Showing 27001 words to 30000 words out of 87761 words
sai dai maganar ya ke yi tamkar ba da ni ba, ni kuma nayi cak saboda kiɗima ina kallon bakinsa da ke motsawa.
"shugabar makarantarsu ce ta kira, ta shaida min an kai ɗaya daga cikin yarana asibiti har an kwantar da ita, in yi gaggawar zuwa domin akwai ɓuƙatuwar kashe kuɗaɗe. ina zuwa likitan ta shaida min ciwon ciki ne amma sun ɗauki hoto anyi gwaje gwaje, tun bayan awa biyu yanzu Atika na cikin matsanancin hali na rayuwa, bata farka ba, har yanzu bata motsa ba Sa'ida! bata samun isassan abinci a cikinta haka likitan ya faɗa".
yay shiru da maganarsa, naga ya ɗauko ƙaramar takarda alamun daman ita yake nema tun ɗazu, ya tura durowar ya kulle sannan ya gifta ni zai wuce na riƙe hannunsa na ce,"Dan Allah Hubbi kayi haƙuri, wallahi ban san bata da lafiya ba, ban kula ba kuma bata faɗa min ba".
Zafin hannunta shi ya ratsa shi sosai hakan ya tabbatar masa da zazzaɓi ne a jikinta bana wasa ba, ya kalli fuskarta yaga duk ta canja ga gefen bakinta a fashe, zai so yay tambaya akan silar ciwon, sai dai ba ya son jin wani ba'asi, hasalima fuskarta haushi take bashi.
ganin irin kallona da yake min sai na ɗauka ko ya fara sauka ne, sai na sake marairaicewa ko Allah zai sa ya fahimce ni, kumburarrun idanuna na hawaye na ce,"don girman Allah ka bawa zuciyarka salama ka tsaya ka fahimce ni. Hubbi kana yawan min nasiha akan fushi da haƙuri. Hubbi ka tuna wata rana da nayi fushi da kai tunasarwar da kayi min?...ka faɗa min fushi tamkar taɓin hankali ne ƙarshensa Nadama ne...ka tunasar da ni cewa fushi shi ne tarkon abin da shaiɗan yafi amfani da shi wajen halaka ɗan adam. haka ka ƙara tunasar da ni da faɗin manzan Allah(SAW) akan maganin fushi; yace idan kai fushi idan kana tsaye ne ka zauna, idan kana zaune ne ka kwanta ko kuma kabar wurin da aka saka kai fushin...Hubbi ka tuna...".
bige ni yay yana ƙwace hannunsa, ya nuna ni da yatsa yana cewa,"ba ki kai nayi fushi da ke ba...na sani kina so na sakko ne saboda na buɗe miki kitchen, to kinyi a banza wallahi don ba zan buɗe ba sai dai kema a kai ki asibitin, ai yanda kika hana yarana abinci kema haka za ki kwana babu abinci a cikinki, in yaso ki ɗanɗana abin da suka ɗanɗana. Useless woman".
ya faɗa yana hararata ya shige ya fita ya bar min ɗakin. nayi murmushi mai ciwo kan abin da ya faɗa, ban da abinsa ta ya zan nemi wani abinci a wannan halin bala'in da na ke ciki?, ta ina abinci zai samu gurbi a cikina?, ai hakan ba abu bane mai yuwa a wajana.
ina jin tashin motarsa alamun ya ƙara fita, na jawo ƙafata na fito daga ɗakinsa na koma nawa, na kwanta a kan gado nayi lamo jikina duk ciwo yake min, ina ta karkarwar sanyi. Haka na yini a kwance cikin matsananciya damuwa, ɓangare ɗaya cike da fargabar dawowar su Yaya haka kuma cike da tsananin tsoron hukuncin da Hubbi zai yanke.
tashi kawai na ke in shan ruwa in koma in kwanta har magariba babu abin da ya shiga cikina sai ruwa, na galabaita sosai ga ciwo ga yunwa ga aman ruwa, kwata kwata na rasa me ya ke min daɗin a duniyata, ban isa na tuhumi ubangijina kan jarabawa da ƙaddarar da su ke ta ƙwallo da ni ba tun aure, sai dai zan roƙe shi da ya bani ikon cinyewa zuwa matakin nasara.
