Showing 1 words to 3000 words out of 87761 words

Chapter 1 - ƘAYAR RUWA Book 1 HAUSA NOVEL

HALIMAHZ   

20 Dec 2024

6106

*ƘAYAR RUWA*
October/FitattuBiyar 2023.

*©️Halimahz*
*halimahz@arewabooks*
*Halimahz_@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
__________________________________
*_BISMILLAHIR-RAHMANIR RAHIM. dukkan yabo ya tabbata ga Allah (S.W.T), ina gode masa, ina neman agajinsa da gudunmawarsa da taimakonsa. Salati da sallama da ɗaukaka da daraja, su tabbata a bisa manzonmu Annabi Muhammadu (S.A.W), cikamakin Annabawa shugaban mazanni, wanda Allah ya aiko domin ya zama rahma ga al'umma. Ina roƙon ya Maliku da ya ba ni ikon rubuta abin da zai amfanar da alumma, ya hane ni rubuta abin da zai ruguza al'umma, Ya Hayyu Ya Qayyum yanda na fara lafiya kasa in gama lafiya._*
__________________________________
*_Gaba ɗaya littafin sadaukarwa ne ga Hajiya Binta Garba Saleh Daudawa, Alkhairin Allah ya isar miki, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana, ya biya miki dukkan buƙatunki, yasa ayi kyakykyawan ƙarshe._*
__________________________________
*_Littafin Tukwici ga Fatima Sulaiman Mum Aysar, tabbas ke ɗin ta dabance, ina matuƙar godiya ga ubangijina da ya haɗani da ke a rayuwa, ina kuma roƙonsa da ya lulluɓe rayuwarki da rahamarsa, ya bani ikon kyatata miki da faranta miki, ya baku zuri'a ɗayyiba masu jin ƙan ku, yanda kika sanya farinciki a fuskata ubangiji ya bani ikon sanyaki sama da haka, Allah ya ja da ran mahaifa yasa ayi kyakykyawan ƙarshe._*
______________________________
*GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI GA:-*
*•Anty Habiba Abubakar Imam*
*•Sadiq Abubakar(C.E.O Lafazi Writers)*
*•Jamila Umar Janafty*
*•Safiyya Huguma*
*•Mamugee*
*_Allah ya shiga lamuranku._*
______________________________
*JINJINA ZUWA GA:-*
*•Muhammad Kareem*
*•Jibrin Adamu Rano*
*•Abu Hisham*
*•MD Asnanic*
*•Zaharadden Hazazi*
*•Kabir Yusuf Anka*
*•Rabi'u Lallan*
*•Fatima Musa Anty Nice*
*•Ramlat Mai Dambu*
*•Da dukkan ƴan cikin group na FITATTU BIYAR LIBRARY*
______________________________
*YABO NA MUSAMMAN ZUWA GA:-*
*•Ya Aisha(Mum Sayyeed & Noor)*
*•Anty Bilkisu Rabi'u Ado*
*•Anty Bilqees*
*•Ya Nusaiba*
*•Jamila M Ladan*
*•Ummu Abdallah*
*•Anty Halima Mabo*
*•Aisha Aliyu(Maman Baffa)*
_______________________________
*_Sannan ga masoyana kuma makaranta littafaina, ba ni da bakin godiya gare ku, ba zan gajiya da yi muku adu'a da godiya ba bisa goyan bayan da ku ke ba ni, Allah ya faranta muku ya yafe muku zunubanku, yasa ku gama da duniya lafiya, masu fuskantar ƙalubale a dalilin jinkirin aure ubangiji yasa hakan ya zama alkhairi babba a gareku, haka masu fuskantar ƙalubale a zamantakewar aure Allah ya gyara lamura...A wannan karon dai tafiyar ta dabance, kusa kuɗi ku siya, ba zaku yi nadamar siya da karantawa ba, a nuna min son so...har kullum ƙofa a buɗe take domin karɓar saƙonninku._*
_______________________________
*_All rights reserved. No part of this book may be reproduced or transmitted in any form without seeking permission from the writter. This novel is a work of fiction, Names, characters, business, places, events, and incidents, are either the products of the author's imagination or used in a fictitious manner. Any resemblance to actual persons, living or dead, or actual events is purely coincidental. A person who commits an act of piracy, is liable on conviction to life imprisonment and a fine of not more than N50,000,000...So becareful of copying any part of this story._*
*©️Copyright2023 Halimahz.*
_________________________________
*SHIMFIƊA.*
_A wasu lokutan da bamu tsammaci rikicewar al'amura ba, sai ya zamana al'amuran sun runcaɓe mana babu zato babu tsammani. rayuwa kan canja tayi juyayi da mutum, wasu ta juya da su duniyar rikicewa, firgicewa da tashin hankali har mutum kanji tamkar shi kaɗai aka tsana, yayin da a gefen wasu juyin rayuwa kansa su mance da baƙin ciki, haushi, da damuwa, su dulmiya a jin daɗin rayuwa. babu abin da bai da farko, babu abin da bai da asali, haka babu abin da bai da tushe, kazalika babu abin da bai da ƙarshe, sai dai yarda da Allah kan tafiyar da komai cikin daidaito._
_kamar dai yanda darasi ya ke a matsayin koyarwa da miƙa saƙo, hakan yasa a yau zan rubuta labarin rayuwarmu, sunana Sa'ida Salman, kuma wannan shi ne labarin *ƘAYAR RUWA*..._
________________________________
*(1)*
Kwance na ke akan makeken italian royal bed a cikin tamfatsetsen ɗakin barcina. Wayata ƙirar S22 na gefena ina sauraren karatun alqur'ani mai girma cikin ƙira'ar Muhmood Hosary, idanuwana a lumshe suke tamkar mai bacci, sanyin acn da ke busawa na bin dukkan ƙofofin gashin jikina, yayin da gefe guda hancina yake shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren wutar da na kunna a burner wanda ba ya ko ƙaurin kamawa saboda irin salon yanda nake bi wajen sanya shi.

