Showing 72001 words to 75000 words out of 87761 words

Chapter 25 - ƘAYAR RUWA Book 1 HAUSA NOVEL

HALIMAHZ   

20 Dec 2024

6109

ga lahira, Anti ta shiga mata faɗan cewa ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, amma ƴar nan furrr taƙi tace ai tunda Nazifi ya zama ɗan bantan uba to kowa ma zai zama. Ni dai hmm kawai na ke cewa don na rasa abun faɗa kam, sai gabanin magriba kana muka yi haramar tafiya shima sai da na yi mata da gaske da ta ga na miƙe zanyi tafiyata.  Sanda muka koma gida ƴan taron biki duk an watse sai iya gayyarsu, mutan Abuja ma da su ka je ɗaurin aure an dawo don su muka sama a falon, kuma Safiyya bata bani damar tsayawa ba ta figen muka yi sama duk da ina ce mata bari naje ɗakinsa na duba ko ya dawo na masa sannu da zuwa.

Bayan munyi sallar magriba ta buɗe mana ledar gasashshiyar kazar da ta siya a hanya da gurasa da tsire, haka ta tilasta min ci da yawa, ba Safiyya ta tafi ba sai bayan sallar isha'i direban gidan Antinta ya zo ya ɗauketa, ta tafi tana ta roƙona da Allah akan kar na taka ƙafata zuwa ɗakin Nazifi a daren yau sai in har shi ya kawo kansa gare ni. Na so na yi yanda ta ce amma saina kasa natsuwa kwata kwata, haka na sakko jiki a sanyaye cikin raina ina tuna shi fa yanzu ba nawa ba ne ni kaɗai mijin mata biyu ne.
Ko da na shiga ɗakin nasa na same shi kan gado ya miƙe ƙafafu kunnensa maƙale da waya fuskarsa sai washewa take da wani irin murmushi me faɗin gaske, murmushin da ya bayyanar da dukkan hakoransa waje yana ayyana ainihin farin cikin da ruhi da gangar jikinsa su ke ciki. Zama nayi kan kujera daidai da saukar ƙwayar idona akan manya manyan kulolin abinci na gani na faɗa sama da guda biyar, sai kuma farantan da ke shaida har anci abinci tunda ga saura nan da aka bari har da su roman ganda manya manya, ba sai an faɗa ba wannan kam daga gidansu Amaryarsa ya taho da shi. Nayi saurin ɗauke idona a wajen na mayar kansa ina ji zuciyata na tafarfasa, ya ji sallamata haka kuma ya san da shigowar tawa amma tun duba ɗaya da yay min a wulaƙance sai ya watsar, nayi shiru sai a sannan ne na fahimci da wanda yake wayar, Amaryarsa ce tunda gashi nan har yana faɗa mata ba ita kaɗai ce a matse da wayewar gari ba shi kansa ya matsu, hakan yasa na kasa jurewa na miƙe na fita a sanyaye ina mai takaicin rashin zuciya irin tawa, da na bi maganar Safiyya da ban tarar da wannan wulaƙanci da cin fuskar ba, dama ai ba wata tsiyar naje yay min ba bangajiya zan masa na kuma tayasa murna, daren nan kam duk iya satar bacci bai yi nasara a kaina ba, haka nayi ta faman juyi da saƙe saƙe cikin raina har aka yi asuba, kuma sai bayan sallar bacci me nauyi ya kwashe ni.

Bani na farka ba sai ƙarfe goma da rabi, ina tashi nayi wanka na shirya cikin shiga me kyau, sai dai ko mai ban shafa a fuskata ba. Fita nayi na je ɗakin Iyam na gaisheta, ƴaƴan nata duk sun wuce sai Yaya kawai da sauran baƙinta na ƙauye don ko Ummaa ban gani ba, shi kuwa dama ban ma nufi hanyar ɗakinsa ba don gwara na kama kaina kafin ya kuma yaga ni. Yauma kamar jiya ni na gyara falon da yay mugun kaca kaca ka rantse bai taɓa ganin tsintsiya ba, a kaɗan ɗin lokaci wuri yay fes fes, na shiga kitchen dan ɗora abun kari shima nan na taradda shi an kaca kaca da shi an ɓata uban kwanuka, Allah ya gani sam ban iya ƙazanta ba balle na ɗauke kai na ce zan barwa waɗanda suka ɓata su gyara, balle na san ba gyarawar za su yi ba. Na tattara su duka na wanke su, sai bayan na gama na ɗora jallof na cous cous yanda zai isa har dare ban ɗora wani abincin ba, dan ba lallai idan na hau sama ba na sakko yau za su kawo amaryarsu bana son abunda zai ja min ɓacin rai.

