Showing 30001 words to 33000 words out of 87761 words

Chapter 11 - ƘAYAR RUWA Book 1 HAUSA NOVEL

HALIMAHZ   

20 Dec 2024

6113

tafiyar da ni, baza'a barni a baya ba, Kwantan Ɓauna da Lokaci ne sai in ban same su ba amma ba abin da zai hana in karanta su kam.
da littafin Lokaci ne na fara, kawai sai naji maganar Baba tana dawo min cikin kaina da yake cewa kowacce mace da kalar jarabawarta a gidan aure, tabbas haka ne tunda ga Umaima ma wadda matsalarta da tawa kusan ɗaya ce, sai dai ita nata da lafiya tun da babu tsangwamar dangin miji haka kuma ta samu ciki har ta haife, saɓanin ni da dangin miji suka taso ni gaba, miji babu sauƙi, sharrin ƴaƴan ruƙo, ga kuma nakasun rashin haihuwa da duniya ke ganin shi a matsayin babbar tawaya a gare ni.

murmushi kawai na ke me ciwo domin ni ɗaya na san me naji a cikin zuciyata, haƙiƙa jarabawar da na ke ciki tana da matuƙar wahala, amma babu komai na faɗawa Allah daren jiya, ya amsa sai jiran sakamako wanda na ke da yaƙinin me kyau ne.
can ina cikin karatun Kwantan Ɓauna ina jinjinawa sha'anin hassada da makirci irin na gidan sarauta, naji cikina ya murɗa har nannaɗewa hanjina yake saboda mahaukaciyar yunwar da nake ji, tun ina daurewa naji ina ba zan iya ba, to amma ya zan yi? na san ko na sauka babu abin da zan samu na ci, amma zanje na duba kan dining wataƙila Allah ya taimake ni in samu ko guntun biredin shekaranjiya ne.

abu kamar wasa lokaci ɗaya naji jikina ya kama karkarwa, na yi cilli da wayar gefe na fita a ɗakin a gigice, tabbas yunwa bata da hankali, ji na ke fa kamar zan mutu wallahi. kamar yanda na zata har yanzu kitchen ɗin a rufe yake babu alamar ma an buɗe shi, a daddafe na wuce dining ina zuwa Allah ya taimake ni na samu ragowar yogurt a jarka, ban wata wata ba na ɗauka na kafa kai ban sauke ba sai da na shanye tass. na san ba zai wuce mai gidan ne ya sha ya ajiye ba don ni dai ban san da shi a wurin ba, jiya ban bar komai akai ba da nayi gyara, to ban damu da duk hargagin da zai min ba, ba hauka na ke ba a yanda na ke jin raina na neman fita sanadin yunwa ba zanga abinci in ƙi ci ba, duk abin da zai min yay min na riga na saba yanzu.

ɗaki na koma na ɗora karatuna daga in da na tsaya, a hankali naji cikina na motsa min da ciwo, can kuma na fara ji kamar ana ɗaure min hanjin cikina, nayi saurin miƙewa zaune ina riƙe cikina idanuna a runtse, tambayar kaina na fara anya youghurt ɗin da na sha me kyau ne?, ko dai ba Hubbi ne ya sha ya rage ba?, to wa ya shigo da shi?.
da ƙyar na samu ciwon ya lafa na kwanta ba shiri, haka nayi ta sauke numfashi ina jin bacci yana ƙoƙarin ɗaukata, dama na ware a.c sanyin sai ratsa ƙashina yake. ban san bacci ya ɗauke ni ba sai ji nayi ana taɓa ƙafata, na buɗe ido a hankali, ido muka haɗa da Hubbi yana tsaye hannayensa zube cikin aljihun wando, ji nayi zuciyata ta motsa, nayi dakiyar ɓoye tsoronsa na ɓata rai ina yin miƙa, zuciyata kuwa ta dunƙa zugani akan in juya masa baya in koma baccina amma sai naji ba zan iya ba, haka na miƙe zaune kamar ina so kamar bana so nama kasa gane kaina.

shi dai yana tsaye kamar wani gunki kallona kawai yake yi, ya shirya cikin manyan kaya riga da wando na yadi milk colour, yayi bala'in kyau kansa babu hula. kasa daina kallonsa nayi saboda masifar kyawun da yayi min, ba tare da shiryawa ba murmushi ya suɓuce min yayin kallonsa, kalmar kayi kyau na ke shirin faɗa masa, amma sai dai saƙon da ke a saman fuskarsa yasa na sunkuyar da kaina ƙasa na ce,"Ina kwana".

