Showing 63001 words to 66000 words out of 87761 words
da ubana ba wallahi babu wanda ya isa ya sakani shiga kitchen na dafa masa abinci, don ko me gidan yau sai dai yaci a inda yake zuwa zance, ko in ya rage na rana ya ci.
Knocking ɗin ƙarshe ne ma Rumana tace,"Anty ni ce please ki buɗe min".
Ba zan iya ƙin buɗe mata ba don Allah ya sani yarinyar ta shiga raina musamman da Allah yasa ta gane hanyar daidai, duk da ba wani yarda na gama yi da ita ba tunda jinin Yaya ne ke yawo a jikinta. na miƙe na ƙarasa na buɗe, ta na jin na cire key kuwa tayi saurin danno kai ta shigo ta mayar ta tura ƙofar tana cewa,"Anty sauri saka key".
kallonta na tsaya yi duk a tsorace ta ke. "lafiya?".
Ta marairaice fuska kamar zata yi kuka sai kuma ta rungume ni tana saka kuka tana faɗin,"Anty ki daina fushi da ni Allah na daina yi miki duk irin abunda mu ka yi miki a baya, wallahi ba zan ƙara ba anyi mana wa'azi a islamiyarmu ma, ina sonki Anty".
Na janyeta ina cewa,"na ji, yanzu ya aka yi?".
Shiru tayi bata ce komai ba, don haka na mata nuni da ƙofar ina cewa,"to je ki sai da safe". Na faɗa a hasale don haushin kowa da ya shafi Nazifi na ke.
Ta kama hannuna tana ta min rantse rantse da ba ni haƙuri har dai na ƙyaleta, sai da na koma na zauna ina lazimi kana take ce min wai haka aka ce su je su faɗawa Abbansu suna jin yunwa kuma tun rana ban ba su abinci ba, shine ita ta gudo Atika kuma ta tafi.
Gajeriyar dariya kawai na yi, na rasa wannan bala'i na su na rashin son in zauna lafiya a gidana, haka kuma na rasa masifa da jarabar da ke cikin so da duk abunda ke faruwa har abunda ya faru a yau na ke jin Nazifi a raina. Rumana ta miƙo min homework ɗinta in yi mata, na karɓa na duba sai naga english ne kuma turancin kam yafi ƙarfin kaina tunda dai ni ba wani jinsa na ke sosai ba balle ma har na wani iya bayani akan abun da aka tambaya. nace ta tashi ta kaiwa Fati tayi mata amma ƙememe yarinyar nan taƙi wai sai da safe yanzu idan ta fita za'a iya dukanta. bayan na gama jin karatun da aka yi musu a islamiya sai ta kwanta bacci.
Ina zaune har ƙarfe tara kan darduma na kasa kwanciya, haka ban san ma tunanin me na ke yi ba. hannu na miƙa na ɗauko wayata ina sauke ajiyar zuciya, so na ke nayi waya da wani ko na ɗanji salama cikin zuciyata, bashin kamfani na ciwo na nera ɗari na danna kiran Maman Yasmin, ko da ta ɗaga muryarta da nuna tsananin damuwa take tambayata lafiyata da wannan daren haka. ban san lokacin da na fashe mata da kuka ba ina cewa,"Maman Yasmin aure zai ƙara".
"Aure? Nazifin ne zai ƙara aure?".
"Ehh Maman Yasmin, ɗazu ma su ka kai lefe jibi ɗaurin aure, ban san ya zan yi ba Maman Yasmin ina ga Nazifi so ya ke ya kashe ni, wallahi yanzu haka zuciyata ciwo take yi min, kuma Maman Yasmin ina sonsa ba na son wata tayi silar rabani da shi".
Maman Yasmin tayi wani murmushi da sautinsa ya fidda jin daɗi ta ce,"To kuma sai mene na kuka Sa'ida? Sai me don Nazifi gayyar tsiya zai ƙara aure? Ke yanzu har wani kishinsa kike bayan bai ganinki da mutunci daidai da ƙwayar zarra, to ni wallah ce na ke ma kin daima sonsa kina dai zaune ne jiran ƙaddarar da ta haɗa ta zo ta raba".
