Showing 66001 words to 69000 words out of 87761 words
na ɗora taliya fara dama akwai sauran miya. Don haka abincin da na haɗa na daidai cikin Iyam ne ita kaɗai, na ɗeba na kai mata ɗaki, basu ma san da shigowata ba saboda shewa da hayaniyar da suke yi, can na hango Iyam daga wajen wadrobe ɗinta ƴaƴan jikoki sun sakata gaba tana yi musu wasa, na wuce mutanen kan hanyar da babu wanda ya amsa sallamata a cikinsu, na durƙusa har ƙasa na bata haƙuri bata dai ce da ni komai ba na ta shi na fita bayan na aje mata abincin, ina jin Ummaa na faɗin Allah ya shiryeni yasa kishiya ta koya min hankali, a raina na ce ta dai koya muku.
Da rana ina zaune da waya a hannu, na kunna data na hau whatsapp, da ma ni shi kaɗai na ke dan shi kawai Nazifi ya yarje min in ke yi, babbar wayar ma da ƙaƙa ya bari na riƙe, Ina cikin kallon status na buɗe na Adamu ƙaninsa, nan take na yi karo da hoton da ya zamar min yajin albasa a ido. Hotuna da bidiyo na Nazifi da Amayarsa, irin hotunan nan da ake yi na kafin aure, kasa ɗauke ƙwayar idona nayi akai, kyan da suka yi ko hasidin iza hasadun, shi ya saka yadi me tsada ita kuma cikin wata doguwar riga ta net, kana ganinta ka ga jinin shuwa, hanci kaman tsinin biro ga ido da gashin ido masha'Allah, ba ƙarya tana da kyau iyakar kyau irin kyan da namiji ba zai gani ya ƙyale ba, wataƙila kuma wannan kyan shi ya ruɗe shi domin a rayuwarsa yana matuƙar son kyakykyawar mace. da gani ta girmeni kam zata iya ba ni shekaru uku, idonta kaɗai zai shaida maka a waye take kuma tasha boko kamar yanda ya faɗa, ban san lokacin da na jefar da wayata ba ganin yacca a bidiyon yake faman ruƙota zuwa jikinsa ita kuma har tana kwantar da kai a ƙirjinsa.
Kaina na jinginar jikin gado ina hawaye sosai. Tsawon wani lokaci wayata tayi ƙara na ɗauko, sabuwar lamba na gani a jiki, muryata na saita kana na ɗaga tare da yin sallama.
Daga can ɓangaren aka ce,"Ke Sauna ba hoton mijinki da wata na ke gani ba yana yawo a IG?". Muryar kawai ta shaida min wacece, kuma sosai nayi farin ciki da kiran nata, Safiyya ce ƙawata ta ƙud da ƙud tun aji ɗaya a makarantar boko, ita kaɗai ce wadda yau zan nuna in kirata da sunan ƙawa, ina sonta fiye da yanda take sona kamar yanda itama ke cewa tana sona fiye da yanda na ke sonta, rabona da ita kusan shekara uku da rabi kenan da Babansu Allah ya ɗaga shi gwamnati ta ba shi matsayi suka koma Abuja da zama.
"Hello Beb".
Na murmusa kuncina kaɗan murya a sanyaye na ce,"Na'am Beb".
Ta sauke numfashi da cewar,"ohh i thought i was mistaken in ce wa kuma zan ƙara nema ya ban numbernki...hey tukunna ma are you well naji muryanki somehow cool".
Na ce,"Safiyya natsu muyi waya da kyau mana har yanzu kina nan yanda kike, kuma ni ki min hausa zalla ki daina haɗa min da turancinki tunda kin zama baturiya".
Tayi dariya sosai kana tace,"To matar Ustaz ai ni ban iya larabci ba balle nayi miki. Beb ba fa ki da mutunci wallahi, kinga wahalan da na sha before i gat your number, i so much missed you almost four years. Bamu da zumunci gaba ɗayanmu mun zama wasu ƴan banza".
Na ce,"ai ni ina gwada lambarki bana samu".
