Showing 6001 words to 9000 words out of 87761 words

Chapter 3 - ƘAYAR RUWA Book 1 HAUSA NOVEL

HALIMAHZ   

20 Dec 2024

6103

shiga na gyara ɗakin kaman ko da yaushe da na saba. na hau sama na kwaso kayan abincinsa na sakko da su, akan tebir na ajiye, haka kuma ban canjawa warm coolers ɗin da na tarar ba waje. Ayyuka na daban na tsira duk dan in mance da cin zarafin Yaya, ina ji aka fara kirayen sallar isha'i, ban tsaya da aikina ba naci gaba kasancewar ina cikin jinin al'ada, gyara na musamman na yiwa bedroom ɗin nasa a wannan daren, duk wani kai komo da nake maganganun Yaya ba su bar haska min a cikin kaina ba, sai dai ina ta ƙoƙarin kawar da komai ɗin domin bana son hakan ya tsaya min a rai, don ko Hubbi ba zai san da wannan labarin ba, shiru shiru har ƙarfe tara Hubbi bai dawo ba, kuma bai kirani ba bai tura min saƙo ba.

Ɗakina na koma na sake wanka don idan ina cikin jini sam bana sakewa, sai in ta jin kaman jikina duk ya ɓaci, haka kuma kaman ina ta ƙarni.
Murmushin takaici nayi da na kalli kaina a madubi, me yasa nayi wannan saken?, ta ya zan bari jikina yay wannan lalacewar?, dududu shekarata nawa?, ni akaran kaina ƙirjina ya daina burgeni balle kuma miji da kansa, ba komai ya lalata ni ba irin saka damuwa a rai, ni da ban taɓa shayarwa ba ai bai kamata ace na bar nonuwana sun zube ba yaraf, bayan na san Hubbi na matuƙar son su, to dole na miƙe tsaye, zan dawo asalina mai cikakkiyar sura ta ko'ina, in kuma fita daga cikin sahun mata masu dugun kai a gidajen aurensu ta ɓangaren shimfiɗa soyayyar aure. Sai da na gama kimtsa jikina tsab tukunna na fito ɗakin na kulle duk ɗakunan sama da kitchen, na sakko ƙasa na kashe fitilun falo tare da kunna karatun ƙur'ani wanda dama da shi muke kwana kullu yaumin. Agogo na kalla naga har ƙarfe goma daidai, tsammanina zuwa lokacin Hubbi ya dawo tun da na jima a ɗakina, sai dai ina shiga ɗakinsa naga babu alamarsa, kenan har yanzu bai dawo ba, take zuciyata tayi zullo na fara jin tsoro, ban san me yake faruwa ba, fatana ɗaya Allah yasa lafiya.

Kasa tsaye nayi na kasa zaune, in kai mari in kai gauro saboda kiran lambarsa da nake yi bata ko tafiya. Tunanin in kira office ɗinsa yazo min, sai dai ko da na kira aka tabbatar min da cewa ai tun biyar ya bar office. nan fa hankalina ya tashi, na rasa wa zan kira tun da shi ba wasu abokai gare shi ba, haka yake kamar mace mara son ƙawaye.
laluben lambar ƙaninsa na shiga yi, ko da ya ɗaga bamu wani tsaya gaisawa ba na tambayi ko Hubbi yaje gida, yace ba ya gidan tun da rana da yazo gaida Iyam. muna gama wayar na ƙara gwada kiransa, wani sanyi naji a raina da ta fara ringing, sai da nayi kira har sau goma bai ɗaga ba sai daga ba ya message ɗinsa ya shigo.

