Showing 24001 words to 27000 words out of 87761 words

Chapter 9 - ƘAYAR RUWA Book 1 HAUSA NOVEL

HALIMAHZ   

20 Dec 2024

6111

zan iya tashi, ka tambayesu har kwatanta hakan na yi naji ba zan iya ba, kai kanka ka san in ba lalura ba babu abin da zai kwantar da ni a ɗaki har wa yanzu duk kuwa halin da muke ciki, amma na rantse da Allah ban bari sun fita ba su ci komai ba saboda mugunta ko rashin so ba, Hubbi ban tsani yaranka ba, ban taɓa jin ina ƙin su ba balle har in ƙuduri cutar da su, Allah shahidi shi ne shaidata yanda zan so ɗan cikina haka na ke sonsu, Hubbi ƴaƴan ƴan'uwanka ne fa, kai kuma ɗin nan ina sonka, mijina ne kai, Hubbi don me zan ƙi abin da aka baka?, don Allah ka sassauta fushinki ka ke daina faɗin duk abin da ya zo bakinka...".

buge hannuna yay daga jikinsa yana ƙara faɗin,"shashasha kawai, bagidajiya wadda bata san hakkin yaro ba. sai ki laifi da an miki faɗa ki fashe da kuka, a hakan kike sona?, idan kina sona ai ba za ki wulaƙanta ƴan uwana ba, ba zaki ƙi yarana ba. kuma ki sani wallahi tallahi yanda kika azabtar da su da yunwa haka kema zan hukuntaki, Sa'ida sai kin yi matuƙar danasanin abin da kika aikata a yau, wawiya mara aiki da iliminta".

fita yay daga ɗakin yana ta surfa masifa, na daskare wuri ɗaya ina bin bayansa da ido, ƙirjina naji ya matuƙar yin nauyi, me na yiwa Hubbi a wannan rayuwar ne?, wanne kuskure na aikata masa da ban cancanci yafiyarsa ba?, mijina me kyan hali da nagarta ne, ta ko'ina amfani da yake da tarin ilimin addininsa, amma me ya sauya shi?.

ban san lokacin da na zamo daga gefen gadon ba gwiwoyina su ka dire a ƙasa, na fashe da matsanancin kuka. me yasa aurena zai tashi daga rayuwar farinciki ya juye zuwa rayuwar baƙin ciki?, mun auri juna ne don muna son juna, mun fuskanci ƙalubale da yawa tun daga haɗuwarmu har aurenmu, duk tarin ƙalubalen da muka fuskanta bamu taɓa ji a ranmu cewa zamu haƙura da juna ba haka har muka yi nasara, amma me ya kawo canjin a lokaci farat ɗaya haka?, lokacin da ya kamata ace munji daɗin rayuwarmu, mun dulmiya cikin kwanciyar hankali da natsuwa.

Haihuwa!, kalmar ta motsa da zuciyata, kenan yau da zan haihu shikenan komai zai sauya?, kowa zai koma sona tamkar a baya?, za'a daina tsangwamata da tashin hankali?, idan kuma ban haihu ba shikenan haka za'a ci gaba da tafiya?. zuciyata ce ta fara jujjuya tunanika, wa ya kamata in kira in shaida masa halin da na ke ciki?, wa zan sanarwa da cewa rayuwar aurena ta juya cikin tsananin baƙin ciki da ƙuncin da ban taɓa tsammani ba, wa zan kira ya lallashe ni ya bani haƙuri da shawara?.

mahaifiyata ce ta zo cikin kaina, sai dai ba zan taɓa iya kiranta in sanar mata da matsalar nan ba, ba zan iya faɗa mata matsalar gidan aurena ba, na ƙwammaci in zauna a hakan ko zan mutu in mutu, har kullum farin cikin iyayena da kwanciyar hankalinsu na ke so, saboda haka ba zan taɓa bari su san halin da na ke ciki ba.

kai na kifa a gefen gadon, idona a rumtse yake kalaman cin mutuncin Hubbi nata yawo cikin kaina, lokaci guda kuma wani lokaci ya haska a cikin idanuna, yayin da wasu kalamai na lokacin su ka haska tarr a cikin kaina, jinsu na ke suna amsawa a ƙoƙon kaina tamkar yanzu yake faɗar su.

