Showing 21001 words to 24000 words out of 87761 words

Chapter 8 - ƘAYAR RUWA Book 1 HAUSA NOVEL

HALIMAHZ   

20 Dec 2024

6100

rashin haihuwar bai damunki, shiyasa na ke ganin mu'amalar tamu ma bata da wani amfani. amma yanzu da na sami yarancan sai na ji kaso saba'in ya yaye na damuwar rashin haihuwar da bamu yi ba. amma kin sani ina sonki, matsayinki bai taɓa canjawa ba daga gare ni, don haka kar ki ƙara cewa na daina sonki kinji ko, ni na ki ne na har abada, ke ɗaya jallin jal Sa'idan Nazifi".

murmushi nayi ina kallonsa, jin maganganun nasa nayi kamar daɗin baki, sai dai kuma ba hakan ba ne, tabbas shi ɗin mai tsananin sona ne duniya kanta zata shaida hakan. sabuwar soyayyarsa naji ta kamani, sai dai na kasa amayar da duk wata magana da ke narke a cikina. duk tarin baƙin cikin da ya ƙunsa min naji ya gushe, tabbas ina son Hubbi, ina ƙaunarsa, kuma sonsa da ƙaunarsa ne yasa zan ci gaba da haƙurin rayuwa tare da shi ɗin, domin a ƴan kwanakin nan kaɗai na lura soyayya da komai nasa da ya tattare ya ɗora akan yaran can zai iya haifar min da babban ƙalubale.

"ya kamata mu sha soyayyar da zata mantar da mu komai da ya faru, komai ɗin ya zama tarihi".

ya katse tunanina da faɗin hakan. kuma lokaci ɗaya naji yana tattare rigata zai cire. lokaci guda ya fara aika salonsa ga jikina, tuni kuma na biye masa muka faɗa cikin duniyar jin daɗin ma'aurata, mun daɗe kafin mu sami natsuwar da muka rasa na tsawon watanni. da mamakina muna gamawa ya tashi ya fita a ɗakin ko wanka bai tsaya yayi ba, saɓanin da anan yake wankansa, wataran ma tare mu ke yi, mamakin hakan ya tsaya min a rai.
na miƙe cikin gajiyar jiki na shiga wanka, ko bayan fitowata kasa komai nayi sai kwanciya saboda ba ƙaramin gajiyar da ni yay ba, sai da ya ƙosar da kansa da yunwar watanni da yawa da ya ɗiba.
Cikin wucewar wasu kwanaki lamari ya ƙara taɓarɓarewa tsakanina da mijina, abun ya koma tamkar sa hannu, bai barni da yunwa ba zan ci in sha, amma babu zaman lafiya sam, na rasa kwanciyar hankali da jin daɗi daga gare shi, komai nayi ba daidai ba ne, abinci idan na yi ba ko da yaushe zai ci ba, magana idan nayi sai yaga dama zai amsa min, makarantar tahfeez ɗin da na ke zuwa ya soketa ya ce in har da aurensa akaina na gama zuwa makaranta. idan na zo masa da buƙatar wani abu ranar sai yayi tamkar ya tashi gidan da wuta, ya dinƙa masifa ban da aiki sai shegen tambayar a bani a bani kamar don ni kaɗai ya ke neman kuɗinsa, kullum a nurƙufanci ya ke fuska ba wata walwala, ya dinƙa ƙunci da ɗacin rai, ba zan san fitarsa ba haka ba zan dawowarsa ba. zaman haka na ga ba zai kai min ba na tambaye shi jari, dalilin haka har kuka nayi saboda cewa yay na sakawa dukiyarsa ido, ban da godiyar Allah sam, menene ba ya yi min da har sai na zubar masa da ƙimarsa, salon a ce ya gaza wurin kula da iyalinsa, cuta in zan mutu sannu ba zai ce min ba, haka zan ƙara ci ciwona in warke babu ganin likita balle magani, sai ranar ma da ya ɗan ji tausayina ina matsanancin ciwon kai ya siyo paracetamol kwali guda ya bani wai in aje kar in sake ciwo ya kama ni in zo masa da zancen magani ko asibiti, wannan ya ishe ni ko da ciwon ajali na ke.

