Showing 33001 words to 36000 words out of 87761 words
dalili ba".
na ɗago kai a jikinta ina zaro ido waje in ce,"shekara! tabɗijam, sai ka ce waɗanda aka kai kurkuku, duk haƙurina ba zan iya ba kam sai dai in haƙura da auren".
harara ta watsa min tana dungure min kai ta ce,"ke dai anyi autar gaske, Sa'ida aure sunnah ina ke ina cewa za ki haƙura da shi. hakan ma ki gode Allah mijinki ba mai tsananin kulle ba ne".
"Allah Ummani ko a haka ina jin rashin daɗi, shi ma ai kusan tsananin gare shi akan fita".
"eyy fa to ba laifi kam Nazifi shima ba ya son fita amma ai ba kamar wanda za ki ga sun wuce wata uku biyar babu in da suka leƙa, kuma ke fa duk wata hidima idan ta tashi ya barki kije. kuma ni fa daɗin hakan naji bacin haka Sa'ida in aka biye miki ai rana ɗai ɗai ne ba zaki zo gidan nan ba".
lafewa na ƙara yi a jikinta ina murmushi, ina jin tsantsar farin ciki da jin daɗin kasancewa da ita na ratsa zuciyata. idona a lumshe naji tana cewa,"mage sarkin son jiki sai ki tashi ai kije ki gaida mutanan gidan".
na zame a jikin nata ina cewa,"wai ina su Yasmin da aka barki ke ɗaya?". na faɗa ina ƙoƙarin karɓawar wuƙar hannunta ita kuma tana cewa,"waɗannan yaran yanzu ai sai Annabin yabo, kan in ƙyalla ido sai dai kiga na neme su na rasa. yanzu fa zancen da na ke miki ban san da fitar su ba kuma da suna zaune nan Walida na kafa min sharaɗan kar in musu miya me yaji".
nayi dariya ina cewa,"sai na fara make Walida in bata yi wasa ba, wato tsabar ta kai Babata ma take kafawa sharaɗi, lallai samun wurin zama, to kuwa rabon in kwasheta in mayar da ita wurin uwatta ne".
Ummani tayi dariya sosai ta ce,"ke da ubanta ai kun fi kusa. ni dai ƙyale ni da tayin aikin kije ki gaida mutan gidan tukunna". sai kuma ta ƙara cewa,"a'a sai yanzu ma abin yazo kaina, ina ƴaƴan na ki ba ku taho tare ba?".
allon ƙirjina naji ya girgiza, na tuna da yaran da nake jinsu yanzu har raina, na ce,"kin san da makaranta, musamman tasu da ba'a fashi, shiyasa na kai su wajen Iyam, amma suna ta rigimar za su biyoni su zo wurinki na ce su bari sai anyi hutu sa zo suyi kwanaki ma".
tana murmushi da ya nuna jin daɗin furucin nawa ta ce,"Allah sarki yaran albarka, wallahi Sa'ida sosai na ji daɗin kyautar nan da aka maki. zan samu lokaci in je har gida in yiwa Iyam ɗin godiya".
na yunƙura zan miƙe ta ce,"ke dakata me na ke gani a fuskarki haka? Na ganta a kumbure".
Gabana ya faɗi amma haka na ƙaƙalo guntuwar dariya na ce,"sharrin mura ne...shekaranjiya ta saka min azababben ciwon kai, muka je asibiti suka bani wani magani, shi ne ni kuma saboda tayi saurin tafiya na sha overdose ya juyar min da kai na koma kamar wata ƴar maye, garin sakkowa a bene layi ya ɗebe ni na ƙuma fuska a hannun bene".
ta kalle ni da kyau tana girgiza kai ta ce,"ke kam naga ranar da za kiyi hankali, ina ke ina shan maganin mura har over, ko da ya ke da aka samu ɗin ma kika sha".
fuskata ta ƙara washewa da gajeriyar dariya na ce,"Ai fa shima haka yayta faɗa".
"ai dole yayi miki faɗa, da kin gangaro daga saman fa?".
na datse maganar da cewa,"Allah ya taƙaita ai, Ummani ni fa yunwa na ke ji mura bata barni na ci komai ba yau, zumuɗin zuwa nan ne ma yasa na kasa tsayawa girki".
