Showing 60001 words to 63000 words out of 87761 words
kuma saboda ya ƙara ci min fuska ya ce,"Idan kin gama sai ki shirya gobe dangin matata za su zo suyi jeren kayan arziƙi, iyayenta su ne suka siya mata kayan ɗaki ba da na mijinta zata yi amfani ba, kuma kar inji kar in gani, idan ba haka ba kuwa za ki sha mamakina...za ki iya fice min daga ɗaki".
Na tsaya kallonsa babu ko ƙifce, lallai masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce mutum mugun ice, mutum butulu, Namiji Ƙayar Ruwa, Namiji ƙanin ajali, Namiji rigar ƙaya. wato Nazifi ya manta duk wani faɗi tashi da nayi da wuya ba daɗi duk akansa kafin zuwan matsayin da yake kai yanzu, ina tare da shi tun baida ko sisi, na zauna da shi cikin tsananin talaucinsa ban guje shi ba, kullum cikin ƙoƙarin in faranta masa na ke in kwantar masa da hankalin damuwa da yake yi, amma shi ne yanzu saboda dukiya ta samu zai juya min baya, har da ƙaro aure yana min gorin kayan ɗaki da iyayen aba su siya min ba a sanda zamu dawo sabon gida, kai jama'a anya duniya da amana?, kai babu!, domin in akwai da ruwa bai dafa kifi ba.
Na danne zuciyata ina ɓoye bala'in raunina da ke neman karkaryewa a gabansa, naja dogon tsaki na juya zan bar masa ɗakin saboda zuciyata ingiza ni take yi akan in aikata ba daidai ba. Ina shirin fita mahaifiyarsa ta danno kai, na yi saurin komowa da baya domin bata hanya, haka ta tsira yanzu duk sanda ta so shigowa take kai tsaye babu neman izini balle shayin a yacca zata shigo ta tarar da mu.
Na sa kai zan fita tayi saurin dakatar da ni da cewa,"korar ki na yi?".
Nace,"a'a Iyam da ma zan fita ɗin ne".
"To dawo".
Na dawo na tsaya daga gefe, ta kalle ni da fuskar nan tata ta marasa mutuncin uwar miji ta ce,"hayaniya na jiyo tun daga ɗakina lafiya?".
Ban yi magana ba nayi shiru saboda gaba ɗaya sun mayar da ni banza wadda bata san abin da take ba. cikin raina na ce,_"hmm ko ba komai ana barin halak don kunya dai, kuma insha Allahu da sannu za ku gane kurenku"._
Ɗan nata ya ce da ita,"ki zauna".
Ta gama fahimtar abin da ke faruwa hakan yasa ta juyo gareni tana faɗin,"yauwa ki kwashe tarkacenki na ɗakin kusa da matakalar bene, saboda baƙi za su fara zuwa gobe za su sauka anan, taron biki za'a fara a gidan ban sani ba ko kin sani, na san dai duk kinga ai na kusa da abun".
Ina jan yatsuna na ce,"na sani, amma Iyam ɗakunan gidan da yawa ai da sai a duba wani, wancan ɗin har yaushe na gama kwashe kayan cikinsa".
Ta jijjiga kai ta ce,"zan sa a fito miki da su tsakar falo in ya so kya kwashe su anan. Ai dama na san ke dai sai kin yi baƙin ciki da auren nan, to ba'a aure ke aka auro ki?, ko ba'a zama da kishiya uwar ubanki ta zauna da ita?, Ni fa dalilin mugun halinki yasa na ce kar a bari ki sani don ban san irin malaman da za ki bi ba, to koma dai menene Sa'ida aure Nazifi zai ƙara ko za ki mutu sai dai ki mutu, akan me zai ta zama da juya irinki wacce ba'a san ranar haihuwarta ba?, kina zaune jaɓar sai cinye masa kuɗaɗe ki ke ba aikin fari balle na baƙi, kina ɗauko dangi da ɗai ɗai kina a taimaka musu da abinyi, to dukiyar ɗana ba zata lalace a taimakon ƴan uwanki ba kawai, na san wannan dalilin ne ma yasa kika sha abin da zai hanaki haihuwa, kai muguntar ɗan talaka ma bata yi ba wallahi".