ya daina tambayata ko shawarar duk abin da ya kamata ya aje a gidansa, sai dai ya kira Yaya, abin da ta ce shi zai yi, to yanzu ma ta ce da shi duk su nama da kayan marmari da ya ke ajiyewa ya daina domin ta lura ina masa almubazzaranci da kayan abinci, kuma ɗiba na ke ina bayarwa ba tare da saninsa ba. abubuwan baƙin ciki su ka taru su ka min yawa, shi na rasa laifin me na masa da duk ya ke ƙuntata min. ya hana ni fita kwata kwata, rasuwar da aka yi ta wata kakarmu ya barni da ƙyar ita ma sai da na sha kuka wajen magiya da roƙo, ita ma ɗin kafin ya bar ni sai da ya gama ci min mutunci da cewa ai idan na fita gulma da munafurci ke kai ni, da koyo fitsarar wulaƙanta aure da dangin miji, tun daga wannan furucin na sa kuwa na cirewa raina son fita ko da gidanmu ne.

A ɓangaren Rumana da Atika kuwa, zuwansu gidan ban da matsala da nesanta tsakanina da mijina ba abin da ya haifar, yara su ka zamar min annoba, don zan iya cewa ta silar su ne hargitsi ya girmama a cikin gidan aurena, har akansu ina neman na kamu da ciwon zuciya. ya nesanta tsakanina da shi ya kusanta tsakaninsa da yaran fiye da tunani, da su ya ke shawarar duk abin da zai yi a gidan, ko magana zai min wacca ta kama dole sai dai ya faɗawa ɗaya daga cikinsu ta faɗa min, ga yaran sun raina ni, ba wacce na isa na mata magana sai ta min rashin kunya da fitsara, har kallon idona su ke su faɗa min ai Abbansu ba ya sona su ma don haka basa sona, ko abinci na ba su sai su ce ban iya girki ba ba zasu ci ba, idan ya dawo kuma su gilla masa ƙaryar ban ba su abinci ba, ba zan taɓa baƙi ba ƴaƴan nan su ga baƙona da ƙima su gaishe shi. ranar da na tsawatar musu akan ba su gaida Ya Imam ba, Hubbi na dawowa su ka ce ai na zazzagesu na ce zan koresu a gidan, alhalin kuma sun gaida Yayan nawa amsawa ne bai yi ba. ranar na yi kuka na gode Allah, don zagi na cin mutunci da ƙare dangi yay min a gaban yaran. wannan dalilin na cin zarafina da ya ke a gaban yaran sai ya ƙara ba su lasisin yi min duk abin da suka ga dama, ji na ke har gwara kishiya da su, don su idan su ka kunna wata wutar bala'in ba zaka taɓa cewa yara ba ne kuma ba zaka iya kasheta ba. ga sun iya kirsa abin kamar koya musu ake, a gabansa ladabin da su ke yi min kamar uwarsu, amma da zarar an ce bai gidan duk wacca ta ganni ma sai dai tayi min tsaki, ban isa ko ɗaga murya in yi musu ba nayi hakan na shiga uku ranar, idan suka ɓata wuri nasa su gyara sai yaci zarafina. na yi musu faɗa akan ƙin makarantar da su ke hakan sai ya zama tashin hankali har yana faɗin saboda ba ƴaƴana ba ne ba kuma ƴaƴan ƴan uwana ba ne, ina baƙin ciki yayyuna sun kasa sadaukar min da ɗansu ko guda, shi ne shi saboda an ba shi zan takurawa yaransa, to in cire idona daga sha'aninsu tun da ba ni ke ɗaukar nauyinsu ba.