Sai kuma ta numfasa ta ƙara cewa,"in faɗa miki gaskiya wallahi mugun daɗi naji ba kaɗan ba da batun nan, ai gwara ya ƙaro auren ya kawo wacca zata ci kutumar ubansa ta gasa masa aya a hannu da shi da duk ƴan uwan nasa tunda ke kin kasa ƙwatarwa kanki ƴanci. Allah ne ya dubeki ya kawo maki mafita, saboda haka ki bar damun kanki ki zuba ido kiyi kallo kina daga kwance za'a rama maki duk abunda aka yi miki. da yardar Allah auren nan sai ya saka su cikin baƙin cikin duniya ƴan bantan uba marasa mutunci, za su auro daidai da rashin mutuncinsu ne don ba za su samu wacca za su juya irinki ba lusarar banza da haƙurinta ke halakar da ita".
Haka Maman Yasmin ta dinƙa zazzaga bala'i, ita da na kira ta kwantar min da hankali, ƙarshe sai ga shi zage zagen da take ya haɗe har ni, wai saura in bari kuma idan Amaryar ta zo na bata wuri itama ta takani son ranta. Awannan gaɓar ba shawara ko haƙuri zata bani ba har gida zata zo tayi min mugun dukan da zan kasa motsi.
Yashaik ne ya amshe wayar daga hannunta don yanda take bambamin bala'i tamkar ita za'ai wa kishiyar, to da yake shima yanzu ya san komai dangane da halin da nake ciki, don lokacin da ya takura kansa da zuwa gidan C.I.D ɗin da Kaka ya saka shi, Ummani ta zaunar da shi ta fahimtar da shi komai, da ike indai ta faɗi abu to ko ba haka ba ne ya yarda kawai, cikin ikon Allah kuma sai gashi ranar ya zo ya taradda Yaya na yi min tijara shima Nazifin nayi min, dama yana daga ƙofar falo zai shigo yaji duk abunda ke faruwa, shigowar da bai yi ba kenan ya juya, a daren ranar ya kirani yay ta bani haƙuri ya kuma lallasheni shima yay min nasa nasihohin, har yake cewa zai bani jari sai na faɗa masa ai tuntuni Nazifi ya hanani sana'a kowacce iri, wai in ba a aikin gwamnati ba matarsa ba zata yi kasuwanci ba tasa a ke masa kallon ƙaramin mutum.
Tunda Yashaik ya fara lallashina da kalaman kwantar da hankali gami da nasiha mai ratsa jiki, wallahi sai naji tamkar Abbaana, dama shi komai nasa na Abbaa ne hatta muryarsa wani lokacin. cikin ƙanƙanin lokaci sai naji raina ya fara washewa a ƙalla baƙin cikin Nazifi ya ragu, bai barni ba har sai da yay silar da na saki murmushi mai sauti, da haka muka yi sallama bayan na ce ya gaida su Yasmin da Ajmal sannan na ajiye wayar daga gefena. Har na aje wayar sai kuma na ɗauka na kira Ummani, itama hankalinta ba ƙaramin tashi yay ba da ganin kiran nawa, musamman da ta jini ina kuka sosai.
"Sa'ida me yake faruwa ne? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un".
"Ummani aure zai ƙara kuma bai faɗa min ba tsabar bai ɗaukeni da daraja da ƙima ba a cikin gidan nan, Ummani na gaji ni kam na gaji ba zan iya ci gaba da zama ba don ban san da manufar da ya ƙullo auren ba, ki cece ni Ummani kar su kashe miki ni da baƙin ciki".
Daga ɓangaren Ummani ta jinjina kai tayi shiru domin ita kanta lamarin ya taɓata, ƙarin aurensa ba abun mamaki ba ne, kawai ta yanda ya ɓullo da lamarin wajen ƙin shine abin takaicin da ɓacin rai. To ya za'ayi ita uwa ce, bata da wani kalami da zata faɗawa ƴarta wanda ya wuci nasihar dai da ake yi kullum, sai kuma ta kwantar mata da hankali, in ace ma Abbaa ya sauko ne sai tace to da safe ta taho gida ta zaune ta rage zafi in suka gama bidirin bikinsu ta koma in ƴan uwan nasa sun bar gidan, amma tabbas Nazifi bai kyauta ba ko kaɗan, ita tsoronta ma kar su illata zuciyar ƴarta amma babu komai adu'a bata bar komai ba, tana yi mata za kuma ta ƙara dagewa akan hakan.
