Showing 18001 words to 21000 words out of 87761 words

Chapter 7 - ƘAYAR RUWA Book 1 HAUSA NOVEL

HALIMAHZ   

20 Dec 2024

6101

hutu za su zo?".

"iyayensu sun bar min su halak malak, kinga kuwa ba hutu zai kawo su ba. zan koma Babansu ke kuma Mamarsu, sai ki shirya tarbar Ƴaƴan da aka ba ki".
Ƴaƴan da aka ba ki! kalmar ta ƙarshe ta daki ƙirjina. Rumana da Atika, gaba ɗayansu ba su wuce shekaru takwas ba, yaran ba su kunya ga rashin ji shisa jininsu ya zo ɗaya, ko iyayensu kuka su ke da halinsu, shi ne ni kuma yanzu zai ce zai ɗauko min su in riƙe a wannan sanyin halin nawa?, salon wataran su fusatani in sauke musu fushina in ƙara baƙin jini, dama ya lafiyar kura bare an taɓota. na san dole akwai wata a ƙasa, sai dai ina roƙon Allah ya ɗora ni a kansu, ya kuma sauya duk wata baƙar manufa da aka ƙulla akan hakan.

murmushi na ƙaƙalo na ce da shi,"ai ko dai muna godiya matuƙa, Allah taya mu ruƙo, naji daɗi sosai, ko ba komai ma rage kewa".

na faɗa ina nuna jin daɗin da bai kai har zuci ba, domin cike na ke da fargabar rayuwarmu tare da yaran.

bai ce da ni komai ba yay shiru, na sauke ajiyar zuciya na fita daga ɗakin. ɗakina na koma na canja kaya, dama a falo na bar jakata da wayata, kuma da zuwan nawa na tarar da kiran Ummani, sai naji gabana ya faɗi ganin miscalls har guda biyar, take na fara tunanin anya lafiya don bata taɓa min miscalls irin haka ba, Ummani duk in da ta kira waya sau biyu ba'a ɗaga ba haƙura take yi, sai tace bata san uzurin mutum ba, idan ya gani zai biyo baya.

zama na yi kan kujera jiki na rawa na bi bayan kiran, sai dai ko da kiran ya tafi a lokacin kamfani ke shaida min bani da kati. ƙaramin tsaki nayi na ƙorafi tuna fa ashe tun shekeranjiya muna waya da matar Yashaik katin ya ƙare.
ina zaunen Hubbi ya fito, ina kallonsa ɓacin ran hana ni zuwa makaranta ya ƙaru, na kawar kawai na kasa share shi saboda ina so ya bani aron wayarsa. cikin shakkar masa magana na ce,"Hubbi don Allah aron wayarka in kira Ummani".

yana zama kan kujera ya ce min,"me ya sami taki?".

"babu kati".

har zai miƙo min wayar tasa sai kuma ya fasa ya ce,"bari in saka miki katin, wanne layin?".

"Airtel ɗin".

cikin wasu ƴan sakanni sai ga saƙon katin ɗari biyar ya shigo, nayi masa godiya sosai. na danna lambar Ummani na kira sai dai haka ta gama ringinga har sau biyu ba'a ɗaga ba. take gabana ya tsananta faɗuwa, ban san lokacin da nayi mazauni a gefen Hubbi ba ina damƙar gefen rigarsa.

"lafiya?".

a ruɗe kamar zanyi kuka na ce masa,"bata ɗaga wayar ba ne, kuma kaga miscall ɗinta biyar na tarar".

ganin yacca jikina ya ɗauki ɓari ya karɓi wayar daga hannuna, yana ƙoƙarin ƙara kiran sai ga kiran Hindatu na shigowa. ya ɗaga ya miƙo min amma sai na kasa karɓa don ban san me kunnuwana za su jiye min ba. shi ya amsa kiran sai dai maimakon muryar Hindatu naji muryar Ummani na cewa,"Sa'ida ina hanya ne shiyasa ban ɗaga ba, kuma na shigo gidan babu kati a wayar sai na ari ta Hindatu".

