Showing 39001 words to 42000 words out of 87761 words

Chapter 14 - ƘAYAR RUWA Book 1 HAUSA NOVEL

HALIMAHZ   

20 Dec 2024

6108

bashi.
********
na fito daga wanka na saka kaya, ina tsaye na kasa fita sai saƙa da warwara na ke yi, Sauda ta shigo ɗakin tana cewa,"wai ba ki shirya ba? kin san fa yacca abin hawa yake ga shi har biyar da rabi saura, kar muna bakin titi su Abbaa su dawo mu sha faɗa, naga kamar ma ba ki son tafiyar".

ba tare da ta lura ba na share hawayena, a sanyaye ina murmushin dole nace mata,"ke kin raina gida ne, ni in da za'a barni ma ai shekara zanyi".

tana dariya ta ce,"cabɗi abinda ba zai yiwu ba kenan. bara na ɗauko mayafina". ta faɗa tana juyawa ta fita.

daga tsakar gida na jiyo hayaniyar su Walida, ko me su ke wa murna oho ina dai jiyo su sama sama da Ummani. gyalena na ɗauko na yafa daidai kuma da ɗaga labulen ɗakin da Ummani tayi tana shigowa ciki.

"kin gama shirin?".
"ehh na gama, a samo almajirai su fitar min da su kin san waɗancan marasa kunyar ba taya ni za su yi ba". ina nufin su Asad da Khaleel ƴaƴan wurin Baba Tijjani.

tana ta kallona ta ce,"sai kuma ga mijinki ya zo ɗaukar ki".

Da mamaki na kalleta nace,"Mijin wa?."
ta ce,"mijinki mana, ga shi can a waje yana jiranki. ya jido kayan zaƙi ya bawa yara har da kuɗi, Walida dai ta ce cewa yay ta zo ta kamo hannunki ta kai ki zai bar mata motarsa".

da wani mamakin ƙarara a fuskata na sake cewa,"Wai da gaske Ummani?".

"A'a da wasa. Malama je ki dawo ki kwashi kayanki ki wuce ki tafi gidanki lada ya isa".

"Ummani yaran nan ƙarya su ke yi fa, a halin nan dai Nazifi bai zuwa gidan nan balle har ya ce ɗaukana ya zo yi".

"to ai sai kije ki duba idan ba shi ɗin ba ne shikenan, idan shi ne kuma sai kiyi murna".
ta faɗa tana fita. ta barni da bin ta da kallo zuciyata na harbawa cike da mamaki gami da tsoron zuwansa.

mayafin na mayar na ɗauki Hijabi na saka na fita jiki a mace. Yana zaune cikin mota ya hango fitowarta, ya sauke numfashi ji yake kamar an cike masa wani gurbin da ya jima da yin rami a cikin zuciyarsa, a hankali yake ganin takunta zuciyarsa na motsawa, sam ya kasa ɗauke ido daga kanta domin kuwa gani yayi kamar an canja ta, kwana nawa dudu bai ganta ba amma har ta isa ƙara yin kyau da cika haka?, wato ita hankalinta kwance yake ma, shi yana can rashinta a gidan da matsalar da yake ciki sun hana shi sakat.

ko da isa gaban motar sai na tsaya, ina iya jin kallonsa a jikina, fuskar nan tawa naci kunu ina kalle kallen gefe abuna sai ƙifta idanu na ke, yay horn wanda ya ke shaida min na in shigo motar amma sai nayi biris. sai ga shi ya fito da kansa ya taho har inda na ke, yay tsaye gabana hannayensa naɗe a ƙirji.

na ɗan ja da baya ina ce wa,"salamu alaikum".

sautin murmushinsa na ji kana ya ce,"yi haƙuri Ya Sayyada, amsawar sallama ne dole ba yinta ba".

na ce,"haka ne. Abbaan ba ya nan bai dawo daga kasuwa ba. amma Yashaik yana gidansa, in kuma kana iya jiran dawowar mahaifin nawa to tabarma ce da mu".

ina faɗin haka na juya zan koma gida ya ruƙo hannuna.
"wurinki na zo ba wurin Abbaa ko Yashaik ba".

nayi shiru ban ce komai ba. ya faki idon mutane yasa hannu ya ɗago fuskata, na kulle ido ina kauda kai gefe.
cikin dakiyata na ce,"wacece ni da na isa ka zo wurina?".

