Showing 54001 words to 57000 words out of 87761 words
da kansa, amma Allah ya sani ina mutuwar son mijina, kawai na fita a sabgarsa ne saboda zaman lafiya da kwanciyar hankalina. sau da dama ina jin na karaya idan ina kusa da shi amma na kan danne na tursasawa zuciyata, in kuwa na kasance ni ɗaya babu tunanin abunda na ke sai rayuwarmu ta baya tun daga haɗuwarmu zuwa auranmu da muka rayuwa cikin farin ciki da ƙaunar juna kafin shaɗan ya shigo tsakani.
shirina na yi cikin sabon hijab ɗin da Alhaji Yayan su Ummani ya aiko min wancan sati, da maƙulli na kulle ɗakina don yanzu ba na iya idan zan fita na barsa a buɗe, duk da ba raya wani mugun abun zai iya faruwa ba amma idan ka kiyaye sai Allah ya kiyayeka, masu zuwa gidan ba ƙaunata su ke yi ba, to ban san iyaka inda manufarsu ta tsaya ba don satin baya da Anty Aisha ta zo ce tayi sai taga bayana a gidan nan.
na sakko ina ƙoƙarin ɗaura niƙab Faty ta shigo da sallama da yanayin gajiya sosai a tare da ita. ita ce autar Iyam a mata, kuma duk ƴaƴan gidan ita da Salaha ne kaɗai Allah ya ci da su rabon karatun boko me zurfi, yanzu tana polytechnic ta nan ɗorayi, satin Iyam uku da zuwa ta dawo itama wai makarantarta tafi mata sauri daga nan, ni dai adu'ana Allah yasa kar zaman nata yay tazarce dan ba mutunci ta cika ba dama ita tun asalinta haka take, ita da Anty Aisha halinsu ɗaya.
fuskata ta washe da fara na ce mata,"sannu da dawowa ƴan makaranta".
"Yauwa". ta amsa min a ciki tana shigewa ɗakin mahaifiyarta.
shigarta kenan sai ga Iyam ta fito. ganinta yasa na tsaya tambayar,"wani abun za'ai maki Iyam?".
ta ce,"ehhh fa". ta faɗa tana yi min duban sama da ƙasa. "Ce zan yi dama ki haƙura da fitar kawai, kayan wanki ne na ɗebo su, nawa ne da na Faty, kuma yaran naji suna faɗar kayan makarantarsu na gobe ba'a wanke ba, kinga fita kuwa bata kama ki ba, ki bari zuwa goben sai ki je duk inda za ki tunda ba tashin duniyar za'ai ba".
shiru nayi hakan yasa ta ɗaga murya da cewa,"ko kuwa ba za ki ba Sa'ida na ga kin ɓata rai, ina uwar mijinki ban isa na sa ki aiki ba kenan?".
ido na rufe na sauke ajiyar zuciya, murya ƙasa na ce,"ya za'ai na ce ba zan yi abunda kika saka ni ba, don Allah ki bar faɗin haka".
"na ji bana son kissa, yauwa ki wanke yanzu kar ki ce sai anjima yamma tayi su ƙi bushewa har dare su zo suna warin rima".
sai ta shiga ƙwala kiran "Faty! Faty! fito min da kayan nan da na ɗaure, ki tabbatar kin sako duk kayanki na dattinkar daga baya ki zo kina min mitar kin rasa kayan sawa in za ki wuce makaranta".
Fatin ta fito da damin ƙunshin kaya na cullo su gabana tana faman hararata, kallon kayan na yi kawai na san da gayya aka ɗebo su, kuma rabi na san na Fati ne tunda ko cikakken sati banyi ba da yiwa Iyam wanki. abun yana ci min rai yana ƙonan zuciya duk sanda Iyam ta bani wankin kayan Fati, ƙanwar miji fa? ba ma dole yarinyar ta dinga gani na a wulaƙance ba.
maganar Fatin ta katse tunanina tana cewa,"ba ki ba ni abinci ba kuma".
ban ko kalleta ba na duƙa zan ɗau kayan Iyam ta ce,"jin abunda ta faɗa ne ba ki yi ba ko kuwa abincin ne ba ki da niyyar bata isashshiya. ko kin mata gidan Yayanta ne uwa ɗaya uba ɗaya?".
kayan suna da nauyi sosai ban ɗauka ba na ɗago ina kallon Fatin na ce,"amma ai kin san hanyar kitchen ɗin Fati ki shiga ki zuba mana ko na taɓa hana ki. idan ma shiga kitchen ɗin ba za kiyi ba ai ga flask ɗin su Atika nan kan dining ki zuba mana".
