Showing 48001 words to 51000 words out of 87761 words

Chapter 17 - ƘAYAR RUWA Book 1 HAUSA NOVEL

HALIMAHZ   

20 Dec 2024

6122

jawa mahaifiyarki shiga matsala".

ya kalli Nazifi yace,"Allah yay maka albarka".

ya ce,"amin Abbaa, na gode Allah ya ƙara muku lafiya...amma ayi haƙuri da batun zu...".

"dakata wannan hukunci ne da na riga na yanke, ka riga ka san kaifi ɗaya ne ni bana sauka daga maganata. zuwa gidana na haramtawa matarka zuwansa ko da bisa izininka ne, idan tana so ta haɗu da mahaifiyarta su haɗu a wani wajen".

ɗakin yay shiru don hatta sautin kukana babu domin nasa hannu na toshe bakina kamar yanda Yashaik ya umarce ni, babu abu mafi ciwo da naji irin hukuncin da Abbaa ya yanke min. haƙuri su ke ta bashi bayan nima sun saka na fuskance shi na rissinar da kai na ba shi haƙuri tare da alƙawarin ba zan kuma cutar da yaran ba, ba zan ƙara yi masa wani laifi ba. kuma memakon komai ya lafa sai ma sabon faɗa ya tashi, Abbaa dai bai ce komai ɗin ba bayan maganar da yayi sai Yayyuna da Kaka ne kamar za su cinye ni ɗanya.

sai da Abbaa ya buɗi baki yace da Nazifi muna iya tafiya sannan ya miƙe yay gaba, Yaya Imam da Yashaik suka bi shi, ni dai kasa tashi nayi sai lokacin na rarrafa na ƙarasa gaban mahaifiyata wadda ko tarinta banji ba a wurin, na kifa fuskata saman cinyarta, kuka na ke yi sosai a hankali ina faɗa mata ban aikata ba, ba ni ke da laifi ba akan komai, to roƙa min Abba ya sauka akan hukuncin da ya yanke.
ta ɗora hannunta a saman kaina, kafin ta kai ga magana Abbaa ya doka min tsawa ya ce,"zaman uban me kike da ba za ki tashi ki bi mijinki ba".

da sauri na miƙe jiki duk babu ƙwari ina jin jiri na neman zubar da ni, na saita kaina tare da janyo fuskar hijabina don kar yaran su fahimci abun da ya faru, Ummani ta ruƙo hannuna muka fito daga ɗakin. falonta mu ka shiga muka tsaya a tsaye, a hankali ta ce,"tsakanin ke da mijinki ban san bayan wa zan bi ba, ke da shi duka akwai yardata akanku. amma ni dai ki sani haƙuri yana daga cikin abun da ya ke taya bawa samun nasara a duniya da lahira Sa'ida, duk abun da aka ce babu haƙuri da juriya a cikinsa to zai wuya abun ya kai ga nasara. kwantar da hankalinki ki cigaba da rayuwar ki cike da tawakkali tare da godiya ga Allah, har kullum ina faɗa miki Allah na tare da ke, zai tsaya miki akan lamuranki muddin ba ki da nufin cutar da wani. ke dai riƙe addu'a ki tsarkake zuciyarki ki riƙe yaran da zuciya ɗaya ba cuta babu cutarwa, sannan kar ki ɓata zaman lafiyarki da mijinki, don Allah kar ki ɗauka huɗubar sheɗan ya zuga ki aikata abun da za ki zo kina danasani, yara ne ki gyara musu idan suka yi kuskure na goyi da bayanki domin alhakin tarbiyarsu akanki ya ke, amma ban da cutarwa don Allah Sa'ida, ki ɗaukar min wannan alƙawarin".

na so ace na sami wadataccen lokaci tare da mahaifiyata tana lallashina da min nasiha, na samu na amayar mata da abun da ke cikina ko naji salama, amma ina Kaka na fitowa ya kama yi mata faɗa, ita kuma jin wannan da sauri ta sakeni ta ce na tafi saboda bata so sauran mutanen gidan su san abun da ke faruwa.
a hanya muna tafiya yay wani ƙasa da murya yacca yaran ba za su ji ba yana min magana a hankali irin ta neman a shirya, don munafurci wai haƙuri ya ke ba ni, yana faɗa min in kwantar da hankali kar in saka damuwa a rai, zai fahimtar da ni idan mu ka koma gida. ni dai banza na yi masa har lokacin kuma idona bai daina zubar da hawaye ba, tsabar neman gindin zama har wani tambayata ya ke wanne restaurant zamu je muci abinci idan mun koma na huta da girki. can kuma sai ce yayi,"kin sanni akan son yara shiyasa amma ba don in muzguna miki hakan ya faru ba".