"matata".

nayi guntun murmushi na takaici ina cewa,"ina wuni". na furta a sanyaye ba tare da na kalle shi ba.

ya amsa,"lafiya lau, na sameki lafiya".

nayi shiru. ya sake cewa,"zuwa nayi mu tafi". nan ma nayi shiru. ɗumin iskar bakinsa da ya fesar ya sauka a fuskata. ya ƙara faɗin,"ki shiga ki ɗauko kayanki mu tafi". kamar da dutse dai yake magana. ya daɗa ce wa"Habibty Hubbi fa ke magana". nan ma na masa shiru. sai ya sauke dogon numfashi alamun ya ƙosa kana ya ƙara cewa,"ki shiga ki ɗauko kayanki mu tafi, duk abin da za'ai ma yi shi a can gida".

nayi masa wani kallo na ce,"ba ni da wani gida da ya wuce wannan". na faɗa ina masa nuni da gidanmu. "kana iya jiran mahaifina ya dawo ka sanar masa ka zo mayar da ni ne. kuma bari kaji zan koma cikin gidanmu amma ba don in ɗauko kaya in bika mu koma wancan prison ɗin ba, ba zan koma in da ban da wata daraja ba".

"Habibty mu mance faruwar komai anan. ni ba zan iya tsayawa inga Abbaa ba domin ina jin kunyarsa akan abin da ya faru, kiyi haƙuri ki zo mu tafi kinji".

hmm wato tunaninsa ansan turoni gida yay, tsaki kawai bar masa na shige gida. Ummani bata san da dawowata ba saboda tana ɗaki, sai bayan kusan minti goma sha biyar sai gata a ɗakin nawa tana faɗin,"ke lafiyarki? ai ce na ke ma kun wuce".

kamar zan yi kuka na ce,"zan tafi ne Ummani".

"wanne irin za ki tafi ne, shi mijin naki zaman jiranki zai tayi".

na mayar da ƙwallar idona na ce,"ai ya jima da tafiya. maƙullin gidan ya kawo min ne".

kuma ina rufe baki sai ga sallamar yaro yana cewa,"wai Sa'ida ta fito inji mijinta su tafi".

Ummani ta ce da shi,"kace gata nan".
sai ta dawo kaina da faɗa sosai.

"ke bana son sakarcin banza, kwashi kayanki ki fita ki bi mijinki kar in saɓa miki. in kin fi ƙarfina kuma ai Yashaik na gida sai in aika a kirawo shi wallahi".

tashi nayi babu shiri, na fara fitar da kaya bakin ƙofar ɗakin, Sauda ta fitar min da su ƙofar gida.

"waccan ledojin ba naki ba ne, kar dai ki manta wani abun".

na waiga ina kallon ledar da ta min nuni. na ƙarasa na ɗauka ina buɗewa, magungunan mata ne da ƴan uwa suka bani a ƙauye, wai in amfani da su kafin na koma gidana. a lokacin girgiza kai kawai nayi, basu san tuntuni mu'amalar aure ta daina shiga tsakanina da mijina ba, jo hannun juna bamu riƙewa, shiyasa bana wani tayar da hankalina akan gyara kaina dan bana son abin da zai jawo min matsala. sai kuma ɗayar ledar da Maman Yasmin ta bani, itama ciki kayan gyara ne masu inganci don ita dama ba daga nan ba, yawancin daga nijar ake yo mata haɗin gyaran jiki ciki da waje, shiyasa duk ta susutar da Yashaik.

na fito na leƙa muka yi sallama da mutanen gidan, Ummani dai tuni ta ɗau fushi da ni don ko da na zo ina zan tafi a daƙile ta ce min ki gaida gida. na samu na lallaɓa uwata ta saki ranta, ta ƙara min faɗa da nasiha ta ban shawarwari da zan fara aiki da su tun a yau, haka na barota ina mai cike da kewarta don sam bana son tafiyar.

ni dai tun da na shiga mota wurin da yake ban kalla ba. motar ta ɗauki shiru sai can naji ya kamo hannuna. "wai Habibty daina magana tayi ko kuma Hubby ta daina kulawa?".
ya furta hakan cikin taushi yana kallona.