ɓangaren ƴan uwansa kuwa sun taso ni gaba da gorin haihuwa, ba su tsaya iyaka nan ba har faɗi su ke wai me ake da auren ƴan talakawa, sam ba su ga abin da aurena ya tsinanawa ɗan uwansu ba, ban da ma tawaya da yaja masa, da sun san haka aurena zai zamarwa ahalinsu masifa da ba su bari ya aure ni ba. idan na shiga cikinsu tamkar mushe haka suke ja baya da ni suna habaici, a ke min gorin wai ai ko da aka auroni haka na zo babu kayan gara. ƙalilan cikinsu ne ma su tausaya min, sauran duk daga kyara sai hantara da nuna ƙyama, shi yasa na kama kaina na ja gefe domin wulaƙancin na su ya fara min yawa, har bana so abun zuwa cikinsu ya ta so, mugun haƙurina kawai ke sawa na sharesu bana bi ta kansu, idan na ce zan fanɗare ba su isa ma su min kallon banza ba, to bana son tashin hankalin iyayena da damuwarsu, sannan kuma ina tsoron abin da zai jawa igiyar aurena samun matsala.

duk matsaltsalun da ke ta faruwa da sanin surukata, tun ina zuba ido in ga ta tsawatar akan abubuwan da ƴaƴanta su ke min naji shiru, ga mamakina ma sai na ga tana goyon bayansu, itama ta hau kan layinsu, ƴaƴanta su min, ɗanta yay min, itama tayi min. gaba ɗaya na rasa ta ina ƙiyayyar ta samo asali, na rasa laifina. idan na bada haƙuri sai ya ƙara zama wani babban laifin, abin da na lura da shi ma ba akan rashin haihuwa kaɗai yasa su ka tsane ni su ke tsangwamata ba, akwai wani dalili na su a gefe wanda su ka barwa kansu sani.
tabbas babu babban tashin hankali a gidan aure irin ace uwar miji ta sanyo ka gaba, ni a baya ban san wani matsalar uwar miji ba, idan naji ƙawayena suna ƙorafi akan uwar miji sai in ce ku ne dai baku iya zama da ita ba, ku sota tamkar mahaifiyarku sannan ku mata biyayya kamar taku mahaifiyar, to duk sanda na faɗi haka Hassana Tijjani ta kanyi murmushi kawai ta ce Sa'ida ba za ki gane ba, in uwar miji na sonki tana sonki kawai, in kuwa bata sonki to wallahi duk son da ɗanta ke miki zaman auren ba zai taɓa yi miki daɗi ba, in kuwa tana sonki to ko ɗanta bai sonki kya sami ƴar salama, ita uwar miji idan ta sako ki gaba duk wani kalar biyayya da za kiyi mata a banza ne, ashe hakan da su ke faɗa gaskiya ne domin kuwa ga shi ina ga ni, kallon banzanta gareni ya fi tsorata ni fiye da na ɗanta.

duk wannan tashin hankalin da na ke ciki iyayena da ƴan uwana babu wanda ya sani, ban taɓa faɗa ba kuma ban taɓa nunawa ba, sai dai kawai fa duk wanda yay min farin sani yana ganina zai ce ina cin matsala, hankalina ba'a kwance yake ba. domin kuwa lokaci guda na fita a hayyacina na ƙara yin wata muguwar rama, nayi duhu duk na sakwarkwace, na zama kamar mara lafiya ƙwaƙwalwa saboda kullum a firgice na ke, haka na ke jin duk rayuwar ta fita a raina, har so na ke dare yayi ɓarawon bacci ya ɗauke ni in sami ƴar salama, don bani da babban tashin hankali sama da wayewar gari, da zarar gari ya waye na shiga fargaba da taraddadi kenan.

uhmm so kenan, wallahi duk wannan tsananin da na ke ciki na gidan aurena har yanzu banji soyayyar mijina ta taɓu a raina ba, ban ji ina nadamar aurensa ba, ban taɓa jin ina ma ya sawwaƙe min in huta ba, sonsa na ke da dukkan raina, sam bana fushi da duk abin da yake min, uzuri na ke masa da kuma adu'a, tun bayan aurena da shi ban canja akalar adu'ata ba, kafin na yiwa kaina shi na ke yiwa, ni har na fi so ya zo yana min bambami akan ya shareni kwata kwata babu magana, kuma kullu yaumin bana fasa zuwa neman yafiyarsa da basa haƙuri a kowanne daren rana kafin kwanciyata, zan ta haƙuri ba zan karaya ba, Allah na zan ta faɗawa ya daidaita tsakaninmu, ya kuma bani ikon cinye jarabawar.