"naga alama ɗaukin zuwa ƙauye yay miki yawa. je ku gaisa ɗin kafin ki dawo miyar ta kammala, nima sauri na ke tayi kar uwar tawa ta dawo ta cinye ni ɗanya da mitar Kakanta yayi cefane da wuri ni kuma naƙi gama musu abinci".
ta faɗa tana tashi ta shiga madafa. dariya ta ban sosai da ta ce uwarta, Walida ce ƴar gidan Yaya Imam, ƴar nan ba dai tsufanta ba kamar aljana, tun da aka kawota Yaye shikenan ta zama ƴar gidan, tsakaninta da gidansu ziyara, har faɗa ma take ita fa Ummani ce Babarta ba Momi ba, ita da Daddynta Babansu ɗaya, duka Abba ne ya haife su.
Gidanmu ba wani babba ba ne sosai, tsaka tsakiya ya ke, sai dai bai saka yawan mutanen da suke rayuwa cikinsa ba sun takura, dan zaka samu kowanne ɓangare akwai ɗakunan yara har biyu bayan na iyayensu, asalinsa ginin ƙasa ne daga baya aka sabunta shi da na bulo a hankali a hankali. gidan gado ne da iyayenmu su ka gada a wajen mahaifiyarsu, don haka ahalin mutum uku ne a gidan da su ka fito ciki ɗaya, tun bayan rasuwarta da aka raba musu gado sai suka yanke shawarar zama wuri ɗaya don babban burin mahaifiyar tasu kenan, mahaifinsu na raye shi kuma tun da ya samu karayar arziƙi har ta kai ga ya sayar da duk kadarorinsa hatta kuwa da gidansa da suke zaune saboda biyan basukan da ke kansa, shi ne ita Hajiya Umman tasa yaranta su ka gyara nan gidan nata da itama gadarsa tayi suka koma da rayuwa cikin rufin asirin ubangiji, dama ita ɗaya ce matarsa har ta mutu, don itama bata rasu ba sai da ta tsufa sosai.
ɓangarenmu ne a farkon shigowa gidan, idan ka shiga daga ciki ta tsakiya kuma ɓangaren Baba Tijjani da nasa iyalan, shi ne mai mata biyu da tarin ƴaƴa goma sha biyar. sai daga gefen hagu na ɓangaren nasa nan Baba Sabi'u ya ke, shima matansa uku amma sun rabu da ɗaya, ƴaƴansa takwas duk mata ne Allah ya ba shi. zaman gidan namu dai kadaran kadahan ne, waɗanda ba su son zaman lafiya Mamu da ƴaƴanta, ita ce fitinanniya a cikin matan iyayen namu, duk wani rikici da zai ɓarke a cikin gidan to zaka samu daga gareta ko ƴaƴanta ya soma, kuma da Allah ya tashi sai ya bata kishiya daidai da ita. Mamu da ƴaƴanta akwai baƙin cikin bala'i, ita babban tashin hankalinta taga cikin ƴaƴan gidan wani yafi nata, haka ta tsani taga facalolinta sun fita da wani abun, ko fita za su yi tare taga shigarsubtafi tata to tabbas ta haƙura, ƙiri ƙiri ta ke nuna hassadarta bata iya ɓoyewa, kuma ko da yaushe ita ɗin dai ita ce koma baya, shiyasa bama wani girmamata a dalilin abin da takewa iyayenmu da kuma raba tsakaninmu da ƴaƴanta da tayi.
mahaifiyata tana da haƙuri da kawaici, kuma tana cikin irin mutanen da ba su fiya son shiga hulɗar kowa ba, barsu da halinsu su kaɗai sai na jikinsu, bata ƙi ka mata abu ba taƙi ɗaga kai ta kalleka, Ummani ta ƙware a bawa iska a jiyar mutum. amma fa idan aka taɓa mata ƴaƴa to anan ake ƙure haƙurinta, anan ake gane bata da kyau ko kaɗan, sam sam bata kawaici ta wannan ɓangaren, bata iya bari ƴaƴanta su halaka saboda haƙurinta, haƙurinta ba yasa ta bari a shiga hakkin ƴaƴanta.
