Showing 81001 words to 84000 words out of 87761 words
na firfitowa waje, tashin hankali na farat ɗaya na bijiro mata.
"Ranki ya daɗe mutum na buge...".
Bai ƙarasa maganar ba Mrs Jadda ta ƙwalla ƙara sakamakon tozalin da idanuwanta suka yi akan uban jinin da ya wanke rabin gilashin motar, bata san lokacin da ta fiddo da hannuwanta da ke ɓoye cikin mayafinta ba ta ɗora su aka tana biyo kalmar innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Tun driver bai ƙarasa bayaninsa ba ta buɗe murfin motar ta fita a sukwane, lokacin jama'a har sunyi cincirundo a wurin, cike da tsantsar tashin hankali ta raɓa ta tsakaninsu, ganin yarinya kwance cikin jini yasa ta ɗora hannu aka tana salati tare da zube gwiyoyinta a ƙasa.
"Wayyo Allah na, jama'a ku taimaka min mu shiga da ita cikin mota". maganar take cikin bala'in tashin hankali mara misaltuwa.
"Muntaƙa mu wuce asibiti". ta ƙara faɗa tana kamo yarinyar jikinta.
"You are under arrest". taji sautin muryar wani babban mutum a saman kanta, tana ɗaga ido taga ƴan sanda guda biyu suna ƙoƙarin sanyawa Driver ankwa. hankalinta ya kuma kaiwa ƙololuwar tashi, nan da nan ta shiga roƙonsu akan su yi haƙuri su bari tukunna a isa asibiti koma meke da akwai sai ayi. Kuma take anan hannu na rawa ta ɗauko waya ta kira mijinta ta sanar masa halin da ake ciki wanda ta mance da ya ba ya ƙasar ma, da kanta ta ɗauki Sa'ida da ke kwance cikin jini ta sanya a mota, har lokacin salati kawai take yi ganin kamar yarinyar ta rasa ranta, driver yaja motar a miliyan yayin da motar ƴan sanda ta mara musu baya.
Babu wanda ya lura da Safiyya da ke ta ruzgar kuka sai a yanzu, tsoro da fargaba da tashin hankalin da ya risketa yasa ta duƙe a wuri ɗaya ta ɓoye kanta a tsakanin cinyoyinta, jikinta gaba ɗaya rawa yake yi tana kiran sunan Sa'ida, ba ita kaɗai ba duk wani me zuciyar imani in yaga mummunan haɗarin sai hankalinsa ya nemi ya gushe. Wani dattijon mutum ya ƙaraso wajenta, yana taɓata ta ɗago a furgice, idanuwanta har sun yi luhu-luhu, bakinta na rawa tace masa,"Sa'ida tah kar ta mutu Baba don Allah kar ta tafi ta barni".
Sai kuma tayi shiru tana ƙara fashewa da sabon kuka. "Ya Allah? Ya Allah". iyakar abunda take faɗa kenan ta kasa yin aduar da take son yi.
"Kinga kwantar da hankalinki ina ne gidan ku?".
Sai ta miƙe a rikice tana girgiza kanta,"ba zani gida ba, ba zani ba hankalin Abbaa zai tashi Ummani zata yi kuka".
Kai da kaga yanda take maganar kasan ba'a hayyacinta take ba, tsohon ya riƙeta da kau aka tari me napep suka shiga don nufar gidansu ko na su Sa'ida
*YAKASAI B, LAYIN KWALE-KWALE.*
Ƙarfe takwas na dare a lokacin, unguwar ta ɗan yi tsit ba kamar da rana ba, gajiyayyen gida ne madaidaici daga ɓarin dama cikin tsakiyar gidaje biyar ɗin da ke jere, irin ginin gidan daga waje jar ƙasa ce sai ciki kuma aka yi ɗan gyare-gyare da bulo sai dai babu filasta, da zarar ka shigo dogon soron gidan guda biyu zaka ji warin daddawa na tashi, soron farkon duhu dunɗum baka iya ganin ko da yatsanka, a soro na biyu kuma zaka yi karo da manyan botikan da ake wanke kalwar yin daddawa, shima babu haske sai na farin wata da ya ratso ta ƙatuwar ɓular langa langar soron, duk da cewar dare ne a lokacin kuma babu hasken fitila amma kana iya ganin ƴan tsirarrun ƙudaje sun yi yaɗo a saman bokitan kalwar.