Maimakon amsa gaisuwar tawa sai ji nayi ya ce,"Kafin nan da awa guda ki tabbatar kin tattara kayan ki kin bar min gida, kije gidanku ki zauna har sai san da na neme ki".

a zabure na waro idanu waje har ban san lokacin da na sauko akan gadon ba saboda ruɗani, hannuna dafe da ƙirji idanunsa cikin nawa na ce,"Hubbi me ka ce?".

ransa a haɗe tamkar hadari ya ce,"Kinji ai ba kya buƙatar na maimata miki, ki tabbatar kafin na dawo kin bar gidan nan in ba haka ba za ki yi karo da abin da ba ki taɓa karo da shi ba, wallahi muddin na dawo na sameki sai na miki wulaƙancin da kare ma ba zai shinshina ba".

ya faɗa yana nuna ni da yatsa, kafin ya fita ya barni tsaye cikin maɗaukakin mamaki da tsantsar al'ajabi, haka na ƙame kamar gunki ƙofar kawai na ke kallo idona ko ƙiftawa ba yayi, tashin hankali da firgicin da su ke zuciyata kuwa tamkar zata faso ƙirjina ta fito.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un". na faɗa a bayyane ƙirjina yana harbawa hannayena har lokacin dafe da ƙirjina.

"lamarin har ya kai haka?, duk haƙurin da na ba shi?, wanne irin bala'i ne wannan?, in tafi gida fa har sai ya neme ni, me yay zafi har zai yanke tsatstsauran hukunci haka? akan dai iya abin da ya faru jiya ko kuma da wani laifin daban a gefe da ban san da shi ba? to ni kuwa in je in ce da su Abbaa me?".

a fili nayi maganar ina jan numfashi sama. daɓas na zauna kan gadon na kafe wuri ɗaya da kallo, cikin kaina na rasa tunanin me zan yi, na kuma rasa inda zan ɗora wannan al'amarin me girman gaske. ban san lokacin da hawaye ya shiga zarya a idanuna ba, lallai ina cikin jarabawa, kuma tabbas na yiwa kaina alƙawarin cinyeta, ba zan taɓa bari na faɗi ba in Allah ya yarda.

zuciyata ta fara bani umarnin gaggawar tashi in bar gidan karma ya dawo ya same ni yay min abin da zai zama sanadin bugawar zuciyata a yau, a karon farko naji bana son ganin ko da inuwarsa. haka na buɗe wadrobe ina ɗebo kayana, ina zubawa cikin akwatu ina magana tamkar zararriya.

"Me zan ce idan na koma gida? Na ce musu mijina ya ce in je gida sai ya neme ni?, bisa laifin me? da wanne ido zan kalle su in musu bayani? Hasbunallahu wani'imal wakil, Hubbi meyasa! Me na maka a rayuwa Hubbi?".

ina kuka sosai haka na gama haɗa kayana, na ɗauko hijabina zan saka wayata da ke kan madubi tayi ƙara, na rufe wardrobe ɗin na ƙarasa da sauri na ɗauki wayar don na shaida kiran Ummani daga ringtone ɗin da na saka mata na Uwa Uwa Mama me share min kukana.

sai da na saita kaina da danne yanayin da na ke ciki na ce,"Salamu alaikum Ummani, ina yini".