"Ba na son damu akwai abin da nake yi".

abin da ya rubuto min kenan, kuma ina gama karantawa na aje wayar jiki a sanyaye, ko ba komai naji dama-dama tun da lafiya yake, sai dai naji babu daɗi sosai, domin kamata yay ace in akwai adalci ya ɗaga wayan ya faɗa min uzurinsa, ko kuma ya rubuta min idan babu daman ɗaga wayar, amma saboda rashin sanin hakkina da girmama aure yana can lafiya ya barni anan cikin damuwa da tashin hankalin halin da yake ciki, ko abinci na kasa ci haka cikina yake fayau tun ruwan safe da na sha.

gudun tunanin da ka iya rufe ni na miƙe na kwanta akan gadon. Sai dai me? daga kwanciyar tawa na saki marayan kukan da nayi ta dauriyar riƙewa tun tafiyar Yaya, sautin kukan ya cika ɗakin, kuka nake kamar wadda aka yowa aiken mutuwa don kawai in samu in fitar da baƙin cikin da ke raina. na janyo filo na toshe bakina da shi amma duk da haka sautin kukana bai ɓuya ba. Lokaci ɗaya jikina ya ɗauki zafi na kama kyarma dama ni ban iya zazzaɓi ba. A wannan lokacin duk wani mai imani ya ganni sai zuciyarsa ta motsa da tausayina. Haka na ke ta faman zubar da hawaye, ban isa na goge su ba don ina gogewa wasu na sakkowa.

Na daɗe ina kuka don har wajen sha ɗaya da rabi, zuwa wannan lokacin kam na fidda ran dawowar Hubbi, banga alamun yau zai kwana a gidan ba. saboda haka na miƙe na shiga banɗaki na wanko fuskata ina hana kaina ci gaba da kukan da baida amfani gare ni, adu'a maganin annoba ita ya kamata in riƙe ba wai damuwa da kuka ba. Ina fitowa na wuce nasa key na kulle ƙofa duk da zuciyata na faɗa min komin dare zai dawo, bai da wani wajen kwana a daren nan sama da nan ɗin dai da yake ƙauracewa, tsakin ƙasan maƙoshi nayi, to ina ruwana da dawowarsa, raina ɓace na fita falo na bi duk ƙofofi shigowa na saka musu maƙulli, zanga ta in da zai shigo, ai sai dai yay kwanan ɗakin mai gadi, ba abar banza ba ce ni, auroni yay don yana so ba cusa masa aka yi ba, kuma a gidan iyayena ya ɗauko ni ba gidan marayu ba. kamar ma in koma ɗakina amma sai na dawo ɗakin nasa, na murza key na kashe fitila me haske na bar mara hasken wacce ke kan durowar gefen gado.

Bacci nake ta so nayi amma gaba ɗaya na kasa, sai juyi da nake ta faman yi, zuciyata kuma cike da saƙe saƙe, kaina kuwa ya cika fal da tunani daban daban. Ni dai lafiya ƙalau muke da mijina, sai dai tun bayan dawowarmu nan gidan da wata bai fi biyar ba komai ya canja na daga yanda muka saba rayuwa, ni da shi kamar abokai haka muke, amma yanzu ya zamar min wani horo har tsoronsa nake yi, magana ma shakkar masa na ke, komai nayi ban iya ba, saɓanin a baya duk abin da nayi ko da bai masa ba zai yaba min kuma yace nafi kowacce mace iyawa, yanzu abu kaɗan zan yi ya zama laifi, zama da shi ban isa ba in ba haka ba ya dinƙa ƙunci kenan ni kuma bana son ƙuncinsa, hatta makarantar tahfeez ɗin da nake zuwa yanzu nema yake ya kashe zuwanta, don duk san da zan tafi sai yayi ƙorafi akai, sai yace ai tunda na iya karatun sallah na san wankan tsarki na kuma san zaman aure ya ishe ni, da nayi magana sai yace ai shi ke biyan kuɗin ba wani ba saboda haka yana da ikon ya hana zuwan.

