci tace in ke zuzzubawa ga plate ina kaiwa baƙi. Kamar na juyawata na koma ɗaki ganin an raina min hankali amma haka na daure kawai na shiga buɗe kulolin ina zuzzuba abincin, alala ne da dambu aka yi sai lemon zoɓo da na jinja, idan na zuba kamar faranti biyar sai in ɗauka in je in raba kana na dawo, hidimar baƙin nata dai ta dawo hannuna gaba ɗaya kuma ko kaɗan ban bar wani shaida da za'a karanci ƙunci da kishin da ke danƙare a zuciyata ba balle aji daɗin yaɓa min magana amma a haka ma ban taira ba, don ina jin ƙusƙus ɗin wasu na cewa ko dai ba na son mijin dama ko kuma akwai abunda na ƙulla don haka banza dai ba zan ke wannan sabgogin ba.

Sai da lokacin sallar ƙarfe ɗaya kana na yakice na koma ɗaki, sallah nayi na kishingiɗa ina hutawa don na gaji kam. Lubabatu su ka shigo ɗakin ita da baƙi wanda ta rako, matan abokansa ne da suka yi tasowar yarinta kuma ban yi mamakin ganinsu ba dan dama da su ne mu ke ma'amala ta mutunci tun a tsohuwar unguwarmu, na tarbe su cikin mutunci nasa Lubabatu ta kawo musu abinci duk da ina fargabar kar Iyam ta hana, to da yake taga baƙin sun shafi ɗanta sai ga uban abinci kuwa an hayo da shi, mun yi hira da su sun nuna min kulawa kusan zan ce don su taushe ni ma shi ne maƙudin zuwan nasu ba kamar yanda nayi tunanin ƴan taya murna ba ne kamar yanda na san mazajensu za su taya shi.

Bayan tafiyarsu Iyam tace na zo mu ci gaba da aikin raba abinci ni da Lubabatu, lokacin ƙarfe biyu da rabi a sannan ne Lubabatu ke labarta min ba'a jima da ɗaura auren ba yanzu haka wasu har sun kamo hanyar dawowa, furucin nata yasa gabana faɗuwa da ƙara jin matsananincin kishin Nazifi. ina tsaka da rabon lemo sai ji nayi anwa hannuna muguwar damƙa, na kaikato kaina wajen ganin waye don har ga Allah zatona ma ko su Anty Aisha ne ƴan neman bala'i da hana kwanciyar hankali suka dawo, sai dai me! ware idon da zanyi sai ganin Safiyya na yi, ban san lokacin da na watsar da kayan hannuna ba na ɗago gaba ɗayana na rungumeta cikin murna da jin daɗi sai kuma kuka kamar dama jiransa na ke yi.
Bata ɗago kaina daga kafaɗarta ba ta kama hannuna zamu bar wajen bayan ta buga wani uban tsaki da ni kaina sai da ya shige ni. Sannan na ɗago ina cewa da ita,"bara na ƙarasa rabon nan sai mu je". Wata muguwar harara ta watsa min tana cewa,"ke dai wallahi anyi asararriya, to idan kin ƙarasa Allah ya tsine min, lusarar mace kawai".

Ina kallonta da murmushin ƙarfin hali na ce,"ba wani abu ba ne lokaci guda ne anyi an wuce wurin fa, bara saur...".

Tsawa ta sakar min,"ke dalla rufe min baki idan bassu da hannun ɗauka su mutu ko kuma wanda ya tarasu ya zo ya raba musu, dama ga su nan duk kalar yunwa, muje ni kina ɓata min lokaci".

Ni dai daɗi duk ya cikani nama rasa ya zan kwatanta murnar ganinta nace,"Safiyya ta ya kika zo gidan nan?".

Maimakon amsa tambayata sai ce tayi,"Ina ne ɗakinki?". tayi maganar a zafafe.

"Ɗakina na sama".
Tana riƙe da hannuna muka hau sama, muna shiga ɗaki ta isa ga wadrobe ta buɗe ta ɗauko mayafi ta cillo min,"saka mu je".