"hmm to waye ba ya son yara? Ba da tarbiya ne kawai ba kowa ya iya ba".

"hmmm". ya ce yana kira sunan yaran, su ka amsa yana ce musu,"Antynku ta ce muje restaurant mu ci abinci amma wai wanne kuke so mu je?".

caraf tantiriyar cikin na su wato Atika ta ce,"Anty inda muka je last week yafi kyau Anty aje can".

jin ban kulata ba ta ratso ta tsakanin kujerunmu tana leƙo kanta wajen fuskata. "kin ji Anty please".

sai a sannan na yi murmushin da ya fidda sauti na ce,"tom shikenan yanda ku ke so".

"ina kenan?". ya tambaya idonsa a kaina.

na ɗaga ido na masa wani kallo na ce,"Calido".
"tom shikenan". ya faɗa yana ɗauko glass ya miƙo min,"saka wannan". na san dalilin bani glass ɗin, saboda haka na karɓa ban musa ba na saka, don duk me hankali kallo ɗaya zai min ya san na ci kuka na ƙoshi, haka kuma ina cikin matsananciyar damuwa.

a wajen cin abincin ban iya cin komai ba, tagumi kawai nayi idona akan teburin ina tunani kala kala, shi kuma ina jinsa da yaran suna cin abincinsu hankali kwance, komai suka gani su ka ce suna so sai ya ce a kawo musu, ƙarshe dai nawa abincin sai takeaway aka yi min.
sai biyar muka koma gida, ni na fara fita a motar, muna shiga ciki ni da yaran muka yi sama, shi kuma yay ɗakinsa na ƙasa, don shi ra'ayinsa bai fiya wani son hawa bene ba, ko da za'ai ginin gidan saboda na ce ina son bene yasa aka yi amma da niyyarsa duk girman gidan ayi flat. ina shiga ɗaki na kulle tare da faɗawa saman gado na yi lamo abun duniya duk ya ishe ni, jina na ke kamar marainiya mara gata, bani da masaniyar dalilin da yasa Allah ya ƙaddaro min wannan lamarin ba, amma ina roƙonsa ya bani ikon cinye jarabawarsa da dukkan iyawata.

ina kwance naji ana ƙwanƙwasa ƙofa, nayi banza saboda na riga na saka maƙulli babu damar a shigo, haka kuma ba zan buɗe ba don sam bana son ganin Nazifi da yaran, kusan mintuna ɗaya ana ƙwanƙwasawar sai kuma naji muryar Rumana ta na cewa,"Anty ki fito ga Iyam ta zo".

ban san lokacin da bakina ya suɓuce da faɗin innalillahi wainna ilaihi rajiun, hasbunallahu waniimal wakil, ina fadar hakan kuma naji gabana ya sassauta faɗuwar da yake tare da samun wani guntun kuzari na sauko a gadon kamar mara jini na ƙarasa na buɗe ƙofan.

"Iyam ce ta zo, Abban kuma ya fita".

na ce mata gani nan zuwa kana na koma ciki na wanko fuskata da sabulu tare da tsayar da kukana. na ɗau mayafin abaya na yafa na fita.
jin takun saukata ta kallo bene tana cewa,"kina takaicin zuwana ne da kike wani sakkowa a hankali".

maganartata sai naji kaman ta harɗe ni don saura ƙiris in faɗo daga benen. na ƙarasa wajenta cikin sauri ina durƙusawa in ce,"sannu da zuwa, an zo lafiya".

banzan kallo ta min tana cewa,"kina ɗaki abinki a kwance har da su rufe ƙofa, kika bar yara komai zai faru da su ya faru da su ba asararki ba ce".