"Eyyah that number ai ba yayi, tun da naje saudiya na jefar da layin shikenan nima sai na rasa na ki, ba yanda ban yi ba wajen in sameki na rasa, in ta shiga kafafen sadarwa ina searching sunanki bana gani, ke har yanzu kina nan da duhun kai".
Da murmushi nace,"Yanzu ai na kika samo lamban nawa?".
"Akwai wata something Tijjani oho that fat girl dai da ta nace miki na tsaneta, sai da na ɗauke numfashi aka rirriƙeni kana na iya kiranta fa na ce ta bani lambanki, itama numban nata wurin Uncle Maths na samu kin san Yayanta ne, Beb ina kishinki sosai".
"Hmm Allah ya shirya min ke. yanzu dai mu gaisa ina Baba da Mama?".
Cikin saurin maganar nan tata ta ce,"Ke Babanmu ma ya ƙaro walaƙanci ya danƙarowa Mama kishiya ai kuwa na kora kishiyar in faɗa miki, bari wannan labarin sai mun haɗu. Yanzu kina jina na shiga IG ne ina kallon page na arewaweddings i then came across a picture of someone who looks like your husband, har na wuce kamannin suka tsaya min a rai na ce sai na nemeki na ji. Mijinki ne ko Ya?".
Na ce,"a me kika gansa?".
"Umm like ango haka, wallah sak mijinki kin san Allah mai halitta sai ki ga me kama da ke ma. Amma dai wannan na san ba shi ba ne kama ne kawai may be kuma brother nasa ne ba?".
Na ce,"Shine Safiyya".
"Shi wa?".
"Mijin nawa mana".
Wani zabura tayi daga kan gadon da take kwance tare da faɗin,"A'uzubillahi". Sai kuma ta danno ashar ta ce,"kina nufin kishiya aka yi maki?". Na ce,"za dai ayi gobe in Allah ya kaimu". Yadda ta daki ƙirjinta da ƙarfi ina iya jiyo sautin dukan ta ce,"kuma sai kike mene ke yanzu?". Yanda tayi maganar kaɗai ya sakani sakin murmushin da ban shirya ba ina ƙara haskota da yanayin al'amuranta a cikin idona. "Beb na ce sai kike mene yanzu da za'ai miki kishiya?". Na ce,"sai na ke zaune mana gani muna waya da ke ina jin daɗi". Ashar ta ƙara lailayowa ta yarfa min. "Sa'ida Salman Madobi bura'ubanki na ce, za'ai maki kishiyan kike gaya min kina zaune miji da amayarsa na can hotuna na yawo a media ba ki tafi kin bankawa ƴan iska wuta sun babbake ba, kai Allah ya tsinewa sanyin halin da na sanki da shi. Kar dai ki ce min babu wani mataki da kika ɗauka kan lamarin, na wawoo i cant imagine wai Nazifi ne zai miki kishiya, hey duniya ba tabbas wai yau Nazifin Sa'i zai haɗata da wata, hewoo ni ko ina zan taɓa yarda da namiji".
Na ce,"Wai ba zamu gaisa ba ne Safiyya kina ta faman magana".
"Ba za'a gaisa ba ɗin, za ki hanani magana saboda na taɓa zuciyarki. Kin san yanda na kaɗu da lamarin kuwa? tukunna ma! kuɗi ku ka yi ne don naga ba shigar tsumma yay ba, kuma yay ƙiba ya murmure abunsa har da tumbi, if i guess right Nazifi Mai Kalwa yay kuɗi ya juya miki baya shine har zai ƙara aure. Ke kuma shashasha Sauna kina kallonsa you didnt take any worst action. Wait let me drink cold water becoz ina jin numfashina na seezing kar in faɗi in mutu lokacina bai yi ba".
Ina jiyo yanda take kwankwaɗar ruwa, bayan ta gama sha tace,"Na fi kowa saninki, ba ki komai ba akan lamarin auren nan, ba kuma za ki ba, kina nan kina kuka idan kika gama ki kama kiran sunan Hubbi. To Hubbi ya ci bantan bura'ubansa ɗan shegiya annamimi butulu mara halacci. Kinga kina jina ba, just give me your address ina lagos yanzu haka na zo wata seminar, zan yi hayar ƴan daba mu zo gobe, sai na sa an karairaya Nazifi Sa'ida kinji na faɗa miki, ita kuma shegiyar da ke ƙoƙarin shairing miji da mijin Ƙawata zan yanke mata nonuwa duka don uban babanta, lamarin Nazifi wasa ne. Kinga gida guda za ku zauna?".
