Showing 75001 words to 78000 words out of 87761 words

Chapter 26 - ƘAYAR RUWA Book 1 HAUSA NOVEL

HALIMAHZ   

20 Dec 2024

6117

mayar da ɗan kunnayen na yafa gyalena na bi bayansa. Bakina ɗauke da sallama na shiga, na samesu kan kujera ɗaya ita tana daga gefen hagunsa, na wuce na zauna kan kujerar da ke gefen damansa. lokacin ta ɗago kai muka haɗa ido da ita, sai sannan naga fuskarta don ɗazu da aka kaita wurina fuskarta na lulluɓe cikin lafaya, ba laifi kam tana da kyau amma ba yabon kai ba tabbas na fita kamar yanda Safiyya ta ce. kallon kusan minti guda tayi min kafin ɗauke ido daga kaina, in da na kasa gane manufar kallon nata don har motsa baki tayi ina ga gaisawa zamu yi sai kuma ta fasa, nayi ta kallonta ta gefen ido ina so na karanci yanayin da ke saman fuskarta, a raina na ce Allah ya tura miki aniyarki in har bada nufin alkhairi kika min wannan kallon ba.

Shima ina kallonsa yay min wani kallo, ni na kasa gane musu ko kwalliyar da ke jikina ne ya janyo hakan oho, tunda dai ya san ba shi ya siya min abin da yake jikina ba tun daga sama har ƙasa, ko kuma yanda na watsar da shi da lamarin bikin ne ya dame shi ohon masa dai, ga yaga kwana biyu yana faɗa ina mayar masa babu kuma tsoronsa ko shakkarsa tare da ni.
Ya tashi ya koma kan kujerar da ke fuskantarmu ni da ita, salati yace muyi ga shugabanmu fiyayyan halitta kafin nan yay bismillah tare da koro adu'oi kana yay gyaran murya ya shiga magana.

"Na san kun san dalilin da ya taramu anan ko da ban faɗa ba. Sa'ida da ina zaune da ke ɗaya matsayin matata yanzu kuma na kawo miki abokiyar zama gata nan Zahra'u, bani da wata manufa ta cin mutunci ko tozarci ga ɗayanku, Allah ne yay lamarinsa, ya ƙaddara cewa zan zauna da ku biyun matsayin matana, haƙiƙa zan kwatanta adalci a tsakaninku iyakar iyawata bisa yanda addini ya ce, sai fatan ku bani haɗin kai".

Ya numfasa kana ya sake cewa,"Sa'ida ke ce Babba wato uwar gida amma a shekaru ke ce ƙarama".
Ya dubeta ya ce,"Zahra'u ke ce ƙarama a zaman gidan nan amma a shekaru ke ce Babba. Saboda haka kowacce ta kama matsayinta, kuma ina roƙonku da ku kama mutuncinku ku girmama juna ku zauna lafiya, ba na son fitina ba na son tashin hankali, a son raina idan da zaku haɗa kanku ku zama tamkar ƴan uwan juna zanyi matuƙar farin ciki da hakan, duk da ina ji a jikina ba za ku bani kunya ba".

Kaina a ƙasa ina wasa da yatsuna na ce,"in sha Allah ta ɓangarena ba ka da matsala na san kai kanka kana da wannan yaƙinin, na maka alƙawarin zama lafiya tare da kai da matarka, zan kuma iya shugabancina matsayina na uwar gida, ina fata itama daga gareta matsayin wacca ta fini shekaru ".

Itama ta ce,"nima ba zaka ji wata matsala ta kunno kai daga gare ni ba. fatana ka zama adalin miji".

Ina kallonsa ya gyara zama ya ce,"sai maganar kwana, Sa'ida ke ce Babba me za ki ce akan hakan?".

Shiru nayi ina ƙoƙarin daidaita natsuwata don kar su fahimci halin da na ke ciki, ya maimaita maganar daidai da buɗe bakina da yawun cikinsa ya bushe sannu a hankali na ce.
"To ni duk yanda ka yanke ba ni da ja akai daidai ne a wurina".

