Showing 84001 words to 87000 words out of 87761 words

Chapter 29 - ƘAYAR RUWA Book 1 HAUSA NOVEL

HALIMAHZ   

20 Dec 2024

6126

saurinsa ya zo ya zuje gate dalilin horn ɗin da Ahlan ya danna har sau biyu.
"Sannu da dawowa, Ranka ya daɗe barka da dawowa an sauka lafiya?".

Me gadin ya faɗa sa'ilin da Ahlan ke shiga da motar zuwa cikin gidan, ya samu yay parking motar a tsakiyar compound saboda ba jimawa zasu yi ba za su ƙara fita. Shi ya kashe sautin waƙar da ke tashi kafin ya fita ya bar Yayan nasa a ciki wanda ke zaune ya kafe wuri ɗaya da ido kamar ba zai bar cikin motar ba. Richard Mille RM 56-02 Sapphire Tourbillon tsadaddan agogon doller miliyan biyu kenan, shi ne ɗaure a damtsen hannunsa, kalarsa upwhite, ƙwayar idonsa ya kai ya duba lokacin da ke tafiya, bayan ƙirga wasu ƴan sakanni a can ƙasan ransa ya buɗe motar ya ziro ƙafafunsa waje, sai da ya shafe kyawawan mintuna uku sannan ya fito daga cikin motar yana mai tsayuwa akan ƙafafunsa, hannayensa dukka biyu zube cikin aljihun wandon jeans.

Ma sha Allah, tsarki da dukkan yabo su tabbata ga Alhakimu, Alkaliqu, mabuwayin sarki mai azurtawa, ubangiji mai girma da ɗaukaka, mahaliccin da ya halicci wannan bawa nasa. lokacin da yake cikin motar ba zaka san da cewar asalin kyau ne da kansa ke zaune ba sai a yanzu da ya fito ya tsaya a tsaye, ƙwarai ubangiji ya zuba tsarin sura a jikin wannan halittar, kyakykyawan saurayi ne na gaban ai kwatance, ba fari ba ne tas amma hasken fatarsa na da ɗaukar hankali, hancinsa har baka, ga yankan madaidaicin baki da tausasan laɓɓa pink colour, idanuwansa madaidaita irin oil eyes farare tass da su babu datti ko kaɗan a cikinsu sai ƙyallin maiƙo da ruwa ruwa haka, kuma maimakon black eye lens irin na mutane nasa sai ya kasance aque blue mai burgewa, ga wani kwantaccen saje da ya shimfiɗu a fuskarsa tamkar an zana masa, ƙananun kaya ne a jikinsa, black jeans da black T-shirt mai ƙaramin hannu, a gaban rigar da bayanta an rubuta *S.JADDA* da manyan baƙi, haka ma a p-cap ɗin da ke kansa ita ma kalar baƙa, sosai shigar kayan su ka ƙara fidda ainihin kyan surarsa, halittar da idan kayi mata kallo na farko ba zaka so idanuwanka su ƙara ƙiftawa akanta ba, haka kuma gabanka sai ya yanke ya faɗi saboda girma na kwarjini, cikar haiba da zati da cikar kamala da natsuwa da yake da ita, ƙamshin da ke fita daga jikinsa kaɗai ya isa ya shaida maka shi ɗin na musamman ne, kuma da gani ɗan masu ƙumbar susa ne a ƙasar Najeriya, irin su ne dukiya an tara an ajiye musu kuma ana kan ganiyar ajiyewar, ko basu nemi na kansu ba ba zasu taɓa sanin wani abu wai shi Babu ba, ba ga su kaɗai ba hatta ga jikokin da za su haifa.

Tun fitowansa a motar yana tsaye ne jingine da jikin motar ya harɗe ƙafafunsa yana fuskantar entrance ɗin da zai shigar da kai cikin gidan gaba ɗaya, ƙwayar idonsa ta cikin baƙin glass da ya kewaye idanuwansa tayi ƙyam tamkar ba zata ƙifta ba. idonsa ba akan agogo yake ba, amma kuma da bugun zuciyarsa yake lissafin adadin mintuna goma sha biyar ɗin da suka rage masa ya shiga ciki ya shirya sannan ya fito ya nufa wurin mahaifiyarsa. A hankali ya kai kyawawan hannayensa masu cike da gargasa ya cire hular p-cap da ke saman kwantacciyar sumarsa wadda ta cika ta sha gyara sai ƙyalli take yi, ga ta a nannaɗe gwanin burgewa da sha'awar taɓawa, kana ganinta ka san sumar buzayen asali ce ta ƴan ƙasar Gabon mai ɗaukar ido. fatabarakallu ahsanal kaliqin, ai asalin bayyanuwar kyansa sai yanzu da ya cire p-cap ɗin, kamilalliyar fuskarsa ta fito gaba ɗaya ta bayyana tarr, sumar kansa har gaban goshi kamar wanda yasa gashin indiyawa, fuskarsa kuwa da ka kalla zaka shaida shi ɗin mutum ne mara hayaniya da kuma rashin son hayaniyar haka a gefe guda kana iya shaida shi ɗin ba mai girman kai ba ne.

