Showing 12001 words to 15000 words out of 87761 words

Chapter 5 - ƘAYAR RUWA Book 1 HAUSA NOVEL

HALIMAHZ   

20 Dec 2024

6104

sannan mu fita.

Wani daɗi naji da yanda naga ya sakarwa Hassana fuska, kaman ba shi ne miskilin kwana biyu ba, cikin mutuntawa da girmama juna suka gaisa har da kansa yake bata haƙuri akan rashin zuwana barkan haihuwan Jamil, na kuwa ji daɗi sosai don ni kunya ma sawa tayi na kasa ce mata komai game da hakan.

Har muka fito farfajiyar gidan suna ta maganganunsu, yana tambayarta amma dai ba yau ne zata wuce can Wudil ɗin ba, ta ce ai mota babu wuya tana zuwa tasha zata samu motar da zata ta shi.
Haka muka baro gida, ya sauko kamar ba shi ba, wanda nayi mamakin hakan matuƙa, yanda bana so Maimuna ta fahimci akwai matsala tsakaninmu shi ma a nasa ɓangaren haka, don har da tsokanata ya dinƙa yi.

Tashar kano line muka kai ta, ya zaro dubu bakwai ya bata tayi kuɗin mota, aikuwa ta dinƙa godiya da sa albarka tamkar yawun bakinta zai ƙare, to nima ɗin dai bata sani ba da tawa ƴar dubu ukun da na ƙunshewa Jamil a wando sai taje gida zata gani, Hubbi da kansa ya sauka ya samar mata mota ta hau sannan ya dawo muka ɗauki hanyar da ban da masaniyar zuwanmu. Sai dai fa tun daga sauke Hassana motar ta koma tamkar ta kurame, ƙarar ac da sautin radio kawai kake ji, duk yanda na so in ja shi da hira sai gajiya nayi naja baki na tsuke, haka har muka iso ƙofar wani babban asibitin kuɗi UMC Zhahir Hospital anan janbulo 3rd gate.

Zuwan namu ya bani amsar tambayata da na rasa na ina mu ka dosa, ai babu ma ƙarin bayani na san me ya kawo mu, ban manta jiya ba, ban manta Yaya da cin mutuncinta ba, don haka zuwan namu asibiti a yanzu na san dalilin duk da bai fito da bakinsa ya ce min kanzil ba.

Aka zuge mana gate mu ka shiga da motar zuwa ciki, bayan kashe motar ya kaikaito da kansa ya dube ni ya ce,"yau ya ɗauke ko?".

Na ce,"me?".

"Period ɗin ki".

"Ummm". Na amsa masa a taƙaice.
"Ok ki jira ni ina zuwa".

Ban ce komai ba ya fita a motar, cikin asibitin na ga ya nufa, bayan mintunan da ba su haura uku ba sai ga shi ya fito hannunsa riƙe da wata takarda. tun daga nesa yay min alama na in fito daga motar, kafin ya ƙaraso na fito, yana zuwa yasa maƙulli ya kulle, idonsa a kaina ya ce,"mu je".

Yana gaba ina biye a bayansa kaman yarinyarsa, ba ka ce mata da miji ba. da shigarmu ɗakin gwaje gwaje naga mun nufa, a lokacin da muka tsaya bakin ƙofar lab ɗin gabana ya yanke ya faɗi, kaina naji yay bala'in sara min, sai naji lokaci ɗaya idona na ƙoƙarin kawo ruwa, babu shiri na mayar da su. mun kusa minti biyar zaune a reception naji an kira sunana Sa'ida Salman Madobi. Jin kiran mu ka ɗago kawunanmu a tare, yanda na ke kallonsa shima haka, bakina ƙunshe da tambaya sai dai ban ce komai ba domin ban san ta ina zan fara ba. girarsa ya ɗan sosa kana ya ce da ni,"ki je, ki kuma natsu".

Jiki a sanyaye na ce,"Hubbi har da allura?".

