Showing 42001 words to 45000 words out of 87761 words

Chapter 15 - ƘAYAR RUWA Book 1 HAUSA NOVEL

HALIMAHZ   

20 Dec 2024

6124

saboda wata manufa ya ke son sasanta komai, don har yanzu babu ainihin muryar Hubbi a dukka kalamansa da yayi, kuma har yanzu babu wannan haƙiƙanin son da yake nuna min idan muna tare.

"Habibty ni dai na san dukka abubuwan da na ke yi miki wanda basu dacewa, kuma nayi alƙawarin gyara su, to amma kema ina so ki faɗa min me kike so na gyara?".

hawaye ya cika idona na ce,"Hubbi ni so na ke ka dawo mai kulawa da ni da tausaya ni, kuma ka ke min adalci wurin tsayawa ka fahimce ni a duk san da saɓani ya gifta, sannan ka bani damar zama uwa mahaifiya wacce ta tsuguna ta nayi naƙuda bayan ɗaukar cikin wata tara akan Rumana da Atika, ba zan cutar da su ba kamar yanda ba zan so in ga sun halaka ba, in suka yi ba daidai ba akwai buƙatar a gyara musu, don haka kar ka tsammaci gyara tarbiyarsu wurin tsawatar musu da zan yi yana nufin bana ƙaunarsu. wallahi ina ƙaunar su Hubbi tun da aka ce an baka su, kaima ka sani ina tsananin sonka, da kai na ke so na ƙarasa rayuwata, don Allah kar ka kuma goranta min akan ƴaƴan nan, sannan don Allah da Annabinsa Hubbi ka faɗa min sakamakon da asibiti su ka bayar...".

kuka yaci ƙarfina nayi shiru, da sauri ya ɗora haɓarsa saman kaina yana ƙara rungume ni, shiru na ƴan sakanni ya ce.
"insha Allah ba zan kuma yanke hukunci ba tare da na tsaya na saurareki ba, kuma insha Allah ba zan ƙara nuna miki cewa su Rumana ba ƴaƴanki ba ne, na ba ki izini daga yau kiyi musu duk yanda kike ganin za kiwa yaron da kika haifa da cikinki, na damƙa dukkanin tarbiyarsu a hannunki domin ina da tabbacin za ki fini iyawa, abu ɗaya kawai zan fiki akansu shi ne so, kuma ke za ki zama shaida akan yanda na ke so yara. batun kuma gwajinki sakamako ya nuna lafiya lau kike ba ki da wata matsala lokacin haihuwar ne kawai bai yi ba, ni da ke duk lafiya muke Allahne bai bai kawo mana ba".

a ƙalla naji sanyi cikin raina, amma ban san me yasa na kasa gamsuwa da shi da zancensa ba, haka hankalina yaƙi kwanciya gaba ɗaya, sai dai naji daɗi sosai da batun cewa mahaifata lafiya ƙalau take. a hakan dai sai da ya san yanda yay yasa na saki jikina ɗari bisa ɗari da shi kafin muyi bacci.
sai da na kwana biyar da dawowa sannan ya ce in shirya muje gidansu, a kwanakin har wani murmurewa nayi saboda samun natsuwar zuciya da ta ruhi, tsakanina da shi ba wani rikici ko saɓani hankalin kowa kwance, duk da akwai canjin dai da ya kasa gyaruwa, ban sani ba ne ko shikenan har abada ba zamu taɓa komawa yanda mu ke da shi ada ba, wani lokacin zai ta nurƙufanci yana shareni amma ba zai ɗauki lokaci mai tsayi ba ya sakko, sai dai fa yanzun kam na gama karantar shi shima duk yana min abin da yake min ne saboda ina da tawaya ta wajen haihuwa, dukkan fatansa da burinsa bai wuci ace ya samu ɗa ba ta jininsa, na yi yunƙurin zama da shi da dama akan mu shawarta ko aure zai yi amma na kasa, idan nayi yunƙurin haka sai zuciyata ta karye.