Kammala aikina yay daidai da zuwan Safiyya kamar yanda tayi min alƙawari jiya cewar zata dawo yauma ta ɗebe min kewa. Tana ta hararata saboda na sakko nayi aiki muka hau sama, murnar ganinta a yau kam sai yafi min na jiya, saboda tafe take da takardar sakamakon gwajin da aka yi min jiya, wanda ya tabbatar da cewa lafiya ƙalau na ke bani da wata matsala, haihuwa lokacinta ne kawai bai zo ba.
Wannan albishir yasa naji kamar anyi min bushara da aljannah, sai lokacin hankalina ya kwanta don ko sanda Nazifi ya faɗa min cewar lafiya na ke ban yarda ba. Ai kuwa take na kira Ummani na shaida mata itama tayi murna tayi murna tare da adua to Allah ya kawo nan kusa.
Safiyya ce ta zaunar da ni gaban madubi tayi min kwalliya irin ta zamanin nan da ake yi, kasancewar ban taɓa shafa irin su foundation ɗin ba sai nayi wani kyau na masifa hancina ya ƙara tsayi, kayan da ta siya jiya ta damƙa min tace nawa ne, ba rasa suttura nayi ba haka ba rasa suttura masu tsada nayi ba amma sai naji kyautar ta zamar min ta musamman kuma tafi min dukkan sutturun da na ke da, nayi murna sosai, shaddar na saka wadda ta min masifar kyau, tayi min ɗauri na ture kaga tsiya, ni dai duk sai na rasa ma bakin magana don dawowa nayi tamkar bani ba, ashe ban sani ba haka na ke da masifar kyau, dama an ce in kana da kyau ka ƙara da wanka, ai kam adu'a iya adu'a nata zambaɗawa Safiyya tare da fatan ɗorewar amintarmu. Ta kira min Ummansu mu ka gaisa wacca itama ta ɗauki lokaci tana ce min,"Sa'ida kina jina".

Na ce,"Ehh Umma".

Ta ce,"Yauwa to ki buɗe kunne da kyau kiji ni, zama da kishiya ya banbanta da zamanki ke ɗaya da mijinki, duk yanda ki ka kai da danne kishinki wataran sai ranki ya sosu kin bayyana shi, haka sai kin matuƙar kauda kai daga kan rawar kansa, abin da zan ƙara maimaita miki shine ki riƙe adua, kyautatawa, girmamawa, ladabi da biyayya tsakaninki da mijinki da mahaifiyarsa. tsafta da caɓa ado gami da iya narka soyayya kar ki bar wata tayi miki zarra, idan kika riƙe waɗannan abubuwan ba boka babu Malam Sa'ida za ki kama miji a tafin hannu ki bar wata ta sakakken baki. Ina kuma shawartarki da yin tsafatataccen kishi bisa sunna ba tare da kin bi hanyar saɓawa mahallicinki ba, zaman kishi zaman gasa ne don kowaccenku so take tayi abin da zata fifita a wajen miji, don haka ki zauna ki karanta hanyar tattaro hankalin mijinku gare ki a ko da yaushe. Tsakaninki da kishiya gaisawa banda zaƙewar shiga lamuranta ko bata fuskar shiga naki lamuran, da zarar kin bada fuskar hakan rainin wayo zai samu mafaka, Ki kama mutuncinki da darajarki ta yadda cacar baki ko faɗa ba zai haɗaku ba don ba ajin mace da kimarta ba ne yin faɗa da kishiya, faɗa da kishiya shine babban abun kunya ga mace ki kuma janyo miji ya ke miki kallon mara wayewa. iya abin da zan ce miki kenan Allah ba ku zaman lafiya kema kuma ya azurtaki da haihuwa me albarka, ki kwantar da hankalinki komai lokaci ne, kar ki saka damuwa tunda har bincike ya tabbatar da baki da matsalar komai kina da lafiyar da zaki ɗau ciki har ki haife".