_"na yi miki alƙawarin zan tsaya a tare da ke a kowanne irin yanayi, nayi miki alƙawari cewa duk wata matsala ta hanyarki ni zata fara fuskanta, na yi miki alƙawari zan ba ki kariya ta kowanne gefe, na yi miki alƙawari ba zan taɓa bari idanunki su yi hawaye ba, na yi miki alƙawari a kowacce rana zan yi ƙoƙarin dacewa da ke, ba zan juya miki baya ba, ba zan taɓa canja miki ba, nayi miki alƙawarin cire ki daga duk wani baƙin ciki, nayi miki alƙawari Sa'ida! daga yau da kika zamto matata, dukkan soyayyata, amanata da rayuwata naki ne ke ɗaya, ina sonki Sa'ida, alƙawarin dawwamammen farin ciki Habibty"._

waɗannan sune kalaman da yay min a ranar ɗaurin aurenmu, bayan ɗaurin aure san da suka zo gidanmu gaisuwar surukai, na same shi a ɗakin Yashaik kafin a gama kimtsa cikin gidan su shiga. lokacin da na shiga na tsaya na kasa zama wurin da yake min nuni saboda kunya, wanda hakan yasa shi tasowa ya tsaya gabana tare da kamo hannayena duka biyun ya saka cikin nasa ya haɗe, kaina na ƙasa a wannan lokacin amma haka ya ɗago fuskata da dogon hancinsa, ya tilasta min saka ƙwayar idona a tasa kafin ya shiga karanta min waɗancan kalaman fuskarsa na me washewa da dukkan murmushin farin ciki da jin daɗi gami da alfahari.

sabbin hawaye ne masu zafi suka shiga zubo min, a raina ina tambayar duk ina wannan tarin alƙawarin da yay min?, shin mantawa yay ko kuma fatali yay da su?. doguwar ajiyar zuciya na sauke tunawa da farkon rayuwar aurenmu, sai kawai na saki murmushi me ciwo, ko ba komai ai nayi farin ciki tare da shi ko ya ya ne, ina alfahari da iyaka wannan ma.
tsaida kukana na yi na miƙe na shiga banɗaki na wanko fuskata, na gyara jikina sannan na fita jiki a saɓule, tunanina me zan dafawa yaran cikin ƙanƙanen lokaci, amma me daɗi wanda zai gusar da rashin jin daɗinsu, abincin da su ke matuƙar so na tuna, wanda hakan yasa na sauka daga benen cikin karsashi, sai dai da zuwana ƙofar kitchen na murɗa handle naji ta a rufe, na zaga ta ɗaga ƙofar itama a rufe.
doguwar ajiyar zuciya na sauke, kenan da gaske ya ke akan furucinsa na zai hukunta ni akan barin ƴaƴansa da nayi da yunwa. yanda ban ba su sun ci na safe ba haka kenan nima yau zan wuni babu ci?, dama ana horo da yunwa?.
kan kujera na koma na zauna na rafka tagumi, jefi jefi sai na sa hannu in goge hawayen da ke sakko min, tunani na ke yi daban daban, sai dai akan kowanne na rasa irin warwarar da zan masa. na kalli agogo naga ƙarfe goma da minti sha biyar, kuma kaɗawar lokacin ya haɗe da ƙugin da cikina yay saboda tsabagen yunwa, dama banci na daren jiya ba, lokaci guda dukkan tunanina ya tsaya cak, take kuma nauyin kaina ya dawo naji yay bala'in sara min, nayi saurin dafewa ina mai rumtse ido tare da jinginar da kaina jikin kujera, wucewar daƙiƙu uku na miƙe jiki babu ƙwari ina matuƙar jin jiri, a daddafe da bango na fita daga falon zuwa farfajiyar gidan.

can ta bayan gidan na nufa wajen da shuke shuken fulawoyi su ke, na nemi manyan duwatsu da busassun itatuwan fulawa da aka ciccire na haɗa murhu, na gangaro durum na kawo shi bakin tagar kicin. takawa nayi na zura hannu ciki, da dabara na samu na buɗe murfin durowar sama da ƙyar tukunna na lalubo ashana, dama tagar da ɗan faɗinta da haka nayi nasarar ciro ƙaramar tukunya.
zuwa nayi na iza wuta na ɗora tukunyar, sannan na dawo na gangara durom ɗin zuwa tagar suto, shi dama ana iya shiga ta tagar don haka na shiga ta ciki na ɗebo macaronie da kayan sarrafata wajen girkawa, cikin sauri sauri na ke komai gudun kar mai gidan ya dawo.