Ban ce komai ba ya sake cewa,"Ashe za ki iya kwana har bakwai ba tare da kinji ko da muryarta ba balle ki so ganina Habibty, ni fa kin ganni murna na ke tayi da ganinki na kasa riƙe shauƙina, amma ke ba alamar jin daɗi tare da ke".

Kallonsa nayi shima ya waigo, muka haɗa ido ya mayar da hankalinsa kan titi. "ummm Habibty kwana fa bakwai banji motsinki ba, kin san Allah gidan kamar bursun". nayi shiru ban ce komai ba amma har raina wani daɗi na ke ji, duk da ban gama yarda da shi ba.

A sanyaye ya sake cewa,"ba kiyi kewa ta ba ne?". Nan ma ban amsa ba sai ya matsa hannuna yace,"Habibty fushin ya isa haka kar mu ƙarasa gida a haka, Na san nayi laifi a yafe min". ya furta cikin muryarsa mai daɗi da kwantar da kai.
Nan ɗin ma shiru na masa don ni sam bana ganin zan iya tanka masa. amma haka ya ke ta zuba bakinsa ko gajiya bai yi, muryarsa a ƙasa ya ƙara cewa,"ba za ki min magana ba ko? ai shikenan zan saka kiyi magana ne bara mu koma gida, ni ban san ma Ya Hayaty haka ta iya fushi ba sai yau, to Allah ya huci zuciyarta".

ɗago ido nayi na kallesa. wai Ya Hayaty, rabon da inji wannan sunan a bakinsa har na manta. kuma kawai sai na tsinci kaina da yin murmushi me sauti kuma mai kaifi, shima sai ya murmusa daga haka kuma kawai na ɗan sakko, wata maganar in amsa masa wata nayi masa shiru.
zuwanmu junction ɗin gadon ƙaya muka tarar da anyi accident. police sun cika wurin don motarsu ce guda ta zo, suna ta fama da matashin saurayin yaƙi barin naushin me adaidatar da ya dakar masa mota, Hubbi ya ke cewa ai ya san lambar motar yaron, a banza ma in ƴan sanda in sun tafi da shi don ba zai rabin awa ba a station zai fito, to yana cikin maganar ma muka ga wata farar mota ta faka in da na ciki ya fito, fuskarsa cikin facemask da p-cap, ya kama hannun saurayin da ya gagari kowa ya shigar da shi motarsa yaja suka tafi, sannan ne hanya ta buɗe aka sami sauƙin go slow.

komawarmu gida Hubbi da kansa ya ɗebar min kayana zuwa ciki, daman mun tsaya a hanya ya siyo abinci don yana min ƙorafin yana jin yunwa ni ko nace ka nemi abinci don banga zan iya girki ba, kuma abin tausayi a lokacin sai ya amsa min to, da har zance ya bari zan girka in mun koma ɗin sai kawai sai na ƙyale shi.
bamu jima da dawowa ba ya ƙara fita sakamon kiran gaggawar da Malam yay masa, sai bayan isha'i ya dawo, lokacin ma ni har ina shirin in kwanta tun da nayi wanka ne, da abinci ya zo daga gida ba yanda bai da ni ba akan na ci na ce masa a'a, na tashi na barshi na koma ɗakina na ƙasa.

ina kwance cikin tunani kiransa ya shigo wayata, na ɗaga nayi shiru, shi kuma ya ce,"ba ki gama abin da kike ba ne?".

"ba abin da nake yi ai, na kwanta ne".

yay muryar tausayi da cewa,"Habibty ni ɗaya za ki bari na kwana? plss ki taso ki zo ina so na nemi afuwarki".

kaman a gabansa na turo baki na ce,"komai ya wuce a wurina sai da safe".

cikin baccina naji ana shafa fuskata ga numfashin mutum a jikina, nayi saurin buɗe ido zan miƙe ya janyoni jikinsa ya rungume.
"kiyi haƙuri da abin da ya faru, ɓacin rai ne. kuma kin san ina da son yara sosai ba zan jure ganin wani abun ya samesu ba, hakan shine ya tashi hankalina har ya kai ga abin da na aikata miki. Amma kiyi haƙuri ba za'a sake ba in sha Allah".

hawaye na fara tunawa da irin horon yunwar da yayi min da kalamai marasa daɗin da ya faɗa min, to ni in laifukansa gare ni ma ai sunyi yawan da ba za su ƙirgu ba, ga laifin su Yaya amma a haka ya sallame ni zuwa gida ba tare da yi min uzuri ba.
jin hawayena na jiƙa jikinsa sai ya ƙara rungume ni sosai yana faɗin,"na san nayi laifi babba kiyi haƙuri ki yafe min Habibty don Allah."