"Muje ina?"
"Gidan yankan kai". Ta faɗa tana wurga min harara da ke bayyana tsantsar jin haushina da take yi. Sai kuma ta kama faɗin,"Shashasha kawai mara aji, mijinki na ƙara aure amma saboda rashin sanin ciwon kai ke ce da rabon abinci wa ƴan bikin da ba gayyarki ba, ai wallahi ke dai banza ce ta ajin ƙarshe wacce ta rako mata duniya, to idan tunaninki wannan biyayyar aure ce kike magana ta gaskiya zubarwa da kai daraja ne da neman suna irin na jahilan mata. Su kansu waɗanda ki ka zage kina bawa abinci kallon typical mahaukaciya su ke miki".

Hannuna na ɗora bisa kafaɗarta na ce,"numfasa don Allah, ni wannan abun ba ya damuna don haka kar ki bari kema ya dame ki".

Ta tunkuɗe hannuna,"to ita Jummai cangal ɗin nan ta dawo ta tare naganta a compound tana faman ba da istruction".

Kallonta na ke yi sosai da yanda ƙwayar idonta ta kaɗa tayi jajir, na sauke numfashi na ce,"na faɗa miki ki daina kiranta da wannan sunan ko dan darajar auren ɗanta da na ke".

Ta fusata ta ce,"Ki sa a yanka ni Jummai cangal ba zan fasa faɗa ba".
Tayi maganar tana ɗaga kiran da ya shigo wayarta, tayi sallama tare da cewa,"na je Ummani". Tayi shiru na ɗan wani lokaci kafin ta sake cewa,"insha Allahu Ummani ba za'a sami wata matsala ba, naji faɗanki kuma ba zan saɓa daga nasihar da kika min ba, amin ya Allah".

Ta sauke wayar na ce,"Gidanmu kika je?".

Ta ce,"Ehh da nake ta kiranki kika ƙi ɗauka saboda ga annoba na kiranki sai na nemi waccan fat friend taki ta tura min lambar Ummani, ke ni tsautsayi ne ma ya kai ni gidan don ba a haka na zo garin nan ba. kinga kayan jikin nan nawa sai da naje can na sauya su, da na bacci na zo da hijab ɗin me aiki don ina tashi na kira Baba na ce a yankar min tiket, jiya fa ban iya barci ba Sa'ida ina ji ma jinina ya hau sai na koma zan yi bp. Ummani ce tayi min faɗa da nasiha banda haka da shigowata gidan nan tuni anyi asibiti da kaf zuri'ar Nazifi da wanda ya zo taya su murna, ke kaɗai za ki rage kema ɗin kuma ba haka zan barki ba sai na raunanaki".

Ina murmushi na ce,"Uhmm ke dai ki koyi haƙuri kam, wannan zafin zuciyar taki yay yawa, duk akan wata kishiya ki ɗaga hankali. Ko da yake ni naji daɗi ma sanadinta ga shi Allah ya kawo min ke bayan rabuwar shekaru da yawa".

"Mtssswww Kinga ba doguwar magana na zo muyi ba saka mayafinki mu je".

"Wai sai ce kike in saka mayafi muje, ina zamu? Kuma ai kin san ban tambaya ba".

"To me miji ai na faɗa masa tifa tayi awon gaba da kishiyar uwata zamu wuce asibiti da ke tare dubiya, in kuma yarda ne ba kiyi ba duba kiga". Ta faɗa tana nuna min message, da gaske kam take yi dama ba wani shiri su ke da shi ba don haka duk amsoshin da ya dawo mata da su a gajarce ne kamar yanda itama ta tura masa saƙon kamar tana basa umarni.

Na ce,"To ai bana fita da mayafi kin fi kowa sani, miƙo min hijab".

"Ƙunshe ki da ake da hijab ya zama past Beb, so yafa mayafi mu tafi, a tarihin Amaryar Nazifi da na duba babu saka hijabi idan zata fita a al'amuranta kuma auren Nazifi ba zai sauya ra'ayinta ba, infact ba macen da Namiji zai juya ba ce yanda ya so and tana da mutunci sai dai akwai ji da kai. Duk nayi wannan binciken akanta ne bayan gama wayarmu da ke jiya, mun ma yi waya da ita na karanta mata bani da hankali ko na misƙala zarra har feɗe mutum ina iya yi, kuma gasa fatar na ke nasa ayi masa romon kayarsa ya ci, don haka ta kiyaye taɓa wacca zata shiga gidanta don gatan ta cikin gidan ya fita da kaf abunda ta ke taƙama da shi, sannan ta shirya kurɓan baƙin cikin gidan aurenta domin wanda zata aura annamimi ne".