cike da ladabi na ce,"da yake ban jima da shiga ɗakin ba ne, tara muka hau saman da su ma suka shiga ɗaki ban san sun sakko ba".

taɓe baki tayi tace,"in kana da ƴaƴa ai baka shiga ɗaki ka kulle ka barsu su ɗaya ba, zama kake ka kula da su".

a hankali na ce,"ayi haƙuri. ina wuni".

bata amsa min ba ta mayar da hankalinta ga jikokinta.
na miƙe a sanyaye na shiga kitchen, abincina da mu kai takeway na juye mata na haɗo da drink da ruwa na kawo mata. kallonsu kawai tayi kamar bata gani ba kuma bata ji me nace ba. na zauna a rakuɓe ƙasan carpet tace,"shi Nazifin yayi ina ne haka?".

"bara na kirawo shi a waya".

ta dakatar da ni,"da tawa wayar ai, ungo kira min shi".

hmm dama ko da na hau saman ma wallahi ba kiransa zan yi ba, zan sha zamana ne in sakko in ce mata wayar bata shiga. sai bayan katsewar kiran farko sai ga shi ya kira, na ɗaga na mika mata, suka gaisa take faɗa masa,"na zo ne ai ake cewa baka nan".

ban san me yace mata ba naji ta ce,"to shikenan sai ka dawo ɗin, amma ka hanzarta".

ita da yaran suke ta hirarsu, ni ba abin in tashi ba na jawa kaina magana, don haka na gyara zamana na jingina da kujera ina salatin Annabi cikin raina.
sai da aka yi sallar magriba ya dawo yake bata haƙuri da cewar yaje ne gidan Alhaji Fari. na basu wuri na koma ɗaki bayan wasu mintuna ya kirani a waya ya ce na sakko.
da na fito ina jin surutun yaran a ɗakinsu suna musun da suka saba akan assignment.

ni da shi duk muka zauna a ƙasa, kamar wata basarakiya sai da ta ja lokaci kafin ta ce,"Sa'ida me yaran nan su ka yi miki ne kike azabtar da su umm?".

da ƙwarin gwiwata na ce,"ni ba su yi min komai ba Iyam, kuma abun da zuciyar kowa ke faɗa akan ina zaluntarsu sam ba haka ba ne, sai dai ba me yarda da ni amma Allah na shaidata".

wai wannan ƴar maganar da nayi sai ta tunzurata ta kama cewa,"a'a tou ai ba ce nayi ki faɗa min magana ba Malama ƴar gidan Malamai da su kaɗai su ke da Allah. to ni dai batun jikokina ne zan shata miki layi tsakaninki da su, ba sai na rantse miki ba domin ni maganata ko babu rantsuwa tabbatarwa nake na aikata abun da na faɗa, Sa'ida in har kina son zamanki da ɗana to kar ƙara bar min jikoki da yunwa, hakana kar hannunki ya kuma kaiwa jikinsu, ke ɗaga murya ma ban yarda ba. idan wani baƙin ciki ne a ranki kike so ki huce akan wani to ga shashashan mijinki nan ki huce akansa, ki cutar da shi shi ɗaya amma banda jikokina...na san ba komai ke damun ki ba face baƙin ciki da hasssada, yo banda ma dai halin ɗan adam na butulci ba ki haifa masa ba kuma ki ce ba za'a ba shi ba, ke kawai da ke ɗaya zai zauna ba batun wani ya raɓe shi, in da ya so ai aure zai ƙara wata matar ta haifa masa ba ya tsaya karɓar ƴaƴan wasu ba, amma ke saboda ba ki san halacci ba shine za ki ɓige da cutar da yara saboda ki raba tsakaninsa da ƴan uwansa, to ta Allah ba taki ba, ba yanda za'ai yayi ta cika miki ciki da abinci kina kasayarwa a masai, wanne kalar taimako ne baiwa ƴan uwanki ba? ina ce har kasuwa ya kai Yayanki. butulu marar halacci, to yara ne dai jinin Nazifi ne, shi da uwayensu ciki ɗaya suka fito kuma nono ɗaya suka sha, kinga kuwa ba ki isa ki raba shi da yaran nan ba sai dai baƙin ciki yasa ki haɗiyi zuciya ki mutu ruwanki. ni to bara ma na faɗa miki abin da baki sani ba, yanzu sam zamanki tare da shi bana ƙauna wallah, Allah ya gani ƙaunar jin zanceki ma bana yi, kin sire min kin fita a raina, badan kar ace na zama sheɗaniya ba da tuni na yiwa tufkar hanci, yo me amfaninki auren macen da bata haihuwa, zama da juya ai ƙaddararran zama ne, haka kawai ina so naga tsatson Nazifi kin babbake gida kin hana".