Daga cikin gidan kuwa tsakar gidan yay ƙal, ko'ina fes fes, duk kuwa da rabi da kwatan simin ƙasa ya farfashe. kai da ganin yanda komai yake a killace a tsabtace kasan ba gidan ƙazamai ba ne duk da cewar gidan talakawa ne sosai, ba zaka taɓa cewa gida ne da ya tara iyali da yawa ba saboda tsananin tsabtarsa, kuma da zarar ka zuƙi kyakykyawar iska zaka zuƙo ƙamshin turare ɗan tsinke sama-sama.
"Kambun-baka gaskiya ne domin yana faruwa kuma yana iya kai mutum ga mahallaka (mutuwa) saboda tsabar tasirinsa a jikin mutum, saboda haka ya zama wajibi mu nemi kariyar ALLAH Shi kaɗai, sai riƙo da hanyoyin samun waraka ko riga-kafi wadanda suka inganta a shari'ar Allah wajan kare kanmu da iyalanmu daga sharrin Kambun-baka da hassada. Kambun-baka ko Kambun-Ido, Nassi ya yi bayaninsa kamar yadda itama Hassada akayi bayaninta, kuma duk an bayyana mana irin illar da Kambun-baka yake yi ga lafiyar mutane domin yana iya hallakar da mutum ko kaga mutum yayita fama da rashin lafiya mai tsanani. Addini ya koyar da mu hanyoyin da za mu nemi ALLAH ya kare mu daga sharrin dukkanninsu da ma masu yin su gaba ɗaya, mu nemarwa kanmu, iyalanmu, dukiyarmu da duk wata ni'imar da mu kasan muna da ita kariya da tsarin ALLAH Ubangijin kowa da komai kuma mai iko akan kowa. yana da kyau muyi Riga-kafi akan kambun baka, wato (neman kariyar Allah kafin abin ya faru da mutum har yayi tasiri akansa), da kuma yin maganin da bai saɓawa Shari'ar Allah ba idan abin ya faru har yayi tasiri akan mutum. saboda haka mu yawaita karanta Ayatul Kursiyyu da Surorin Falaqi da Nasi musmaman a lokacin da za mu kwanta bacci saboda neman Allah ya kare mu daga sharrin Kambun-baka da na hassada, saboda tasirin sharrinsu a jikkunan mutane ya zarce wanda shafar jinnu ke haddasarwa, ga naci da ƙalata wajen son dauwama a jikin mutum da sanya cututtuka iri-iri, ubangiji ya kare mu da kariyarsa".
Maganar da ke fitowa kenan daga cikin ɗaya daga ƙananun ɗakuna biyar ɗin gidan, Kowa a cikin ɗakin zaune yake bisa ƙatuwar tabarmar da ke malale a tsakar ɗakin, kamar dai yanda suka saba kullum a gidan duk bayan sallar isha'i, sun kasa kunnuwa cikin natsuwa suna sauraron karatun da mahaifin su Malam ke musu.
Ummaa kishingiɗe a kusa da Malam, sai Iyam kwance gefen Malam ɓangaren damansa Gwaggoje mahaifiyarta na yi mata firfita, Amarya daga bakin ƙofa riƙe da tourchlight mara haske dalilin sanyin batir, sai yaran su a kusa da juna rabin hankalin su akan Malam sauran rabin akan Iyam da bata da lafiya tana fama da ciwon ƙafa da ko takawa bata yi, yayin da duk wani rai zuciyarsa kema Iyam adu'ar samun lafiya domin kusan ita ce garkuwar iyalan Malam Bala Mai Kalwa.
Jummai(Iyam) ita ce matar Malam ta farko wadda aka yi aure tun ƙuruciya, tana da bala'in kishin mijinta ga fafutukar sana'a don kusan ita ce jigon kasuwancin kalwar da Malam ke yi a ƙauyuka da birni, ita ce take dafawa tayi aikinta tas shi kuma ya fita da ita kasuwa a siyar. Ƴaƴanta goma banda waɗanda su ka rasu, Hashimu(Yaya Babba) Maijidda(Yaya), Najibu, Aisha(Anti), Rabilu(Yayan Shago), Nazifi(Yaya Ƙarami), Adamu, Lubabatu, Basira, sai auta Fati.
Asiya(Ummaa) ita ce ta biyu yaranta bakwai; Basiru, Sadiya, Zubaida, Habiba, Musa, Jabiru sai Garzali.
Fauziyya(Amarya) ita ce ta uku yaranta biyar; Radiya, Musbahu, Naziru, Sumayya, Sharifa.