"banga zan iya yin duka biyun ba, kece matar gida kece da dafawa da zubawa. saboda haka ki zuban abincina kawai ko na haɗaki da Yaya Ƙaramin shi ai ya isa da ke idan ita Iyam ɗin kin rainata".
kallonta kawai na ke raina na sosuwa har ta wuce ta zauna kan kujera tana ɗaukan remote ta canja tasha. Iyam ta shiga ƙwala kiran Nazifi, gabana na faɗuwa nayi saurin barin wajen ina nufar dining, abincin na zuba mata na ce da ita ga shi nan, kamar bata jini ba haka tayi banza da ni.
ina niyyar barin wajen sai ga shi ya fito daga ɗaki, Iyam na ce masa,"a'a da ce tayi ba zata bawa Fati abinci ba na ce to bara na kiraka ƙila taji maganarka tunda ni ban isa ba".
kallona yayi yana cewa,"bisa wanne dalili za ki hanata abinci? wai ke ki hora mutum da yunwa daɗi ya ke miki ne? wato abunda na ɗanɗana miki kwanaki bai ishe ki ba?".
Iyam ta katse shi,"kaga duk ba wannan ba, Fati dai gata can zaune ma kallonta take, kallon dole don dawowarta kenan yunwa take ji, ka ce kawai ta bata abinci".
"ki bata abincinta karnki ƙara hana wani nawa abinci tunda ba ke kike siyowa ba, don kin dafa ba yana nufin kina da iko da shi ba ne".
muryana na shaida damuwa na ce,"ban fa ce ba zan bata ba, ce nayi taje ta ɗiba. kuma ga shi na zuba mata na ce ta zo ta ɗauka tayi min shiru".
"ohh in magana ki ƙaryata". cewar Iyam
"ni ba ƙaryata ki nayi ba amma yanda kika ce ai ba haka ba ne...".
maganata ce ta katse dalilin saukar marin da naji a fuskata.
"duk ranar da mahaifiyata ta ƙara magana kika nemi ki ja akai sai na mugun saɓa miki, uwata fa tana faɗa kina cewa ba haka ba, me kike nufi in ba ƙaryatata ba".
idona ya ciko da hawaye ina dafe da kuncina. na jiyo shi yana cewa da Fati. "ke kuma zo ki ɗauki abincin".
ta marairaice tana cewa,"Yaya Ƙarami ƙafata ce naji ciwo bana iya takawa inama shirin ce maka zanje asibiti ne".
ya waigo ya kalle ni daidai lokacin da na ke niyyar barin wajen murya a sama ya ce,"na gama magana ne da za ki bar wajen?".
na dakata ba tare da na juyo ba.
"ki ɗauki abincinta ki kai mata kina ganin ai tana da lalura".
na danne kukana na mayar da hawayena, na ɗauki abincin na je na miƙa mata ta karɓa tana ƙunshe dariya, cikin raina na ce Allah ya saka min.
Barinsa wajen na nufi bene nima, gaba ɗaya na manta da batun wani wanki, sai munafukar yarinyar ce take cewa da Iyam wai na tafi na bar mata kaya. ita kuma ta ce ta ƙyaleta da ni zamu zuba. ni kam ban tsaya ba nayi ɗaki ina jin babu daɗi a raina, zama nayi saboda raina ya ɗan yi sanyi amma har ga Allah na jima ban ji ɓacin rai ba irin na yau.