wata wawiyar ajiyar zuciya na sauke ina hamdala ga ubangiji, yayin da Hubbi su ka shiga gaisawa da ita yana shaida mata rikicwar da nayi akan rashin ɗaga kiran nata, bayan sun gama ƴar hirarsu ya miƙo min yana murmushin leɓe tare da tsokanata, wanda hakan ni kuma yasa raina sanyi, domin rabona da ganin annuri a fuskarsa har na manta balle kuma murmushi irin haka.
cikin wani irin jin daɗi mara misaltuwa mu ke waya da mahaifiyata, kira kawai tayi taji ya muke, ashe ma ko da ta bar min miscalls da yawa ba ita tayi kiran ba Yahanasu ta bawa, ita kuma dama bata iya kiran hankali ba, kusan kullum sai Abba yay mata faɗa akan hakan. muna wayar naji duk damuwata ta gushe, tana ta bani labarai masu daɗi, ni kuma ba ni da wani labari da zan bata wanda zai sanyata farin ciki, sai da naji muryarta ta fara sauyawa wadda ke shaida min tana ƙoƙarin gano cewar ina cikin matsala ne, sai nayi saurin gusar da tunanin hakan a ranta nima na bata labarin su Atika da aka bani, ina shaida mata cewar ma yau za a kawo su, aiko farin ciki kamar tayi me, taji min daɗi sosai tana ta yiwa su Yaya godiya da shi albarka, ta ce ma na bawa Hubbi shima tayi masa murna, ni kuma tayi min nasiha sosai a game da ruƙon yaran. sai kuma kawai naji ta koma ambaton wannan kyauta ce daga Allah na sameta ya bani ta silar wasu, na riƙe ƴaƴana da amana kar in cutar da su, yarda da aminta cewar zan kula da su yasa har iyayen yaran suka bamu duk da cewar sun yi domin ɗan uwansu ne, amma duk da haka don suna da yaƙinin matarsa mutuniyar arziƙi ce yasa su ka ba shi.

nasihohinta su ka karayar min da zuciya sosai tun ma inji tana ambaton ƴaƴanki, sai na dinga jin wani irin yanayi na tsarga min a dukka jikina, haka zuciyata ta dinga motsawa, ban san ma ta yanda zan kwatanta abin da na ke ji ba a tare da ni. hawaye naji na sakko min, nasiharta ta ƙarshe abin da tace min,"ki so su tamkar ke kika yi naƙudarsu, kar ki cutar da su, kar ki dinƙa musu kallon ba ke kika haife su ba, ki kuma yi haƙuri da duk halinsu domin ko ɗan da ka haifa sai kayi haƙuri da shi, Allah ya tayaki ruƙo ya albarkaci zuri'a, idan kina da rabo kema Allah ya kawo lokacin muna raye".

da haka muka yi sallama da ita, kuka sosai na saki, sama sama Hubbi ke lallashina da ike ma yaji duk wayar tamu. haka na miƙe ina jina wani iri na shiga aikin tarbar ƴaƴana, har na hau sama zan fara gyara musu ɗakinsu sai kuma na ga dai gwara in fara ɗora abincin. na sakko na shiga kitchen.

ba ni na gama girki ba sai azahar duk da cewa da wuri na ɗora, to amma da yake dashishi ne yafi dambu wahala shiyasa na jima. ina kitchen ɗin ne na ke jiyo kamar tashin hayaniya daga falo, na wanke hannuna na fita cikin sauri.

tsaye na tarar da su Anty Aisha. da fara'ata na ke gaisheta, ta amsa min babu yabo babu fallasa. hannu na buɗewa su Rumana ina murmushin jin daɗi, jikina su ka shige ina rungume su tsam. ba tare da sani ba naji saukar hawaye a kumatuna, na janye su a jikina muna gaisawa da su, yaran suma sai murna su ke yi, dama dai in dai yara ne suna son zuwan gidan Yaya Ƙarami.

Anty Aisha ta ce,"ce na ke gidan ma ba kowa da mu ke ta sallama ba'a amsa ba, wannan ai sai a shigo ayi sata ba ki san anyi ba".

shirunta ya haɗe da sakkowar Yaya daga saman bene, tana watsan wani kallon banza ta ce,"da kina ciki amma kina jin mutane kika kasa fitowa".

"wallahi Yaya banji ba, da yake na kunna radiyo ne ina girki. sannunku da zuwa".