dalilin da yasa Mamu ta shafa min lafiya kenan a yaran gidan, ko sharrinta ne ya tashi bata cika haɗawa da ni ba kam, don ta san bakin Ummani ba zai mutu ba akan haka, a cikin ruwan sanyi zata yaɓa mata maganar da zata hanata bacci. Ummansu Hindatu ce lakwaf lakwaf, shiyasa Mamun ke mata yanda ta so ita da ƴaƴanta duk da ba miji guda su ka haɗa ba, sau tari sai kishiyarta ce ke shigar mata idan tayi mata abu, ita Ummani babu ruwanta haka take cewa kowa tashi ta fishshe shi.
tun bayan da Yashaik yay aure aka bige ɗakinsa aka ƙara girman kitchen ɗinmu da tsakargida, sai duk tsakar gidanmu yafi na sauran girma, ga shi Yaya Imam da Yashaik suka haɗa kuɗi aka zuba mana fasashshen tayels, shikenan tun daga wannan gyaran fa Mamu ta ɗaura gaba da Ummani da ƴaƴanta, tsakaninta da mu harara da gyatsine, amma a hakan duk san da na zo Ummani sai ta tura ni ta ce inje in gaisheta duk da ta san ba zan samu tarbar arziƙi ba.
Ɓangaren Baba Tijjani na fara shiga, shi ne wanda Abbaana ke binsa. ina ta sallama daga tsakar gida babu wanda ya amsa min ga shi ina jiyo hirarsu a falon na su, sai da na ɗaga labule na leƙa falon tukunna. cikin yaran ba wanda yay min kallon arziƙi kamar yanda mahaifiyar tasu tayi min, don haka a tsaitsaye na gaisheta na fito na wuce ɓangaren Babanmu, shi kuma shi ne yake bin Abbaana Baba Sabi'u kenan, ƴaƴansa ke ce masa Babanmu duk sai muka ɗauka, na same shi yana nan muka gaggaisa har yana tambayar zuwan nawa na lafiya da rana tsaka haka, na ke shaida masa zancen zuwa ƙauye amma duk da haka sai ya kama min faɗa me yasa ban bari sai gobe da safe na taho ba, hakan ai rashin hankali da tunani ne, saura kuma idan an tafi bikin inga wajen zama in mance matar aure na ke.
mu ka fito tare da Hindatu tana min dariya, wacca na haɗe fuska tun ganinta ina aika mata harara saboda fushin da na ke yi da ita akan rashin zuwa gidana, zan iya cewa sau ɗaya taje sabon gidan nan namu, tsohon kuwa tsab zan ƙirga zuwanta shima. ko da yake mu haka iyayenmu suke, sai ka ce zaka je gidan ɗan uwanka a tsareka da tambayar me zaka je yi.
dawowata na iske Ummani har ta kammala girki, ta zuban abincin ta aje. sannu da aiki na mata sannan mu ka zauna ni da Hindatu, wacca ke faman tsokanar bai kamata a bani abinci ba ta san sai da na gama cin me maiƙo na taho. ban tanka mata na shiga cin abincina, loma biyar nayi naji abincin ya fita a kaina gaba ɗaya, ajiyar zuciya nayi yayin da zuciyata ke min ƙuna tunawa da abinda Nazifi yay min, nayi saurin mayar da ƙwallar da ta cika idona ina saurin miƙewa na je ga fanfo zan face majina.
Ummani ta bini da ido kafin ta ce,"kin ƙoshi ko me?".
"Ummani wannan murar ban san ya zan mata ba wllahi, ina son cin abinci amma sai in kasa ci".
"to Allah ya ba ki lafiya, ai da sauƙi ma tun da kina iya ci ko babu yawa".
sai sannan na ke tambayarta Kaka saboda na leƙa ɗakinsa ban gansa ba. ta shaida min Yaya Kamal da Yaya Al'ameen sun je kaishi wurin magani in da ake masa gashin ƙafa.
jakunkunan kayana na kwashe na shiga da su cikin ɗan ƙaramin ɗakina, na bar guda ɗaya wadda na ajeta nan kan tabarmar da muke zaune ina cewa,"ga kaya nan Ummani za'a kai ƙauye".