to ni wankinma bai cin min rai ba kamar zuba abincin in kai mata kuma ta karɓa tana min dariya, in wanki ne dama tunda Iyam ta dawo ta hana badawa da guga tace masa gatan yayi min yawa komai sai a kashe kuɗi ayi min banda aiki sai kwanciya, don haka bisa umarninta kar a ƙara bayar da wanki a gidan, kayan wankin guda nawa su ke da ni ba zan wanke ba sai dai ai ta ɓarnar da kuɗi ni babu tausayi saboda ban san wahalar da yake sha ba kafin ya samesu, to in dinga ƙwarara jiki ina motsawa, haka ma fa firij tasa an ɗauke na kitchen an kai ɗakinta, duk su lemo da nama in ya kawo sai yanda ta bani, duk sona da maltina yanzu sai haƙura na ke yi saboda idan naje karɓa ta dinga mita kenan.
Da rana ina cikin wankin sai ga shi ya shigo yana faɗin,"wanne irin rashin hankali ne wannan? Kin bar tukunya zata ƙone kin taho wani aikin na daban, ki bari ki fara kammalawa da ɗaya mana, wannan ai ba dabara ba ce. kin san yanda gas ke kara tsada kuwa, wallahi za ki ja na koma ajiye miki buhun gawayi".
Da alama bai san wankin na waye ba shiyasa, Na tsame hannuna a ruwan da sauri, ta gefensa na wuce na nufi kitchen ɗin, ina zuwa na tadda ruwan zafin ko tafasa bai yi ba, ni dai dama nayi mamaki domin kuwa nayi ƙasa da wutar sosai, kai bawa dai da komai kayi sai ya zama laifi, nufinsa da yay maganar in tsaya masa bayani ya hasala ya gaggaya min babu daɗi. ina kitchen ɗin ya dawo ya sameni, ya ce in fito falo na iske shi, sauri sauri na wanke shinkafar na zuba na fita, yana tsaye hannayensa harɗe ta baya, hannun kujera na zauna ina ce masa,"gani".
kuɗi ya miƙo min tare da cewa,"akwai abunda ya taso min na ke so a taya ni da adu'a, ga wannan dubu talatin ne, idan kin gama aikin sai ki leƙa gidan Malama Hadiza, akwai buhun shinkafa da wake na bayar akai gidan, idan kin je sai ki tambayeta adadin kuɗin da ake buƙata, jallof ne za'ai da ƙosai da kunu ayi sadaƙa".
ina kallonsa na kai hannu na karɓa na ce,"Allah ya karɓa ya biya buƙata".
Ko amsa ni bai yi ba, ya nemi kujera ya zauna ni dai na bi sa da kallo don naga kamar yana cikin damuwa. sannu a hankali na ce da shi,"ko wani abu ne ke faruwa?". ba tare da ya kalle ni ba ya ce,"plazar cikin gari gwamnati ke son rushewa wai filinta ne".
na ce,"to subhanallahi, Allah ya saita al'amura, kar ka damu insha Allahu zata dubeku ta bar muku abinku, adu'a ce kawai zata yi aiki".
ya amsa da,"ilahee ajib".
na buɗi baki da niyyar in wata maganar wayarsa tayi ƙara, ido ya ɗago yana kallona bayan ya gama kallon screen ɗin wayar, a hankali yace,"ki bani wuri".
tashi nayi na bar masa wajen na koma bakin ayyukana, sai dai tuni na shiga damuwa da lamarin plazar da ya faɗa min, tabbas aka rusheta ba ƙaramin asara zai yi ba, don duk ita ce jagaban kasuwancinsa. nayi nisa a wankin sai ga Fati da kaya a hannu, tana zuwa tsabar rashin mutunci ta watso min su cikin ruwan wankin, raina ya ƙuntata na waiga a fusace sai zuciyata ta taushe ni kawai na ƙyaleta, don yanzu ina magana tashin hankali zai biyo baya.
"ki wanke min fuskar da hannayen da kyau".
ta ce da ni cikin gadara da nuna rashin kunya, ban ce mata komai ba har ta fita. kafin na gama wankin har na gama girki dama saboda haka nayi dabarar haɗa aikin biyu, kar in kai dare ban gama girki ba Iyam ta ɗaga min hankali da cewar na bar yara da yunwa, tayi nata mai gidanma yay nasa.