bayan nayi sallar magriba ina zaune jugum, lokacin na kira wayar Hubbi yafi sau goma bai ɗaga ba duk saboda naji ya jikin Atika, hatta ita Yaya da Iyam sai da na kira su amma babu wanda ya ɗaga wayata, ban san wanne asibiti ba ne balle na bi bayansu, sai Lubabatu na kira tace min duk suna asibiti itama an barta ne da yara a gida, amma sun yi waya ance jikin da sauƙi. ajiyar zuciya na sauke don sai a sannn na sami relief, na kwantar da kaina gefen gado ina jan carbi, cikin tunanin da na ke zuciyata ke faɗa min ya kamata in kira mahaifina mu gaisa don mun kwana biyu bamu yi waya ba.
duk da ina fargabar in kira shi saboda yacca zai saurin gano damuwar da ke kan muryata, haka na daure na danna kiran saboda ko ba komai waya da shi ɗin zai yaye min damuwar da na ke ciki.
nemo lambarsa nayi, nafi ƙarfin minti uku ina saƙa da warwara akan in kira ko in fasa, can kawai na danna kiran ya tafi, kamar yanda ya saba duk lokacin da na kira shi yauma hakan ce ta kasance, ya katse kiran nawa sannan ya biyo baya.
da adu'a na samu raunina ya ɓoye da na ɗaga wayar nayi sallama.
"Salamu alaikum Abbaa".
"Wa'alaiki salam da ma'aikaciyar lafiya, Ƴar albarka ya aka yi saƙon zuciyata ya iso gareki da wuri haka, yanzun na ke cewa bara nayi sallar isha'i na kiraki, ina fatan lafiya kike da ke da mai gidan na ki ko?".
wani sanyi ya ratsa ni na farin ciki da jin muryar mahaifina. nayi dakiyar danne kukana na ce,"muna lafiya lau Abbaa, fatan kuma lafiya ku ke?, ya kasuwa?".
"lafiya lau fa Sa'ida, komai lafiya kinji, ba dai ki da wata matsala ko?".
kamar ina gabansa na ɗaga kai alamar ehh,"babu matsalan komai Abbaa".
"to ma sha Allah haka ake so ai, Allah yayi muku albarka gaba ɗayanku, Allah ya ƙara muku zaman lafiya da kwanciyar hankali, ya kauda duk wata fitina da saɓani a tsakaninku, Allah yay miki albarka kinji Sa'ida, Allah ya ba ki nasara da sa'a a rayuwa, mafi alkhairi yay ta bibiyarki. ki tura min lambar akawunt ɗinki zan saka miki ɗan abin da ya sawwaƙa".
"tom Abbaa na gode, Allah ya ƙara arziƙi ya ƙara muku lafiya da tsawancin kwana".
"amin ya hayyu ya qayyum, ya makarantar tahfeez ɗin na ki kuwa, ba dai kya wasa da zuwa ko?".
"ina zuwa Abbaa".
"kema da ke cikin masu saukar ta bana ne?".
"a'a sai wata shekarar Abbaa".
"to Allah ya bada ilimi mai albarka, ki gaida mijin naki. yanxu ina masallaci sai in na koma sai ta kira ki".
har nayi haka zan kashe kiran sunana da yay ya dakatar da ni. na amsa masa sai naji yay shiru, tunanin ko kiran ya yanke ne hakan yasa na kalli screen ɗin kafin na kuma mayarwa kunne in sake cewa,"hello Abbaa".
ajiyar zuciya naji ya sauke, shiru bai ce komai ba sai can yay nisa ya ce,"kina jina Sa'ida".
na ce,"ehh Abbaa ina ji".
ya ce,"walwala ta burin zuciyar ɗan Adam tsakanin abubuwa guda biyu take, farin ciki da baƙin ciki. idan abin farin ciki ya ratsa zuciya fuska zata nuna, za ta yi ƙyalli, zata sake sosai wajen bayyanar da farin cikinta, daga nan kuma murmushi da dariya su ziyarceta. idan kuma baƙin ciki ya ratsata sai tayi baƙi, ta turnuƙe, idanu suyi jajur su cika da ƙwalla, idan ya tsananta hawaye su jiƙa fuska, murya ta bada labarin yanayin da ake ciki...Ƴata kar ki manta da wanda kike waya, mahaifinki ne mai iya gane halin da kike ciki ko bai kalle ki ba, Sa'ida saki kukan da kike ta dannewa tun a sallamar farko, yi kukanki yacca kike so ba zan hanaki ba kuma ba zan tuhume ki dalili ba, domin shi kuka hanya ce ta rage raɗaɗin da ke cikin zuciya, sai dai ina so na tuna miki cewa kuka ba ya maganin matsala...yi kukan iyaka iyawarki ina sauraronki".