Da kalamai masu daɗi da tausasawa mahaifiyata taita lallashina tana bani baki tana nusar da ni fa'idar haƙuri da ɗauke kai da miƙa dukkan lamura ga ubangiji, da sannu komai zai shuɗe ya zama tarihi.
Tun bayan gama wayarmu da Ummani na kwanta babu abunda na ke sai hawaye, hawayen da sai da ya jiƙa filon da na ke kwance, ban san dalilina ma na damuwa akan lamarin auren nan ba, ai tun ranar farko da Yaya ta zo taci zarafina na sakawa raina muddin ba haihuwa nayi a gidan nan ba ba fa zan huta da gori da cin mutunci ba, aure kuma kamar Nazifi ya riga yayi ne na san da wannan don da hankalina ai da tunanina take takensa kaɗai sun isa su sanar da ni hakan, to da yake dai kishi halitta ce a jikin tsokar zuciya babu yanda zanyi sai dai nayi ta adu'a Allah ya sauƙaƙa min, sabon tozarci ne dai na san zan fusance shi idan matarsa ta zo, haka nayi ta faman lissafin yanda zan fara gudanar da sabuwar rayuwata a cikin gidan daga gobe.
Kaman yanda na saba cikin dare nayi sallolina na kaiwa Allah kukana, karatun ƙur'ani tunda na fara sai da na sauke izu goma ina karatun ina kuka, kuma kaman ɗaukewar ruwan sama haka hawayen idona ya ƙafe babu ko saura da ke son fitowa daga zuciyata, wani ƙwarin gwiwa na shigana wanda ban taɓa jina a cikinsa ba dangane da abunda na ƙudurta a raina.
Washegari da safe ban farka ba sai wajen ƙarfe goma na safe duk da ba baccin daɗi nayi ba, Lubabatu dai ta leƙo wajen takwas tace Rumana ta fito za'a kaisu ƙunshi da kitso to tunda na mayar da ƙofar na rufe ban ƙara buɗewa ba duk da naji an zo an buga nayi biris.
Shi kuwa dama yau ban shirya zan leƙa wurinsa ba sam balle tunanin abunda zan shirya masa ya ci. Na yi wanka nayi shirina nai zamana a ɗaki na kunna data na hau online don ɗebe kewa amma duk da haka can cikin zuciyata na ƙarayin babu daɗi, ina cikin tunanin abunda zai faru tsakanina da su idan na fita sai kawai ganin Yaya nayi ta shigo cikin ɗakin babu sallama tana banka min uwar harara, ban san garin ya aka yi na mance ban saka maƙulli ba don ni ƙudirin da nayi yau cikinsu babu me ganina.
Ƙirjina ya buga na sauke dogon numfashi, kafin tayi magana cikin sanyin jiki kuma a tsorace na ce,"ina kwana".
Ta zuba min ido wajen kallona ta ce,"da ban kwana ba za ki ganni ne tsaye gabanki, wato ke ba ki da mutunci ko, wuyanki har yay riƙar da gari zai waye ki ƙi sakkowa ki dafawa mahaifiyarmu abinci saboda ba ki da tarbiya ba ki san darajar iyaye ba, idan uwarki ce za ki hanata abinci ko da ita ta saka aka yi miki kishiyar?".
Kaina a ƙasa na ce,"don Allah kar ki ƙara sako mahaifiyata kiyi komai akaina ni ɗaya".