Sanye na ke cikin doguwar rigar material mara nauyi, rigar na ɗaya daga cikin sutturun da nake so sosai a kayana duk da material ɗin ba wai mai tsada ba ne, fuskata fayau babu kwalliya ko ɗiso, sai hakan ya ƙara fito da ramar fuskata.

Gaba ɗaya yau jina nake yi kamar mara lafiya kuma kaman an yi min mutuwa, sai dai babu ko ɗaya a ciki, tun safe da na tashi bakina babu ɗanɗanon komai ga tsananin faɗuwar gaba na damuna, hakan yasa tun lokacin nake ta adu'oi da tasbihi, kuma karatun ƙur'anin da na kunna ina saurare ina bi shi yake d'ebe min kewa, to amma dai duk da hakan ina ji a jikina cewar akwai wani babban al'amari da zai girgiza duniyata nan kusa, ina jin kamar nan kusan zata zamar min ƙarshen komai na rayuwata ne.

Ajiyar zuciya na sauke mai nauyi, na juya kwanciyar da nayi inda a yanzu na ke fuskantar bakin ƙofar shigowa, cikin zuciyata ina roƙon ubangiji da yasa komai zai faru ya zama alkhairi, ya kuma ba ni ikon cinye kowacce kalar jarabawa da iya ɗaukan ƙaddara.
zoben azurfar da ke hannuna na ke ta kallo ina jin wani abu mai girman gaske na tsarga min, yayin da tunanin wasu shekaru yasa fuskata ƙwacewa da murmushi mai faɗi, murmushin da za'a kira shi da na yaƙe.

Wayata na ɗauka don duba lokaci, ƙarfe biyar da mintina na yamma ya nuna min, zaune na miƙe da mamakin gudun lokacin a cikin raina na furta "har biyar?, Lallai duniya na gudu, Allah kasa mu cika da imani".

Da azama na zuro ƙafafuna ƙasa ina gyara ɗaurin ɗan kwalina, ji nake kamar zan faɗi saboda rashin ƙwarin jiki, kaman wadda ta sha zawo ya zabgar da ita a yini ɗaya. Tsayuwa nayi gaban tafkeken madubin ɗakin na tsaya ina ɗaukar tissue in shiga goge kwantsar ciki saboda ciwon idon da nake fama da shi daga shekaran jiya zuwa yau.