Daga can ɓangaren ta ce,"barkan ki dai Sa'ida, an yini lafiya, ya kike ke da mai gidan naki?."

na ce,"Lafiya lau Ummani, duk kuna lafiya?".

ta amsa,"lafiya lau, amma ya naji muryar taki kamar ba ki da lafiya."

na ce,"Ehh wallah Ummani na tashi da ciwon kai ne yau, yanzu na tashi a bacci ma shisa kika ji muryan nawa haka, dama ina cewa zuwa anjima zan kiraki".

na faɗi hakan ina dafe kaina yayin da sabbin hawaye masu zafin gaske ke zaryo min.

ta ce,"subhanallah to kin dai sha magani ko?".

na ce,"ehh na sha, shi ne ma naji daɗi ai".

ta ce,"to Allah ya sawwaƙe. daman maganar zuwa ƙauye zan miki na bikin ƴar gidan Kawu Musbahu, gobe ne tafiyar da safe in Allah ya kaimu, ga shi na ji ki babu lafiya sai dai ki haƙura kya je musu daga baya ko".

tamkar anyi min bushara da kujerar makka haka naji maganar Ummani, wani farin ciki ya lulluɓe ni har hakan na bayyana akan fuskata, cikin saurin maganar da ban taɓa yi ba na ce,"lahh ai ciwon kaine fa kawai Ummani, kuma na faɗa miki naji daɗi ma".

sautin murmushin manyancenta ya bayyana har ya taɓa zuciyata, ta ce"ke dai kawai za kiyi ƙarfin halin naki da kika saba, to Allah dai ya ƙara lafiya. sai ki faɗawa mijin naki, idan ya barki kin fito da sassafe to mu tafi tare, in bai barki ba kuma kya taho ke ɗaya tun da kuna da direba".

na ce,"ai kamar ma na sani muka yi maganar da shi ɗazu, da yake shima yana shirin tafiya za su koma dubai, kin san dama nayi miki magana an gama ginin ɗaya plaza ɗin da ya buɗe. sai na ke ce masa to daga biki kuma sai in ɗan yi kwanaki a gida ya ce babu matsala".

ta ce,"ah tou faɗuwa ma ta zo daidai da zama, shikenan to sai kin zo ɗin. kya ce masa ina masa Allah kiyaye".

da haka muka yi sallama ina mai farin ciki na samun damar da zan fake da ita ba tare da kowa ya san dalilin zaman da zanyi a gida ba bayan gama biki, wanda ina roƙon Allah yasa zuwa lokacin komai ya saisaita. sai dai kuma a gefe guda zuciyata cike fal da tarin fargaba da tsoro mara misaltuwa.
Cikin farin ciki na ci gaba da shirina, har da kayan da zan bayar a ƙauye duka na haɗa, ban san lokacin da zaman zai ɗauke ni ba tun da bai ce ga iyaka adadin kwanakin da ya bani ba, dalilin da yasa na tabbatar da na ɗauki duk abin da zan buƙata kenan. har wani ɓari na zuciyata ma na faɗa min wataƙila tafiyar da zanyi tafiya ce ba ta dawo ba, imma mutuwa ta ɗauke ni imma kuma sanadin zaman auren kenan. jikina naji ya mutu gaba ɗaya sai dai kuma ba wani jimawa naji wani ƙarfi ya ziyarci jikina na musamman, dan ma banda isassan lafiyar da ƙarfin zai tasiri sosai a jikina.

bayan duk na gama fitar da kayan can compound na dawo domin rufe ƙofar ɗakin, sai dai a lokacin da na ɗora hannu bisa hannun ƙofar zan jawo, idona ya maƙale akan cikin ɗakin na kasa ƙiftawa na wucewar mintuna uku. zuciyata ta matse, ƙirjina yay zafi, gabana yay mummunar faɗuwa, hankalina ya kai ƙololuwar tashi, ruwan hawayen da na tsayar na ce ba za su ƙara sauka ba a yau sai ga su tamkar an kunna famfo. cikin mutuwar jiki da fargaba na janyo ƙofar na rufe ina mai juya mata baya, yacca na ke sakkowa daga matakalen benen kamar marar lakka a jiki, kalamansa ne su ke maimaituwa cikin kaina na inje har sai randa ya neme ni, cikin raina sai na ke jin shikenan wannna tafiyar tafiya ce da ba zan ƙara waigowa na kalli wancan ɗakin a matsayin ɗakin aurena ba, sai na ke jin kamar ya furta min kalmomin saki ne kuma saki na har abadan ɗin da ba zamu ƙara rayuwa tare ba, na ke jin sai dai na fara amsa sunan tsohuwar matar Nazifi ba matar Nazifi ba.