Tayi shiru tana jan tsaki, ta mayar da kallonta ga ɗanta ta ce,"kai kuma lusari ka bari mace zata ɗaga maka hankali akan zaka ƙara aure, ba ka gaya mata da izinin mahaifiyarka zaka ƙara, mata nawa Allah ya halasta ma ka zama da su?, in ba zata iya ba ta kama gabanta mana wani ya riƙe mata ƙafa ne ko akwai wanda ya rufe mata ƙofa. ina dalili a hanaka auren mace mai ilimin zamani da wayewa wacce take haihuwa ba juya ba...".
Ba zan iya ci gaba da tsayuwa ina jin waɗannan bakaƙen kalaman ba, da sauri na fice a ɗakin cikin fashewar kuka, ina zuwa parlo na tarar da Yayan Shago tsaye, da alama ya shiga ɗakin Iyam ne ya tarar bata nan ya fito. Dauriyar tsayar da hawayena nayi ina gyara natsuwata na duƙa na gaida shi cikin girmamawa, ya amsa cikin tausayawa yanayin da ya ganni.
Murya a sanyaye nace da shi,"ka zauna mana yanzu zata fito".
Zama yay ni kuma na shiga kitchen na kawo masa ruwa da lemu. ko da na duƙa wajen ajiye tray ɗin hannuna kasa ɗagowa nayi kawai naji sabon kuka ya ƙwace min, bakina na rawa na furta,"Yayan Shago yanzu abin da aka min anyi min adalci kenan?".
Shima cikin rashin jin daɗin faruwar lamarin ya ce,"ko kaɗan ba'ai miki adalci ba Sa'ida, ba ɓoye miki auren kaɗai ba hatta kishiyar kanta da za'a miki wallahi ba'a kyauta miki ba indai kan dalilin da suke faɗa ne, babu irin shawarar da ban bawa Nazifi ba akan auren nan yaƙi jina sam, ƙarshe ma kada baki yay ya faɗa min shawara kowacce iri ce in dai daga gareni ne ba ya so in riƙe girmana kawai. to kin san sha'anin mu maza in muna son abu idonmu rufewa yake musamman aka ce aure...amma kiyi haƙuri kinji dama ke ɗin me haƙuri ce, ki barshi yayo aurensa ke kuma ki riƙe adu'a ki kuma tsarkake zuciyarki a zamantakewarku, kar ki taɓa bari zugar shaiɗan ko ta ƙawaye su canja tunaninki, ki kama aurenki ki riƙe kar kishiya tayi silar rasa igiyoyin aurenki, idan da son samu ma Sa'ida ki ɗan nemi sana'a za ta ɗebi miki kewa".
Ya ƙarasa maganar cikin alamar rarrashi, cikin ƴaƴan Iyam Yayan Shago da Lubabatu na daban ne, su na da kyawun zuciya, duk abubuwan da ke ta faruwa su kaɗai ne abun duniya bai sauya kyakykyawan ɗabi'arsu ba. Na sa hannu ina goge majinar hancina sannan na ce,"babu komai in sha Allahu zanyi haƙuri, zan jajirce kuma zan daure, na gode Yayan Shago".
Na miƙe daidai da fitowar Iyam, ta taho tana faɗin,"wani abun ta kitsa maka kenan, to Rabilu me za ka iya yi?, kai kam ai sai dai kallo, batun aji maganarka ma ai bata taso ba".
Maganganun da Iyam ke faɗa masa su ka taɓa zuciyata, tausayinsa ya kama ni, cikin yaranta maza shi ne babba amma saboda ba shi da kuɗi ya zama abin banza, babu ruwanta tai ta yaɓa masa magana, ta mayar da shi ƙarami a cikin ƙannensa, an mayarshi tamkar wani bare.
Allah ya kyauta na faɗa a raina ina barin wajen. "Keeee!". muryar Yaya ta faɗi hakan wanda tsakiyar kaina ma sai da ya amsa, na rumtse ido ina juyowa in kalleta cikin tsananin jin haushinta, yanzu sam sunana ma ta daina kira sai dai kee. Shiru nayi ta wurga min harara tana cewa,"me za ki je sama kiyi a wannan lokacin?". kafin na bata amsa ta kalli Iyam ta ce,"wannan yarinyar bata san da zuwan baƙi ba ne?, Na duba kitchen na ga babu abincin da za'a ba su".