Mayafin ta dankama min aka muka fita ina kallonta baki sake, ita ta rufe ƙofar tana riƙe da hannuna muka sauka, gabanin zamu fita a falo Iyam ta shiga dakatar da mu da saurin murya. ni na juyo amma Safiyya tsayawa kawai tayi shima kuma dan na tsaya ɗin ne na ruƙota. Iyam ta iso garemu tana faɗin,"ki kaita ina? Ke kuma algunguma gidan uwar wa za ki je".

Buɗar bakin Safiyya zata yi magana nayi saurin saka hannu na rufe bakinta dan na san magana zata yaɓa daidai da tambayar da Iyam tayi. Nayi ƙasa da kaina ina cewa,"zamu je dubiya ne Iyam amma babu jimawa zamu dawo".

"To ba za ki je ba dawo".

Safiyya ta juya ta fuskanceta tace,"Algungumin mijin da take Aure ya bata izinin fita bai kuma ba ta umarnin idan wani ya hanata tafiya ta hanu ba".

Raina ya ɓaci na ce,"wai mene haka Safiyya".
Ta ce,"ba ta haife ni ba haka kuma ba auren ɗanta na ke ba".

Kafin na ƙara wata maganar ta figeni mun yi waje, tunda muka fito bata tanka min ba har muka hau napep tace masa jan bulo second gate, ƙofar S Fari Beauty Saloon ya ajemu, mu ka shiga ciki, wajen ya mtuƙar haɗuwa don sune lamba ɗaya na wajen masu gyaran jikin mata, babban wuri ne na gani na faɗa don suna da reshika wuri wuri a faɗin nigeria, farashinsu kaɗai zai shaida maka ba wajen zuwan ƙanan mata ba ne, sai dai fa duk rashin kuɗinki aka miki gyara sau ɗaya a wurin ba za ki ƙara sha'awar zuwa wani wajen ba gwara kike tarin kuɗi ko da ashirin ashirin ne, wurin na su ba ɓoyayye ba ne kana sauka second gate zaka hasko shagon nasu na kallo Hayfa Furnitures.
Da hannu Safiyya ta tankaɗani gaban me wankin kan tace,"don Allah wanke min kan shashashar nan ya fita kiyi masa desng me kyau irin wanda zai gigita miji".

Me wankewar na dariya ta ce to an gama ranki ya daɗe, ni kaina sai da na yaba da gyaran da akawa kaina ashe gashina haka yake da kyau ban sani ba, bayan an gama gyaran gashin aka yarfa min jan lalle da baƙi, hannayena da ƙafata suka fito shar da su. duk wannan abun da ake fuskar Safiyya a ɗaure don har muka je wani shago a rijiyar zaki ta siya danƙareren less da yaji uban aiki a jikinsa irin wanda ake siyarwa a ɗinke da kuma shadda. Da mamakina naga mun wuce asibiti sai da muka je take gaya min za'a min gwajin haihuwa ne, ai ba ƙaramin daɗi naji ba don dama tuni na ke so naje asibiti a duba ni to amma ban san me zan ce wa Nazifi ba idan zanje ga shi sam bana son masa ƙarya.
Barowarmu asibitin gidan wata Antinta muka wuce, nan ta zaunar da mu da yake sun jima ba su haɗu ba, kuma ni kaina sai naji daɗin zuwan sosai don gaba ɗaya ma sai na mance da batun wani biki a gidana balle kishiyar da za'a min. A wannan zaman ne muka yi hirar yaushe gamo da Safiyya har take shaida min ta fara aiki a babban asibiti, na tayata murna sosai na kuma ji ina ma ni ce a matsayin da take, sai dai ni na riga nayi watsi da damata na tarwatsa mafarkin Abbaana. ina mata maganar aure ta harzuƙa tana cewa ita da aure ai sai yanda taga rayuwa ta ƙarewa Nazifi, ta yanda ta san Allah zai ci uban nata mijin tun anan duniya kafin aje

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login