sai da ya fita wurin aiki ya dawo sannan muka tafi gidansu, sai dai kamar wancan zuwan da nayi na ƙarshe babu wata tarba mai kyau daga uwar mijina, jin haushina tsantsa bayyane a saman fuskarta, don ko da na gaida ita da ƙyar ta amsa mini, sona kam dai yanzu ba shi a tare da ita. zama da nayi a ɗakinta ma sai ce tayi da in fita daga parlo ko wajen Amarya tana so zata huta. haka na kwaso jiki na fito parlo in da anan na sami ƴan mata gidan suna kallo ana hira, Rumana da Atika na ganina amma yaran nan babu wacce ta gaida ni kamar ma ba su sanni ba, Atika ma da nayi mata magana sai tsaki ta min tayi wucewarta ɗakin Iyam, abin ya taɓa zuciyata sai naji ina ma kar su koma gidan namu don gani nake komawarsu zai ƙara taɓarɓara zamana da Hubbi.

yini muka yi a gidan, da Amarya muka ta hira duk ta ɗebe min kewa, dama ita Ummaa ba wani sakin fuska take ba, Lubabatu kuwa dama ta gidana ce, in muna tare sai ka ce Hassana da Hussaina, na samu na saki jiki daga takurewar da nayi, don duk na damu da rashin nuna halin ko in kula na uwar mijina, ban san me na mata ba na kuma rasa ta hanyar da zan bi na gyara alaƙarmu.
sai dare ya zo ɗaukarmu da yaran, kuma tun a mota yay musu faɗa sosai, faɗa irin na uba da ƴaƴansa, yace in har suna so su shirya da shi to su girmama ni kamar yanda za su girmama Yaya da Anty Aisha, don yanzu ni ce matsayin uwa a gare su kamar yanda shima ya koma uba a garesu.

to tun daga wannan ranar kam sai dai in ce Alhamdulillah. sati biyu tsakani ina zaune a parlo muna waya da Hubbi, sai ga su Maman Yasmin sun zo, nayi tsallen murna na tafi na rungume su, naji daɗin ganin su sosai, yau dai Hindatu ta wanke laifinta na rashin zuwar min da take yi, a hakan ma ashe da ƙyar Babanmu ya barsu su ka zo, wai yana tambayar me za su je suyi min a gida bayan ba jimawa na zo gidan suka ganni.
tare da Hindatu da Sauda mu ka shiga kitchen, dama ban ɗora abinci ba da yake Hubbi ya tafi Kaduna yau, kuma sai dare zai dawo, shiyasa ban wani ɗora girki ba na ce idan yaran sun dawo a makaranta na dafa mana indomie.

gidanmu mayun taliyar hausa ne da manja da yaji, ko a gida idan za'a dafata haka mu ke haɗuwa da ƴan ɓangarenmu da Ƴaƴan Babanmu, dama Ƴaƴan Baba Tijjani tsakaninmu da su kallo, gwara ma Surayya ta kan shigo cikinmu bata da mugun hali irin na ƴan uwanta. taliyar na bayar aka siyo mana muka dafa tun da naji suna murna a dafa ɗin, Sauda ta haɗa mana lemun tsamiya don Maman Yasmin mayyarsa ce.
muna cikin cin abinci sai ga Rumana sun dawo daga makaranta, ba don mun haɗa ido da su ba ba za su gaida ƴan uwana ba, gaisuwa na ɗaya daga abin da basa so, don ko ni da muke kwana tare mu tashi tare ba kullum su ke gaishe ni ba sai dai Abban na su, nayi iyakar yina akan su ɗoru akan hanyar hakan amma lamarin na su sai adu'a.

na ce suje su cire kayansu suyi wanka su zo su ci abinci kafin lokacin islamiya yayi, Yasmin sarkin son yara ƴan uwanta nan fa daɗi ya cikata da ganinsu, duk da sun girmeta don ita shekara bakwai take yanzu. muna ta hirar saurayin Hindatu da zai kawo kuɗi Maman Yasmin na mata tsiya akansa, sai ga su sun sakko, idan na gansu fes fes raina yana sanyi da hakan, sai in ƙara jin sonsu sosai, don wallahi ko fushi na ke yi na gansu ɓacin raina kan gushe duk da dai ga yanda mu ke da su, ba su ɗauke ni uwa ba kamar yanda ni na ɗauke su tamkar ƴaƴan cikina.