Shiru ban ce da ita komai ba, gwara na barta ta gama zazzaga masifar sai muyi wayar arziƙi. jin shirun na wa kuma yasa ta cewa,"kai Allah ya kwashewa Nazifi albarka kasa ya ɗaiɗaice, ya rasa wadda zaiwa kishiya sai ke Sa'ida, Allah ya isana ban yafe masa ba wallahi, ina ma mota tabi ta kansa ya mutu dama ai ba son aurenku na ke ba".
Nasa hannu na goge hawayena, sai kuma kukan yaci ƙarfina na kasa riƙe shi. Nan hankalina Safiyya ya tashi ta sassauto ta shiga lallashina har sai da nayi shiru. Na bata labarin komai da ke faruwa, tayi shiru kiran yana ta tafiya sai da na kira sunanta kana ta ce,"na suma ne bari na farfaɗo tukunna, ai ban san abun yay tsamari haka ba, ke kuma duk kika manta kina da ni, ko da ya ke ba wani sona kike ba dama kin fi son wannan gantalallan mijin naki".
Nuna mata nayi bana son tana zagar min miji, hakan yasata cewa,"Am sorry Beb amma zan shigo kano just becoz of you indai ina da rai da lafiya. kin san ina jin magananki so nayi shiru da zage zagen, Nazifi ne yaje da halinsa amma wallahi ba zan fasa tsine masa ba kuma Allah yasa matan ta kwashe kuɗinsa duka ta gudu ta barsa da paralyzed, kuma ba zai taɓa haihuwa ba ko zai auro mata ɗari, ina ma abun nasa ya ruɓe in ga ta inda shi zai haihun".
Kai na girgiza kawai na ce,"kinga mayi wayar wani lokacin".
Na faɗa ina kashe kiran don ba zata daina wannan mugggan adu'an da maganganun nata ba, bata san zata iya faɗa a bakin mala'iku ƴan amin ba.
Da Yamma ina kwance ɗaki abun duniya ya ishe ni Hajjo ta zo ita da yaranta biyu Amina da na ke kira Mamana da kuma Muslimata. bayan mun gaisa na kawo musu abun sha tana kallona tace min,"Nazifi ya kira ni ya karanta min duk halin da ake ciki, faɗan da kika ji ina yi miki ɗazu nayi ne saboda fuskantar yana wajen. Mahaifiyarki ta faɗa min gaskiyar komai dan ko da muka yi waya da shi ba yarda da zancensa nayi ba, namiji me kai ƙara ba abin yarda ba ne. Daga can gidan naku na ke yanzu, itama mun yi magana ni duk sai yau na ke jin komai, tana ta faman nanata min kalmar haƙuri kin san hali, na ce mata ai shiyasa mata da yawa ake wayan gari zuciyarsu ta buga sun mutu saboda baƙin cikin ɗa namiji, to ƙilan kema so take ki mutu ina jin dai sun gaji da ke ne. anji haƙuri ba ya yawa kuma me haƙuri shi ke da riba amma irin haƙurin da ke kike yi ba komai ba ne sai cutarwa Sa'ida, kawai saboda kina da haƙuri sai aka ce kike ɗaukar kowanne cin kashi, bama na miji ba kawai har da ƙanne da Yayye, anji mahaifiyarsa idan ta miki anan ki kauda kai, amma banda ƴan uwansa saboda haka ki takawa kowa burki Sa'ida kina jina, ko matarsa ce ta shigo karki wani sakar mata fuska balle ta sami fakar rainaki har ta kai ga cin mutunci, ke mu'amala da ita ma ba dole ki barsu idan haɗe miki kai za su yi can su ƙarata, banda hauka ma duk sun zo sun tare miki a gida ita tana gani saboda uwar kawai ce bata san abunda ya kamata ba taƙi tsawatar musu. To ni dai na faɗa miki ki taka musu burki hatta shi kansa karma ya kawo matarsa ya dinƙa