Na faɗa muryana kana ji ka san a tsorace na ke. kafaɗa kawai ya ɗaga min alamun bai sani ba shima. Na wuce kamar marar lakka zuwa wani room da nurse ta nuna min. ni dai tun shigata ina ga mun kusa rabin awa sai aikin jagwalgwala ni ake, ai wancan ai wancan, gwaji kusan kala nawa, kalma ɗaya na riƙe na dai ji ana faɗin ko HCG ko mene dai oho. bayan kammala komai na fito, Hubbi na inda na barsa, yaga fitowar tawa amma sai ya ɗauke ido tamkar ba ni ya gani ba, kuma raina yay bala'in sosuwa da hakan.

Kusa da shi na sami wata ta zauna, fuska haɗe na dubeta na ce,"matarsa ta dawo wurinta".

Kallona tayi sannan ta kalle shi taga idonsa ƙyam akaina, na ja tsaki ina daɗa cewa,"ko sai an taimaka miki ne kafin ki sami damar tashi?".

Yanda taji nayi maganar da yanda amon sautin ya fita ta san ko da na faɗi haka ba abu me kyau zan aika ba, domin kuwa a ƙule na ke. babu shiri ta miƙe tana faɗin,"yi haƙura".

ta faɗa tana miƙewa ta wuce ta gabana, naja dogon tsaki ina cewa da ita,"shashasha marar kamun kai". ta jini sarai amma sai bata tsaya ce min komai ba ta wuce.

Tsaye na yi na ɗan jingina da kujerar bayana ina harɗe hannaye a ƙirji, gaba ɗaya na cika nayi fam, bala'i kawai na ke so in zazzaga in sami sauƙi, hasko maganar da suka yi na ke da abin da suka tattauna. murya a ciki na ce masa,"nan zamu kwana ne?".

wani kallo ya watsa min yana cewa,"ba ki iya bayani ba ne?".

Da har zan ce masa,"ban iya ba". Sai kuma dai na ce,"wai a jira na awa ɗaya".

Agogonsa ya kalla kafin ya ce,"to zauna mana kin wani tsayan aka".

Kaucewa nayi na basa wuri zan sauya kujera na ce,"bana zama wurin da yake da najasa".

Kuma kafin in zauna ya taso yana cewa,"muje mu dawo".

Bayan fitowar tamu daga asibitin wajen masu siyar da kayan marmari mu ka nufa, ina daga cikin mota ya fita, haka aka jido komai na kayan marmari sai da aka cika leda. ya buɗe bayan motar aka zuba su, sannan ya tafi wani kanti, bayan mintuna ya dawo tare da yaron shagon hannunsa riƙe da katan ɗin maltina da na madarar gwangwani peak ta ruwa.

Bayan ya dawo motar ya zauna ne ya ke cewa da ni,"sai mai ya kamata akaiwa mara lafiya?".

Na ce,"ko iya wannan ma yayi, amma in da dama a siya kaza gasashshiya ko nama balangu".

"Ok". ya ce, sannan ya tayar da motar muka wuce. Kaji ya siya manya guda uku anan wajen wani cin abinci na albaik, daga nan kuma mu ka wuce asibitin Imamu Wali shi ma anan jan bulo ɗin ya ke gaba da asibitin da muka je. Sai da muka isa asibitin ne tukunna ya sami damar buɗe baki yana min bayanin wai yaron da ya kaɗe jiya zamu duba. da "to". kawai na amsa shi muka ɗebi kayan dubiyar da muka siya muka wuce zuwa ciki.

Ni dai bin sa kawai na ke zuciyata na ƙissima min wasu abubuwan, emergency ward muka je, ashe da gaske ne yaron ya bige, ai da ya faɗa min ce na ke ya faɗi hakan ne kawai don ya kare kansa. Kuma Allah sarki yaron ƙarami ne ya sha jiki don har karaya ya samu a ƙafa, sai dai jinin ma da Hubbi ke cewa zai bayar an samu wani ƙanin Baban yaron zai bayar. Mun ɗan jima kafin mu yi musu sallama, suna ta godiya kuwa kamar yawun bakinsu zai ƙare, ni ban sani ba ma ashe kusan kowa ya zo a ƴan gidan su Hubbi, uwar yaron har da hawayenta wajen yi min godiya wai mijina mutumin arziƙi ne.