Rumana ta zo ta zauna kusa da ni tana faɗin,"Anty abinci fa".

kafin nayi magana Atika ta ce,"Anty wai wannan taliyar hausar aka dafa?".
ta faɗa tana nuna taliyar da ke cikin bowl Maman Yasmin na bawa Irfan.

na ce mata,"ehh ita na dafa har ma da salad, in kika ci kunnenki sai ya kusa tsinkewa".

na faɗi hakan ina buɗe cooler sai ce tayi. "ni ba zan ci wannan taliyar ba gaskiya".

ina kallonta na ce,"to me kike son ci?".
"a dafa mana wani abun, soyayyan biredi da ƙwai zan ci".

ajiyar zuciya na sauke, bana tunanin ko ɗan da na haifa zai juyani kamar yanda su ke juyani, ina binsu ne a yanda suke so ba don komai ba sai don in zauna lafiya a gidan aurena. Rumana da tace zata ci na zuba mata nata suka koma gefe ita da Yasmin wacca ta ce zata ƙara. ita kuma na tashi na shiga kitchen na soyo mata biredin na kawo mata, yarinyar nan tun da na bata ta karɓa sai ta tsaya kallonsa tana aikin ɓata rai alamun bai yi mata ba.
raina ya ɓaci na ɗaga mata murya da cewa,"ba za ki wuce kije kici ba sai anjima ki zo kina min kukan yunwa. idan shima kuma ba za ki ci ba sai ki kai ki ajiye don ba zan kuma dafa miki wani abun ba ai na faɗa miki ku dinƙa cin abin da ya samu".

daga mata wannan maganar sai ta saka kuka kamar wacca nasa hannu na buga. nayi mata banza na wuce na barta, Maman Yasmin na kiranta akan ta zo amma ko kallonta bata yi ba, Hindatu kuwa lallashin duniya ba wanda bata mata ba har tana tambayarta me take so amma bata tanka ba, dama zuciyar bala'i ce da ita.
ƙarshe kawai sai ta yar da plate ɗin, da yake na tangaran ne take ya fashe, ta tunkuɗe hannun Hindatu a jikinta tana cewa,"Ni ki ƙyale ni". tana fuzgar numfashi ta ce,"kuma in Abba ya dawo sai na faɗa masa an hana ni abinci".

ai ko na dalla mata harara na ce,"kar ki fasa faɗa masa kinji mara kunya fitsararriya, yanzu ma ki bisa can ki faɗa masa".

yarinyar nan da ke ta ƙwanƙware a rashin kunya cikin ƙunƙuni sai ce tayi,"ni ba fitsararriya ba ce, abincin naga ai Abbanmu ya siyo, dama an ce juya bata san darajar ƴaƴa ba, kuma tun da kike azabtar da mu da yunwa ba za ki taɓa haihuwa ba".
Ai karaf magar a kunnen Maman Yasmin. ta buɗe baki tana kallonta da matuƙar mamakin furucin nata, kafin tayi mata wata muguwar cafka ta fizgota gabanta. "kika ce me? ba ki da kunya dama? don ubanki ita ba Babarki ba ce".

"ni ba Babata ba ce, Mai gidan ne Abbana".

Abin ya matuƙar ɗaure kan Maman Yasmin naga ta ware ido tana kallonta ta ce,"kaiiii haka kike?". ta faɗa da al'ajabi da mamaki.

ban san me tace ba kuma bana da buƙatar na sani, iya wannan ɓacin ran ma ya isa. saboda haka na shiga roƙon Maman Yasmin akan ta ƙyaleta kawai, abincin ne dai ba zan ƙara dafa mata wani ba ko me zata yi kuwa.