Ai kuwa ta fusata tayo kaina zata mareni na riƙe hannun da ƙarfin da ban san ina da shi ba, a hankali na sakko na tsaya gabanta ina kallon cikin idonta na ce,"Kin bani shekaru sama da sha biyar, a haife kuma kin haife ni, ba iya aurar da kamata kika yi ba har jikoki kina da. Bai kamata ace da girmanki kina dabi da ƴar cikinki ba kuma matar ƙanin ƙaninki, kamar hakan abun kunya ne, don haka na roƙe ki kija sauran guntun mutuncin da nake ganinki da shi kar kiyi saken da zan bi ta kai in taka na wuce, bana saurin rama abu ina da haƙurin shanyewa amma duk ranar da tura ta kai bango babu wanda zai ji daɗina, ba zan so in gwada miki a yanzu ba saboda darajar ƴarki da ke hannuna".
Kallona take yi cikin tsananin mamaki, sai kuma ta harzuƙa ta ƙwace hannunta da na ke riƙe da shi tana faɗin sai tayi min duka taga wanda ya tsaya min. Hargaginta ya janyo hankalin ƴan ƙasa sai ga su yuya guda kamar za'ai yaƙi. Suwaiba matar Yaya Babba ce ta riƙeta tana bata haƙuri, ita kuma cikin huci take faɗin,"barni Suwaiba in daki yarinyar nan ta gane Annabi ya faku, ƴar cikina tayi min rashin kunya in ƙyaleta, idan ban sa Yahya ya ɓaɓɓalata ba shegiya na ke sai dai muyi shari'a. Kamarta fa na shayar da wannan Nonon". Ta faɗa tana nuna nononta da kuma juyawa ta kalli Fati ta ce da ita,"ke sauka kira min su Mardiyya ni ba zan yi da ita ba sai dai Ƴaƴana".
Ko ɗar ban nuna mata tsoro ba, ina tsaye yanda na ke ƙam su ko sai faman haƙuri suke bata, ni dai abu ɗaya kawai na sani ba zan daku ba kuma ba zan yi duk abunda za'a saka ni ba sai idan naga dama. Nazifi ne ya shigo duk kuma sai suka ja da baya suna ba shi wuri, ya kalli Yayan yana ce mata,"me yake faruwa?".
Daga tambayar kuma sai ta kama balbale shi da masifa, ai ya barni duk na raina su bana ganinsu da ƙima, ƙarshema rashin mutuncin nawa har ya kai ga kan mahaifiyarsu, shi kuma da bai san darajar uwarsa ba ya bar matarsa na barinta da yunwa, to ko ya ɗau mataki ko kuma ita ta ɗauka da kanta. Shi kuwa cikin girmamawa ya shiga bata haƙuri kana ya juyo gareni nima yace na bata haƙurin, ba don raina ya so ba na ce tayi haƙuri kana suka fita a ɗakin su ka barmu.
Tun bayan fitarsu ban kalle shi ba na nemi wuri na zauna. Ina jin kallonsa a jikina wanda na ke hango fuskarsa ta cikin madubi na shaida tsananin ɓacin ransa. Can yay nisa ya ce da ni,"me ya hanaki yin girki?".
Kai tsaye na ce,"saboda bana jin yunwa".
"Idan ke ba kya ji sauran mutanen da ke cikin gidan fa?".
"Wanda nauyin dafa masa ke kaina ma ban dafa na ba shi ba".
"Kina nufin me kenan Sa'ida?".
"Ina nufin mijina ma ban dafa na ba shi ba balle wasu da hakkin ci da su ba a kaina ko na me gidan yake ba, wanda ya damu da yaci ai ya san hanyar kitchen".
"Har da mahaifiyata?".
Nayi shiru ban ce masa komai ba, ya ɗaga murya da ke shaida ɓacin ransa ya ce,"tambayarki na ke yi har da mahaifiyata ma sai dai ta shiga ta dafa da kanta?".
Shiru na yi na ƙi cewa komai. Yay ƙwafa yana jijjiga kai kafin ya ɗauko waya a aljihu, bayan wucewar sakannin da ba su wuce goma ba na ji yana faɗin,"Kiyi haƙuri Hajjo zan takura ki, kamar yanda na faɗa miki ne dai a ɗazu na kasa yin shiru kan abubuwan da Sa'ida ke min a gidana saboda bana so azo ga matakin da kowa ba zai ji daɗinsa ba, ta san me ya faru a baya to ina tausaya mata shiyasa ba zan mayar da ita gaban su Kaka ba don har yanzu ta kan hukuncin Abbaa da ya yanke mata na rashin zuwa gida, amma hakan bai sa ta gyara ɗin ba".