zuciyata naji ta matse wani abu ya daki ƙirjina, Abbaa da kansa yau ke bani izinin yin kuka, mutumin da sauyawar yanayina kaɗai ke tada hankalinsa amma yau shi ke ce min nayi kuka iyakar yina, shin ya san matsalar da na ke ciki ne?. lokaci guda dauriyata ta ƙwace na fashe da matsanancin kuka me taɓa zuciyar duk me saurare, kamar yanda Abbaa ya faɗa sam bai yi ƙoƙarin hanani ba, bai kashe kiran ba haka bai ce komai ba, sai dai ina jiyo saukar numfashinsa, haka nayi kukana na gode Allah, murya a dusashe na ce,"Abbaa na gama, amma babu wata matsala, dama kukan soyayyarku ne kawai na ke yi".
murmushin manyance naji yayi, bana ganinsa amma ina da tabbacin sai da ya gyaɗa kai kafin ya ce,"yaro yaro ne". kana ya ƙara cewa,"na sani soyayyar da kike mana zata iya sawa ki zubar da hawaye musamman idan kika tuna cewa akwai wani tabbataccen lokaci da dole mutuwa zata raba mu. sai dai ba hakan ne musababbin kukan na ki ba, muryarki kawai ta shaida min akwai matsala, haka ne?".
na rumtse ido nace,"haka ne Abbaa".
"to me yasa za ki ɓoye min?".
"kayi haƙuri Abbaa".
yay shiru na ƴan sakanni kafin yay gyaran murya. "saurare ni da kyau Sa'ida. mu iyayenki ne, babu wanda zai tsaya miki tsayin daka a duniyar nan sama da mu bayan mahallicinki. adu'armu a gareki kaɗai ta isa ta magance miki kowacce matsala da kike ciki, kuma ki sani adu'a na canja ƙaddara". yay amfani da kwantaccen lafazi wajen faɗin hakan.
murya na rawa na amasa,"haka ne Abbaa, ba wai na ɓoye muku ba ne saboda tunanin ba zaku iya min komai ba, kawai shiga damuwarku akan hakan yasa Abbaa, amma kayi haƙuri Abbaa, adu'arka kawai na ke so".
nayi maganar da muryar kuka ina me share hawayena.
"Sa'ida ni mahaifinki ne, ba lallai sai kin ɓoye min kina cikin matsala da damuwa ba, muryarki zata bayyana min. ba zan tsaya shiga sha'anin aurenki ba, sai dai ina so na tuna miki duk lokacin da tsananin rayuwa ya dame ki, abu na farko da zai sa ki farin ciki shi ne ki tuna ke musulma ce kuma Masoyiyar Manzon ALLAH [S.A.W]. Duk tsananin da kike ciki ki tuna cewa akwai wanda ya fiki shiga tsanani, Ki tuna cewa kinfi mutane da yawa jin daɗin rayuwa. wannan rayuwar tamu ta duniya da kike gani gaba ɗayanta jarrabawa ce, Sa'ida aure kan saka mutum ya yi farin ciki a rayuwa sai dai duk tsananin farin ciki ba shi zai hana ma’aurata fuskantar matsaloli ba. ba abin mamaki ba ne idan a wasu lokuta anata fuskantar matsaloli a auratayya, domin rayuwar aure gaba ɗayanta haƙuri ce, haka kowacce mace da kalar jarabawarta a gidan auranta. ko babu komai ki gode Allah da ya baki miji me tsananin sonki da ƙaunarki gami da tausayinki. ni dai abin da na ke so da ke kar da ki dinƙa barin damuwa a ranki, hakan zai cutar da ke. kamata yayi duk san da kika kasance cikin halin tsanani, to ki ɗaura alwala ki fuskanci alƙibla ki gana da ubangijinki, a gaban mahallicinki ya kamata ki zubda tarin hawayenki, ki ƙaskantar da kanki a gabansa kina me roƙonsa cikin kirari da tsarkakewa, shi ya san halin