Nayi sa'a kayan su ka bushe da wuri. na ɗebo shanyar na linke na ajiye su akan kujerar falo, ina jiran nayi wanka na ɗan huta sai na zo na goge, kafin na bar wajen sai ga Iyam ta fito ta zo tana cewa,"gugar kuma fa bayan ga wuta nan kika wani linkafesu kika yasar da su anan koma ki kai min ɗaki. Ko ajiye min kika yi na zo na goge da kaina?".
"A'a Iyam dama ina so ne zuwa ɗan ajima sai na goge".
"mene wani anjima saboda dai ki bar min kaya da ƙura, dama ai ba so kike ba kika wanke, saboda Fati ta kai miki hijabi biyu shine har da yi mata tsaki ke da ba kya ƙaunar zaman lafiya, ai ba ita ta saka ki wankin ba ni ce nan, me kike yi a gidan Sa'ida in ba a saka ki aiki ba nufinki sai dai kici ki kasayar ki kwanta? kuma yarinyar nan kina gani daga makaranta ta dawo tana so ta huta ta ina zata yi wanki, anfanin duk wata hidimar gida na matar gida ne. don haka Malama zauna ki goge su kar nefar su ɗauke wutarsu, gugar solar nan ba wani kyau take ba, ko kuwa haka kike so na dinƙa saka kaya a yamutse ana zagar min ɗa, gwara ma ni akan yaran".
Tunda na zauna gugar ban tashi ba sai da aka yi kiran magriba, na ɗebi waɗanda na goge na kai ɗakinta na ce mata zan yi sallah tukunna sai in ci gaba. ba dai ta ce min ƙala ba na fito na wuce ɗakina, sai alokacin nayi wanka na shirya cikin doguwar rigar atamfa. jikina banda ciwo babu abunda yake yi min, na kwanta ina ta aikin nishi, na manta rabon da na ce na huta na minti biyar tunda Iyam ta zo. Rumana ta shigo ɗakin zatonta bacci na ke yi don sai da ta zo daidai kaina kana ta shiga taɓani a hankali tana cewa,"Anty Abbaa yana kira".
Na kalleta da gajiyayyun idona, zama tayi kusa da ni tare da taɓa wuyana tana cewa,"Anty ba ki da lafiya?".
na murmusa kuncina na ce,"lafiyata lau Rumana, gajiya ce kawai".
kanta ta kwanto bisa kafaɗata tare da riƙe hannuna. "Anty don Allah kiyi haƙuri da duk abunda muka yi miki, ni dai wallahi na daina, yanzu tausayinki na ke ji kuma ina sonki".
Na shafa kanta ina cewa,"Anty ba ta fushi da yaranta, nima ina sonki Allah yay miki albarka".
tashi nayi na kama hannunta muka fita, tana min surutun in ce Abbansu ya kaini asibiti idona baya da lafiya kuma duk na rame, hmm ni yanzu na masa magana ma ai ce zai yi je ki chemist.
Ɗakinsa na iske shi, ni sai da ya kira ni ma na tuna da saƙon da ya bari. wani kallo ya watsa min yana cewa,"ke ba kya taɓa son a zauna lafiya, ya za'ai na bada saƙo tun ɗazu sai yanzu muyi waya da mata tace min ba a kai mata ba".
"kayi haƙuri ba wai haka kawai ba ne. kaima ce kayi idan na gama aiki kuma har yanzun da kake faɗan ba gamawa nayi ba".
"Sa'ida wai mene matsalarki? Me ya ke damunki ne da kika bar ɗaukar maganata da muhimmanci? na fa gaji da wannan banzan halin na ki da kika tsira".