Allah sarki zuciya da abin da take so, hakana tsakanin mata da miji sai Allah, roƙona da yake tayi domin Allah sai naji na nemi laifinsa gare ni na rasa.
na kewaye shi nima ina cewa,"Ya wuce Hubbi. Amma dan Allah ko dan gaba ka dinƙa tsayawa ka fahimce ni kafin ɗaukar mataki....".

ya dakatar da ni,"shiii hakan ma ba zai sake faruwa ba fa, duk wani saɓani a tsakaninmu ya zo ƙarshe".

haka muka jima rungume muna jin ɗumin jikin juna da bugun zuciyoyinmu, kafin ya ɗago kaina ya kalli idona ya ce,"Habibty kina jina?."

na ɗaga kai alamun eh yace,"nayi kewarki sosai ba kaɗan ba".

a sanyaye na ce,"Nima nayi kewarka Hubbi." na faɗa muryata na neman karyewa.
Yayi murmushi yana ta kallona yace,"Habibty na tambaye ki?."

Na ɗaga kai alamun eh yace,"Akwai wani abu wanda aka ba ki kina sha ne na gyara jikinki..? Ina nufin na gyaranku na mata."

Kallonsa nake yi ban ce komai ba hakan ya saka yace,"in akwai ki daina sha ya canja min ke gabaɗaya, bana jin ki kamar da. ba gyara yake miki ba ɓatawa yake."

ido na sunkuyar ƙasa, lallai namiji, wato sai yanzu lokacin faɗa min gyarana yayi, a yanzu da zanyi amfani kenan.

"Habibty kin jini ba ke ci komai ba".

Na ce,"to Allah ya gyara amma ni dai babu wani abu da na ke sha, asalin ɗanɗano na daka sani shi ne dai ban sha abin da zai ƙara min ba balle har ta kai ga ya rage min, amma karka damu zan koma mai daɗin da kake so".

nayi furucin domin na daina ƙullewar kai, na cire kaina a sahun matan da ke jin kunyar mazajensu ta fannin soyayya.

Yayi murmushi yaja kumatuna yace,"yauwa Habibty nah".

zameni yay a jikinsa yana cewa,"bara na rufo ƙofan falo".

ya faɗa yana ficewa na bishi da kallo. Yana fita nayi saurin ɗauko maganin da Maman Yasmin ta bani na fara sha nan take sai da na shanye haɗin zumar tasss, harda goro ma da akace naci rabi amma haka na cinye guda. na leƙa falon naga baya nan nayi sauri na shiga kitchen na buɗe fridge na ɗauki ruwan rake da ke cikin jarka na zuba garin maganin, na kafa kai shima na shanye sannan na tsaya sauke numfashi ina zare ido don duk ƙarfin hali nayi wajen shan su.

ni tun aurena ban san shan wani abu maganin mata ba, ko lokacin aurena in aka bani bana sha, saboda gab da aurenmu da kansa ya ce don Allah kar in sha komai na gyara da za'a bani, in ke ba shi yana ajiyewa akwai dalilinsa na faɗin hakan. to kuma bayan auren sai ya ce dama yana so ya ɗanɗani asalin zaƙin halittata yaji, to kuma iya wannan daɗin ma ya ishe shi ba sai na ƙara da komai ba, kar in zo ina sha in canja daɗi kuma, saboda haka duk ya tattaro wanda ya ajiye da wanda nima na ajiye muka zubar.