wulaƙantaki a gabanta, hanyar ma da kika ɗauka kici gaba da yin hakan ba zan ce miki ki daina ba, ta hakanne za ki mutunta kanki. Kuma daga yanzu duk wata matsala idan kina da ki tafi kanki tsaye wurin Yayan mahaifinki ki faɗa masa, ai ban taho ba sai da na jira ya dawo na sameshi na faɗa masa yace shi waccan shari'ar ma bai san da ita ba har kawo yanzu da na ke faɗa masa. Kuma Allah yasa Malam Mudassir(ƙanin Kaka) yanan da ike ya san daidai sai yay ta faɗa yana akan me yasa ita mace ba'a bata ikon da zata yi magana ko ta kare kanta kawai shikenan duk abinda miji ya faɗa kai za'a hau a zauna ga uban masu daidai da gaskiya yay magana, mace ta kawo kukanta gidansu da take tunanin samun sassauci sai a ƙi sauraronta balle tayi magana kawai a yanke hukunci, ba dole baƙin ciki yaywa mutum yawa ba, shiyasa ai ga matan nan duk ba'a rasa su da ciwon zuciya da hawan jini, sai ƴarka ta mutu bincike ya nuna ciwon da yay ajalinta a zo ana inama inama, me yasa da take raye baku bata izini da ikon da zata faɗi damuwarta ba, shikenan da yarinya tazo ku iyaye maza ku ƙi sauraronta ke kuma uwa bakki da aiki sai na tayi haƙuri kowacce mace haƙuri take yi, to don kowa na haƙuri shikenan sai aka ce matsalar wata bata fi ta wata ba, duk rashin bawa ƴaƴa ikon faɗar halin damuwar da suke ciki ke sawa zuciyoyinsu su buga".
Hajjo bata jima ba ta tafi bayan ban baki da ta babbani, ta kuma bani adu'oi da ɗora ni akan dabaru masu tsari. Tun bayan tafiyar Hajjo ban ƙunshe kaina a ɗaki ba, idan fita ta kama fita na ke nayi sabgogina na dawo, sai dai kaf cikin yara da manyan babu wanda ya ishe ni kallo banda Rumana da suka dawo a lalle take nuna min itama na ɗauke kai kawai nayi gaba tare da mata gargaɗin kar in ga ƙafarta a ɗakina.
Tashin hayaniya na jiyo kaman na faɗa hakan yasa na fita da sauri na leƙa tunda masu jeran kayan amarya sun zo suma, tunanina ko da su ta haɗosu sai dai ina leƙa kaina ƙasa na hango Yaya Babba wato Babban ɗan Iyam wanda Yaya take bi, Da yake shi ba nan garin yake ba can kaduna ya ke zaune yana kasuwancin gwanjo, kowacce ta natsu a falon hatta ita Yayan yana musu faɗa.
"Haka ake yi dama sai ka ce garin mahaukata, ku zo ku wani tare a gidan mutum, kuma don rashin hankali kun zo kuna ɗaga hankalin matar gidan, ai duk an faɗa min abubuwan da kuke aikatawa, hisabi ne dai yanzu tun a duniya Allah ke yi ba sai anje lahira ba da gaggawa Allah ke sakayya kar wacce ta fasa mugun halinta".
Ashe har da Nazifin shima yana wajen naji yana ce masa,"Kai kuma susun banza ai da iliminka, ina addini ya ce saboda ka aurota ka bar mahaifiyarka da ƴan uwanka su wulaƙantata? Ina ce addini ce yay ka tsareta ka tsare mata mutuncinta da kimarta, ko ita ɗin jaka ce ko daga sama ta faɗo ka tsinceta ka aura da zaka bar ƴan uwanka na cin zarafinta?...".
Iyam ta iso wajen tana cewa,"Sam sam sam ban yarda da hakan ba, babu ruwanka da shishshigi, idan matarka ka zo ɗauka to ɗaukarta ku tafi ba zaka saka yarana a gaba kana faman yi musu faɗa ba".