sam bana wani gani da kyau na ƙarasa na ce da mai gadi ya tayani fidda kayan waje, idan an sami adaidata sahu ya taimaka ya taro min. kamar ya san abin da yake faruwa na ga jikinsa duk yay sanyi har ya gaza haƙurin furta min lafiya dai ko Hajiya?, na ɗaga masa kai ina riƙe yanayina da cewa,"ana biki ne a gida zanje in kwanaki".

anan bakin gate na tsaya ina jiran ya dawo daga samomin adaidaitar, shiru shiru babu labarinsa kawai na gaji na samu wasu yara na ce su ɗaukar min jakunkunan su kai min titi, muka dandale yanda zan biya su sannan su kai gaba ina biye da su a baya.
sai bayan zuwana titi na tuna da babu fa ko sisi a hannuna, mafi kusa na samu shagon p.o.s na je na ciri kuɗi dubu huɗu, kuɗin da Abbaa ya turo min ne jiya da daddare, banda Allah yasa ya turo min da ban san ya zan yi da tafiyar ba, dole sai dai in tafi a ƙasa don ba zan dai je gidanmu in ce a bani kuɗi zan bawa me machine ba, ko a rayuwar baya ban yi haka ba balle yanzu, ba zan iya tonawa kaina da mijina asiri ba.

na sallami yaran na tsaya nan jiran samun mota, na mance gaba ɗaya ban saka niƙabi ba ga zafin rana sai dukan fuskata ya ke. na tsayar da masu adaidaita sahu sun fi shida babu wanda ya tsaya, duk wanda na cewa makwarari sai ya ce ba can yay ba, a taƙaice dai sai da na shafe mintuna kusan sha biyar tsaye kafin na samu wani ya tsaya, shima bayan na gama yi masa kwatancen in da zai kaini sai yace kai ba zai shiga ciki ba, har yay gaba kuma sai ga shi ya dawo yana cewa in shigo.

zan tsaya ciniki ya ce ba matsala abun biya ba zai gagara ba muje kawai, da kansa ya taimaka ya saka min kayan a ciki, wasu ƴan mintuna su ka kawomu ƙofar gidanmu don tun da muka taho bai yi tsaye tsaye ba, in an tsayar da shi ba ya tsayawa, har na ce masa ya ƙara samun passenger ya ce a'a babu matsala yafi so ya sauke ni tukunna.
ya sakko min da kayana, Yaran da suke can ta gefen gidanmu na kira na roƙe su suka shigar min da kayan cikin gida, su ka barni ina ƙoƙarin baiwa mai adaidaita kuɗinsa, sai dai kafin ma na kai ga buɗe jakar naji ya tashi machine ɗin yana shirin tafiya.

dakatar da shi nayi da cewa,"ban baka kuɗin ba".

ya ɗan leƙo kai yana cewa,"Hajiya ai an biya".

"an biya?". na tambaya da mamaki. kafin na ƙara cewa,"kaman ya an biya Malam, ban baka kuɗi ba fa tun da muka taho kace ne in bari mu ƙaraso".

ya ce,"ehh tou Hajiya da kika tsayar da ni da farko nayi gaba, sai wani bawan Allah ya dakatar da ni ya ce in dawo na ɗauke ki, da ina ce masa ba zani ba gaskiya to kinga abin da ya bani shi ne dalilin dawowa na ɗauke ki, kuma daga sauke kin nan na tashi a aiki sai bayan kwana biyu kuma".

ya faɗa yana zaro farar envelop a aljihunsa ya buɗe ya nuna min ƴan dubu dubun da su ke ciki sabbi karrr masu yawa, daga ganinsu daga injin bugu sai hannun manajan da ya zuba su ciki, a iya ido adadin su kasan ba iya ƙirgen yatsun hannu ba ne sai an haɗa da na ƙafa.
mamaki ƙarara ya bayyana a fuskata, ƙwayar idona kuma na kallonsa da ayoyin tambayoyi da son tuhumarsa.