a wurin me gadi na aro wuƙa da ce masa na nemi tawa na rasa, don haka yankan kayan miyan nayi tun da babu abin jajjage. nan da nan na tashi jalof ɗin macaronie, adu'a na ke tayi ta dahu da wuri har in samu na zuba akaiwa ƴan makaranta abinci tun da break biyu su ke fitowa dama, babu ƙaramin cooler da zan zuba musu abincin don haka ɗakina na koma dole na lalubo wani ƙaton flask me guda ɗaya, ashe da ranarsa da har ina cewa Kakarmu da ta bani bana so, a cikinsa na juye musu abincin na rage kaɗan wanda zan ci.

bayan na kammala haɗa musu komai ina sauri in fito in kaiwa Me gadi ya taimaka ya kai musu, isata bakin kofa in ɗaga labule na jiyo kamar tashin hayaniya daga compound, sai dai kafin nayi wani tunani akai aka cakumar min wuya.
tsoro yasa na ambaci sunan ilahu da ƙarfi, sai dai idona na sauka kan wacce ke damƙe da wuyana abin ya bani girgiza ni. Anty Aysha ce sai huci take tana hararata, gaban rigata na ƙara kallo in da ta cukume da kyau, kafin nayi magana Anty Aysha ta riga ni da cewa, "don bura'ubanki wacece ke?, wanne kalar jahilci ne cikin kanki?, uban me kike gadara da shi a cikin gidan nan da kike ganin kin isa ki yi kowanne kalar iskanci ki zauna lafiya?, to koma me kike ji da shi yau zan banbance miki tsakanin aya da tsakuwa, zan sauke miki kowanne kalar buyagi Sa'ida, tabbas yau za ki ciji yatsa kina me nadamar abin da kika aikata don kutumar ubanki".

baki sake na ke kallonta da maɗaukakin mamaki, ba kalaman ba ne su ka shige ni, zagin shi ya girgiza ni. ko ban kasance matar ƙaninta ba ina ganin ai babu dacewa ta danƙara min zagi na rashin ɗa'a irin haka. sai dai kafin na kai ga wani motsi Yaya da ta iso ta ɗauke ni da gigitaccen marin da ya kai ni kifewa ƙasa, sai dai nayi jarumtar riƙe kaina a tsaye.

kuma kafin zafin marin ya sakeni ta ƙara min wani ta ɗaya ɓarin, wanda a ruɗe na ɗago ina ƙoƙarin ƙwace riƙon da Anty Aysha tayi min inyi ta kaina.

ganin hakan Yaya tace,"Au ƙoƙarin ƙwacewa ma kike?, guduwa za ki?, To bara nayi miki dukan tsiya sai naga da wanne ƙarfin za ki ƙwace ki gudu, Sa'ida ai yanda kika kwantar min da Yarinya a asibiti kema sai na illataki wallahi".

tana faɗin hakan ta fara dukana, duk inda hannunta ya kai a jikina nan take duka kamar wacce ta samu ganga, ni kuma duk wannan bala'in da na ke ciki tunanina ba ya ga in ƙwaci kaina ko in ɗau matakin cin zarafin, a'a hankalina da tunanina na kan furucinta na cewa na kwantar mata da ƴa a asibiti, wacce ƴar?, mene dalilin kwanciyar?, kar dai sharri yaran su ka haɗa min?, waɗannan su ne tarin tambayoyin da ke cikin kaina kuma amsarsu kawai na ke da buƙata.

sai da na farga daga hallakanin da suke shirin yi tukunna na fara kiciniyar ƙwatar kaina, amma ina sun riƙe ni gam sai dukana su ke babu ta yanda za'ai na iya ƙwacewa kun san ance sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi.

"Yaya ki daki cikin shegiya tunda babu uwar komai a ciki sai kashi".