Kallon kaina na tsaya yi a cikin madubin, lallai in har akwai rayuwa da shekaru to tabbas akwai sauyi, gaba ɗayana kamar ba ni ba, kallo ɗaya da zaka min ba sai ka ƙara na biyu ba zaka ga zallar ƙuruciyar da ke kan fuskata, wanda zai bayyana maka cewar shekaruna ba su da yawa. Sai dai kuma in har kayi min farin sani a baya, to a yanzu zaka ce na sauya, ba wai sauyi na ɗabi'a da halayya ba, a'a sauyi na halittar jiki. A baya ni ɗin ƴar duma duma ce mai kyawun dirin jiki tubarakallah, ina da irin jikin nan da babu kalar damuwa balle yunwa, saɓanin yanzu da ko'ina a jikina ƙashi da jijiyoyi ne suke magana, ido kuwa ramar da ta fito da shi waje yanda kasan na mujiya, gefen kumatuna duk ya zurma ciki, shi kansa uban hasken da nayi ba na komai ba ne sai na shegiyar ramar da nayi, albarkatun ƙirjina kuwa duk sun kwanta shalaf kamar wacce ta shayar da ƴaƴa ɗari, duk na zama wata babu kyan gani kai baka ce me tashen ƙuruciya ba shekaru ashirin da huɗu a duniya.

Lokaci guda idona ya cika da tarin ruwan hawaye, sai dai basu sami nasarar zubowa ba, cikin yanayi na bala'in tausayin kaina na sunkuyar da kaina ƙasa ina jin wani dunƙulallan abu na tsaya min a maƙogoro yaƙi wucewa, hakan sai ya zama famin ciwo a gare ni, wanda da zan samu in korashi da yawun bakina ko kuma ya wuce da kansa wataƙila da na sami sassauci. Cikin ƙarfin halin da na saba na ɗago kaina ina mayar da tarin ƙwallar da ta cika min ido, ɗakin kawai nake bi da kallo, ko a iyaka shi aka bar bawa rayuwa ya ishe shi jin daɗi da more rayuwa, damuwarsa ta gushe, ballantana kuma ace rayuwa kake yi a cikin tamfatsesen gidan nan da yake sai kace a ƙasashen turawa, lumtsum nake a cikin daula, duk wanda yazo gidana ba ya son tafiya, iya dukiya dai an narkata wajen ginin gidan, zaka rantse da Allah ba duniyar da talakawa ke rayuwa ba ne, idan ba Allah ya soka da rahma ba sheɗan sai ya shagaltar da kai da yin ibada.

Sau tari ƙawayena da ƴan uwana kan ce min ke kam Sa'ida kin more, ba ki da saurin baƙin ciki da takaicin duniya domin Allah ya kashe ya ba ki, arziƙi ta ko'ina, kalli gidan da kike ciki kamar ba za'a mutu ba, irin motocin da ake fita da ke a cikinsu zamansu kaɗai yasa kiyi ƙiba ki fresh, abinci kullum da nama, ke kam ba ki da sauran damuwa, ba su san da cewa ba anan take ba wai abin da yawa mutuwa taje kasuwa, sai da kwanciyar hankali ake jin daɗin.

Madubin da ke gabana na kalla da kyau, na sauke babbar ajiyar zuciya tare da yin murmushi mai ciwo, ina mamakin masu faɗa min irin wannan zantukan, ban sani ba ko iyaka daular da Allah ya ajiye ni a ciki kawai suke kallo shiyasa ba su taɓa lura da cewar akwai ƙalubale mai wahala a gefe, bana jin daɗin gidan, bana farin ciki sam, su ka kasa ganin irin lalacewar da nai, su ka kasa fahimtar gwara ma rayuwata ta baya akan ta yanzu, su ka kasa fahimtar ina da buƙatar taimakonsu. Su na ganin cewa zan iya yi musu komai tun da su na kiran wannan ƙaton gidan da gidan Sa'ida, ba su san cewar babu abin da zan iya, domin ba ni da komai, tun da komai ɗin da su ke kallo ba mallakina ba ne ba taƙamata ba ne.

Ƙwarai kuɗi da rai da lafiya rahma ne, kuɗi komai ne bayan lafiya, babu abin da yafi ace yau kafi ƙarfin komai, ace yau kai ne kake ɗauka ka bayar ba wai a ɗauka a baka ba, kaci mai kyau kasha mai kyau ka kwanta a mai kyau kasa sutturu masu kyau da tsada, ka hau jirgi ka keta hazo zuwa in da kake so, ka ɗiba ka kashe babu mai ƙayyade maka, kayi mu'amala da mutanen da su ka fika. To amma me?, duk da irin tarin dukiyar da kake da ita, da irin daular da kake rayuwa a ciki, muddin babu kwanciyar hankali to babu farin ciki da jin daɗi. Ni a wurina gwara in rayu cikin talauci akan ace ga tarin dukiyar amma babu zaman lafiya babu kwanciyar hankali balle na sami natsuwar zuciya.