Muryar da ya jiyo na sababi yay sanadin lumshe idanuwansa, wanda hakan yay nasarar bayyanar da zara-zaran gashin idonsa da kuma motsawar pink lips nasa tare da sauke wata wawiyar ajiyar zuciya, yay saurin mayar da p-cap ɗinsa haɗi da daidaita zaman baƙin gilashin fuskarsa, sai fuskan ya ƙara ɓoyuwa ta yanda ba zaka yi saurin shaida shi ba. bugawar sakan ɗaya, biyu, uku ya buɗe idanuwan nasa daga lumshen da suke tare ɗan juyasu yana jin wani sanyayyan abu na biyowa ta babban yatsansa yana shiga jikinsa, kafin sannu a hankali ya ɗaga ƙafafunsa ya fara takawa zuwa ciki.

"Kuma fa ba gidan Ubansa ba ne amma ya ke wannan fiffiƙar kya ce da shi za'a raba gado. Ko da ya ke haka ɗan talaka ya ke bai iya shiga rigar arziƙi ba, kuma fa ni nasa Uwassa ta kawowa Dr shi saboda tausayinsa da na ke shi ɗaya a cikin ƴan uba, to fisabillah da ace na kirki ne ai sai ya kwanta ma yace in bi ta kansa in wuce tunda nayi masa rana".

Marfu'a taja ɗan gajeren tsaki na takaicin mita da sababi irin na Kakarta sannan ta ce,"Madam na ba ki jakarki ne nayi gaba kya taho?".

Madam ta juyo tayi mata wani kallo ta ce,"ki tafi in bi wa? Ba ki kallon wulaƙancin da wancan wargajajjen yaron yay min ne, in sama da ƙasa zata haɗe ai ba zai kaini ba, ki jira ni mu wuce kawai".

"To don Allah ki zo mu tafi tun da dai duk maganar da kike bai san kina yi ba, kinsa muna ta ɓata lokaci".

Ta faɗa tana yin gaba, Madam ta bi bayanta tana ci gaba da faɗin,"yanzu in ba don kinga na zo gidan ubanki ba ai ba kya na bani Umarni haka ba, kamar dai ba ki san ni na haifi wanda yayi silar zuwanki duniyar ba".

"To ni me na ce kuma".

Ta faɗa tana ɗaga wayar hannunta, magana tayi na tsawon mintuna uku ta sauke kana ta miƙawa Madam wayar. "Abla ce". Da sauri Madam ta karɓi wayar ta saka a kunne tana faɗin,"Kar ki harhaɗo wasu kalaman ƙaryarki ki faɗa min saboda kare kai, ki baro gidanki kawai ki taho kima mutanen gidan nan da suke riƙe da ɗanki jaje, tsakani da Allah a faɗa miki abu tun daren jiya ki kasa ƙoƙarin bugo asubahi ki taho kije ki duba matacciyar yarinyar can a gadon asibiti, yanzu idan ita Dr ɗin ce ai tuni ta kwan ta yini a gidanki wallahi, haba ake duba da hankali da tunani mana, wannan rashin lissafi ne sam".

Da gama faɗin haka ta kashe wayar tana tsaki fuskarta na nuni da ɓacin rai. "Ni ban san zunubin da na aika har ma na haifi wannan yarinyar ba itama ta haifi wancan gantalallan yaron nata, duk ba su da lissafi. Ke kuma wuce muje ko sai an ƙwala Assalatu tukunna za ki tuna da Asibiti muka nufa".

Marfu'a ta kalleta tana kumbura fuska tace,"To motar zan ɗauko na kawo nan ki shiga ne?".

Harara ta ɓalla mata bata ce da ita komai ba, kuma kafin ta ɗaga ƙafa sai ga SJ ya wuce ta gabansu cikin sassarfa. Ta waro ido ta cikin gilashinta tana dubansa da cewa Marfu'a,"Kamar SJ ko?".