Ya kalleta ya ce,"Zahra'u ke fa?".
Tayi shiru na ƴan sakanni kamin ta ce,"ba kwana biyu ne ake yi ba dama? amma dai kai ne shugaba kai ya kamata ka yanke".

Numfasawa yay yana dubanmu ya ce,"na yanke kwana bibbiyu na san hakan ba zai sa wata ta cutu cikinku ba. Sannan ke Sa'ida tsawon sati guda za ki kasance a kitchen, kuma idan kinyi girki za ki ke haɗawa ne gaba ɗaya har da ƴar uwarki. Zata karɓi girki a washegarin rana ita yau wato asabar me zuwa kenan".

Ƙwalla ta cika idona nayi ƙarfin halin maida ita na ce masa,"tom babu matsala, asha amarci lafiya. Allah kuma ya bada ikon yin adalci a tsakani".

Jiki a saɓule na miƙe na fita bayan mun shafa adu'a. Ai fa tun da na shiga ɗaki kuma sai kuka haka na dinƙa jin zuciyata kamar zata buga, karo na biyu da na raya dare yanda naga rana don sam bacci yay ƙaura a idona, wani azababben kishi na ke ji yana neman haukatar da ni musamman idan na tuna cewa yanzu fa Nazifi tare yake da wata wacca zai yi mata dukkanin abubuwan da yake yi min. da nanata salatin Annabi a raina na samu zuciyata ta fara sanyi har na kwanta bacci lokacin ma gari ya waye.

Kuma da safen shi ya zo ya tashe ni a bacci yana tambayata paracetamol, na ce masa banda shi duk kuwa da ina da shi ɗin. zan koma baccin ya ce na tashi inje in ɗora abincin kari ko ban duba lokaci ba ne, Zahra'u na da ulcer kuma shima ai na san ƙa'idar lokacin cin abincinsa, yara kuma za su tafi makaranta don haka tun muna daɗi da shi kar na tsiri abin da zai zo yana mana babu kyau. sai da ya tabbatar na tashi kana ya fita a ɗakin bayan ya kora min kashedin kar na bari Iyam ta buɗe ɗaki ban kammala haɗa abincin safe ba.

Cikin kwanakin da suke ta shuɗewa Nazifi da Amaryarsa amarci su ke ta sha na ban mamaki, tun ranar da aka kawota ba ya fita ko'ina idan ba masallaci ba, kullum suna ɗaki maƙale da juna, ko masallaci zai je sai ta raka shi har gate, haka duk lokacin da na fito zan sauka sai na jiyo sautin dariyarsu nuni da cewar suna cikin jin daɗin duniyar, dariyar Nazifi da zan ce na kusa shekara ban jita ba, shi yasa na ke baƙin cikin tarewarsu anan saman domin abin da matuƙar ciwo amma haka na ke shanyewa, sai dai dole ya raba mana ko na koma ƙasa gaba ɗaya ita ta dawo saman ko ni na dawo sama ita ta koma ƙasa, don na lura da gayya su ke abin na su.

Rabon da na saka shi a idona tun washegarin kawo masa amaryarsa da ya zo ya bani dubu ashirin ya ce ko da zan buƙaci wani abu da kuma kuɗin makarantar yara idan sun buƙata saboda ba ya son damu kar suke zuwa can wurinsa, tun daga wannan ranar ko abinci na gama zai ce na barsa a dining za su sakko su ci, duk wata magana ta waya mu ke yinta, da kansa zai kira ni da safe mu gaisa, idan bai kira ba kuma shikenan ba dai zan gansa ba ko da inuwarsa tunda aiki ke fitar da ni, da na sauka na gama na dawo ɗaki shikenan yanzu sam bana zaman falo gudun ɓacin rai, shi kuwa yana ɗakin amaryarsa ko da zai fito ma ba sani zan ba, ɗakin yaran ya mayar musu ƙasa kusa da na Iyam da wataƙila in ke cin darajarsu idan ya zo dubasu ya leƙo ɗakina.