"yauwa". ta amsa a daƙile kafin ta ƙara cewa,"Baban yaran nan ya ce ɗakinsu na sama, na hau da kayansu kuma naga ba wani ɗaki gyararre".

cikin fargaba na ce,"ehh ɗakin kusa da nawa ne na su, aikin da na ke yi ne ma yasa ban samu na gyara musun ba. da ike za'a kawo gadajensu to su ma masu kawowar shiru naga basu zo ba".

Anty Aisha ta ce,"gyara ya hau kanmu kenan, to bara muje mu gyara musu...".

na yi saurin tarar numfashinta da cewa,"haba Anty Aisha ban isa ba, saboda su wallahi na ce gwara in gama dafa abincin. amma ai nama gama yanzu zan je in gyara musu".

ta wuce ni tana faɗin,"a'a gwara dai kiyi abin da kika saba ki dafa kici ki kwanta. ni ai bana iya tafiya in bar su haka ban ga sun sanya haƙarƙarinsu a makwanci ba, ba zan samu sukuni ba sam, ba da sauƙi nayi naƙudar ba, don ma dai Nazifi ne ban da haka ai wallahi da ƴata zan juya. ka yi sadaukarwar abin da ka haifa sukuntum guda kuma tun ba a je ko ina ba an nuna maka kulawa zata yi wuya, ko da ya ke sanin ciwon ɗa sai wanda ya haifa. Yaya ni nayi nan".

zuciyata ta matse sosai da zafi, na mayar da ruwan hawayen da ya cika idona, ban iya cewa komai ba, Yaya ta bi bayanta su ka haye saman su ka bar ni nan da yaran. na maida kallona ga yaran da ke tsaye a gabana, na dafa kafaɗunsu ina ƙaƙalo murmushi na ce,"yaran albarka in zuba muku abinci?".

Atika ce ta ce,"Matar Yaya Ƙarami me kika dafa?".

na kama kumatunta ina cewa,"abu me daɗi, har sai kunnenki yay rawa".

su ka ɗanyi dariya Rumana na cewa,"ferfesun kaji?".

kai na gyaɗa na ce,"ehh har da shi, sai kuma dashishi".

Rumana na tsalle ta ce,"irin wanda Ummaa ke yi?".

na ɗaga mata kai tabbacin haka. duk ɗin su suka kama murna, ina riƙe da hannayensu muka wuce kitchen. a tray na zuba musu na sanyo musu ferfesun naman kazar a bowl, su ka taya ni ɗauko wasu muka fito, nan kan carpet na ajiye musu su ka zauna su ka fara ci ni kuma na juya kitchen ɗin don zubowa su Yaya na su.

kiran Hubbi ya shigo wayata na ɗaga ya ke shaida min ga masu furnitures ɗin nan sun zo. na fita na hau saman na shaidawa su Yaya, sai sannan na ke ƙara ganin ashe ma basu kaɗai ba ne har da nasu baƙin wanda su ka zo da su suyi musu gyaran. cikin su biyun dai babu wacca ta tanka min bayan waɗancan da su ka gaishe ni. na juyo na sakko ina faɗawa me gadi yaywa ma'aikatan iso, ai na fita hakkinsu tun da na sanar musu za'a shigo.

ina ɗakin Hubbi na jiyo muryar Yaya na kwakwazon faɗa,"mene haka na ke ganinku zaune a ƙasa kamar wasu almajirai, don me Nazifin ya siyo wancan dining ɗin ya ajiye, ko dama na kwalliya ne?, kai ku tashi ku koma can ku ci abinciku, kar a ƙara baku abinci ace ku zauna kan kafet ku ci. ba baƙi ba ne ku, nan gidanku ne gidan Babanku, kuyi yanda kuke so yanda ku ka ga dama kar ku ji shakkar yin komai, duk abin da ku ke so kuyi magana da Babanku, idan Antyn tayi muku wani mugun abun ku dinga faɗa masa kun ji ko".

sai kuma Anty Aisha ta ɗora da faɗin,"umm ni dai Yaya ban da kin ce wallahi yaran nan ba za su zauna ba. ji fa don Allah yanda aka barsu su kaɗai a falo kamar wasu marayu, wallahi ko baƙo aka yi sai ya ce ƴaƴan ruƙo ne bana gida ba, don an bambamta ƙiri ƙiri. to ni dai har ga Allah ina ganin wani canji da ban gamsu da shi ba zan zo in ɗauke yarinyata, ba zan cutar da kaina ba akan yiwa ƙanina kara".

da babbar murya Yaya ta ƙwala min kira, kamar wacca aka hankaɗo daga ɗakin sai ga ni na fito jiki sai ɓari ya ke yi. a dabarbarce na ce,"kun sauko, ga abincin...".