Haihuwa! Juya! kalmomin nan nasa zuciyata matsewa, dalilin furucinta hawayen da ban san da su ba suka fara sauka.

shi kuma ta shiga cewa da shi,"Kai kuma ka ɗauki mataki, ka gargaɗi juyar matarka akan taɓa min jikoki, idan ba zaka iya ba duk kalar matakin da na ɗauka akanta ita ta jiyo".

ya ce,"kiyi haƙuri Iyam, ai na mata faɗa kuma tayi alƙawarin zata gyara".
"ya dai fi mata kwanciyar hankali".

ni dai ban ce komai ba, ban sani ba yin shiruna ne ya ƙular da ita ko mene oho, na dai ga ta fusata ta ƙara ruwan bala'i sai faɗin maganganu take na cin mutuncina da zarafina.
Shi da kansa ya shiga bata hakuri, bata dai yi shiru ba ta haɗe faɗan har da shi ɗin tana zagi, ya rikice yana dubana rai tamau tare da watsa min mugun kallo ya ce,"wai Sa'ida me yake damunki ne, a gaban mahaifiyata fa kike, kin yi mata laifi kuma ba za ki iya buɗe baki ki bata haƙuri ba, zan ɓata miki rai fa".

ido na ɗaga na kallesa na sauke, in bada hakuri! akan laifin da banji ba ban gani ba? ai haƙuri na gama bayar da shi a gaban iyayena, sai dai komai zai faru ya faru amma ban bawa kowa haƙuri a cikinsu, da me zan ji?, Cin mutuncinsu da zarafinsu? Ko kuma sharrin yaran da makircinsu?

ƙuluwa yay sosai ya shiga jijjiga kai yana nuna ni da yatsa ya ce,"mahaifiyata! kin fi ƙarfin bata haƙuri ko Sa'ida, za ki gane kuranki".

Iyam ta ce,"ƙyale mahaukaciya marar hankali da tausayin yaro, juyar banza da wofi mara tarbiya da bata san darajar uwa ba, Allah dai ya rabamu da ƙyashi da baƙin ciki da girman kai, ki bari randa kika haifa ko iyayenki suka zama wasu kyayi kowanne iskanci, amma yanzu wace ke, juya ko ƴar talakawa? kina gida zaune ba ilimi babu aiki, komai sai dai a miki".

zagin ya ci min rai, nayi kamar na miƙe amma na daure na zauna saboda tunawa da iyayena.
faɗan Abbaa da kashedin Kaka gareni ya fara tariya cikin kaina, na hango ɓacin ran da ke shimfiɗe saman fuskar mahaifina. kawai sai na gyara zama cikin karyewar zuciya, na fuskanci Iyam cikin raunanniyar muryata na ce,"don Allah don Annabi kiyi haƙuri da dukkan abun da ya faru".

shima na fuskance shi a hankali na ce,"kaima kayi haƙuri".

cikinsu babu wanda yace da ni komai. kaina dai a ƙasa duk wanda ya kalleni sai ya ji tausayina. shi kuma ya numfasa ya ce da mahaifiyar tasa,"Yanzu zan kai ki gida ko sai anjima?".

kamar wanda ya tsikareta tayi saurin cewa,"wanne gida kuma Nazifi, ka mance yau Malam ya bar ƙasar ne, kai dai Allah yay maka albarka ya ƙara buɗi, ko don sanin girman iyaye da kayi ba zaka taɓe ba wallahi. ai zuwa nayi na zauna tare da ku zuwa Baban naku ya dawo, tunda naga lamarin gidan na ka yanzu sai ƙalu innalillahi, to kuwa kaga ai gwara a sami babba ya zauna tare da ku ko a samu raguwar wasu iskace iskancen. ni tun wancan karan da ta hora yaran nan da yunwa hankalina ya daina kwanciya gaba ɗaya, to yau kuwa da naji batun tana neman sumar da su ai bana ci gaba da zama ba ayi kisan kai muna can nesa, gwara in zo in zauna tare da su ganin idona yasa a rage wata muguntar".