"ai wallahi Hajiya ban taɓa taka sa'a a rayuwata ba irin yau, ni dai naji daɗin ɗaukarki wallahi. ban san waye ba amma idan rabonsa ce ke Allah ya haɗaku domin ya ce kar in ma yi kuskuren shaida miki shi".

rai na haɗe na ce,"kai Malam ni fa matar aure ce, ko da ka ganni daga gidan mijina na zo gidanmu. kai kawai kaga mutum baka san da ga ina ba ya kama baka kuɗi ka karɓa, to ni da kuɗina don haka ga hakkinka nan, babu ruwana da kuɗin da wani ya baka".

yay ƴar dariya da cewa,"ah ban ga kin yi kama da matar aure ba gaskiya, kuɗinki kuma ko na karɓa ma wallahi sadaƙa zan miki da su, gwara ki ɗauka ki rage zafi kafin Alhajin Allah ya bayyana a gareki ki huta da hawa abin haya".

ko kusa ko alama tunanin Nazifi a lokacin bai zo cikin kaina ba, idan ma tunanin nasa ya zo ba zan kawo shi ya biya ba dan babu ta yanda za'ai ya ɗau wannan uban kuɗin ya bayar kawai kuɗin motar da bai wuce ɗari shida ba, abu sai ka ce a film ko littafi, ai ba hauka ake ba, kuɗin ba tsigarsu yake yi ba.
don haka tsaki naja dogo na wuce gida ina faman masifa akan irin ƴan rainin hankalin adaidaitar nan.

shi kuwa me adaidaita ya murɗa babur ɗinsa ya bar ƙofar gidan, tafe yake kawai idanunsa na haska masa hoton arniyar motar waccan mutumin, da shi kansa mutumin da kamarsa ta nuna tamkar sarki, ko ba sarki ba to ya ratsu cikin jinin sarauta, irin su ne zaka musu kallo ɗaya kasan da ba su taɓa sanin babu ba, haka ba su ƙyashin fiddawa su bayar. me ɗan sahu dai har ransa yaji mugun tausayin Sa'ida idan har mutumin yazo wajenta taƙi amince masa don yaga da gaske namijin aure ne.

ina shiga gida na tarar da Ummani a tsakar gida tana gyaran alayyawu, ta riƙe haɓa tana kallona ta ce, "Amma dai kuwa Allah ya shirye ki Sa'ida, haka sai da kika taho yanzu?."

yanayin fuskata kuma yasa ta ƙara cewa,"to ke da wa kuma daga zuwa sai ɓacin rai?".

dafe kai nayi ina zaunawa a kusa da ita na ce,"wani banzan me adaidaita sahu ne mara tunani da lissafi kawai".

ta ce da ni,"ai sai haƙuri, suyi haƙuri da mu muyi da su haka lamarin ya ke. sai ki saki ran naki haka kuma, ni ina zan wani farin ciki ina ganinki rai ɓace, ai sai kisa ni a damuwa".

jikinta na faɗa ina kwantar da kaina bisa kafaɗarta ina cewa,"Ummani nayi kewarki sosai wallahi, tun fa mutuwar Inna Talatu ko?". na faɗa ina shigewa jikinta kaman zan koma cikinta.

ta ce,"Kai jama'a, wai Sa'ida kam sai yaushe za ki girma ne ni kam, kita maƙalƙale ni kaman wacce bata bar shan nono ba? To ko dai cikin zan mayar da ke?"

ta faɗa cikin ƴar dariya tana mai tarairayo ni jikinta, yayin da farin cikin ganina ke lulluɓe da ita. murmushi nayi ina ƙara narkewa a jikinta ina jin wani irin tasirin natsuwa, so, ƙauna, salama, jin ƙai, na fitowa daga jikinta yana ratsa ilahirin nawa jikin.

na ƙara cewa,"Nayi kewar ki ne sosai Ummani, gaskiya mata muna ƙoƙari wallahi, in ba auren ba me zai nesantaka da ɗumin jikin mahaifiyarka har akai watanni da yawa".

Ummani ta ce,"to ya za'ai auren kenan, kuma ai ku godewa Allah ma da zamani ya canja, mu lokacin da akayi namu auren tsakaninmu da gida ai sai shekara shekara in dai ba da wani babban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login