"Ba kama ba ne shine ɓarawon da kika so kurmawa ihu ɗazu".

"Allahu akbar yaushe ya dawo ƙasar? Ki ce Allah ya rufa asiri da yanzu shima an kwashe shi sumamme, gwara da Allah yasa kika ƙaryata ganina kika ce sharrin aljanu ne. Da yau Uwassa tsab ta baro wancan tashin hankali ta dawo kaina tana zunduma ihu. To maza tsayar da shi mu wuce tare don na san shima asibitin ya nufa".

"B ɗin za ki bi Madam? To ai kina da lambarsa kira shi, ni kam kinga tafiyata".

Murya ta kalar masu tausayi ta ce,"Shi ai yana iya yarda mu tafi indai zan masa shiru ba zan cika shi da magana ba. Kawai dai Na-Madam ne yafi shi daɗin tafiya ana tafe ana hira ana raha, to shi matsalarsa a wargaje yake mutunci bai ishe shi ba. Amma dai da zamu bi SJ ɗin da yafi ana ta yiwa Amb ɓarnar man mota".

"Sai kuma ki yi ai, ni na tafi".

Marfu'a tayi gaba abinta tana barin Madam a baya wacca ke gyara zaman lafayar jikinta. Tsohuwa ce sosai amma ji take da gayu tamkar ƴan mata, ga lafiyayyan jiki ma sha Allah irin ɗan ciwon ƙafar nan na tsaffi ma ita ba ta da shi, ba ranƙwafawa babu tamushewar fatar jiki da yawa, haƙoranta ras lafiyayyu ko irin cutukan nan da zaka samu tsofaffi ita ba ta yi, Allah ya bata kam, don gayu take ci abin ta har da su hoda da jambaki kamar tsofaffin amuruka. Cikin tafiyarta da ke yanayi da ta SJ ta taka zuwa motar Marfu'a, da shigarta ciki wayarta tayi ƙara, ta amshi jakarta hannun Marfu'a tana ciro wayarta ƙirar iphone 7 kai baka ce wayar tsohuwa ba, ganin sunan mijinta na yawo akan screen tayi murmushi kana ta ɗaga tana sallama cikin yarensu na faransanci.

"Bonjour Mon chéri, celui qui fait batre mon coeur j’espère que tu te porte bien". _(Assalamu Alaikum. Fatan mijina abin alfaharina yana cikin ƙoshin lafiya. )_

"Sava très bien celle qui me rend heureuse, je tais appeler sa ne passe pas .comment va la santé de l’enfant a l’hôpital?". _(Lafiya lau farin cikina, nayi ta kiranki ba na samu. Ya wajen yarinyar asibiti?)_

"C’est aujordhui qu’on va allez la voir on dit que sa ne va pas sa santé".

"Quallah lui accorde la santé .mon marie t’aime tous les jours".

"Moi aussi j’aime mon marie ,Quallah nous facilite le coeur .merci?".

*PSC Specialist Hospital Limited, Lamiɗo Cresent.*
Ƙafafun Ambassador Jadda su ka ƙaraso ƙofar room ɗin da aka rubuta V.I.P 05 da bayyanuwar tashin hankali a tare da shi. Wanda saukarsa ƙasar kenan daga ƙasar Italy. Maamee na daga can gefe kan kujera, hango shi ta taso ta taho gare shi da sauri kamar yanda shima ya tafi gareta da sauri.

"Daadee". ta faɗa da ɗan ƙarfi tana faɗawa jikinsa, ya kewaye matar tasa da dukkan hannayensa biyu cikin tsantsar so da kulawa yana faɗin,"Sorry Mon Cheri, calm down, calm down everything will be ok by God Grace". Bata iya cewa da shi komai ba sai sabon kuka da ta saki shi kuma yana ƙara rungumeta ya shiga shafa gadon bayanta ba tare da sunyi la'akari da mutanen da ke wajen ba.

Cikin kuka sosai take cewa da shi,"I am so scared Daadee".
"Don worry relax and calmdown, i am here now, everthing will be oak, you stop crying please".

Ya ɗago kai ya kalli Samra yace da ita,"Iyayen yarinyar fa an samesu?".

Ta ɗaga masa kai,"Yes Daadee". ta faɗa tana yi masa nuni da kan wasu chairs inda iyayen Sa'ida su ke a zaune, tare da su kuma ƴan uwa ne kusan mutum goma a tsaye kowanne cikin jimami. sai yabi wajen da kallo yana ƙare musu kallo me tarin ma'anoni da yawa. Ya tattara hankalinsa da tunaninsa wajensu gaba ɗaya, sunyi tagumi kowannen su fuskarsa bayyane da bala'in tashin hankali da tsantsar damuwa, yanda yay nisa a kallonsu zai tabbatar maka da ya tafi cikin dogon nazari, kuma daga yanda yake faman yamutsa fuska sai kayi zaton ko ƙyanƙyamin kallon na su yake.