"Salamu Alaikum". sallamar da akayi daga tsakar gida taja hankalin su, Amarya ta ɗaga labule ta leƙa bayan ta amsa sallamar.
"Nazifi". ta kira yi sunan nasa idonta a kansa.
"Na'am, ya naji ku a ɗaki kuma".
"ummm yau bamu zauna a tsakar gidan ba saboda sauro".
"kuma kinga na sha'afa ban taho da magani ba". yay maganar a sa'ilin da yake ɗiban ruwa a buta yana kaɓe sumar kansa da ƙasan wandonsa.
Ta sake cewa,"Ka kira wani a cikin su ya taho da shi, a haɗo da battery wannan yayi sanyi neman mutuwa ma yake gaba ɗaya".
"Ai na ma siyo sabuwar tocilayit ɗazu ta caji, na barta ne a gidan su Muntari anjima zan karɓo".
"Ciniki aka yi ne naji fa ana ta cajin da tsada".
"Wallahi yau kasuwar rake kam Alhamdulillah anyi ciniki dan duka wanda na fita da shi sai da ya ƙare, shine ina tahowa naga fitar na siya dubu ɗaya amma ƴar ƙarama ce".
"To masha'Allah, Allah ƙaro kasuwa me albarka, an gode".
Ya amsa da amin sannan ya bankaɗa labulen ɗakin ya shiga, ya nemi gefe ɗaya ya zauna yana gaishe da mahaifinsa tare da Gwaggoje da Ummaa, sannan yabi mahaifiyarsa da ido itama yana yi mata sannu da jiki, duk sai sanya masa albarka suke yi shi kuma yana amsawa cike da jin daɗi da farin cikin alfaharin da ahalinsa suke da shi. Kamar ba shine na ɗazu da yake tura baron rake cikin wasu jemammun kaya ba, yanzu yayi wanka ya sauya kaya zuwa blue jeans and white shirt me dogon hannu, ba sabbi ba ne kuma ba masu tsada ba ne amma yay masifar kyau sai zuba ƙamshi yake yi, lallai duk ranar da kuɗi suka zauna a jikinsa ba ƙaramin shege za'ai ba wajen kyau da iya ɗaukar wanka.
"Yaya Ƙarami zance kaje ne?". Zubaida tayi tambayar da tsokana. ya ɗago yay mata wani kallo ba tare da ya ce mata komai ba, fuskar nan tasa da bata rabo da murmushi na ta ƙyalli. Basira ta amshe da cewa,"ehh fa Yaya Ƙarami ka daɗe baka yi kyau ba irin na yau, ko dai ko dai".
Maficin da ke kusa da shi ya ɗauka ya jefa musu yana faɗin su kiyaye shi. kallon da mahaifinsa ke yi masa yasa shi miƙewa cike da kunya yana cewa da Amarya,"Abincina fa?".
"Ka duba kicin yana nan a wannan koriyar robar, ka ɗiba naka ka barwa sauran".
Bai fita a ɗakin ba ya zaro ɗari biyar a aljihunsa ya miƙawa Malam, mahaifin nasa bai karɓa ba ya girgiza masa kai alamar A'a, har ranso bai so ba, sam baya jin daɗin su bawa mahaifin su kuɗi yaƙi karɓa haka su ke fama ko da yaushe, ya ce shi ɗauke masa nauyin ci da gidan ma da suka yi kaɗai ya ishe shi, ban da ƙananun hidindimu da duk su ne suke yi. Manya samarin dama su huɗu ne, dukkansu bige bige suke yi babu me ƙwaƙwarar sana'a, amma a hakan su ke ƙoƙarin ganin su ciyar da gidansu da ɗaukewa mahaifinsu duk ɗawainiyar da ke kansa, kullum cikin ce masa suke ya huta ya daina fita Allah ya basa su za su masa amma yaƙi. shi yasa adu'ar Nazifi ta kullum Allah ya buɗa masa Malam ya huta yaji daɗi, sai dai a yanda ya ke ganin rayuwarsu abin da kamar wuya, duk da komai yin Allah ne, bai san abin da Allah ya aje musu ba anan gaba.
Ummaa ya miƙawa kuɗin ta karɓa tana faɗin Allah yay albarka. Ya fita a ɗakin ya shiga kicin ya buɗe koriyar roba babba wadda akayi kwaɗon kwaki ya ɗibi nasa sannan ya fice zuwa waje don su ci shi da abokinsa.