Ita kuwa mun haɗu sau biyu ranar ina kicin ta shigo muka gaisa da fara'arta, tayi min sannu da aiki tana cewa zata tayani na ce mata a'a ba na saka amarya aiki ba ta bari ta gama shan amarcinta, taƙi tafiya ta zauna muna hira da ita jefi jefi babu laifi dai tana da kirki a yanda na fahimta duk da ba lokaci guda ake gane halin mutum ba, har da cewarta yanayina na burgeta ita kam, sai kuma take tambayana ya yanayin cin abinci a gidan ya ke saboda ta san yanda zata tsara lokacinta, hutun sati biyu aka bata a wurin aiki ga shi aikinsu fitar ƙarfe bakwai ne kuma sai huɗu ta ke baro office, na faɗa mata duk lokacin da na ke girkina ta jinjina kai cikin harshen turanci tayi wata magana da ban shaida me tace ba haka kuma ban nuna mata ban gane me tace ba ɗin.
Rana ta biyu kuwa da ta yini a ɗakin Iyam ranar ina yiwa Iyam gugar kaya, suna ta hira da ita akan wata mata da ita Zahra'un tace tana yi musu aiki ita kuma Iyam na cewa ai ƴar garinsu ce, shine har ta ɗauko dutsen gugarta ta zo muka ƙarasa gugar tare duk da Iyam na ta ce mata ta ƙyale mini na yi amma tace babu damuwa taga ai na sha aiki.

Haka dai rayuwar taci gaba da tafiyar min zaman gidan Nazifi haƙuri kawai na ke yi domin ba daɗinsa na ke ji ba, duk wasu ayyuka da ɗawainiyar masu zama ƙarƙashinsa ni ce, idan na yi kuma kullum a ban iya ba nake a wajen Iyam, wulaƙanci kuwa ban fasa shansa ba sai wanda ya ƙaru ita ta min ƴan uwan idan sun zo suyi min duk da sun rage zuwa yanzu ina ga ko sun bari a gama cin amarci ne. Yawan kuka da sanya damuwa a rai kawai na ragewa kaina saboda gudun kamuwa da wani ciwon, amma haƙurin duk da na ke kam ina yinsa ne saboda abu guda biyu zuwa uku, na farko ina tunawa da rantsuwar Kaka na cewa idan har na fito to ba zan zauna a gida ba sai in ya mutu, da kuma tunanin shin idan auren ya mutu to wa zai auri bazawara irina wacce ke da naƙasun haihuwa? Kuma idan ma auren zan yi wanne kalar mijin zan ƙara aura? don ni tun daga kan Nazifi na sare da duk wani namiji da ita kanta rayuwar auren, ga mahaifiyata da na ke ta son gani amma har wa yanzu Abbaa bai sauka akan bakansa ba.

Ranar cikar sati guda da yamma lis ina ɗaki muna chart da Safiyya, Nazifi ya shigo, shigowar tasa kuma ta matuƙar bani mamaki da ɗaure kai gami da tunanin me ya kawo shi, domin rabonsa da ɗakina yau kwana biyar, ni sai naji gabana ma ya faɗi da zuwan nasa. Na gaida shi ya amsa fuska babu yabo babu fallasa, ya ce na tashi na ɗauko masa kujerar madubi zai zauna, na bisa da kallo na ƴan sakanni kamar dai lamarinsa babu lafiya ko kuma yana rashin lafiyar rabuwa da amaryarsa ne oho, na ɗauko na ajiye masa ya zauna ni kuma na ci gaba da danna wayata.

Tsakanin mata da miji sai Allah, duk irin yanda na ke matuƙar jin haushinsa da fushi da shi sai yanayin shirun nasa ya dame ni duk da hakan ba sabon abu ba ne, to amma yanayin yanda ya sakani a gaba ne kamar akwai damuwa babba, wani abu da na tuna yasa na ɗago na dubesa na ce,"Baka da lafiya ne?". Na tambaya cike da tsantsar kulawa har ina kai hannu na taɓa wuyansa sai dai naji jikin nasa sanyi ƙalau.

Ya ce,"Lafiya lau na ke. Ya ƙoƙarinki? na gode".