furucinta ya zama daidai da saukar tsawa a tsakiyar kaina, na ambaci innalillahi wani innalaihi rajiun, zaman Iyam a gidan nan? wanne irin zama za'ai kenan? shikenan kuma na ƙara shiga gagarumar matsala, farin ciki kam nayi bankwana da shi, sai abin da naji na gani.

"wanne ɗakin zan zauna? ko kuwa ma ɗaki ɗaya zamu tare da yaran, don ni gaskiya ina tsoron sharrin wannan ƴar, kar ta koma bin cikin dare ta cutar da jikokina, ba ka san wanne shiri mugun mutum ya ke yi ba, Allah dai ya karya alƙadarinta kawai".

ya sauke numfashi ya ce,"su a sama su ke, ke kuma kinga ba za ki juri hawa da saukar ba, tunda akwai ɗakuna a ƙasa sai a kimtsa miki wanda kika zaɓa".

ya miƙe yana ɗaukar jakar kayanta, suka yi ɗakina na ƙasa, suna zuwa naji ta ja dogon salati tana faɗin,"Nazifi ya zaka kawo ni wannan ɗakin, na san mene a cikinsa zaka ce in kwana, ai wallah sam ba zai yiwu ba. gwara ka barni in ke kwana a falon na ku ni ba baƙuwar zafi ba ce, amma wannan ɗaki kuwa sai in ƙur'ani aka sauke masa akayi turarukan karya sihiri shine sai in iya kwana, amma ba haka sakaka ba ban yo shirin komai ba duk da cewar azikarin safe da maraice bai wuce ni".

ya ce,"haba Iyam ko baƙo ai ba za'a barsa ya kwana a falo ba balle ke mahaifiyata, ɗakin naki ne sai an kaɗe ƙura tukunna kin san ba wani amfani ake da su ba, kuma dole sai an sanya gado a ciki".

"ai Nazifi ko a dandariyar ƙasa ni mai kwana ce akan dai kwanan ɗakin matarka".

"tom bari naje na gyara miki".

su ka dawo falon har lokacin ina zaune yanda suka tafi suka barni, suka wuce zuwa ɗakin da zata zauna ta dakatar da shi da cewa,"a'a to wai ita waccan shafaffiya da mai ɗin ƴar waye da tafi ƙarfin zuwa tayi gyaran".

ta juyo gare ni tana cewa,"ashe haka yake tsoronki shiyasa ya kasa ɗaukar matakin komai game da rashin haihuwarki. to tashi maza gyara min wancan ɗakin na farko a shi zan zauna. in aka ce mutum na da haƙuri sai ai ta cutarsa, yanzu a ƴaƴana in ba shi da yake da uban haƙuri ba wa zai zauna kallonki kina ƙin girmama ni".

haka na miƙe na wuce na shiga ɗakin, ni dai tunda muka zo gidan zan ce sau ɗaya na taɓa buɗe shi na shiga shima ranar Malam ya bada turare ne aka yi a gidan cikin kowanne ɗaki.
Awa guda da wasu ƴan mintuna na ɗauka ina gyaran, na ci wahala sosai don bayana kamar zai karye. bayan na gama na saka turaren wuta da air freshner sannan na fito na sameta ita da jikokinta, na kalli agogo ƙarfe tara da rabi, cikin girmamawa na durƙusa gefenta na ce,"Iyam na kammala ko za ki duba ki gani".

tashi tayi tana cewa,"mu je in gani Allah sa ba gyaran son zuciya kika yi ba".

tayi gaba ni kuma na ɗauka jakar kayanta na bita, hankalina sam yaƙi kwanciya da zamanta ɗin a gidan. tsaye na sameta tana bin ɗakin da wani irin kallo, har cikin ranta nasan yayi mata amma kawai dai saboda a kushe a nuna baka iya ba don an tsaneka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login