Ai yana cewa Hajjo na zuba masa ido, idan nasa mamaki a matsayin kallon da nake masa tabbas na yiwa kalmar rashin adalci.
"Tom shikenan gata". ya miƙo min wayar na karɓa ina kallon screen ɗin da ke ɗauke da sunan Yayar mahaifiyata Hajjo, ƙirjina ya buga na runtse ido nasa wayar a kunne, ina ga dai hankalinsa ba zai kwanta sai ya shiga tsakanina da kowa nawa tukunna, ita kuma ko me haɗa ya faɗa mata oho, kai Namiji Ƙayar ruwa baka san da ita ba sai ka taka, kamar yanda ban san da wannan ɓoyayyan halin na Nazifi ba sai a yanzu da duniya ke gara masa.
Hajjo ta katse Sallamata da ce min,"ke kuma mijinki yay ta kai ƙararki hakan kika zaɓarwa kanki ko Sa'ida?".
Na rumtse ido ina jin zuciyata na bala'in matsewa, muryana a hankali kuma a raunane na ce,"ba haka ba ne Hajjo kiyi min alfarmar tsayawa kiji ta bakina kar ki yanke irin hukuncin su Kaka...".
Murya ta ɗaga wajen dakatar da ni,"dalla can rufe min baki, wanne irin iskanci ne da rashin sanin darajar iyaye yasa za ki ƙi dafa abinci ki bawa uwar mijinki, dan ubanki da bata haiifa ba har kya ganshi ki so ki aure, wawiya kawai idan ba ki bi uwar miji ba ta ina za ki kama mijin naki a tafin hannu, ko haka kika ga matan yayyunki na wa mahaifiyarki, ba gida guda su ke ba amma kullum da kwanon abincinta a gidan matar Sa'id. Kishiya kuma akanki a ka soma? kaf cikin mu biyar da mahaifiyarmu ta haifa wa kike gani tana zaune ita ɗaya banda mahaifiyarki? Kuma ƴan uwanki Samira da Husna duk ba kishiyoyin ne da su ba, kin taɓa zuwa kinga wacca kishiyarta ta zauna akanta? Ko kin taɓa jin wata cikinsu mijinta ya kai ƙararta akan kishiya, sai ke saboda sakarci da shashanci za ki ɓata rawarki da tsalle, to ki shiga taitayinki wallahi, kar na ƙara jin makamanciyar magana irin haka ta kin hana uwar mijinki abinci, ita kam ko ce tayi ki kwanta tabi ta kanki ki kwanta biyayya dole, Saboda haka yanzu muna gama wayar da ke ki wuce ki girka abinci ki kai mata tare da bata haƙuri kina jina".
Na ɗaga kai kamar ina gabanta na ce,"zan bi umarninki in yi yacca kika ce in sha Allah".
Sai kuma ta kama yi min faɗa sosai akan rashin bashi hakkinsa da na ke, shi ko kunyar kai mata wannan ƙarar ma bai yi ba. Tana faɗan tana haɗawa da aya da hadisi har ta gama kana mu kai sallama da ita bayan ce min da tayi tana tafe nan da anjima zata zo in gwada mata kalar iskancin da nake yi tunda har an iya akai min akwatuna na watso su waje.
Na miƙa masa wayarsa suka ci gaba da magana da ita, ina ji tana ce masa,"kayi haƙuri Nazifi, na dai yi mata faɗa idan taji ta gyara shikenan, idan kuwa bata gyara ba kanta ta yiwa kuma ba kowa ta wulaƙanta ba sai iyayenta".
Yay mata godiya suka yi sallama, ya fita a ɗakin na raka shi da kallo, kafin na miƙe cikin karaya wasu zafafan hawaye na sauka akan kuncina yayinda a zuciyata na ke faɗin tsakanina da Nazifi sai Allah ya saka min.
Shayi na dafa na zuba a flask daidai cikin mutum guda, kana