da kike ciki kuma shi zai magance miki. kuma hakan zai sa ki samu rangwamen komai, tun haihuwarki mu ke miki addu'a kuma ba zamu daina ba har mu kai ga kushewa, kuma ina miki alƙawarin ƙara dagewa akan yi miki adu'a Ƴata. Allah bai hanaki don baya sonki ba, bai bawa wasu don yafi sonsu akanki ba, kema yana sonki kuma zai ba ki mafificin alkhairi cikin yardarsa da amincinsa. Allah yay miki albarka, Allah ya shiga dukkan lamuranki, ya yaye miki dukkan ƙunci, ya kawo miki salama da natsuwa. ayi haƙuri a ƙara haƙuri a kuma ci gaba da haƙuri kinji ƴar albarka, ina faɗa miki hakan ba kuma zan fasa faɗa miki ba ko da yaushe; haƙuri, uzuri, kawar da kai da kuma yafiya, ki kamasu tabbas kin kama makaman nasara da farin ciki, Sa'ida wanda ba ya haƙuri ba ya uzuri ba kuma ya yafiya to shi ne ke samun naƙasun farin ciki, amma me haƙuri da tawakkali da fawwalawa Allah komai wallahi ba ya tawaya, bayan tsanani sai daɗi da izinin Allah".
yay shiru, ni kuma kukana ya ƙwace, cikin muryar da ta disashe da majina na ce,"na gode Abbaa nah, na gode sosai, ubangiji Allah ƙara muku lafiya, yaja min da ranku, yasa kuyi kyakykyawan ƙarshe".
"amin ya Allah ƴar albarka. amma ki daina kukan, ki kuma yi min alƙawarin ba za ki ƙara ba".
"in sha Allahu Abbaa".
"zan tura miki kuɗi sai dai kiyi hakuri babu yawa".
"na gode Abbaa Allah ƙara arziƙi da wadata"
"amin ya Rahman, sai gobe kwayi waya da Ummanin, kar taji ki a wannan yanayin ta hana kanta sukuni, Allah ya sadamu da alkhairinsa, ki gaida ɗan nawa".
ya ƙarasa faɗa yana kashe wayarsa, wani sabon kuka na ƙaunar mahaifina ya zo min sai dai nayi saurin toshe bakina tunawa da alƙawarin ce masa ba zan ci gaba da kukan ba. kai na kifa a gefen gado ina lallashin zuciyata da tuna kalaman mahaifina waɗanda su ka fara kwantar min da hankali, tabbas ina mai godiya ga Allah bisa ni'imar barmin su da yay a raye. wallahi ina son Abbaana, ban san ya zan kasance ba a duk san da aka ce ba ya raye, ni na sani ta kowacce fuska nayi dacen mahaifa, adu'ata Allah yasa suci moriyata kafin mutuwarsu, ya kuma sada su da aljanna maɗaukakiya.
banɗaki na shiga nayi wanka, bayan shiryawata na shiga laluba jakar makarantata, cikon hukuncin ubangiji sai ga shi na samo wata matacciyar ɗari biyu, hamdala nayi ga Allah ina miƙewa na fita cikin ɗan guntun farin cikina na samun kuɗin, wurin me gadi na isa na ba shi na ce ya taimaka ya siyo min maganin ciwon jiki, idan akwai sauran canji ya siyo min awara ko gurasa. cikin mintunan da ba su haura ashirin da biyar ba sai ga shi ya dawo, nayi masa godiya sosai sannan na koma ɗakina, awarar ɗari da hamsin ce ba wata mai yawa ba guda uku, na ci na shiga banɗaki na sha ruwa na kuma sha maganin. har aka yi sallar isha'i ina ta jira ko zan ji motsin dawowar Hubbi amma shiru, ni hankalina ma gaba ɗaya na kan halin da aka ce yaran suna ciki, idan na ɗau waya zan kira shi sai zuciyata ta kwaɓeni akan hakan, daga ƙarshe kawai na aje wayar na kwanta bayan nayi sallar isha'i.