Iyam ta kyaɓe baki ta ce,"yau tana jin kanta da hayaƙi ina zata yi wani aiki, ai kawai ki kwaɓe ki shiga kiyi da kanki ko kuma ki tattara yara suyi, in ba haka ba kuma a san in da za'a kai a biya kuɗi su girka".
Yaya ta kama masifa tana faɗin mene amfanina a gidan da sai an fidda kuɗi an kai wani waje girki, tayi min tatas ta ce in shiga kitchen in ɗora abinci mai sauƙi saboda masu zuwa ɗaukar kayan lefe na kan hanya. kamar mara galihu haka na wuce ina jiyota tana faɗawa Iyam wai Malam ya ce shi ba da yawunsa ba cikin ƙannensa mata wata taje kai lefe, shi ne Iyam ɗin ke faɗin to kar ya barsu suje ɗin itama ai tana da ƙannen kuma ta isa da su kuma sun isa zamewa Nazifi wakilai.
Cous cous na ɗora jallof saboda nayi saurin gamawa gudun tashin hankalin Yaya, ba ƙaramin dauriya na ke ba wajen ɓoye halin da na ke neman shiga na azababben kishi. kafin la'asar gida ya cika da mutane, baƙin fuskar ba wasu da yawa ba ne, yawanci ƴan uwan Iyam ne sai ƙannen Malam su biyu Mama Laraba da Anty Huduriyya, sai ƙawayen Iyam da kafatanin ƴaƴanta mata, sai Ummaa itama da nata mutanen, tawagar dai duk ta marasa kirki ce, shiyasa dama tunda na dawo naga wannan gayyar kaina ya ɗaure na ke ta rayawa a raina ina cewa sai kace za'a yi biki, ashe ashe ile sace da ni shashasha ina ta harkokin gabana ban san miji zai danƙaro min kishiya ba. Abincin da na tafe kula da shi sai da suka cinye shi tass masu santi nayi masu kushewa nayi, ni dai ina kammala abubuwan da zan yi a ƙasa na haye sama saboda na daina jin ma habaice habaicen da su ke ta aikin yi tun zamansu falo.
Tun da na shiga ɗaki gaba ɗaya na kasa sukuni, yayin da mamaki ya cika ni fal, na kuma kasa gasgata abin da ke faruwa a yau, kuka na ke rabza kamar an aiko min da mutuwar uwata, kukan da nake ba na komai ba ne face kukan abu mafi zafi a duniyata, kukan butulcewar Nazifi da gorinsa gami da ƙarin aurensa ba tare da na sani ba. ban taɓa zaton akwai ranar da Nazifi zai iya ƙaro aure ba, na dinƙa tuna irin yanda Nazifi ya ke matuƙar ƙaunata ada tunanin da kullum sai nayi, da irin gwagwarmayar da muka sha tare wanda zan ce ma na fisa. Na girgiza kai cikin tsananin danasani da nadamar damar da nayi sakaci da, haɗi da gangancin ɗora dukkan yardata akan ɗa namiji, ni sai a yau ma da batun kishiya ya tashi komai na farkon haɗuwata da shi ke zuwar min daki daki, kuma sai a yau naji ashe duk wasu wulaƙancinsa na baya ba komai ba ne ga ainihin wulaƙanci nan, domin akan wannan ne ya iya buɗe baki ya gaggaya min maganganu ma su ƙona zuciya har yana faɗin yana kunyar shigar da ni cikin jama'ar kunyarsa, banda wayewa! Ina zaune daɓas! satifiket ɗin sakandire!, ba zai zauna da mara haihuwa ba! hmmm lallai Nazifi.
bayan kukana ya lafa na kwanta jiki a sanyaye, kaina jinsa na ke tamkar zai tsage, cikin tsananin damuwar da nake ciki naji ana ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin, na miƙe cike da fargaba naje na buɗe, sai da na sauke wawiyar ajiyar zuciya ganin ba azababbiyar da nake tsammanin gani ba ce. murmushin yaƙe na saki ina cewa da Lubabatu,"to shigo ciki mana kin tsaya".
ta girgiza kai tana faɗin,"a'a Anty Sa'ida ba zan ja miki magana ba, Yaya ce ta aiko ni wai ki sakko yanzu ki ga lefen amarya za'a tafi kaiwa".