Samra da ke kallon mahaifin nasu ta fakaici idonsa a hankali kuma cikin dabara ta zura hannu cikin aljihun rigarsa ta zare kwalin sigaret ɗin da ke ciki. Da sauri ta bar wajen da nufin zuwa ta jefar, idan da abunda suka tsana a duniyarsu bai wuci shan sigari da mahaifinsu ya mayar tamkar abinci ba. Barinta wajen ƙarasowar Madam da Marfu'a, Daadee ya zame Maamee daga jikinsa yana yiwa mahaifiyarsa barka da isowa. Marfu'a kuma ta wuce da ƙaton basket na abinci taje suka gaisa da su Ummani kana ta dawo ta zauna kan kujerar da Samra ta tashi tana karɓar yaronta a hanun Nani.

"Saukar yaushe?".
Madam ta ce da Dadee suna tafe zuwa wurin su Ummani ita da shi.

"Yanzun haka, don ina shigowa kuna zuwa".

Daadee ya ce da ita daidai da ƙarasowar tasu wajen dangin Sa'ida waɗanda suka kame kansu a gefe guda suna jiran tsammanin rai ko mutuwa na ƴarsu. Madam ta miƙa hannu ga Ummani tana cewa,"Bayin Allah sannunku, ya muka ji da wannan tashin hankali?".

Daadee shima ya miƙa hannu ga Abbaa da Kaka suka gaisa. Kafin nan ya shiga basu haƙurin hatsarin da ya afku yana kwantar musu da hankali akan da yardar Allah ƴarsu zata sami lafiya. Suka amsa da amin tare da godiya bisa karamcin tsayawa da aka yi akan ƴar tasu wannan kaɗai ma basu da bakin godiya sai dai su ce Allah saka da alkhairi, hatsari kuma ai afkuwa yake ba da gangan ba saboda haka babu buƙatar ake basu haƙuri ai an masu mutunci ma da aka ɗauke musu ɗawainiyar asibitin. Daadee ya kai ƙwayar idonsa ga hanyar shigowa wanda yay daidai da shigowar SJ kuma take annurin fuskar Daadee ya ɗauke, yay saurin ɗauke idonsa daga wajensa yana kawarwa gefe fuskarsa na nuna ɓacin rai, shima ɓangaren SJ ganin mahaifin nasa a wajen yasa shi dakatawa da tafiyarsa ya tsaya daga can nesa, haka kuma yanayinsa na sauyawa zuwa wani yanayi me wuyar fassaruwa, tabbas in ace ya san mahaifin nasa ya dawo to bai ga abin da zai kawo shi wajen nan ba, kamar yanda a ɓangaren mahaifinsa shima cikin zuciyarsa ke faɗin in da ya san SJ zai zo asibitin da babu abin da zai kawo shi a lokacin da zai zo.

Ahlan yaywa Maamee nuni da SJ, ta kai kallonta wurin suka haɗa ido da shi yana tsaye hannayensa sarƙe a ƙirji sai kallonta ya ke babu ƙiftawa, fuskarsa na nuni da rashin jin daɗin ganin Daadee da yay a wajen. Ta tashi ta ƙarasa gare shi don ta san ba zai ƙaraso ba kam, tayi mamakinsa ma da bai koma ba kamar yanda tayi mamakin Daadee shima bai fice a fusace ba, ita a duniyarta kam bata da wata damuwa bacin ta SJ da Daadee da basa jituwa ko na misƙala zarra kamar ba Uba da Ɗa ba.

Da isarta wajensa ya kama hannunta ya riƙe a nasa, tana kallonsa ta ce,"Me yasa ka baro aikinka?". Ta faɗa cikin harshen faransanci.

Yay shiru na ƴan sakanni kana shima cikin harshen na su ya ce da ita,"Maamee karon farko da naji sautin kukanki, kinga har yau zuciyata motsawa take da zafin kukan da naji kina yi".

Yay shiru yana rufe idanuwansa yana shafa hannun mahaifiyarsa da ke cikin nasa, bayan numfasawar minti guda ya ce,"Yarinyar fa?".