A can asibitin da muka je aka min test muna zuwa ya karɓo result ɗin, ya jima a ofishin likita kafin ya fito, ni dai tun da ya fito na kalli yanayin fuskarsa naji jikina yay sanyi, na nemi sukuni na rasa, hankalina duk ya tashi, ko magana bai yi min ba yay gaba na bi bayansa. Motar ma yacca ya figeta ka ce wani bala'in yaƙi za'a yi, da haka muka baro asibitin ni dai na kasa magana kuma maganar na ke so in yi, shi kuwa kana kallonsa zaka san cewar ransa babu daɗi kwata kwata.

Lokaci ɗaya idona ya cika da ruwan hawaye, ba'a faɗa min gwajin da aka yi min ba, haka kuma ba'a faɗa min sakamakon da aka samu ba, amma tuni zuciyata ta gama raya min abin da sakamakon ya bayar, shikenan tawa kuma ta ƙare, ta tabbata da gaske bana haihuwa, yanzu cikin wannan tsananin halin wa zai rarrashe ni?, madafar da na ke gani in ji daɗi yanzu bata ni ya ke ba, fatana ɗaya kar aurena ya dagule ta silar hakan.

hijabina na saka na goge hawayen da ya sakko min, Allah kaɗai ya san me na ke ji a zuciyata, yanzu shikenan har in koma ga mahallicina ba zan ga jinina ba?, ba zan haifi yaron da zai kalle ni ya kira ni da mahaifiya ba?, zan mutu ban bar wanda za'a ke gani ana tunawa da ni ba in ci arziƙin adu'a ta dalilinsa, shikenan duniya ba zata kira ni da sunan uwa ba?.

Ƙwarai na san an buɗe min babin ƙalubalen dangin miji na tsantsar cin mutunci da gori akan rashin haihuwa?, canjin matsayi a wurin miji?, ƙarin aure ya tabbata lahu na sani, don haka dole ne cin zarafi daga kishiya, wani sabon kuka ya zo min, na kifa kaina a saman ƙafata ina rera shi a hankali, na sani tabbas duk wani abu da zai samu bawa daga Allah ne, kuma hakan alkhairi ne a gare shi, fatana ɗaya ubangiji ya ba ni ikon cinye wannan jarabawar rayuwar.

Ina cikin kukan na jiyo muryarsa yana faɗin,"wai ke babu ranar da za ki girma ne?, kina wani kuka sai kace jaririya, mene hakan?, ba'a miki komai ba ki kama kuka, wannan ai shirmen banza ne".

Na ɗaga ido ina kallonsa, gaba ɗaya babu wani tausayina a saman fuskarsa, balle a biyo ga batun rarrashi da ban haƙuri da nasiha, dama tuni ya saka hijabi a tsakaninmu kan waɗannan abu ukun. ba a komai ne ka ke da buƙatar ayi maka bayani ba, wani abun hankalinka da tunaninka zaka sa ka fahimta, tsawon watanni ban san matsalar da ta kawo canjin yanayin zama tsakanina da shi ba, amma daga abin da Yayarsa ta zo tayi min jiya na ɗora samun saɓaninmu da shi akan hakan, don na san dai tabbas in har laifi nayi za'a faɗa min, shi mutum ne dai baya ɓoye wannan. hmmm ƙwarai na sani yanzu zan shiga wata sabuwar rayuwa ne, ba fata na ke wa kaina ba, amma na sani na gama rayuwar farin ciki a gidan aurena, domin banga alamun Hubbi zai karɓi wannan ƙaddarar tawa ba, banga alamun zai taya ni mu cinye jarabawar tare ba, lamarin zai zama tamkar ni na gaza ne.