Nace,"ai ba sai na gani ba su kai kawai".
Ta kamo hannuna tana cewa,"kiyi haƙuri kawai ki je kar akan wasu banzan kayan lefe a ci miki mutunci a gaban mutane".
Kai na kaɗa na juya ciki na ɗauko mayafina na yafa muka sauka tare, lokacin ana ta firfito da akwatunan daga ɗakin Iyam, abin ya ɗaure min kai, ban taɓa sanin da ana haɗa wani lefe a ɗakinta ba, ko da yake sha'anin kuɗi ƙila a rana ɗaya aka haɗa su aka ajiye sai yau da za'a kai aka bani damar gani. Kujera ɗaya mu ka zauna ni da Lubabatu har lokacin tana riƙe da hannuna tana tausata a hankali gudun kar su jita su babbakata da masifa. tana ta min ƴan hira duk dan ƙarfafa min gwiwar in daure in nuna musu abun da su ke ta rawar kai akai ba komai ba ne a wajena. haka aka jere shegun akwatuna guda goma sha shidda kowacce akwatu aka buɗe maƙil take da kaya na alfarma, bakin kowa ya buɗe sai maganganu ake da irin ƙoƙarin da yay wajen haɗa kayan, ita kuma Yaya na faɗa musu ai wadda za'a auro ɗin ba ƴar ƙananan mutane ba ce, mahaifinta me kuɗi ne kuma itama yarinyar tana aikinta a wata babbar ma'aikata, har tana faɗar sanadin haɗuwar tasu a jirgi ne lokacin da ya dawo daga Dubai.
Iyam ta ce,"wallahi ai sai yanzu ne Shalele zai yi aure, yarinyar ƴar boko ba cima zaune ba, gata lafiyayya don da suka je wannan gwaje gwajen da ake a asibiti an tabbatar da lafiya ƙalau take, ga kyau kamar ka saceta ka gudu fara tasss da ita, ƴar manyan gida ce fa don Babanta ma ba ƙasar nan yake zaune ba".
Furucin na ta yay matuƙar ba ni mamaki, wato duk wanda ya san a yanda na auri Nazifi da yanda ahalinsa su ke a baya, la shakka sai anyi rubutun babban littafi na butulci akansu.
Ni dai duk ɗage ɗagen kayan da su ke yi kaina na ƙasa, na ƙagu su tattara su kwashi kayansu nima in tashi in bar wajen. Ƙawar Iyam ta kira sunana tana cewa,"Uwar gida ba ki ce kaya sun yi ba".
Iyam tayi caraf ta ce,"tana baƙin ciki ai bata faɗa ba, wa ya san me ke zuciyarta yanzu. Kuyi kuyi a rufe su kafin ta cinna musu wuta".
Ni dai ban ɗago ba kuma ban yi magana ba, banda kuma niyyar cewa ƙala, duk da irin shewar da suke yi na daɗa ƙona zuciyata, kuma dama na san an kira ni na zo ɗin ba don komai ba sai don a ƙuntata min. Ummaa har faɗi take yi wai to duk irin hidimar da Nazifi yay min har na yi baƙin ciki da aurensa ko hidimar da yaywa matar da zai aura in dai ba rashin halacci irin nawa ba, kuma banda abuna ɗan miji ai ɗanka ne, idan ta zo ta haifa duk tsiya nima nace ɗana. A wannan lokacin ne Anty Aisha ta shigo, sallamarta ce tasa na ɗaga kai, taci kwalliya ta caɓa ado tana taunar cingom kamar wata ƴan mata, ni ban lura ba ma babu ita a wajen ba sam, yaran da suka shigo da kuloli ta kalla ta ce,"ku kai can ku ajiye".