Na kau da tunanin matsalata da mijina, na koma tunanin furucin Yaya na za su sa ya ƙara aure, tabbas na sani ƙarin aurensa tozarcin da nake sha sai ya ninku, don sai na ƙwammaci ina ma ban auresa ba, Allah ɗaya ya san irin wulaƙancin da matarsa zata dinga min, balle ta san don manufar da aka aurota, zata goranta min fiye da yanda dangin miji za su min, kuma daga zarar ance ta sami ciki ta haihu shikenan tawa ta ƙare, zaman auren sai ya ishe ni, takaicin da zan sha ba daga wurinta ba kaɗai har da shi uban gayyar. ni kaina na sani Hubbi yayi ƙoƙari, ba kowanne namiji ne za'a kai wannan lokacin ace bai yi ƙorafi ba, kamar yanda Yaya ta faɗa shekara takwas ban taɓa ɓatan wata ba balle azo ga maganar ɓari, kuma ko da wasa Hubbi bai taɓa min magana ba, balle ya nuna min damuwarsa ko ƙorafi, ni ce ɗin ma na ke damuwa, don sau tari har kuka na kan yi, sai yay ta min nasiha yana ƙara faɗa min lokaci da rabo ne, idan na ɓata masa rai akan nuna masa kar a fara cewa bana haihuwa ya dinƙi faɗa kenan, yace min duk wanda ya fasa faɗar hakan ba ya ƙaunar Allah, kai duk wanda ma yay min gorin haihuwa in sanar masa hukuma ce zata raba su, watarana kuwa da nace masa muje asibiti a duba ni bai ci abincina ba. yanzu kuwa yanda muke zaman babu daɗi da shi ai nayi kaɗan in kai masa ƙarar Yaya akan cin mutuncin da tazo ta min, kuma ko da ace shima wannan ne dalilin samun matsalarmu ba zanga laifinsa ba, a yanzu kam yana da buƙatar magajinsa, wanda zai ɗora akan kasuwancinsa ya kuma mallakawa kadarorinsa. sai dai fa ya tuna ana barin halak don kunya, ko mai zai yi min banda wulaƙanci, don ni na sha gaban ya wulaƙanta ni a rayuwa, domin na masa abin da ko ƴan uwansa basu masa ba, ya kuma san hakan, sai dai in ya butulce, kuma shi butulci dama ai ba sabon abu ba ne a wajen ɗan adam musamman wanda ka yiwa rana.
Haka dai a wannan dare nayi ta tunane tunane, in raya wancan in saƙa wancan, in lissafa wancan, sai dai na kasa warware komai, haka duk na ƙosa gari ya waye, ni ba sallah ba balle in yi nafilfili, a haka dai har ɓarawon bacci ya ɗauke ni a lokacin da ban san ko ƙarfe nawa ba.
Washegari ban farka ba sai wajen ƙarfe tara da rabi na safe dalilin bacci da wuri da ban samu nayi ba, sai dai Alhamdulillahi isassan baccin da na samu yau ɗin da ya kaini har wannan lokacin sai ya zamana ban tashi da ciwon kai da zazzaɓi kamar yanda na saba tashi da su ba a ƴan kwanakin nan. Sai da na gyara ɗakinsa tukunna na fita na wuce ɗakina, kafin na haura saman kuma sai da na tsaya na buɗe ƙofa saboda zuwan mai yi min wanke wanke da share share.

Ko da nayi wanka na ke shiryawa zuciyata cike take fal da matuƙar mamaki gami da saƙe-saƙe daban daban akan al'ammarin nan mai girman gaske, yo mai girman gaske mana tunda miji bai kwana a gida ba bayan ba tafiya yayi ba, kuma abin da bai taɓa faruwa ba tsawon shekaru. Har yanzu ƙarfe goma sha ɗaya da na ke muku wannan maganar banga alamun Hubbi ya dawo gidan ba, na leƙa farfajiyar gidan babu motar da ya fita da ita. Nauyayyan numfashi na sauke, tarin tambayoyin da ke kaina a game da inda ya kwana da rashin dawowarsa da abin da ya tsaresa suna da yawan da har suke neman fasa min kai.

Wayata da ke ajiye kan madubi na ɗauka zan kira wayarsa, ina buɗeta kuwa na fara cin karo da saƙonsa na jiya da yake faɗa min ba ya son damu. Da sauri kuwa na dire wayar ina kulle idona kafin na buɗe bayan wucewar daƙiƙa ɗaya. zuciyata cike da ƙunci na fita a ɗaki na sauka ƙasa, a falo na tarar da mai aiki tana goge gogen gilasai, wanda tuni ta gama shara, ko'ina ya ɗau ƙamshi, dama ni ɗin gwanar ƙamshi baka taɓa zuwa ka riski gidana ba ya tashin ƙamashi tun daga harabar waje.
Muka gaisa da ita na wuce kitchen, ruwan shayi na dafa na soya ƙwai, na zubo nawa na barwa mai aiki nata, falon na dawo na zauna na kunna tv, ina shan shayin ina kallo hankali da tunanina kuma na can wani wajen.