Ummani ta jawo jakar tana duba kayan tace,"kai kai ai ko kin gwangwaje su, wannan kaya masu kyau haka, ai fa bari na ɗebewa amarya ma su kyan".
ta faɗa tana ɗaga wata abaya, ai ko Hindatu tayi saurin cafewa da magiya. "Ummani don Allah ki bar min wannan don Allah Ummani".
Ummani ta saki baki tana kallonta. "ke Hindatu me za ki da wannan rigar? duk uban kayan da kike da su saboda dai rashin godiyar me sama".
ta langaɓar da kai tana ci gaba da roƙon Ummani har sai da ta haƙura ta bar mata, kuma Ummani na tashi zuwa ta kai kayan abinci ɗakin Abbaa tayi sauri ta wawuri wasu kayan ta arce tana ce min ai batta ƙara fitowa sai gobe kuma. zaman da nayi ni ɗaya sabon zafin baƙin cikin gidan aurena ya shiga huda ƙirjina, sai dai haka nayi ta kokawa da kaina don ganin na dakatar da fallasa yanayin halin da na ke ciki akan fuskata, yanda na zo gida sam bana son abin da zai sa in ke tunawa da gidan Nazifi, a yau sunansa ma ciwo ya ke min mai raɗaɗi.
Ummani na can ɗaki tana kimtsawa, na miƙe na shiga ɗakina na hau gyaransa, bayan na gama na shiga ɗakin Ya Al'ameen na kunna tv, har akai magriba ina ɗakin ina kallo ni da su Yasmin da suka dawo daga yawonsu, kallon ma duk sun hanani da surutunsu, kowacce sai aikin tambaya da ita zan koma gidana? yaushe Yaya Ƙarami zai zo ya basu alawa?
sai bayan sallar isha'i Abbaa ya dawo, a tsakar gida ya samemu muna ta hirarmu, yaran ma har sun yi bacci sai ni da Ummani da Sauda ƙanwar Hindatu da ta shigo wajenmu. cikin tsoro da fargaba na gaishe shi, kuma bai amsa min ba sai ya dubi Ummani ya ce,"lafiya dai?".
ta ce da shi,"tayi maka bayani da kanta mana".
ai lokaci guda Abbaa ya juyo kaina ya hauni da faɗa sosai akan ya hana ni zuwa gida in kai dare irin haka, kuma tun yaushe ya haramta min zuwa kwanan gida idan ba da babban uzuri ba. sai da ya gama faɗan tukunna Ummani ta ce masa ai tafiya Nazifi zai yi shiyasa ya ce in taho ɗin kawai, nan ma dai ba'a tsira ba wani faɗan na daban na sha kamar zai duke ni. ni dai a raina ce na ke kai da gidanku wai ba zaka zo ka sarara ba kaji ɗumin mahaifanka. yanzu ba ga shi tun da na zo ganin mahaifiyata da hirar da na ke da ita ya mantar da ni wata matsala da na ke ciki da damuwa, duk da cewa dai hakan na maƙale a raina.
shima Kaka da suka dawo sai da yay nasa faɗan akan me zan zo kwana gida ana zaune lafiya, shi mijin na baida hankali da zai biye min, don haka ai maza maza a kira masa shi ya zo ya ɗauke ni mu kuma, in bikin ne gobe ya kaini tasha in hau mota, mene saina zo wani gida ban da fitina da neman magana.
ni dai fara faɗan nasa ƙirjina ke dukan tara tara, tsoro fal raina, dama shi wannan tsoho kwai jarabar masifa, in ya fara sai dai ayi shiru ai haƙuri kawai har ya sauke, ga ba ya fara magana ace za'a yanke shi. yaji ma da lafiyar jikinsa da bata ishe ahi ba amma inaa sai faɗan bala'i. ni dai hawaye kawai na ke saboda na san shikenan asirin da na ke ɓoyewa zai falla su, da adu'ar da na ke tayi cikin raina dai Allah yasa ya haƙura yay shiru da maganar. na sauke wawiyar ajiyar zuciya ni dai na tashi na shige ɗaki bayan yi musu sai da safe, kuma sai bayan na shiga ɗakin ne kuka mai sauti ya ƙwace min, tiryan tiryan komai ya dinƙa dawo min tun daga ranar farko na canjawar mijina da ƴan uwansa har zuwa yau da ya ce naje gida ya bani hutu. shigowar Ummani ɗakin zata kunna min maganin saura shi yasa na tsayar da kukan nayi shiru ina cusa fuskata cikin tsummokaran da nayi filo da su, a haka kuma bacci ya ɗauke ni ban shirya masa ba.