A hankali na ce,"babu godiya a tsakaninmu. Amma sai dai ban yarda da babu komai ɗin ba, ka faɗa min don Allah akwai wata damuwar ne?".

Sai da ya gama ƴan kamekamensa kana ya ce,"ina so zamu yi magana ne da ke sai dai ban san ta yanda za ki karɓeta ba".

Ina kallonsa sosai da nazari nace,"ka faɗa kanka tsaye ba matsala zan fahimce ka".

Zamansa ya sake gyarawa kana ya miƙo min baƙar leda nasa hannu na karɓa. na buɗe ledar idona ya sauka akan bandir ɗin kuɗi ƴan dubu dubu sabbi masu uban yawa, na ɗaga kai na kalle shi ina jiran ƙarin bayani.

Ya murza hannunsa kafin ya ce,"Zahra'u ce bata da lafiya don yauma a asibiti mu ka yini, to likita dai yace tana da buƙatar kulawa, kinga ƴan uwanta duk ba anan su ke ba balle a samu wanda zai zo ya zauna da ita. Na san ba ki da matsala Sa'ida shiyasa na ce zamu yi magana da ke ta fahimta ki faɗi farashin da za ki siyar min da kwanakinki na tsawon lokacin da zata ji sauƙi".

Yay shiru yana kallona, ni kam har ya gama maganarsa kallonsa kawai na ke yi idona waje tamkar za su faɗo, yayin da a wannan lokacin hawaye sun gama wanke min fuska. Murmushi na yi me ciwo sai dai daga ni har shi zamu iya rantsewa tunda muke tare da juna irin wannan murmushin bai taɓa fita a fuskata ba, cikin wani irin murya da ban san ina da shi ba na ce,"uhmm sai kuma me?". Na faɗa ina haɗiye ƙullutun wani abu me masifar ɗaci.

"Nan dubu ɗari biyar ne, idan kinga kina da buƙatar ƙari ki faɗa ko nawa ne a shirye na ke da na ƙara miki muddin kin amincewa buƙatar da na zo miki da ita".

Na kaɗu da maganar Nazifi sosai, na rasa me zan ma ce da shi kamar yanda na rasa a wanne sahu zan sanya Nazifi, tunani na ke anya kuwa Nazifi cikin hankalinsa ya ke? Me ya ke nufi da wannan maganar da ya zo min da ita? Idan ni ce bai buƙata mene dalilin da yasa yake zaman dole da ni? Ina tarin ilimin addinin da na sani a ƙoƙon kan Nazifi?
Dukkan tunanina ya tsaya cak lokacin da Atika ta faɗo ɗakin tana haki, ɗago idona itama Rumana ta shigo kamar an jefota, kafin nayi tambayar lafiya saboda yanayinsu da ke shaida akwai matsala, sai ji nayi Atika na cewa da shi,"Abba ka je Iyam ta faɗi". Maganar Rumana ta kutsa cikin tata itama tana cewa,"Abba Anti Amarya ce ta mari Anti Fati kuma Iyam taje wucewa hannun Anti Amarya ya bigeta ta faɗi a ƙasa tana can ta kasa tashi, Abba ka taso da sauri Anti Fati tana cewa sai sun yi rigima da Anti Amarya ita kuma Anti Amarya ta ce sai ta faffasa mata baki".

Da saurinsa ya miƙe ya fita yaran suka mara masa baya, ni dai idona ya maƙale akan ƙofar ɗakin ina tunanin na tashi na bi bayansu ko nayi zamana?. Zuciyata ta hane ni da tashi na fita, na zauna cikin girgizar lamarin da Nazifi ya zo min da shi, siyan kwanana! bai damu da nawa hakkin ba!
Jiyo sautin muryar Zahra'u a sama na miƙe na fita, har zan sauka na fasa na leƙa ta saman ina kallonsu. ta na tsaye tasa hannu ta matse bakin Fati wacce ke tsaye a gabanta tana faman matsutsun ƙwacewa.