Yanayin yacca garin yake a lullume, sanyi na kaɗawa ta ko'ina yayinda iska ke busawa sosai, sai ya zamana yanayin ya zamto gwanin ban sha'awa a wurin duk wani rai mai motsi. cikin ƙanƙanin lokaci hadari ya haɗu yay gangami a gabas, garin yay baƙiƙƙirin sosai, sai walƙiya da ke haskawa, alamu na nuna daga kowanne irin lokaci ruwan sama zai iya sakkowa. dalilin hakan yasa kowacce halitta da ke waje ta shiga neman mafaka, yara na shigewa gidajensu da gudu, ƴan tebura na kasuwa na rurrufe kayansu wasu kuma na sakar musu lema, matafiya kan hanya kuwa duk hankali yayi gida saboda idan ruwan ya sauka Allah kaɗai yasan lokacin tsayawarsa, a wannan lokacin kuwa fargaba ta cika zuciyoyin talakawa bayin Allah, dalilin irin yanda suke jiyo gangamin hadari na ƙara haɗuwa yana buga tsawa wacca suke jin tamkar zata rusa ginin gidan na su ya zube, domin a irin ƙarfin iskar ruwa kanyi gyara sosai a gidajen ƙasa, zaka samu da yawa gidaje sun rufta har yay sanadin rayukan mutane da dama.
Yayyafin da aka fara, da kuma tashin iska da ke yin kaman zata ɗauke abubuwa, shi ya bawa masu mota damar ƙara gudun motocinsu, da yawa na zuge gilasan motar, waɗanda ke da matsalar ido kuma na neman wuri suyi fakin kasantuwar basa iya gani da kyau a cikin duhun hadarin. a daidai wannan lokacin ne wata arniyar mota ƴar ubanta baƙa ƙirar Lexus RZ da ke tafiya akan titin dawowa daga filin jirgin Aminu Kano, matuƙin cikinta ya gangara motar zuwa gefe ya faka, motar sabuwa ce karr ko ledar jikinta ba'a gama ɓarewa ba, sai uban ƙyalli take me ɗaukar hankali, ƙamshin da ke tashi a cikinta kana jiyo shi har waje, sai sautin waƙar Ve Maahi by Arjjit Singh ita ma da ke tashi cikin natsuwa. saurayin da ke tuƙin motar me kimanin shekaru ashirin da uku ya waiga kansa ga kujerar kusa da shi yana sauke idonsa kan Yayansa, wanda ya kai dogon hannunsa mai ɗauke da zarazaran yatsu ya ƙaro bolum na waƙar, idanunsa a lumshe ya kwantar da kansa a jikin kujera, wucewar minti ɗaya, biyu, uku, huɗu sannan ya buɗe su, a lokacin ƙwayar idonsa ta sauka akan yayyafin da ya ɗisa ɗis ɗis akan gilashin motar, cikin hukuncin ubangiji duk wannan hadarin da aka haɗa da tsawar da aka dinƙa bugawa ana zaton ruwa zai sauka tamkar da baƙin ƙwarya, sai ga shi cikin mintunan da ba su haura biyar ba anyi yayyafi an ɗauke, sararin samaniya har ya fara washewa, al'amarin ubangiji yafi gaban mamaki.
Dogon numfashi yaja ya sauke tare da ware idanuwansa akan titi yana bin tarin motoci da ke wucewa da kallo, kafin daga bisani ya ɗauke ƙwayar idonsa akai ya ɗauko wayarsa, wayar da kana gani ka san ba ƙaramin kuɗi aka zuba wajen siyanta ba, kuɗin da idan suka je hannun talaka tsab zai mallaki muhalli daidai zama da iyali. zamansa ya gyara a mazauninsa kuma daidai da gama laluben lambar da yake nema zai kira, ya danna kira ya tafi, kiran da ba'a ɗaga a farko ba sai ana biyu shi ma sai da ya kusa tsinkewa tukunna.
Daga can ɓangaren da aka ɗaga wayar murya mace mai zaƙi ta fito da faɗin,"Hello Bhai".
Ta san hali, ta san waye shi, ta san jini, shi ba ɗan sarki ba kuma ba jinin sarauta ba, amma yanda yake ji da girman izza da ƙasaita da uban miskilanci ko sarki da kansa albarka. a yanzu dai shi ya kirata, amma idan zata yi magana sama da sau dubu hamsin ba zai amsa ba tun da har ta san musababbin kiran nasa, in ace ma bata sani ba ne to zai iya ƙarfin hali ya ɗauki minti goma kafin ya faɗa mata abin da yasa ya kirata ɗin. Don haka daga can in da take tayi guntun tsaki a hankali gudun kar ya jiyota ta jazawa kanta masifa da bala'in duniya. kuma ita ma sai da ta ɗan ja lokaci sannan tace da shi,"Nan da ƙarfe bakwai suka ce".