washegari ƙarfe bakwai muka isa tasha, mota guda muka cika, da ni da Ummani, Fati da Zainab ƴaƴan Alhaji babban wan su Ummani, Anty Khairi matar Ya Imam da Maman Yasmin matar Yashaik, Mama Hajara da Umma A'i ƙannen Ummani da su ke uba ɗaya, sai ƙananan yara duk jikoki. haka muka ɗunguma muka yi ƙauyenmu Geza in da nanne mahaifar su Ummani. mutanan ƙauyen sun ji daɗin zuwanmu sosai, murnar ganinmu har tafi ta gudunmawar da muka kai musu na kuɗi da aka haɗa naira dubu hamsin, kun san karramawa a wajen mutumin ƙauye ba kamar mutumin birni ba, aka ɗinka haba haba damu, aka bamu masauki mai kyau da abinci mai kyau.
bikin yini biyu aka yi, da ike babar amaryar sun rabu da mahaifinta, saboda haka ranar farko can gidan Babanta mu ka je washegari kuma muka dawo nan gida yinin mahaifiyarta, da Babarta da Ummani Ya da Ƙanwa ne amma cousins. mun yi ziyara sosai a ƙauyen don dama duk sanda Ummani ta je sai tayi kwana uku huɗu take dawowa, to ziyar ziyarcen da mu ke tayi yasa na manta da batun wani mijina, danginsa da matsalar da na ke ciki. harkokin gabana kawai na ke kamar ba ni ke cikin damuwa ba, na sake nayi walwalata cikin ƴan uwana, kullum a wasa da dariya ake ba babu wani ɓacin rai, sai hakan ya mantar da ni abubuwan da suka faru kwanakin da suka wuce, wataƙila sai an gama biki na dawo hayyacina sannan in koma luntsum cikin damuwar.
amma har wani fresh nayi ƙirjina ya cicciko saboda garin kunun sabaya da ake damawa safe da yamma da dare muna sha da madara da zuma, ni kaina sai da na yaba da irin haɗin don gaskiya na musamman ne tun da na gani a jikina, cikin kwanan shidda kawai yay min aiki, ai ba zan tafi ba kam sai an bani lambar me siyarwar tun da naji Matar Buba ta ce a kano take.
kwananmu bakwai cif muka juyo gida, bayan an haɗo mu da sha tara ta arziƙi, ba kamar ni da aka jido min kayayyaki, tun da suka ji Ummani ta ce ai mijina babu ruwansa ɗan gargajiya ne shikenan fa kowa sai ka ganta da garin masara ne, kuka, daddawa kayan dai girki iri iri, waken suya kuwa sai da aka haɗo ni da rabin buhu da shi da aya, tsintsiyar laushi da kujerun zama sai ka rantse kasuwa muka je siyayya, ga tsofaffin nan duk suka haɗo magunguna na matsalar rashin haihuwa su ka bani su ka ce in amfani da shi da izinin ubangiji zan ɗauki ciki.
washe garin ranar da muka dawo gida Abbaa ya ce in haɗa komatsaina in koma gidan mijina in ya so a haɗa ni da Sauda mu tafi tare tana taya ni kwana. ai tun da yay wannan furucin na shiga tashin hankali, naji ina ma bamu dawo daga ƙauyen ba, duk na hargitse daren ranar da ƙyar na iya bacci saboda tunanin mafita.
da safe ina wanke wanke sai ga Babanmu ya fito zai wuce kasuwa. ya tsaya muna gaisawa nan ya tambayeni ba dai ni da wata matsala ko na ce masa ehh, yay min nasihohinsa na iyayenmu da ba sa gajiyar