"ke dilla can dakata banza mara mutunci, ba yunwatattu ba ne mu, da fari ma in tambaye ki, nan gidan waye?".

kaina a ƙasa murya na sarƙewa na ce,"gidan aurena".

tayi wani makirin murmushi da sake cewa,"to gyara zancenki, domin ko yanzu ba sai anjima ba kina iya barin gidan nan ki tafi a fanko, nan gidan Nazifi ne, Nazifi kuma ƙanina ne, ba ƴan uba mu ka haɗa ba uwa ɗaya uba ɗaya tafi gaban wasa, duk abin da yake mallakina yana da iko da shi kamar yanda duk mallakinsa ina da iko da shi. soyayyar da mu ke yi masa da tausayinsa yasa mu ka ɗauki ƴaƴanmu mu ka ba shi, wannan yaran da kike gani ba bare ba ne yanzu, ba ki da ikon kallonsu ki ce nan ba gidan ubansu ba ne balle kiyi musu iyaka da shi, yanzu Nazifi ne uwarsu ubansu, su kuma ko yau Nazifi ya faɗi ya mutu sun zama magadansa. saboda haka kinga kuwa sun fi ƙarfin ki ci mutuncinsu, ba marayu ba ne ba ƴaƴan kishiya ba ne ba kuma ƴaƴan tsintuwa ba ne. ko da kika ganki matar gida ba wai ke aka bawa su ba, mai gidan aka bawa, don haka ki tsaya iyaka matsayinki".

ni dai take takensu da na lura yasa naja baki ban ce kanzil ba, don haƙurin ma idan na bayar zai iya zama wata rigimar, ƙarshe ma ƙanin na su ya dawo su haɗa masa ƙarya da gaskiya, shima ya juye min nasa rashin mutuncin. yaran su ka tashi daga inda su ke suka bi bayan budurwar da Yaya tasa ta kwashe abincin nasu ta kai musu kan dining, can su ka ci gaba da cin abincinsu. yayin da su kuma su ka koma saman don ƙarasa gyara ɗakin yaran.
ni dai tun da nayi komawata ɗaki ban ƙara fitowa ba, ina jin duk wani kai komo na su da su ke yi, ba wasu yawa gare su ba amma yanda ka san masu jeran kayan amarya duk sun cika gidan da hayaniya. qur'ani na ɗauka ina karantawa don shi zai mantar da ni babinsu, sai bayan sallar la'asar na daina jin motsi, a sannan ne na fito na lura da sun tafi, tafiyar da ko arziƙin sallama ban samu ba.

ɗakin yaran na buɗe na leƙa, zaune na gansu kan gado ɗaya suna kallo. Atika tayi murmushi da ganin nawa ita kuwa ɗayar ta haɗe rai tana juyar da fuska gefe.
na ƙarasa wajen na su, ɗakin na su yay kyau, gadon yara ne guda biyu aka saka kowacce da nata, sai drowern kayansu ma kowacce da nata, ɗakin ya burgeni sosai kam dan dama in ta ɓangaren gyaran gayu ne Anty Aisha ba daga nan ba, zama nayi cikinsu ina masu hira wanda har sai da Rumana ta saki ranta, dama ita ce me bakin magana, nan kuma aka shiga bani labarin ƙawayen makaranta da malamarsu me sa kamun kunne, har tana faɗa min tun da sun dawo nan ga makarantar da zan ce Yaya Ƙarami ya saka su.