wajen ƙarfe biyu na dare na farka firgigit, na sauko da sauri na faɗa banɗaki na yo alwala, sallah na tayar ina ta jero nafilfili kuma cikin kowacce sujjada da tahiya kuka na ke ga Ubangijina, ina mai yi masa kirari da tsarkakan sunayensa, ina roƙonsa da ya kawo min sauƙi a halin da na riski kaina, ya wanzar da alkhairansa a gare ni, ya canja min tsanani zuwa sauƙi, baƙin ciki zuwa farin ciki, damuwa zuwa walwala, tashin hankali zuwa kwanciyar hankali da zaman lafiya.
ni dai cikin ikon Allah tun raka'ar farko na fara jin sukuni na ziyartar zuciyata, haka bayan na idar na ɗau ƙur'ani na fara karatu, karatun da ban daina ba sai da na ji an fara kiran sallar farko, wallahi zuwa wannan lokacin sai naji zuciya tayi wasaisai, naji tamkar ba'a taɓa dasa damuwa da ƙunci ba a tare da ni, haka kawai sai na ke jin wani farin ciki da ban san dalilinsa ba yana ziyartata, naji ina mantawa da faruwar komai yana barin jikina yabi iskar ɗakin. har sai da aka yi sallar asuba bayan na gama lazimi na ji bacci ya ziyarci idona, a sannan na miƙe da ƙwarin jikina da bana jin ciwo ko ɗis na hau gado na kwanta, bakina ɗauke da tasbihi bacci me daɗin gaske yay awon gaba da ni.
ba ni na farka ba sai ƙarfe goma na safe, yau dai hankali kwance na sakko saɓanin da dana ke sakkowa a gigice idan na farka irin haka a makare, ba don komai ba sai don tunawa da abincin mai gidan, ni ai ko babu komai ma kulle kitchen ɗin nasa yay min rana, tun da ga shi nayi natsatstsen bacci, kuma na huta haka babu ƙorafin ba ki kammala da wuri ba, babu ɗauko ɗauko, maida maida.
wanka na shiga nayi, na tsaya gaban madubi ina mamakin irin ramar da nayi, ka rantse da Allah zaftarata ake yi, hannu na kai na taɓa kumburarren ciwon bakina, nayi wata dariyar takaici kawai ina girgiza kaina, hoton dukan da na sha jiya ya haska min tarr a ido, haka zagin da na sha yay amsakuwwa a kunnena, a jiya ina cewa na bar su da Allah ya saka min, amma a yanzu kam na yafe musu babu kuma ƙullacinsu a raina sam, na san zan daɗe kafin na manta abin da suka min amma zan yi dukkan iyawata don ganin na manta ɗin ko saboda kar na dinƙa ganinsu da abin har yasa ni jin ɓacin rai.
humra na ɗauko zan shafa, sai dai ina ɗaukowar fuskata ta washe da dariyar da haƙorana suka bayyana, ba don komai ba sai don tunawa da Ummani, duk san da na kirata na ce Ummani Humra ta kusa ƙarewa zata ce Sa'ida amma shanta kike ko, ko kuma girki kike da ita ne in sa a koma haɗo miki duro guda. haƙiƙa ina son mahaifiyata, Allah dai ya bani ikon kyautata musu a rayuwa. rigar bubu na saka na sanya hular shatali, na ɗan yi tsaki saboda yanayin kitsona da ya tsufa.
agogo na kalla ƙarfe sha biyu na rana da ƴan mintuna, na jijjiga kaina da mamaki, har na nufi ƙofa zan fita sai zuciyata ta dakatar da ni da ce min in fita in yi me?, ai kawai in koma in kwanta lokacin hutawa ne Allah ya kawo min, idan har ya dawo gidan ai dole zai zo ya tada ni ko dan ya ci zarafina, musamman da ya zamana laifin nawa tsagin jikinsa na taɓa.
kan gado na koma na jingina bayana da filo, ba zan iya kwanciya ba don na gaji da ita, waya na ɗauka na kunna data na shiga wattpad na lalubo sunan Oum Mumtaz da Nana Haleema, nayi saving sababbin littafansu a library, na kashe data nan da nan kuwa na hau karatu, karatun littafin hausa sam bai dameni ba, amma ko da na leƙa wani group ranar nan naji ana ta koɗa littafan nasu na ce ni kam in sha Allahu sai anyi