yau na tashi da matsanancin ciwon kai, hakan yasa na kasa fitowa gaba ɗaya, tun da nayi sallar asuba na durƙufa kan sallaya, bacci ma na ke so na koma amma na kasa saboda gabana da ke ta faɗuwa, ga shi ina so na tashi in je in tada yara su yi shirin makaranta sai dai in na tashi jiri sai ya mayar da ni.
da ƙyar dai na lallaɓa na tashi a daddafe na fita, ɗakinsu na shiga, na shiga banɗaki na tara musu ruwan wanka, sannan na fito na tashe su kan suyi wanka. su ka tashi da ƙyar kowacce na faman ɓata rai, zama nayi ina lallashinsu da ba su haƙuri akan cewa watarana sai labari, yanzu ne su ke da dama da lokaci na yin karatu, idan basu yi ba nan gaba za su ciji yatsa.

na lallama su da ƙyar su ka sauko su ka wuce banɗakin, na jaddada musu da su yi sallah in sun shirya. ɗaki na koma saboda sanyin zazzaɓi da ya rufe ni, ina shiga na ƙudundune cikin bargo ina ta karkarwa, kaina jinsa na ke kamar zai faɗo, haka cikina ma wani bala'in ciwo ya ke min. ban ankara ba kawai naji amai, duk ƙoƙarina na kar in yi akan gadon hakan sai da ya faskara, amai nayi sosai mai wahalarwar gaske. gaba ɗaya jikina sai ya saki, da ƙyar na kimtsa wajen a wahalce na dawo na kwanta, hawaye kawai na ke zubarwa saboda ni ɗaya na san irin azabar ciwon da na ke ji a jikina.
ina cikin wannan halin aka turo ƙofar ɗakin, Rumana naji tana cewa,"Anty mun gama shiryawa".

fito da fuskata nayi ta cikin bargon kaɗan, bana iya ko ganinsu da kyau, murya a wahalce na ce da su.
"wayata na kan mudubi ƙarfe nawa?".

Atika ta duba tana cewa,"seven twenty".

idona na rufe, har ga Allah ban da wani ƙarfi da ƙwarin da zan tashi in dafa musu abinci. a hankali na ce da su,"Rumana ban da lafiya, ku yi haƙuri kuje kitchen akwai sauran abincin dare a flask ɗin Abbanku ku ci kun ji, na san bai huce ba. abincin makaranta kuma zan bayar a kawo muku".

su ka yi shiru ba su ce da ni komai ba duk su ka yi cirko cirko. tsoron abin da zai biyo baya yasa na miƙe zaune cikin tsananin azaba, cikin dauriyata na yunƙura zan sauko Rumana ta ce.

"Anty ki koma ki kwanta, a bamu kuɗin makaranta idan mu ka je sai mu siya snacks kafin a shiga class, ba zamu iya cin sauran abincin jiya ba".

na san yanzu Hubbi bai tashi ba, don haka nace da ita,"duba ƙasan littafin can akwai ɗari biyar ku ɗauka".