Muryata gwanin ban tausayi na ce masa,"Hubbi ba ka faɗa min abin da likitan ya ce ba".

"ke kika kawo kanki?".

"Ba ni na kawo kaina ba amma kuma tawa lafiyar aka duba ai, ina son sanin abin da likita ya faɗa kaji, ina son sanin abin da yake damuna".

Maimakon amsar tambayana sai jan tsaki yay. a maimakon gida sai naga mun ɗauki hanyar gidansu, haka kawai kuma a karo na farko naji ina tsoron zuwa gidan, daga waje ya ajiye motar bamu shiga da ita ciki ba. Ni ya bawa ledar siyayyar da mu ka yiwa Iyam, ginin gidan irin ginin tsakiyar nan ne, babban parlo zaka fara shiga, a ciki kuma kowa da ɓangarensa ta can ciki. shigarmu falon mu ka tarar da Amarya, tana ganinmu fara'a ta wanzu a fuskarta tana tafa hannu wajen yi mana lale lale.

Nayi ƙarfin halin ɓoye damuwata na aro jarumtar fara'a da walwala na yafa. na duƙa ƙasa na gaisheta daga bisani kuma su ka shiga gaisawa da Hubbi. nan yake cewa da ita,"na ji gidan tsit".

Ta ce,"umm suna can falon Malam ana hira".

"Iyam ma tana can?". Ya tambaya a lokacin da yake cire hularsa yana susa.

"anya kuwa, kamar dai tana ɗakinta".

sai kuma ta dube ni tana cewa,"kin san bamu jima da gama hirarku ba, na ke cewa ya kamata in samu lokaci in shiga in duba ku, ashe ma kuna tafe a hanya. to fatan dai duk kuna lafiya".

Ina murmushin yaƙe na ce,"muna lafiya lau, ya muka same ku?".

Ta ce,"lafiya lau. Tashi ku shiga ciki nima zan ɗaukowa Malam abincinsa ne".

Hubbi zai wuce ta dakatar da shi da cewa,"Malam yini yay yau bai ji daɗi ba fa, ku fara biyawa ta wurinsa, ɗazu ma da ƙyar ya iya zuwa asibiti duba yaron da ka bige...yauwa Nazifi kaga anata mantawa, AC ɗin falon nan da fankar ɗakin Gwaggoje sun lalace, ita ma Ummaa naji tana akwai gyara a ɗakinta".

Ya ce,"tom shikenan za'a gyara da wuri in sha Allahu".

"Madallah Allah yay muku albarka, ya ƙara maka buɗi da wadata ko don taimakawa ahalinka da ka ke yi".

Sashin Malam mu ka wuce, ina saka ƙafata a falon sai kuwa ƴan yaran su ka taso kowannensu da murnar yana faɗin,"oyoyo ga Anti Ca'ida".

Su ka cukwikwiye ni sai farin ciki su ke da ganin nawa, Lubabatu ce me cewa da su,"ba za ku ƙyaleta ba sai kun yar da ita".

"Ni dai ce matar Yaya kayami ta bani biccit zan caketa".

cewar Sahura ƴar gidan Anti Aisha, cikin muryar gwarancinta me abin dariya.

Abasiyya ta ce,"ai ko to duk wanda bai rabu da ita ba ba za'a ba shi abin da aka siyo ba, tun da duk ba ku iya gaisuwa ba".