Anty Aysha ta faɗa tana kallon Yaya. Ai kuwa kamar Yaya na jiran tuni akan hakan ta dunƙule hannu ta daki cikina da ƙarfi. "Wayyo Allah!". na faɗa da ƙarfi jin azaba wacce ban taɓa jin irinta ba a cikina.

cikani Anty Aysha tayi ta duƙa ta ɗaga ƙafata nayi baya na kifa ƙasa, ta saka ƙafa ta dakar min kwankwaso, a wahalace na runtse ido ina kuka amma hakan baisa sun daina dukana ba. da dukkan iyawata na tattaro ɗan ƙarfina na ture su daga jikina, naja baya da sauri ina ɓoye kaina.
idonuna masu zubar da zazzafan hawaye ya tsaya cak akan Yaya wacce ke numfashin wahala tana girgiza, yanda take abin ba zaka taɓa sanyata cikin sahun manya mutane ba, ba ƙaramar mace ba ce, sai ƙwaƙwalwarta kawai da ke aiki da ƙarancin shekaru, zancen da na ke muku tana kan shekaru arba'in da ƴan kai ne.

"bagidajiya ƴar gidan ƙananun mutane, shashasha wacce bata ajiye komai ba. ke har kina da ikon hana ƴarmu abinci a cikin gidan ƙaninmu?, wawiya kawai, ba ki san da cewa ta fiki dajara da ƙima a idanun mai gidan ba?, ko mancewa ki kai da ana rabuwa da uwa a zauna da Ƴaƴa?...ko kuma ganin an zuba miki ido kina zaune ke kaɗai har yanzu cikin gidan nan shi ne kike son zuba iskancin da kike so. To ta ƙare wallahi, daga yau komai yazo ƙarshe, za ki gane kin hora ƴaƴanmu da yunwa, za ki tabbatar da bani da mutunci bani da kirki ko kaɗan. Kuma na rantse da Allah in kika sake wata cutar ta sami Atika sai na saka an ɓalla miki ƙafa dan ba zan kai ki police ba, sakawa zanyi kema a kashe ki dan uwarki da ubanki, azzaluma wacce bata san ciwon ƴaƴa ba".

Yaya ke wannan furucin da suke daidai da watsa ruwan zafi a jikina, kallo take min mai cike da tsana, yayin da ni kuma ke mata kallon da na kasa fassara shi. idona ya koma kan Anty Aisha da ke cewa,"saboda ba ki san darajar haihuwa ba, ba ki san zafin ɗaukar ciki ba, ba ki san wahalar laulayi ba dole ki bar mana yara babu abinci tun da abincin ubanki ne ya kawo. Mahaukaciya! jahila! juya! wacce da ita da namiji basu da banbanci, har gwara ma namiji zai yi ciki a ɗauka ke kuwa fa?, shekara takwas ba ɓatan wata balle ɓari"

Yaya ta kalleta da ce mata,"Aisha ƙyaleta mu wuce asibitin nan, hankalina na kan sanin halin da yaran nan ke ciki".

sai kuma ta kalle ni ta ƙara cewa,"dangin matsiyata gayyar tsiya, masu baƙin baya".

ta faɗa tana tana kama hannun Aunty Aisha su yi gaba, suka bar ni kwance ina kuka ina sauke numfashi a hankali cikin tsananin jin zafin ciwukan jikina.
da ƙyar na samu naja jikina har zuwa bakin ƙofa na ɗauki ledar abincin da na zuba, cikin sauri na fita ina kwaɗa kiran Yaya! Yaya!

su na gab da fita a gate su ka dakata, na ja ƙafa na ƙarasa gabansu ina miƙa musu da cewa,"na san nayi laifi, na kuma aikata babban kuskure, ban san me yake faruwa ba, kamar yanda ban san a halin da ƴaƴana su ke ciki ba, amma furucinku ya tabbatar min da su na cikin yanayi mara daɗi, ko kusa wallahi summa tallahi bada gangan na bar su suka fita basu ci komai ba, kuyi haƙuri don zatin Allah, tun da ku ka bamu yaran nan na ɗauke musu matsayin ni nayi naƙudarsu. duk wani dogon bayani da zan yi daga baya ne na sani, amma Yaya a gafarce ni don girman Allah, wannan abincinsu ne na break a tafi musu da shi kafin na zo asibitin".

ba wacce ta katse ni daga maganar da na ke, kamar yanda babu idon wacca ya fasa jifina da kallon banza, Anty Aisha ta warci ledar ta ciro flask ɗin, tana buɗewa ta watso min abincin a jikina Allah ya tsare bai zuba a fuskata ba, haka kuma bai zuba da yawa a jikina ba saboda saurin ja da baya da nayi.