Na ce,"in sha Allah Umma za ku sameni mai aiki da nasiharku ba zan bada kunya ba, Na gode Allah ƙara muku lafiya da tsawancin kwana".
Na faɗa ina share hawayena.

Ta ce,"amin yasa na ɗauki jikina wataran. Idan kunyi waya da Mamar taki kyace ina gaisheta".

Muna zaune da Safiyya tana bani labarin irin wahalar da ta sha a karatu ban san ya akai ba kuka ya ƙwace min ba tare da na shirya masa ba, ina faɗa mata ni yanzu ban san ya zan ƙare ba a cikin gidan nan idan har Amaryar ta zo tunda har yana min gorin banda aikin yi kuma ilimina ba na kawo azo aji a gani ba. ga shi yau ina jin na gama karaya akan zan haihu duk da ƙarfafa zuciyata da na ke yi da ƙwarin gwiwar da kowa ke bani, amma ji na ke kaman na tsinke da lamarin don sai na ke ganin binciken likitocin ba haka ba ne. Ta dafa kafaɗata ta shiga kwantar min da hankali akan na daina damuwa sam, shi duk abin da ya faɗa min ya faɗa ne kawai don son ransa da kuma cin zarafi, haihuwa kuma zan haihu lokaci ne.

Turo ƙofar ɗakin yasa muka kai dubanmu ga wajen, Nazifi ya shigo cikin kwalliyarsa da alama fita zai yi, kuma da shigowan nasa kamar dama Safiyya a shirye take sai gani nayi ta ɗauki waya ta kara a kunne tana wayar ƙarya da juya baya karma ta nuna ta san ya shigo, shi kuma ya ƙame kamar an danna masa pause idonsa ko ƙifce babu akaina yana kallona tamkar bai taɓa sanina ba ko kamar yaga sabuwar halitta.

Murya a hankali na ce da shi,"ina kwana".
Maimakon amsa gaisuwar sai ce yay,"baƙuwa muka yi?". Ya faɗa da sigar zolaya saboda adon da yaga na ci.

Na kalle shi naga still kallona ya ke ya kasa sauke idonsa, ba sai ya fito fili ya faɗa ba amma har cikin ransa na yi masa kyau ta yanda ko bai faɗa ba fuskarsa ta faɗa.

"Kin yi kyau sosai, ashe kin iya kwalliya haka".
Hmm kawai na ce ina ce masa,"akwai wani abun ne?".

buɗar bakinsa zai yi magana sai ta maƙale, idonsa ya koma kan Safiyya yana kallonta da matuƙar mamaki kamar yanda nima mamakin ya cika ni ina dubanta laɓɓa a sake, na kasa gane wayar gaske take yi ko dai ta ƙaryan ce.

"Maimuna kema kin girgiza ashe, ni fa sai da na zo na ganewa idona sannan na tabbatar. Ke banda ma dai jaraba irin ta ɗa namiji banga abun da ya gani ya liƙewa wannan abar ba, ina ga farin bleaching ne ya ruɗe shi abinki da ɗan ƙauye da babu wayewa, ko kuma kuɗinta kin san butulu akwai son abin duniya. amma wallahi ba wai don Sa'ida tawa ba ce na rantse da Allah tafi Amaryar komai, indai fagen tsarin kyan halitta ne da cikar surar da namiji zai so to Sa'ida ta mata fintinkau. Sai dai kawai na gaya mata ta dage da adu'a Allah kawai zai saka mata tsakaninta da Nazifi, ke ni na taɓa ganin mutum mara halacci ma irinsa, baiwar Allahn nan ta aureka tun baka da anini kana yawon tura baro haka ta zauna da kai cikin tsanani amma da ya ke dai namiji ƙanin ajali ne kinga ai da yay kuɗi ya juya mata baya har yana ƙaro aure kuma yana faɗa mata haihuwa yake so na ce bar baƙin munafuki ƙarya yake yi algungumi, banda ma zanen ƙaddara ai wallahi Sa'ida ba ajin aurensa ba ce, matar manya ce ba ta ƙanan ƙauyawa da su ka fito gari kwanan ba shima ya sani, sai dai son zuciya irin nasa na butulalle...".
Nazifi yay mutuwar tsaye kawai yana kallon Safiyya da adadin mamakin da ba zai ƙirgu ba, ya sani dama ita tun farkon haɗuwarsa da Sa'ida ƴar adawarsa ce, amma bai tunanin ƙiyayar da take masa har tayi tsamarin da zata dinƙa faɗar maganganu irin haka akansa ba, shi kaɗai ya san me yake ji a game da kalaman nata kamar yanda bai san me zai iya cewa ba don baya da wani kalami a baki.