"in ƙyaleta fa kika ce Sa'ida, kin kuwa ji furucin da tayi? ta ya za'ai yarinya kamar wannan ta faɗi haka kuma a ƙyaleta babu hukunci, maganarta ai ta girmi shekarunta, ai na ma ta san wani kalmar juya don ubanta, ke haka kike barinsu babu kwaɓa babu tsawatarwa kenan?, to in har kuwa haka ne ba ruƙon tsakani da Alllah kike musu ba domin ba ta isa tayi gaban uwar da ta haifeta ba ta ƙyaleta, ai gaba ake ji".

nayi gajeran murmushi jin furucin nata, cikin sanyi murya na ce,"ƙyaleta Maman Yasmin, Allah ya shirya mana kawai, ai ina musu adu'a".

kawai sai ta tsaya kallona, ban san me take tunani ba tun da ban san zuciyarta ba. kawai na san zata iya tunanin mene dalilina na cewa a barta alhalin tayi ba daidai ba. Maman Yasmin kuwa tausayin Sa'ida ne ya kamata, tana ɗaya daga cikin mutanen da zasu bada shaidar haƙurin Sa'ida, kuma tayo gado ne wurin iyayenta. tun farkon zuwanta sabon gidan nan nasu ta fahimci rayuwar haƙurin da take yi, haka ko da aka ce mata an bata yara ta san kuma sai ta Allah, don riƙe ƴaƴan da aka ce ba naka ba sai haƙuri, to naka din ma ya aka cika, ballanta ita an bata yara masu uwa a bakin murhu.
ai tana lure da Sa'idan tun da ta ruƙo hannun yarinyar taga tsoro ya bayyana akan Fuskarta, hakan kaɗai ya isa ya bata shaidar ba a tsawatar musu domin yi musu ɗin ita zai jawowa shiga matsala.

ta girgiza kanta kawai cikin ranta tana faɗin Allah ya kyauta, sannan ta saki hannun Atikar, cikin muryar kashedi ta ce mata.
"ke! kar na ƙara jin kinyi irin wannan furucin a bakinki idan ba haka ba sai nasa Antyn na ki ta zane miki jiki, idan kuma son da take miki ba zai sa ta dake ki ba ni da kaina zan miki duka. kuma daga yau duk abin da Antynki ta ce ki dinƙa yi ban da musu kinji ko, ko ba kiga yanda ƴar uwarki take yi ba? duk wanda fa yake wa babarsa rashin kunya Allah fushi ya ke da shi".

yarinyar ta yamutsa fuska tana tsuketa, ta turo baki tana harar gefe guda ta ce da Maman Yasmin.
"ke kika haife ni da za ki dinƙa min faɗa, ai ko Anty Abbanmu ya hana ta yi mana faɗa sai ke baƙuwa, ina ruwanki, kuma sai na ƙara faɗa ɗin ki kashe ni kiga in Mamana zata ƙyale ki".

farrr na ware idanuwana akan fuskarta, ban tsammaci rashin kunyar Atika ya kai har haka ba, na san har iyayensu ba su bari ba shiyasa idan suka min ban cika damuwa ba, amma ban tsammaci har za su iya yiwa baƙona ba. karo na farko da naji raina yay matuƙar ɓaci akansu, aiko na buɗe murya na daka mata tsawa har sai da tsorata, na tashi na isa gabanta na bata kyakykyawan mari, sannan nasa hannu na bibbige bakin nata yanda zata ji a jikinta. ji nayi hakan bai min ba saboda na kai ƙololuwa a ɓacin rai, na manta me zai iya faruwa sanadin hukuncin da zan mata, na shiryawa fuskantar ko menene, don haka na riƙe hannunta na isa gaban tv na cire caja na tsula mata a jiki sau biyar, sai kokawar ƙwace hannunta ta ke daga ruƙon da na mata saboda ta falla ta gudu.

tana shashsheƙar kukan ta murguɗa min baki wato abin da na mata bai shigeta ba, kuma bata risina ba. na kuwa kama kunnenta na murɗe da kyau har sai da ta ƙwalla ƙara, na kuma daka mata tsawa na ce ta rufe min baki, idanuwana waje na zare mata su na shiga mata gargaɗi.

"Duk sanda kika kuma yiwa babba rashin kunya sai na zane miki jiki wallahi, ko a waje balle a cikin gida, haka na koya muku ko haka Abbanki ya ce kuke yi?".

ta tsorata da yanayina sosai da ban taɓa nuna musu ba, jikinta rawa kawai yake tana sosa dukan da na mata.