Motsin buɗe ƙofa yasa na juya kaina wurin, Hubbi na gani ya shigo yanayinsa kamar tashin bom, ko inda na ke zaune bai kalla ba yay wucewarsa sama fuuuu kai kace tashin iska, ni kuwa nabi bayansa da kallo zuciyata na zullo, kamar in share shi amma sai naji ba zan iya ba, lokaci ɗaya naji abin da nake ci ya fita akaina, hakan yasa na dire na miƙe nabi bayansa da sassarfa. Ina shiga ɗakin na tarar har ya shiga banɗaki, nayi tsaye bakin wadrobe kamar munafuka ƙirjina sai bugawa yake saboda bala'in tsoron da ban san ta ina ya zo ba, wucewar wasu mintuna na dawo hayyacina na buɗe wadrobe ɗin na kwaso masa kayan da zai saka na zaman gida, na ajiye anan gefen gado, duk wani abu da na san zai buƙata na ɗauko na ajiye masa.

Mutumin da ba ya jimawa a banɗaki shi ne yau sai da na fara fidda tsammanin zai fito tukunna sai ga shi ya fito, ƙugunsa ɗaure da towel sai wani ƙarami kuma a hannunsa yana goge ruwan kansa da jikinsa. Ta gabana ya wuce ya isa wajen mudubi, yaja stool ya zauna ya shiga shafa mai, ni dai kallonsa kawai nake yi, wallahi kamar sabon mutum ba mijina ba, maganar da na ke ta so nayi ta gagara fitowa, na rasa tantance abin da nake ji a ƙirjina, tsoro ne ko kuwa shakka. haka ya gama shafa mai da oil perfumes na oud ya taso, yana niyyar buɗe wadrobe idonsa ya kai kan kayan da na ajiye, idonsa ya ɗauke akansu ya ɗago yana kallona, kamar me shirin faɗar wani abun amma sai bai ce komai ba. Kayan ya ɗauka ya saka, jallabiya ce milk ƙirar dubai.

Gado ya haye ya jingina bayansa da filo, sai a sannan na sami zarafin yin magana nace,"Hubbi wai lafiya?".

Shiru bai amsa min ba kamar ma ba da shi nayi maganar ba. Na danne abin da na ke ji a zuciyata cikin raunin murya na ƙara cewa,"Hubbi wai me yake faruwa?, in da akwai wata matsalar ka faɗa min don Allah, jiya fa baka kwana a gidan nan ba, kuma yanzu ka dawo ka ƙi ce min komai, gaba ɗaya fa ka sani cikin damuwa da tashin hankali, idan laifi na maka bisa rashin sani ka faɗa min na gyara in kuma nemi afuwarka, kai ɗin fa shugabana ne".

Nan ma banza yay min tamkar da dutse na ke magana. Na hasala, duk yanda naso in taushi kaina abin ya faskara, kun san an ce mai haƙuri bai iya fushi ba, muryata a sama nace,"magana fa na ke yi maka kana jina kayi min banza, nace aina ka kwana?".

Idanunsa ya ɗago ya waresu tas akaina, kallona yake da irin mamakin ɗaga masa muryar da nayi a karon farko tun aurenmu da shi, da kausashshiyar muryarsa mai kaifi yace,"ni kike ɗagawa murya?".

"Ya ba zan ɗaga maka murya ba alhalin kayi abin da yake ba daidai ba, kuma baka gyara kuskuren hakan ba kake ci gaba da yi, me ka mayar da ni da zan ke magana kana bawa banza ajiyata".

Idonsa kamar zai faɗo wajen kallona ya ƙara cewa,"ok in dawo gida ba ki iya min sannu da zuwa ba, ba ki tambayi matsalar da ta sameni ba, sai tsare ni da banzan tambaya, to matsayinki na wa kike tuhumata?".