Kasa ba shi amsa tayi, ya buɗe ido tare da sanya hannu ya ɗago fuskarta ya ce,"Da ace kuɗi na siyan lafiya da ba'a kawo wannan lokacin ba, sai dai lafiya na wurin ubangiji bamu da yanda zamu yi, shi likita nasa taimakawa ne kawai. Don Allah Maamee ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki zata sami lafiya fa, Yanzu haka da na shigo sai da na fara zuwa wurin Dr yay min bayani kuma ya bani tabbacin zata farka lafiya lau wasu mintuna kawai ake jira, na dai jaddada masa suyi iyakacin iyawarsu wajen ganin Yarinyar tayi surviving and ba tare da zaman wani mummunan rauni a tare da ita ba".

Ya ƙarasa maganar yana sauke numfarfashi tamkar wanda yay tsaren gudu tsabagen doguwar magana nayi masa wahala.
"Amma Bhai kana gani sama da 24hrs fa bata farka ba, kar ya zama na yi sanadin rai".

"Maameeeee".

Jin yanda ya ja sunan nata yasa tace,"To nayi shiru Allah ya tashi kafaɗunta".
Hannunsa bisa fuskarta ya ce,"Marci".

"Ga mahaifanta can da ƴan uwanta muje ku gaisa ka tayani ba su haƙuri".

"Ok let's go". Yana riƙe da hannun mahaifiyar tasa suka nufa wurin. da zuwansu SJ ya duƙa har ƙasa ya gaida su da girmamawa tare da tambayar,"Ya mai jikin?". Sautin muryarsa ya fito da rashin ƙwarewar hausa a bakinsa.

Abbaa ya dinƙa kallonsa lokaci ɗaya sai yaji ya shiga ransa, saurayi mai kamala da natsuwa gami da girman kwarjini. Ya ce da shi,"To sauƙi yana wurin lillahi, tana can kwance dai har yanzu bata farka ba amma likitan ya ce wai zata farka duk da mun barwa Allah yay ikonsa".

Kan SJ sunkuye a ƙasa, cikin tausashshiyar murya ta son kwantarwa da mutun hankali ya ce,"Zata farka kuma cikin sauƙi in sha Allahu, likitoci za su yi iyakar bakin ƙoƙarinsu akan lafiyarta babu wani damuwa ku kwantar da hankalinku".

"To mun gode Allah ya saka da alkhairi".
Ummani ta faɗa tana kallonsa. Ya miƙe yana yi musu sallama. Ummani ta kasa ɗauke idonta daga kansa, kallonsa kawai take yi tana so ta tattara yanayin da take ji akansa ta ɗora a ma'aunin lissafinta kana ta fassara shi, zuciyarta ta harba ɗaya, biyu, uku, tare da kalmar GARKUWA. Duk da halin jimamin da ake ciki hakan bai hana ahalin Sa'ida furta yabo da burgewa ba akan SJ da ahalinsa.

"Akwai buƙatuwar ki koma gida".
"Bhai zan koma ne kawai idan naga farkawar ƴar mutane, sannan naga fitowar Muntaƙa daga station domin ƴan sanda sun riƙe shi sun ce yana tuƙi ba bisa ƙa'ida ba".

SJ ya kalla agogon damtsen hannunsa kana a hankali ya furta,"zata farka Maamee, zata farka ko don saboda samun natsuwar Mahaifiyata".

Ya faɗa yana tsayuwa gefen da Ya Imam ya jingina da jikin bango tare zuba hannayensa cikin aljihun wando gami da fuskantar ƙofar ɗakin da Sa'ida ke kwace rai hannun Allah, kuma fuskantarsa ƙofar ɗakin yay daidai da farkawar Sa'ida wacca ta ƙwallara wata muguwar ƙara da ta amsakuwa a cikin asibitin gaba ɗaya kafin furucin Abbaana ya biyo baya a bakinta. Ai fa kamin ƙiftawar ido cikin sauri kowa ya miƙe anyi cuncurundo a ƙofar ɗakin ana leƙenta ta farin gilashin jikin ƙofar, tana daga kwance tana faman jujjuya kai tana kiran sunan Abbaa. Dr ya ƙaraso wajen cikin hanzari shi da nurses suna a ba su hanya, sai dai sam babu ma wanda ya san suna yi. A hankali SJ ya sauke numfashi yana barin wajen da yake tsaye wanda shi ɗaya ne dama bai bar inda yake ba, ya ƙaraso kusa da Dr ya karɓi stethoscope ɗin hannunsa, sannu a hankali ya ratsa ta tsakanin mutanen da ke ta faɗin Alhamdulillahi yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login