"Na ce kayi haƙuri ko, gugar Iyam zan ƙarasa babu yawa ina kammalawa sai in je, ba zai yiwu na aje nata aikin akan naka ba".
bai ce min komai ba ya sadda kai ƙasa yana duba wasu takardu da ke gabansa, soyayyarsa na ji ta cika min rai, bana so yay zaton ko daina sonsa nayi, ƙaunarsa na nan yanda take a raina, duk irin baƙin ciki da ɓacin ran da ya ƙunsa min tuni na cire a raina na yafe masa, duk da shekaranjiya naji zafin zagin da yay min a gaban ƴan uwansa akan sun zo ban san da zuwansu ba ni kuma na kulle store, da kuma abunda yay min akan Fatin ɗazu. shi dai ko rantsewa nayi ba zan kaffara ba a yanzu ba ya min ko da kwatan son da yayi min a ba ya, rabonsa da faɗa min wani kalaman soyayya tun ranar da buƙatar kansa ta kawo shi kafin ya kai ƙarata gidanmu. ni kam nayi alkawari nayi sai na rama ko da kaso ɗaya ne cikin kason ɓacin ran da ya saka ni ciki, kuma na lura ta banzatar da shi da lamarinsa kawai zan rama don hakan na masa ciwo ko bai faɗa ba.
"kayi haƙuri kaji Hubbi". na faɗa ina tsugunawa a gabansa ganin yanda fuskarsa ta nuna tsantsar ɓacin rai.
bai kalle ni ba ya ce,"no kar ki damu zan yi maganin abun, idan kina ganin hanyar da kika ɗauka ita ce daidai a gareki nima zan san abun yi, kije kici gaba da ɗaukar zugar duk me zuga ki, kiyi yacca kike so Sa'ida amma zan tabbatar da na matuƙar ba ki mamaki wallahi". ya faɗa yana jijjiga kai.
tsayawa na yi ina kallonsa, tabbacin aiwatar da abunda zai aikata kwance saman fuskarsa, ban san me ya ke nufi ba haka ban san mai zai aikata ɗin ba amma ƙwarai na tsorata, bana son abunda zai ƙara kaimu ga gaban iyayena, bana so sam, shiyasa ko hanyar da na ɗauka ta fita a sabgarsa shi da ƴannuwansa na ke bi a hankali ta yanda dole sai dai su buga su barni.
fita nayi naje na ƙarasa gugar kayan Fati, sai da bayana ya zama kaman ya ɓalle kafin na gama don kayan ba kaɗan ba ne, na kai kayan ɗakinta na jera mata cikin wadrobe, sannu wannan bata ce min ba, nima ban damu ba na fito fatana ta barni haka kuma inje in samu na huta. tunda na koma ɗaki na kwanta na rasa natsuwata sai faman juyi na ke yi, tunaninsa duk ya addabe ni, ban san wanne hali yake ciki ba, dole haka na tashi nayi shirin kwanciya na fita, sai da na shiga ɗakin su Rumana na tofe su da adu'ar bacci kafin nan na sauka zuwa ɗakinsa.
a hankali na murɗa ƙofar ɗakin na shiga, har ya kwanta yana fuskantar saman dakin, na tura kofar na rufe, ashema waya ya ke yi ni ban sani ba sai da na zo bakin gadon, amma a haka yayi kaman bai san da shigowata ba. "ina zuwa". shi ne abunda najinya faɗa kafin ya dire wayar yana kallon ɓarin da na ke, cikin sanyin jiki na zago ta gabansa a hankali na shiga basa haƙuri, tun kafin na ƙarasa ya katse ni yana sakkowa daga kan gadon.
"Ai na gama yanke hukunci akan wannan, ki ci gaba da duk abunda kika ga dama wanda ki ke ganin daidai ne a wurinki ba zan hanaki ba, ba zan takuraki ba, nima zan yi abunda na ke ganin daidai ne a wurina, sai dai kar ki ji haushina, yanda ba kya buƙatata nima bana buƙatarki a yanzu tashi ki fice min daga ɗaki kafin ki hasali ni".
Tunda ya fara maganar na daskare ina kallonsa har ya kai ƙarshe, ban taɓa ganin ainihin ɓacin ransa ba sai yau. tsawa ya kuma doka min yana cewa,"ba za ki tashi ki fitar min a ɗaki ba sai na zo ina aikata miki abunda za ki zo kina danasanin sanina, wadda bata san darajar aure