Tun da ta faɗi hakan kuma tayi shiru, ta san dai abin da ya kira yaji kenan, ta kuma faɗa masa yaji, amma yanzu idan tayi gangancin kashe masa waya alhalin ba shi ya bata izini ba, to duk duniya babu wanda ba zai ji su ba a yau, gobe da jibi, shi ɗin kuma ba kashewar zai yi ba haka zai bar kuɗi suyi ta tafiya a iska sai lokacin da yaga dama. Sai dai a jiya tayi matuƙar mamakinsa lokacin da aka sanar da shi hatsarin da mahaifiyarsu tayi. Tana tuna lokacin tsaye take a bakin ward, duk jikinta kyarma yake yi, hannunta da ke riƙe da waya a kunne karkarwa kawai ya ke yana neman jefar da wayar a ƙasa, da ƙyar ta tattaro courage ta maƙale a jikin bango ta tsayar da ƙwayar idonta a ƙofar emergency room sannan ta sami damar mayar da martanin maganar da yay mata a cikin wayar.
"B bata daina ba, tun ɗazu na ke ta lallashinta taƙi yin shiru, ta ce ita ku zo kai da Daadee, Bhai kuma yarinyar kamar fa ta mutu".
Furucin na ta yasa shi rufe ido yaja numfashi sannan ya zuƙi iska a baki ya fesar, sai da ya murza goshinsa kafin ya iya buɗar baki yace da ita. "ki bata wayar, ki saka mata a kunne".
Karo na farko da taji yay magana kai tsaye ba tare da ɗaukan lokaci ba kuma very calm not rudely, haka kuma saɓanin kiran farko da yay ta aikin doka mata uwar tsawa duk ya rikitata. Sai da ta sauke numfashi tukunna ta taka tana tafiya da sassarfa saboda azalzalar da yake yi mata akan tayi da sauri. tana isa ƙofar room ɗin ta ɗorawa mahaifiyar tasu waya a kunne ba tare da ta sanar mata ba. Kuma shashsheƙar kukan mahaifiyar tasa ya tafi ta cikin kunnensa yay mugun duka a ƙirjinsa. "Maamee!". ya kira sunan da wani amon sauti da yake na sa shi ɗaya. "Mun gama waya da ke lafiya but yanzu kina ta kuka for morethan 4hours, don girman Allah ki yi shiru tunda likitocin sun tabbatar da cewa yarinyar tana raye, Maamee duk kin bi kin ɗaga hankalinki kamar ni za ki rasa, tun da ance tana raye mene...".
Tayi saurin tarar numfashinsa da cewa,"Ta ya zan gasgata hakan bayan har yanzu ban ganta ido da ido ba Bhai, rai fa! rai fa!...".
Kuma a wannan lokacin ta tabbata abin da yasa shi kashe wayar kukan mahaifiyar tasu ne da ba zai juri jinsa ba, kuma tun sannan bai ƙara kira ba sai yau da Ahlan yaje ɗaukosa.
Wayar na shimfiɗe a saman cinyarsa ne, yayin da ƙwayar idonsa ke manne akan adadin mintocin da ke tafiya a cikin wayar, lissafi yake yi, lissafin lokacin da ta sanar masa, ta cikin earpod ɗin da ke maƙale a kunnensa kuma yana jiyo masa irin yacca ƙanwar tasa ke faman ƙunƙuni tun bayan maganar da ta faɗa masa, wanda hakan yasa shi gyaɗa kansa yana janyo leɓensa na ƙasa ya cija, wucewar minti ɗaya, biyu har zuwa bakwai sannan ya kai hannu ya kashe wayar tare da jefata saman cinyar ƙanin nasa. A aljihun gaban rigarsa ya zaro kwalin cingom na orbit ya ɗauka yasa a baki ya fara tauna. Ƙanin nasa ya dube shi ya ce,"B mu tafi?". Kansa kawai ya ɗaga masa sannan Ahlan ya tashi motar yana tuƙi kaman zai tashi sama saboda gudu.
*No. 10, Alu Avenue, Nasarawa GRA Kano, Amb Jadda Residence.*
Me gadin da ke zaune daga cikin tamfatsetsen gidan na alfarma ya taso da