"munafuka, kin dafa za ki kai gida ki bawa tsaffi su ci shi ne za ki fake da abincin yara, idan na su ne me ya hana ki basu su ci kafin tafiya, makira kawai".

cewar Anty Aisha, daga hakan kuma su ka buɗe ƙofar gate su ka fice. nayi tsaye ina ina kallon jikina da abincin da ke zube a ƙasa me uban yawa, wani ƙunci na daban ya daki zuciyata. maganar me gadi ta fargar da ni da yazo gabana yana cewa,"kiyi haƙuri ƴata, ga ruwa ki ɗauraye jikinki kar zafin tururin yaywa fatarki illa".

ina share hawaye na ce,"na gode Baba".
ya ƙara cewa da ni,"a ci gaba da haƙuri watarana sai labari".

juyawa nayi na koma ciki da gudu gudu. a falon na zube ban iya hawa sama ba.
_"Gayyar tsiya, dangin matsiyata, masu baƙin baya."_
kalaman Yaya na ƙarshe ya haska a kaina, nayi murmushin takaici ina hawaye, wai yau ni ake cewa dangin matsiyata, ba zan fasa faɗa ina nanatawa ba, tabbas ciki mai manta kyautar jiya!. 

Jingina nayi da kujera ina juya kaina da ke bala'in sarawa, ga cikina na min ciwo sosai wanda na san bayan zafin duka har da na yunwa ma. idanu na lumshe saboda ciwon da na ke ciki na kasa motsin kirki, jikina duk yay tsami, ban san adadin lokacin da na ɗauka ina kuka a wajan ba sai kiran sallar azahar naji. Ganin lokacin sallah yana sake tafiya sai naja jiki da ƙyar na shiga banɗakin falo, nayi alwala na fito nayi sallah a zaune kamar zan kifa haka na ke jina.

A kan sallayar na kwanta ina son yin bacci, ba don komai ba sai don in mance da abin da ya faru da kuma samun sauƙin ciwon jikina. ina riƙe da cikina ji nake kamar zan mutu saboda ciwon da yake min, ganin zan kashe kaina ya saka na tashi na lallaɓa na hau bene da ƙyar, shima da dafa bango har naje ɗaki. magani na ɗauka da niyar sha sai kuma na tuna babu abin da na ci, ko da na sha maganin ba wani aiki da zai min. horn ɗin mota na jiyo hakan yasa na ƙarasa ina dubawa, Hubbi na gani ya faka mota ya fito ya nufo cikin gidan, gabana yay mugun faɗuwar da ban taɓa ji yayi ba, na saki labulen na fita a ɗakin da sauri, jin takun hawowarsa benen yasa na tsaya har ya ƙaraso.

Kamar bai ga mutum ba ya wuce ya shiga ɗakinsa, nabi bayansa na same shi a tsaye a jikin durowa yana lalube da alama akwai abin da yake nema, jiki a sanyaye na ƙarasa ciki, har lokacin ciwon bakina bai daina jini ba.
murya a hankali cikin tsoro da shakkar abin da zai biyo baya na ce,"Hubbi."

Banza yayi min kamar ba halitta mai motsi ke magana ba, ya ɗauke kansa gefe ya cigaba da abin da yake yi.

"Hubbi".
na sake maimaitawa ina kallonsa, nan ma shiru.

gaban ƙafafunsa na duƙa ina riƙe ƙafarsa alamu na neman yafiya.
"Hubbi magana na ke maka fa, na san nayi maka laifi amma kayi haƙuri ka yafe min, kafi kowa sanin halina ba zan hana su Atika abinci haka kawai ba. Meye ribata in na hana su abinci?, wallahi ko wasu ƴaƴan ba zan hana abinci ba balle kuma su da su ke ƴaƴana".

magana ya fara,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login