Tana yin shiru ya kaɗa kai yace,"tom shikenan". Ya juya ya ƙare musu kallo ya ce,"ku ci gaba da zama, wallahi duk wadda ta kwana a gidan nan sai dai gobe taje kwaso kayanta a gidan aurenta".
Ya kalli matarsa ya ce,"ke kuma tashi mu wuce". Yana faɗar haka ya fice fuuuu, ni dai nayi ta mamakin inda yaji labarin, amma nafi tunanin Lubabatu ce ta zayyana masa komai.
Da daddare har na fara bacci kiransa ya shigo wayata wai na zo na sameshi, har zan banza da shi kuma dai na fita. Ina sakkowa naji suna maganar a Abuja za'a ɗaura auren, wasu za su bi jirgi wasu a mota kuma duk shi ya ɗauki nauyi, raina na ce an gaida me kuɗin duniya, na kyaɓe ba ki na shige ɗakin nasa. Na sameshi yana faman shan ƙamshi ban wani bi ta kansa ba na haye gado na kwanta, sai can bacci ya fara ɗaukata naji yana lalubena, yanda ya nuna min yunwarsa dan dole na sallama masa yayi yanda ya so da ni. Bayan lafawar komai ni na fara wanka kafin shi, ni dai wannan daren shi yay bacci ni ina daga gefensa ina kallonsa, azababben kishinsa mai tsanani naji ya mamaye zuciyata, tunani da lissafi kawai na ke yi akan ta yanda abunda na mallaka tsawon shekaru takwas zai koma mallakinmu mu biyu, shikenan yanzu duk irin salon abubuwan da yake yi min a shimfiɗa itama sai yayi mata? Kuma yanzu yafi sonta akaina?
Na rumtse ido ina jin zuciyata na faɗa min dole in miƙe tsaye don ba zai yiwu na bar mata shi ba.
Da asuba bayan ya dawo daga masallaci ina ji ta kirasa a waya, ina ga da wata lambar ta kirasa don sai bayan ya ɗaga ne ya ke cewa,"wannan numbern fa ina na ki wayan?". da haka kuma ya tashi ya fice yayin da na ke jin zuciyata kamar zata yi bindiga.
Ya jima kafin ya dawo ciki, kuma sai lokacin ne ma yake kashe wayar don ina ji yana ce mata,"Kishiyar Iyam ce sai Yayyuna biyu da ƙanwar Malam. Sai dai mun ƙaraso ɗin nan da sha ɗaya jirgin namu zai ta so".
Idona ya cika da ruwan hawaye inda na ke kallon fuskarsa da ke bayyana annurinta. da ƙyar na mayar da hawayen idona da ke son zubowa, na rufe ƙur'anin da na ke karantawa na tashi tare da ninke sallayar duk na mayar da su ma'adanarsu. na zauna gefen gadon ina cewa da shi,"ina kwana".
"Lafiya lau". ya amsa a gajarce.
Tun daga haka ban ƙara magana ba, kuma kamar jira ake gari ya waye sai ga kira na ta shigowa wayarsa, ba ya numfasawar minti guda wani kiran zai ƙara shigowa, har sai da shima ya fara gajiya da hakan don dama tun daren jiyan na lura a gajiye ya ke sosai.
Fita nayi na bar masa ɗakin na kama hidimar gyaran gidana, sun yi kaca kaca da falon har ƙarni yake yi kuma an rasa me gyarawa duk uban ƴan matan cikinsu, gidan dai tsit ina ga sunji kashedin Yaya Babba sun kama gabansu, cikin ƙanƙanan lokaci na kimtsa falon na tashe shi da ƙamshi, kana na koma sama nayi wanka na shirya tsab abina na ci kwalliyata ina ta yin iya ƙoƙarina wajen basar da lamarin bikin nan, kuma Allah sai ya saka min natsuwa a zuciyata, duk da babu ƙunshi babu gyaran kai amma fess na fito nayi kyau da ni, ban baro ɗakina ba sai da na gyara shi na sanya karatun ƙur'ani.
Lokacin da na sakko ƙarfe takwas da rabi, na leƙa ɗakin