Na sake sauke ajiyar zuciya mai nauyi a karo na uku, murmushin da yafi kuka ciwo nayi ina girgiza kaina wanda ni ɗaya na san ma'anar hakan. Abu ɗaya na barwa kaina sani shi ne kowanne matakin nasara ba'a hawansa sai da ƙalubale, kuma komai na duniya fararre ne ƙararre, kuma dogaro ga Allah jari, babu kuma mai yi sai Allah, muddin akwai yau, gobe da jibi to komai zai shuɗe ya zama tarihi. Na gyara ɗaurin ɗankwalin da ke kaina, turare na ɗauka oil na shafa, sannan cikin sanyin jiki da mutuwarsa na fita a ɗakin ina jin ƙafafuna tamkar a ƙanƙara.

cikin sauri da rashin jin daɗi a raina da ban ankarewa tafiyar lokaci ba na fita, na san duk inda Hubbi yake yanzu yana kan hanyar dawowarsa gida, wataƙila ma ya dawo ban sa ni ba, tun da ƴan kwanakin nan bana sanin dawowarsa in ba zaman parlo nayi ba, kamar yanda ba zan san fitarsa ba, ga shi ko abinci ban ɗora ba sakacin da ban taɓa yi ba, abincin da idan nayi ma ba'a masa cin kirki ko kuma a barni da kayana, amma duk hakan ba zai sa in daina ba, zan ta ƙoƙarin sauke hakkin da ke kaina na dafawa tun da an siyo an a jiye. Ina fitowa daga bedroom ko ƙasa ban sauka ba don gani nake zan ƙara ɓata lokaci ne.

kitchen ɗin sama na wuce kai tsaye, babu ɓata lokaci na buɗe fridge na ɗauko gwangwanin bama da nake zuba dafaffen kayan miya a ciki, ni kam ba ruwana da wahalar jajjage ko markaɗe kullum, da ya jido uban kayan miya na ke markaɗe su in dafa in juye a kwalabe. Ina aiki ina ta muraja'a, A ƙanƙanin lokaci na kammala dafa taliya jallof sai tashin ƙamshin busassan kifi take yi da ƙamshin kayan lambu, na juyeta cikin tsadadden kular abincin da Hubbi yazo da su last week daga dubai, wanda naji Hamida na kuɗinsu ya kai dubu ɗari biyu, bayan nan na ɗauko bilenda na haɗa lemun abarba na juye shi cikin jug.

Da kammalawata na kwashi komai na kai parlon Hubbi da ke nan sama na jera akan table, na gyara ɗakin ko'ina ya ɗauki ƙamshi sannan na fito na kulle. da na leƙa parking lot ta window banga motar da ya fita da ita ba na san bai dawo ba, hakan yasa nayi komai a nutse sai dai kuma cike na ke da mamakin rashin dawowar tasa da wuri yau, tun da shi duk inda biyar da rabi take ya dawo gida, da yaci abinci zai kwanta sai an kira magrib zai fita masallaci ba zai dawo ba sai bayan isha'i, in da nake jin daɗi kenan Allah bai bani miji mai son zaman majlisa ba, yafi ganewa zaman gidansa, duk da yanzu na kanyi fargabar dawowarsa duba da bama wanyewa lafiya da shi, ga shi na rasa gane kan dalilin hakan, na rasa silar tashin hankalin, na rasa ta ina aka samu saɓanin.

Ɗakina na koma nayi sabon wanka, na fito na shirya cikin riga da skirt na atamfa da ɗinkin yay matuƙar amsar jikina, skirt ɗin ya fito da cikakken ƙuguna, musamman hips ɗina wanda shi ne abu mafi ɗaukar hankali a jikina bayan baiwar madaidatan ƙirji. Na bar ɗakin ina ta baza ƙamshi, duk da halin da na san ina ciki yanzu a rayuwar aurena, hakan ba shi ke hana ni gyara jiki in ci kwalliya in isa ga mijina ba, ba kuma shi zai sa na waje ya shigo in bari ya gane ina cikin matsala ba, na iya sirrinta zaman aurena.