Yanayin yanda yay maganar cikin ɗagawar murya ya kamata inji tsoro, to amma ko kaɗan sai banji hakan a raina ba, bayan ba ƙara ɓata min rai da yay, kuma tambayar da yay tasa na buɗe kallona da kyau akansa nace,"ohhh ka manta nauyin da ya rataya a wuyanka kenan, to matsayina na matarka ta sunnah, wadda ka auro ni saboda kana so ba saboda an cusa maka ba...yau ko ba aurena kake yi ba tun da har da kanka ka kawoni cikin gidan nan ka je ai ina da hakki kuma ina da hurumin tuhumarka inda kaje ka kwana da abin da ya hanaka dawowa gida".

Ina faɗar hakan na juya zan bar ɗakin saboda marayan kukan da ke neman ƙwace min, wanda ni kuma ko kusa bana so yaga rauni na tun da a yau nayi jarumta. Ina gab da fita ya kira sunana.
"Sa'ida". Yanayin yacca ya ambaci sunan kaɗai zai baka tabbacin gargaɗi yake so yayi haka kuma ransa a ɓace yake.

Na juyo nayi masa kallo ɗaya na watsar nace,"ina jinka". Tasowa yay daga kan gadon yazo gabana ya tsaya, ba don komai ba sai don ya nuna min ainihin tsayinsa, gabana ba ƙaramin faɗuwa yay ba da hakan musamman yanda nake jin tururin zuciyarsa a saman fuskata.

"Ki buɗe kunnuwa da kyau ki jini, daga rana mai irin ta jiya, ko ƙarfe nawa zan kai a waje, kar ki kuskura ki ƙara gigin rufe min ƙofa, idan kuma ba haka ba wallahi tallahi ranki sai yayi mummunan ɓaci, hukuncin da zan ɗauka akan hakan ba zai yi miki kyau ba. Gidana ne ba gidanki ba, ruwana in fita lokacin da na ke so in kuma dawo a lokacin da naga dama, ni ke aurenki ba ke kike aurena ba, saboda haka ina rabaki da tuhuma makamancin haka...don haka Sa'ida, Sa'ida kika ƙara rufe min ƙofa...".

Sai kuma ya ƙyasta yatsu yana jijjiga kai alamu na shi ya barwa kansa sanin abin da zai aikata. Ni kuwa hakan raina fes, ban damu da kalaman gargaɗinsa ba ko kaɗan, ashe ma cikin gidan ya kwana, kuma rufe ƙofan yay masa zafi, don haka na saki gajeran murmushi na jin daɗi na juya zan bar masa wajen aiko a zafafe ya fizgoni na dawo gabansa.

"Me kike nufi?".

Na ɗaga gira nace,"ina nufin sai in har ba ka ƙara kaiwa irin lokacin jiya a waje ba, amma sai na rufe ƙofofina, don ba zan bari in kwana a wangale ba saboda a cikin gida na ke ba'a kango ba".

Kallona ya tsaya yi kamar wani mutum mutumi, wani irin kallon mamaki yake bina da shi da har ya hanasa magana, sai da yaga dama ya sake min hannu yana sauke dogon numfashi tare da cewa,"ki kawo min kayan karin kumallo".

Kai tsaye nace,"rasawa kayi a in da ka kwana?".

Kallonsa da nayi kawai sai naji tausayinsa ya tsarga min, amma hakan na da ke na ƙara ɓata rai nace,"sai dai ka jira na rana".

Ficewa nayi da sauri na wuce ɗakina, a can na sha kuka na ƙoshi, ban ƙara fitowa ba sai da akayi sallar ƙarfe ɗaya tukunna na sauko. Ina shiga kitchen na sameshi gaban cooker gas yana ƙoƙarin ɗora tukunya. Yanda bai kalle ni ba haka nima ban kalle shi ba, na wuce na shiga hidindimuna, yana ta aikin girka ruwan shanyinsa nima ina aikin ɗora shinkafa da miya, har ya kammala ya fice bai min magana ba haka nima ban masa ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login