Ita kam hankalinta kwance take ci gaba da wayarta, tana kallon yanda Sa'ida ta haɗe rai tana hararta ta gefen ido tare da zungurinta amma tayi fiƙi taci gaba da maganarta ba zata yi shiru ba kam sai Nazifi ya harzuƙa ya nemi magana da ita tayi masa da hujja ko kuma ya bar ɗakin.

"Bari ke dai Maimuna ai ganin Allah ya haɗa shi da mace me haƙuri ne banda haka wannan iskancin ai bai isa yayi shi ba, to ita ɗin ce haƙurinta yay yawa, wallah ba ki ga duk yanda baƙin cikinsa da na ƴan uwansa yasa tabi ta rame ba, shi kuwa wannan shafaffen tumjin nasa ya ɗago, ni so na ke ma zuciya ta zugata ta tayar da aljanun ƙarya ta rufe butulalle a ɗaki tayi masa shegen dukan da ba zai kuma moruwa ba, kuma ta tursasa ya saketa sai ta barwa ɗaya matar ta zo tayi zaman jinya....".

Ransa ɓace ya juya ya fita fuuu kamar tashin iska, sai bayan fitarsa kiransa ya shigo wayata da cewar inje in sameshi, ban sami damar maganar da zanwa Safiyya ba na fita cikin hanzari cike da tsoron abin da zai faru. lokacin da na sakko Yaya da su Iyam na falo a zaune ganina yasa suka bini da ido hirarsu ta tsaya, Ko ba su faɗa ba na san sun kaɗu da yanda su ka ganni cikin kwalliya ta kece raini ga shi kuma shi ya sauko daga wajena dole lamarin ya jijjiga su. ina shiga ɗakinsa ya kama balbaleni da faɗa yana cewa in yi gaggawar sallamar Safiyya ta tafi ta bar masa gida idan ba haka ba kuwa ba zai kaffara ba minti goma ta ƙara sai dai na bita mu tafi tare. Ko da na dawo ɗaki na iske har ta miƙe tana ta dariya ranta fess ta ce ba sai na gaya mata saƙonsa ba ta tafi sai wani jiƙon kuma, nima dai na nuna mata bana son ta na magana irin haka akansa tace yanzu ta fara har sai Nazifi ya ɗaiɗaice zata sarara, haka ta wuce ta bar ni raina babu daɗi kuma cike da kewarta.