Sai ta ƙara cewa,"Iyam yamma tayi fa kar dare yay mana a hanya, kin san sun ce a yau za su wuce da lefen can Abuja wurin Kakarta. ga kulolin kayan garan can a mota, kajin kuma da aka soya gaba ɗaya kula uku ne na ɗebarwa wannan ƴar a ciki gashi nan a leda, dublan da alkakin ne dai ga kula guda nan an bar mata".
Haka suka ɗunguma gaba ɗayansu su ka tafi, tsabar yawansu motocin gidan biyar aka ɗiba, bayan fitarsu na tashi na bar wajen ban ko bi ta kan kulolin da aka ce na ɗauka ba, ina jin Iyam na ƙananun maganganu akan na raina abun da aka bani, itama ban kulata ba nayi gaba abuna, kaza dai ba zan ɗauka ba don ba yunwarta na ke ba, dublan da alkaki duk ba na ci sune mayunwatansu.
Da daddare ina kwance sai ga Nazifi ya shigo ɗakina da munafukan akwatinansa guda biyu wai na faɗar kishiya, baƙin ciki ya tokare ni, to ai ko lokacin da zai auren sanda baida uwar komai akwati biyu ya shaƙo min da kaya da ƙaramar jakar bakko ɗaya. don haka ko kallo bai isheni ba shi da kayansa na juya masa baya, ina jin yana faɗin wai ko na raina ne, ban ce masa kanzil ba nayi ma kamar bacci na ke yi, ya gaji da tsayuwarsa ganin banda niyyar kula shi ya ce,"Allah ya gani na fita hakkinki, ga su nan ki ɗauka ko kar ki ɗauka ruwanki. Kuma idan akwai abunda kike buƙata sai ki faɗa min".
Ya faɗa yana juyawa ya fita ya bar min akwatunan, ai kamar an finciko ni haka na miƙe na duro a gadon, ƙafa nasa na dinƙa tura akwatunan har na kaisu bakin ƙofa kana na cilla su waje, kallona ya tsaya yi da mamaki da takaicin jefa masa kayansa a gaban ƙafafunsa, na kalle shi na banka masa harara tare da jan tsaki na danna ƙofata na rufe tare da sanya maƙulli, babu yanda bai da ni ba akan na buɗe ƙofar na ƙi, har da min barazanar zai kira Abbaa a waya yanzu ya faɗa masa rashin mutuncina gaba gaba ya ke yi, ni inda zai kira ɗin ma ai daɗi zan ji, don ko banza ƙila sanadin rabuwarmu kenan, don na lura ba zan tsani Nazifi ba in ba rabuwa muka yi ba.
Wai duk yanda na kai da ƙoƙarin danne abinda ke tasowa daga can ƙuryar zuciyata amma hakan ya faskara, ban taɓa tsammanin cin fuska irin wadda Nazifi yay min yau ba, kawai na fashe da azababben kuka mai ƙaramin sauti saboda Rumana da ke ɗakin, babu abunda na ke buƙata a wannan lokacin irin na samu kafaɗan da zan kwanatar da kaina in zubar da hawaye har a lallasheni, sai dai bani da kowa cikin wannan gidan, Allah ne kawai gata na, yau in ace ka haifa ma ko a wannan kafaɗar ɗanka kayi kukanka duk da hawayen uwa rauni ne ga ƴaƴanta. na jima ina kuka sosai kafin na iya rarrashin kaina. Nayi kuka, kukan da ban taɓa irinsa ba tun bayan da abubuwan su ka canja a gidan nan, ban san a dalilin auren nan kuma ya rayuwata zata ci gaba da tafiya ba.
bayan na idar da sallar isha'i na yi jugum ina ta faman tunani iri iri na game da rayuwar aurena, ya kuma zamu ƙare zama da wacca zata shigo? Itama irinsu ce? Me aka faɗa mata game da ni? Na san dai ba zata taɓa zama irina ba. Rumtse ido nayi ina ji anata knocking ƙofa na ƙi tashi na buɗe kuma da alama aiken zuwan gayyar tsiyar ne ban san ko uwar da zan yi musu ba, ba zai wuce zancen abinci ba tunda naji ba su jima da dawowa ba, ni kuma a yanzu dai in ba uwata