Shi kuma yana tambayar ba'asin abin da ya faru. Ran Zahra'un a ɓace babu sauƙi ta ce,"Honey waɗanna irin gidadawan mutane ka ke bari suna shigo maka gida anyhow? Kawai fa na sakko ne zan je wurin Iyam sai na isketa bisa gaban dining tana buɗe flask na abinci, to ni ban san wacece ba tunda ban san face ɗin nata ba dalilin da yasa na dakata na iskota ina tambayanta, daga tambaya kuma saboda fitsararriya ce unguwar zoma bata mata gashin baki ba shine take da zarran yi min tsaki tana faɗin na raina mata hankali, Honey can you just imagine ƙanwata ta kusan huɗu na min tsaki? Impossible i must teach her a lesson ba na tolerating raini ko kaɗan".

Iyam wadda ta miƙe da ƙyar ta ce,"To Zahra'u yi haƙuri ki cikata ai rashin sani ne. kinga kwana biyu bata gidan shiyasa ba ki shaidata ba Amma daga yanzu ki shaida fuskarta ƙanwarki ce ita ce ƴar Autata, nan take tare da mu ai, ranar biki ne ta koma can gida".

Iyam na yin shiru Zahra'u ta kaɗa kai tace,"Am so sorry to say Iyam amma wannan ba magana kika yi me kyau ba, ba hanyar gyara kuma a ciki, kamata yay ki dubeta kiyi mata faɗa kice ta bani haƙuri before then na saketa, amma ba in ƙyaleta ba gobe taji daɗin repeating ma wani, ban sani ba ko halinta ne haka kuma wataƙila tana yiwa matar gidan tana ɗauka sai dai ni ba me ɗauka ba ce".

Sai tayi shiru tana mayar da kallonta ga Fatin ta ce,"yanzu za ki iyama Yayanki Nazifi tsakin da kika min ko za ki iya yiwa Maijidda(Yaya)? To ki sani ba sa'arki ba ce ni, ke imfact ko da shekaru guda muke da ke tunda har Yayanki ya auro ni na wuci ki min rashin kunya biyayyarki dole garen".

Ta ƙyasta yatsu da ƙara cewa,"And just for today zan ɗaga miki ƙafa amma for the next time idan kika ƙara wallahi sai na saɓa miki kamanni".

Ta saki bakin Fatin da ke aikin zare ido don da alama ruƙon bakin da aka mata ba na daɗi ba ne. Kana ta koma ga Nazifin tana ce masa,"you just kept silent ka ƙi cewa komai. Anyway ka gargaɗi ƙanwarka, idan ma akwai wasu irinta to ka tara su kaja musu kunne, ba ƴar iska ka auro ba so they have to respect me kaman yanda su ke respecting na ka. Kuma zai fi kyau ku yi shari'a da wadda tayi muku rainonta domin bata yi mata tarbiya me kyau ba ta cuceku".

Ta kalli Iyam ta ce,"ki yi haƙuri bana sane na bigeki ban san da zuwanki wajen ba ne".

Ta na gama faɗin hakan ta bar wajen, kuma yanayinta kawai zai shaida maka zuciya ta kai nesa, ganin tayo saman nayi saurin komawa ɗaki. Abin da ya dameni shi ya damen balle na tsaya fassara yanayin da naji akan abin da ya faru tskninsu. Na zauna na saka kuɗin da Nazifi ya bani a gaba ina kallonsu, kallon da yay sanadin haska min hoton wani lokaci can baya shekaru uku da suka gabata wanda ya haska tarrr a cikin kaina, ina hasko lokacin da na fita na bar gida kafin sallar asubahi Nazifi na kwance yana bacci, na fita cikin mamakon ruwan saman da ake narkawa ina me bara gurin ubangiji yasa na zama ta farko a layin da zanje na kamawa mijina, nayi tafiyar ƙasa tun daga Yakasai har Nasarawa GRA a ƙafa ba tare da na tsaya ko hutawa ba balle tunanin abun sakawa a baki. Na ƙara hasko lokacin da na ke tsugune gaban Alhaji Fari ina zubar da hawaye ina shaida masa halin tsananin da muke ciki na rashin cin yau balle na gobe, ina mai roƙonsa arziƙi da ya taimakawa mijina da jari ko da na dubu goma ne ko kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login