Da la'asar ƴan uwan Amarya su ka fara cika gida, ashe a al'adarsu ana zuwa gidan Amarya kafin a kawota yin wasu shagulgulan. lokacin ne nayi sabuwar kwalliya irin ta burgewa nasa danƙareren less ɗin wajen Safiyya, kwalliyar ɗaukar hankali da shaidawa miji da duk me farin ciki da auren ba gabana aurensu yake ba, har sai da nayi hoto na turawa Maman Yasmin na ce ta aika a nunawa Ummani.
Haka na kame kaina natsuwa ta shige ni, babu alamar damuwa tare da ni, ga wani daɗi da naji duk ramata sai ta ɓoye a kwalliyar da nayi, ɓangarensu kam sunata shagalinsu na rawar kiɗan ƙwarya da guɗe-guɗe da rawar al'adunsu. Da ƙarfe shida aka kawo Amarya, kamar yanda al'ada take na kai Amarya ga Uwargida don bada amana haka aka buƙaci da naje na ce da wadda suka aiko a hayo sama nan ne ɗakina, Iyam ta ƙara dawo da me aiken in sauka na ce da ƴar aiken kar ta ƙara zuwar min, haka aka kaɗa aka raya naƙi sauka sai gasu don kansu sun hayo anata faman guɗa, dama na san Iyam ce zata ce dole sai dai ni na sauka na samesu tunda ai su sun san abin da ya dace duk da ban san waɗanna kalar mutane ba ne. Aka shigo da ita ɗakin ina daga zaune kan gado su kuma suka zauna ƙasan carpet. ganin duk iyaye ne na gaida su cikin ladabi suma kuma suka amsa min fuska a sake, ganin da arziƙi da mutunci su ka zo na ba su fuska, nan wata dattijuwa ina ga ita ce Yayar Babanta suka shiga mana nasiha suna cewa ga amanarsu.

Cikin sanyi jiki na miƙa mata hannu muka yi musabaha ina cewa,"ina fatan za ki bani haɗin kai wajen ganin mun zauna lafiya tare da zama kan huɗubar da aka mana yanzu ni da ke".

Ta bani hannu muka gaisa tana shaida min zata ba ni haɗin kai. Da haka su ka yi sallama kuma suka tafi.
Kafin wani lokaci kuma gida yay tsit kowa ya kama gabansa sai bayan isha'i da abokansa da ƙawayenta suka wuce bayan an gama siyan baki.

*Ƙarfe tara na dare.*
Yayan Shago shi Malam ya wakilta a madadinsa na uba akan ya zo yay mana nasiha ni da abokiyar zamana. Haka kuma a gabanmu Malam ɗin ya kira Nazifi yay masa faɗa sosai akan ya kwatanta adalci kar yay saken da ranar lahira zai tashi sahun maza masu shanyewar ɓarin jiki.
Bayan tafiyar Yayan Shago ni da ita da Nazifi muka shiga ɗakin Iyam inda itama tayi nata daidai gwargwado duk da yawancin maganganunta togaciya ne ake yi min. sai dai fa anan na gane tabbas za su janyota jikinsu su mayarta da ita ƴar lele ta gaban goshi, don haka sai abin da na ji na gani kawai amma zan jure sai dai ba zan ɗauka komai ba kamar a baya.

Sanda na koma ɗaki Ina shirin kwanciyar bacci wayata ta ɗauki ƙara, ban waiwayi kanta ba sanin me kiran daga sautin ringtone, bayan wasu mintuna sai ga shi da kansa ya shigo.
Kallo ɗaya na masa na mayar da kaina ƙasa ina ci gaba da cire yari da sarƙar jikina. ganin yanda na bawa iska a jiyarsa a ƙufule ya kama masifa yana faɗin,"Wanne irin wulaƙanci ne kina jin kirana ba za ki ɗaga ba?".

Na kalle shi na ce,"ikon lillahi to ai ban sani ba wayar na silent".

Ya ƙara hawa,"to ban hanaki saka waya a silent ba, kika san wa zai nemeki ko abin da za'a faɗa miki".

Nayi shiru ban ce komai ba, don na ƙudirci ni kam na daina basa haƙuri akan wani laifi dan na lura hakan ne ke basa damar ƙara cin mutuncina son ransa, ya gama faɗan kana yace,"ki fito ki sameni a ɗaki".

Yana juyawa zai fita na ce,"zan kwanta ne fa".
Wani wawan kallo ya yarfe min tare da cewa,"ranki zai yi mugun ɓaci".

"to wanne ɗakin?".
"zan kai sabuwar matata ne tsohon ɗaki? Malama nan ɗakin sama za ki sameni".

Ƙasa da murya na ce,"Daga baya kenan anyi sadaƙa da karuwa, baka ajeta sabon ɗaki ba ai ka ajeta tsohon gida ko".

Ya jini sarai don ina kallon yacca ya watsa min mugun kallo, na harari bayansa kafin na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login