"kalleta ki bata haƙuri dan gidanku, ni za ku iya min komai in ƙyale ku na biku da adu'a amma ba zan lamunci in ga kuna yiwa babba rashin kunya ba Atika, zan aje duk son da na ke muku a gefe in hukuntaku. kuma wallah kika ƙara irin haka ba bakinki zan fasa ba gidan su Siyama zan kai ki a saki a ɗakin karnuka su cinye ki".

ai ko ta tsorata sosai da furucin nawa, don haka ta shiga roƙona in yi haƙuri ba zata sake ba. na juyar da ita ta fuskanci Maman Yasmin, yanda nayi maganan a tsawace yasa bakinta na rawa ta furta.
"kiyi haƙuri ba zan ƙara ba"..

na ƙara firgitata ina cewa,"haka ake bada haƙuri, tsuguna ki ce don Allah".

jikinta na rawa ta tsuguna gaban Maman Yasmin tana cewa,"Anty kiyi haƙuri don Allah, ba zan sake ba wallahi, ki roƙi Anty ta sakar min kunnena".

kashedi na yi mata me kyau kafin na ce ta kwashe biredin da ta zubar ta cusa haka nan taci, haka ta zauna ƙasan tayels tana ci tana kuka, kuma tana gamawa na ce ta tashi a kusa da mu ta tafi ɗaki ta zauna, kuma da kaina zan kaita islamiya in faɗawa Ya Ustaz abin da tayi. ai fa nan hankalinta ya daɗa tashi tai ta ƙara bani haƙuri. ko da su ka shirya tafiya islamiya sai da ta zo har gabana ta duƙa ta ƙara bani haƙuri kar naje islamiya na faɗawa Ya Uztaz in ba haka ba a mari zai sakata. sai da tayi min alƙawarin ta daina tukunna na ce shikenan su tafi makaranta kuma ayi karatu da yawa.

sai bayan tafiyarsu Hindatu ta ce,"cabɗijam! Sa'ida haka kike zaune da yaran nan dama? anata miki murnar samun ƴaƴa ashe ke kina nan kina fama da halin su. to ke kuwa me zai hana ki mayarwa da iyayensu ki ce kin yafe".

guntun murmushi nayi na ce,"Hindatu kenan to ai bani aka bawa ba ko".

"cabɗi to sannu danga uwar haƙuri. ai wallahi da ni ce tuni labari ya daɗe da sauyawa. don wallahi tallahi ba zan ɗauki ƴaƴa marasa mutunci irin wannan ba sai dai in kuwa ya auro wata ta ɗauka, rashin haihuwar hauka ne da za'a ɗauko masifa a dire miki, wannan yarinyar dai a felle take don da gani zata yi makirci".

Maman Yasmin ta numfasa tana cewa,"sun raina wanda ya alaƙantu da ke ina ga ke kanki? Sa'ida haƙurinki yayi yawa gaskiya, na san ba akan ƴaƴan kaɗai kike fuskantar ƙalubale ba harda iyayensu ma, don ina da tabbacin iyayensu su ka basu lasisin cin mutuncinki, in ba haka ba ina wannan ƴar zata san wani juya, kar ki mu sa min domin kin san ina da ilimin karantar yanayin mutum zaman haƙuri kawai haƙurin cutar da kai. don haka ina mai ba ki shawara tun yaran nan ba su girma sun fi ƙarfinki a cikin gidan nan ba ki amso abinda yake na ki, in ba haka kuwa kina ji kina gani Allah sai sun iya rabaki da mijinki. yo da irin ƴaƴan nan ai gwara kishiya, su kansu ƴan uwan na sa ki buɗe musu ido".

haka Maman Yasmin da Hindatu su ka sanya ni gaba da faɗan sanyina yay yawa, ni dai jinsu kawai na ke yi ina binsu da uhmm in sun ce ga shawara kaza da kaza, abu da na san na ɗauka a cikin maganganunsu shi ne takawa yaran burki akan rashin mutuncinsu, don idan ba haka ba zasu raba ni da mutane, tun da ba kowa za su yiwa rashin kunya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login