to yanzu tun da anzo lokacin da asalin halittar tawa ya bar masa daɗi ai sai in kama kaina inyi abin da ya dace ba in zauna da sakakkun laɓɓa ba. har zan fita a kitchen ɗin idona ya kai kan fruit na ɗauka nasha nasha na bar na bari, don bana taɓa mance wata likita da ta faɗa min cewa babu mafi muhimmanci a gyaran jikin mace irin shan kayan marmari, kuma sosai da na lazumci shansu na ga sakamako mai kyau.
ni ko a yanzu ma ban wani yarda da dalilinsa ba, kawai dai ya faɗa ne don kare kai ya kuma wanke laifinsa.

ina shiga na tarar bai dawo ɗakin ba, don haka na shiga tuɓe kayana na ɗauki towel na ɗaura. lokacin ne kuma ya shigo sanye da kayan bacci masu taushi yana ta ƙamshinsa me daɗi.
muka haɗa ido da shi na wuce ina zuba kayan da na cire cikin basket. zan wuce shi ya ruƙoni yana faɗin,"ina baccin?".

da muryar shagwaɓa nace masa,"na kasa, wanka na ke so nayi tukunna".

na ƙwace hannuna nayi toilet ɗin sai dai ina zuwa bakin ƙofar sai na dakata na waigo na kalle shi na ce,"Hubbi kai ba zaka yi ba?".

"daga wanka na fito ai".

na narke idanu ina langwaɓar da kai na ce,"to ka zo kayi min, ni duk na gaji".

murmushi yay wanda na rabon da naga irinsa a fuskarsa zan rantse an shekara. ya cire rigar jikinsa ya naɗe wandon ya kama hannuna muka shiga banɗakin.
Tare mu kayi wankan da shi, kuma tun a banɗakin labari ya fara canjawa, ko da muka fito tuni na kasa daurewa salonsa, ni dai sai in ce rabon da mu mu'amalantu irin ta yau tun daren farko na, shi kansa ba ƙaramin gigicewa yay ba da yanda yaji ni tamkar sabuwa a leda.
yana ta aikin sauke nauyayyan numfashi ya ke min godiya da sa albarka, wannan kam lazim ne duk lokacin da ya samu natsuwa tare da ni.

can kuma ya fara surutan,"Habibty ba ki canja ba, kina nan da daɗinki sai ma ƙara daɗin da kika yi, kinsa naji daɗin da na jima banji ba, ina sonki Habibty, ina sonki, Allah yasa da rabon samun zuri'a mukawa".

hawaye ya fara zubo min, ba komai yasa ba sai tuna baya, lokacin da muke zaman lafiya cikin tsantsar so da ƙaunar juna, lokacin da ko ɗaga murya ba ya yi min, in laifin nayi kuwa cikin kwantar da murya zai min faɗan ya kuma gyara min kuskurena.
sai da cikakkiyar natsuwa ta tabbatarwa kowannenmu kafin muka yi wanka kana muka dawo muka kwanta. lafe na ke kawai a saman ƙirjinsa idanuwana a lumshe, baccin na ke so nayi amma yaƙi zuwa, ba zan taɓa iya musalta daɗi da farin cikin da na ke ji ba a cikin a raina sai dai sam na gaza bayyana hakan a saman fuskata da yanayina. shima shiru yay yana shafa gashin kaina, da ɗaya hannun kuma yana shafa fuskata da tattausan leɓe na, a hankali ya hura min iska a kunne yana ƙara rungumeni jikinsa, muryarsa kwance cikin taushi ya kira sunana.

"Habibty". na amsa da,"ummm Hubbi".
"ba ki haƙura ba har yanzu? ba ki bar fushin da ni ba?".
"na daina mana Hubbi".
"to amma ai ni kin ƙi nuna min, yanayinki sam babu hakan, ki saki jikinki plss ba Nazifin da ya canja miki ba ne cikin wasu ƴan watanni, wannan Hubbinki ne tun na aure. na sani na saki ɓacin rai har adadin hakan ba zai ƙirgu ba, amma kiyi haƙuri da duka kuskurena, ki yarda da ni kinji, mu komawa rayuwarmu ta baya, rayuwar ma'aurata mai cike da tsantsar so da ƙaunar juna, kwanciyar hankali da shimfiɗadden zaman lafiya".

ni dai nayi masa shiru kawai, domin mamaki ne da rashin yarda a raina, gani na ke kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login