In da sabo na fara jure halin ko in kulawar mijina yanzu, hakan yana damuna amma na kan nuna masa bai dameni ba balle hakan ya ƙara ingiza shi, ban taɓa fasa hidimta masa ba, shi kansa ya san ina da mugun haƙuri don idan wata ce tuni anji kansu, a yanzu banda burin da ya wuci mu zauna mu fahimci juna da shi, ya karanta min kuskurena in gyara, domin har ga Allah bana jin daɗin irin zaman da muke yi, auren soyayya muka yi ba auren ƙiyayya ba, kuma tsawon shekara takwas da aurenmu bamu taɓa zaman da za'a ce don mun sami saɓani wai zamu shafe sama da kwanaki babu ruwan wani da wani ba har ta kai ga muna raba makwanci, ga shi yaƙi bani damar magana da shi balle ya karanta min laifina, ni kuma iyakar sanina ban masa wani laifi ba, haka dangisa ma, ban san matsalar da ta gifta a tsakaninmu ba da kowa ke nuna min ƙiyayya ƙuru ƙuru, har shayin shiga cikinsu nake, sun dinga min kallon banza kenan ana jajja baya da ni kamar mai warin jaɓa, sai in shiga taro ma in fita babu wacce zamu yi magana da ita in ka cire gaisuwa da zata haɗa mu, abin da yake matuƙar ɗaure min kai duk wannan matsaltsalun cikin ƴan watanni ne, da can komai lafiya, har gani nake tamkar duk matan duniya babu wacca tayi dacen dangin miji irina, so da ƙaunar da suke nuna min kamar za su cinye ni, miji kuwa ai sai son barka, a ko ina zan bugi ƙirji in ce nafi kowacce mace sa'a, sai dai banda yanzu, yanzu kam ɗaya na ke da wadda aka aurawa mijin da bai sonta.

A yanzu haka so nake na samu wani in karanta masa halin da nake ciki ko na ɗan ji sanyi cikin raina, sai dai gaba ɗaya na rasa wa ya kamata nayi maganar da shi, ni dai ban isa na tunkari ƙawa da zancen matsalar zamantakewar aurena ba, ban ma ni da shaƙiƙiyar ƙawa, mahaifiyata kuma bana so na tunkareta da magana makamanciyar wannan, ba don komai ba sai don gudun shigarta damuwa, tun da a ko yaushe burinta taji nace mata lafiya muke babu wata matsala, haka kuma a kullum nasiharta a kaina in ta haƙuri in kuma guji kai ƙorafi domin hakan na ƙara taɓarɓare zamantakewar ma'aurata, kuma bani da Yaya mace ko Ƙanwa balle in shaida musu halin tsananin da na ke ciki, sai Yayyu maza da Allah ya bani har huɗu, su kam bana jin ma zan yi kuskuren musu wannan maganar, kun san ance mai ɗaki shi yasan inda ke masa yoyo, idan zan kira su in kwan dubu ina faɗa musu matsalar da ke faruwa ba zasu taɓa yarda ba, in ace matsalar daga ni ne to nan za suyi saurin cafewa har a iya samun mai zuwa har gidana ya naɗa min na jaki, amma batun wai in faɗa musu laifin Hubbi ne tabbas ruwan ashariya sai na sha na ƙoshi, ba kuma wai don basa sona ba ne, su na mugun sona tun da ni ɗaya ce mace a cikinsu, kuma su na matuƙar tausaya min, amma batun dai su goyi baya ga laifin mijina sai dai ya zama zance, gwarama ranar da Ya Imam ya zo duba ni yaga duk na bushe ya zauna yay min nasihohi masu ratsa jiki akan zaman duniyar gaba ɗayanta ƴar haƙuri ce. Abbana kuwa zafi ne da shi, ina fara faɗa masa zai sa azo a ɗauke ni ko kuma yace in kwaso kayana in taho, duk ranar da mijin ya san darajata yazo ya bada haƙuri in koma ko ya rabar masa da ƴa, ni kuma ko kusa bana son abin da zai ja igiyar aurena ta sami tangarɗa, ina cikin matan da za su iya shanye kowanne kalar baƙin cikin gidan aure akan dai a sake su, wani waje daban ma ban so inji aure ya mutu bare a kaina.

Tun barowata sama har na sakko ƙasa kiran lambar Hubbi nake yi bata shiga, zuwa yanzu da akai magriba hankalina ya kai ƙololuwar tashi, ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login