a haka Hubbinya dawo ya same mu, annurin fuskarsa kaɗai ya shaida min yana cike da tsananin farin ciki, sai naji tausayinsa duk ya kama ni, ya kenan yau in ace ɗansa ne na cikinsa?, hannu na kai saman cikina ina rufe idanuwana tare da roƙon Allah ya azurtamu da haihuwa kafin mutuwa.
farin cikinsa ya kasa ɓoyuwa, abin da ya siyo musu ya basu suma sai murna su ke yi, wayarsa ya ɗauko ya kira Yaya yana ƙara yi mata godiya da alkhairinta gare shi, Anty Aisha ma ya kirata daga baya. ya tambayi yaren sun ci abinci suka ce masa ehh, yace to su taso suje ɗakinsa, a tare muka fita gaba ɗaya muka bi shi, haka naci albarkacin yaran walwalarsa gareni ta dawo, mu ka ta hira kamar ba shi ba da ya canja ƴan kwanaki, bini bini ya tambayeni me ya kamata a siyawa yaran, ni dai abin da na fara cewa shi ne akai su makaranta da wuri gudun kar ayi musu nisa a karatunsu.

bayan ƴan kwanaki da safe na fito a wanka, turus nayi ganin Hubbi ya shigo ɗakin wanda rabonsa da ɗakina har na manta. kallonsa na tsaya yi wanda shima ya ke bina da kallo, to da yake dai tun zuwan su Atika ya ɗan sakko tsoronsa ya ragu a raina, muryata a hankali na ce,"ina kwana".

ciki ya ƙaraso yana zama bakin gado. "kin tashi lafiya".
"lafiya lau, mun je ɗakin ai na tarar baka tashi ba. na ɗauki ɗari biyu a wallet na bawa su Rumana kuɗin makaranta".

na ƙarasa gaban madubi na ɗauko takarda ƙarama na miƙa masa ina daɗa cewa,"jiya aka basu a makaranta wai sun manta ba su baka ba".

ya kalli takarda yana cewa,"ta mece?".

"ban duba ba".

karɓa yay ya duba ya ajiyeta. sai kuma ya kishingiɗa da gadon yana danna wayarsa. ni dai tun fitowata daga wankan na ke jin tasirin kallonsa na shiga jikina. tun da aka bamu yaran nan naga ya dawo hayyacinsa, kuma alamunsa sun nuna ya gaji da ƙauracewa junanmu, so ya ke ya kasance da ni sai dai ni ɗin kuma na ƙi basa dama da fuska, don ko jiya da naga take takensa na agwiwa ya ke ɗaki na gudo.

yi nayi tamkar na mance da shi a ɗakin, na buɗe wadrobe na ɗebo kayan da zan saka, sannan na ƙarasa na zauna kan kujerar madubi, ta cikin madubi na hasko shi idanuwansa sun kafe a kaina. cikin natsuwa na yin komai nawa a hankali na ɗauko man shafawa ina shafawa, tun da na shafa humra na hasko ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya. na ƙarasa kimtsa jikina da turaruka cikin salo na jan hankali, ina gamawa na wuce zan saka kayana sai naji muryarsa a kasalance yana cewa.

"zo".
ɗago ido nayi na kallesa naga yanayinsa duk ya sauya. rigar nayi ƙoƙarin sakawa ya sake dakatar da ni da cewa,"ki zo na ce fa".

ina ɓata fuska na ce,"Hubbi bari na ƙarasa saka rigar...".

sai da na saka sannan na je wurin nasa, ya ɗago fuskata yana kallona ya ce,"Habibty fushi kike da ni?".

kai tsaye na ɗaga masa kai, sai kuma hawaye ya sakko min. kwanto kaina yay saman kafaɗarsa da cewa,"ba kya kewata?".

cikin muryar kuka na ce,"idan ma nayi kewar taka ya zanyi Hubbi, ka mayarshe ni tamkar ba matarka ta so ba, ka ƙi faɗa min dalilinka na ƙaurace min, duk na baka haƙuri ka ƙi haƙura, ban san laifin da nayi ba ka daina sona".

ya zago da hannayensa ta ƙuguna ya ce,"to kiyi haƙuri na san na miki ba daidai ba, afuwan kin ji". yay maganar ƙasa ƙasa da muryar lallashi.

na ƙara cewa,"to me yasa hakan Hubbi?".

numfashi ya sauke ya ce,"saboda ina so inga na sami ɗa sai dai ke kuma shiru, naga kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login