ɗari biyar ɗin kenan na ke ta ririta ko da wata buƙata ta ujila zata taso min. ta ɗauko tana faɗin babu canji, na ce suje da ita tun da ba su yi breakfast ba, magani nasa ta miƙo min ta fita ta ɗauko ruwa ta kawo min. nayi musu adu'a tare da a dawo lafiya su ka fita, Rumana ɗin ce dama me sauƙi sauƙin kai, don ko yanzu ita ce tayi min sannu tana Allah ya bani lafiya, amma Atika har su ka tafi fuska a murtuke tana ta ƙunƙuni.

ni dai zan iya cewa cikin awa guda na kusa shanye sacet ɗin paracetamol, amma duk da haka babu wani sauƙi da na ke ji a tare da ni, ciwon ma tamkar ƙara shi ake yi, hawaye masu zafi ne kawai ke sauka kan kuncina, idan nayi haka zan ɗau waya in kira shi sai in tuna kashedin da yay min, ba kuma na so in kira gidanmu nan ma ya zama fitina, haka dole na haƙura.
adua na ke tayi, da kaɗan kaɗan kuma naji ciwon na ɗan raguwa tun da har ina iya buɗe idona, cikin baccin da ke son kwashe ni naji muryar Hubbi daga can nesa na kiran sunana da amon sautin da ya gigita ni ya firgita ni, zan iya cewa ban taɓa jin tsoro da firgici irin na kiran da yay min a yanzu ba, take kuwa na ambaci ƙalu innalillahi wa'inna ilaihi raji'un domin na san kiran bana lafiya ba ne, kafin na kai ga buɗe idanuwana ya banko ƙofar ɗakin, kana jin yanda ƙofar ta bada garam ka san a hasale ya ke.

"Sa'idaaa". ya ƙara kiran sunan a tsawa ce wanda hakan ya daɗa gigita ni musamman da na ke jiyo hucinsa kamar mayunwacin zaki.

ta cikin bargon da nake ƙudundune na amsa, sai dai bai ma jini ba, ya ƙaraso ciki ya yaye bargon yana sa hannu yay min wata muguwar fincikar da sai ganina nayi tsaye akan ƙafafuna, da sauri na runtse ido tare da dafe bango jin ina neman faɗuwa. na buɗe ido da ƙyar a ɗan runtse na dube shi na ce,"lafiya?, bana jin...".

ban ƙarasa furucina ba ya wanka min zazzafan marin da yasa ni zama daɓas babu shiri, a ruɗe na shiga girgiza kai ina kiran sunan Allah, tun da na ke da shi, tun da muke rayuwa gefen rigarsa bai taɓa sawa ya duke ni da ita ba, amma yau mari, marin ma a mawuyacin halin da na ke ciki, ban wartsake daga jin zafin ba ya shiga cewa.

"Wacce irin muguwa ce ke mara imani da tausayi, wannan ai tsagoron zalunci ne, banda rashin hankali da tunani irin naki ki bar yara su fita da sanyin safiya ba tare da kin basu abinci sun ci ba, haka babu abincin makaranta, Sa'ida haka aka yi miki da kina yarinya shi ne kike neman hucewa akan yarana?, wato saboda ba ƴaƴanki ba ne, ba ke kika haifa ba shi ne za ki azabtar da su da yunwa, wai me yaran nan su ka miki kika ɗora musu karan tsana?, kawai don ba ke kika haife su ba?, yunwa Sa'ida, kisa fa take yi, ko ke aka bari da yunwa ai an zalunce ki balle ƙananan yara, ba kya tunanin hakkinsu ya biki ya hanaki sukunin rayuwa, yaran nan fa yanzu ni ne mahaifinsu, ko darajata ai sa ci ki sassauta musu, amma saboda dai zuciyarki a mace take, tayi maƙil da baƙin ciki da zalunci shi ne za ki huce haushinki akan su, to Allah ya isansu, kuma ni bazan yafe miki ba...".

tun marin da yay min na nemi ciwon jikina na rasa, kallonsa na ke da mamaki ƙarara, idona tamkar an buɗe famfo haka hawaye ya ke sunturi saman fuskata, jujjuya kaina kawai na ke na rasa bakin magana. cikin kyarmar jiki na kamo hannunsa, na san zafin jikina da ya ratsa shi ne yasa shi ware ido akaina, ina kuka sosai na shiga ce masa.

"don Allah kayi haƙuri, wallahi ko kaɗan ba da gayya ko mugunta na bari su ka fita ba abinci ba, Hubbi ba ni da lafiya, ba ni da ƙarfin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login