da saurinsu su ka sakeni kowacce na gaishe da ni cikin maganarsu ta ƴan koyo, da yake cikinsu duk babu wacce ta haura shekara biyar, Mansur ne ma da ya ƙara wayo kwanan nan maganarsa ke fita sosai.
Shigowar Hubbi falon kuma duk sai suka yi kansa, dama shi gwanin son yara haka ya tarbesu da fara'a yana ba su hannu su tafa. Malam ya fito daga cikin ɗakinsa muka gaishe shi tare da yi masa sannu da jiki, yaji daɗin zuwan namu kuwa sosai, nan aka ɗora hirar da ake yi da mu, Amarya ta kawo mana abinci, ni dai na ce ta haɗe mana da su Lubabatu mu ci tare, dama shi Hubbi bai tsaya wata wata ba ana kawo masa ya tankwashe ƙafafu ya shiga ciki, da ike ma'abocin tuwan masara miyar kuɓewa busashshiya ne. Bayan mun gama cin abinci mu ka miƙe don wucewa, kamar kullum in muka zo Malam yay mana nasihohin da ya saba, da ƙara bamu tarin adu'oin da ya kamata mu riƙe a ko da yaushe musamman na tsari. mu ka yi godiya da adu'ar Allah ya ƙara lafiya sannan mu ka fito zuwa wajen Iyam.

Can na baro Hubbi ya shiga ɗakin Yayan Shago. Shigata falon Iyam babu kowa, don haka na nufi hanyar ɗakin barcinta tun da banda shamaki da duk mallakinta, a hankali na murɗa hannun ƙofar na sanya ƙafafuna ciki bakina ɗauke da sallama. tana daga kishingiɗe akan ƙaton gadonta ta na kallon wani film a tashar gaskiyaplus, da ike ita ƴar gatan ɗanta ce tv biyu gareta falo da ta ɗaki. tun daga yanayin yacca ta amsa min sallama na sha jinin jikina, wani kallo kuwa da ta watsa min sai da na kusa kifewa a ƙasa, anan fa na ƙara tsinkewa da lamuran da suke ta faruwa.

cikin mugun tsoro da shakkar yanayin fuskarta na ƙaraso ciki na durƙusa ina gaida ita, ba yabo babu fallasa ta amsa min gaisuwar tana miƙewa zaune yayin da ta ke gyara ɗaurin ɗan kwalinta.

"Ke ce da daddare haka?".

Da mamakin furucin nata na ɗago ido na kalleta, to sau nawa muna zuwa a lokacin da ya wuce haka ma, sai yau ne zai zama laifi?, sai kawai na sadda kaina ƙasa ina jan yatsu na ce,"tare da shi muke ya tsaya ɗakin su Adamu ne. mun sameku lafiya?".

"Lafiya lau". ta amsa a daƙile ta na jifana da wani irin wulaƙantaccen kallo.

Ledar da na shigo da ita na miƙa gabanta na ce,"ga wannan muka zo miki da shi".

"Nazifin ne ya siya ko, na gode masa kuwa Allah ya ƙara buɗa masa, yaron ariziƙi irin albarka, haihuwa me gidan rana".
ta ɗauka tana buɗawa don duba me ke ciki.
Ni dai nayi shiru raina ina ta jin babu daɗi da yanayin yan da yau ta sauya min, ta fito da duk abin da ke cikin ledar waje tana ta sakawa wanda ya siyo albarka, yacca take faɗa da biyu don kusan magana ce take faɗa min, sai na ji duk na ƙagu ya shigo su gaisa mu tafi.

"To wannan tufar dai ita zan fara ci, wannan yogot ɗin kuma ba in sanya shi firiji zuwa safiya yay sanyi sai yafi daɗin sha".

Sakkowa tayi a gadon nayi saurin yunƙurawa ina cewa,"haba Iyam ina ɗakin sai kin je da kan ki, kawo na saka miki".

Saurin janye ledar tayi tana yarfa min wani kallo, tana min harar ƙasan ido ta ce,"matsa ban wuri".

Matsawa nayi ta wuce ta je ta saka abunta a firij, lokacin Hubbi su ka shigo shi da Adamu da Yayan Shago. ganinsa da tayi tamkar an tsundumata a aljannah, bakinta yaƙi rufuwa nan da nan ta shiga gyara masa wajen zama duk da cewa wurin a kimtse ya ke.
gaisawa su ka shiga yi tana masa tambayoyi dangane da lafiyarsa da aikinsa, can ta waigo tana kallona ta ce,"ɗan je ki daga can babban falo mana, ai ba kya samu a gaba da kallo ba kamar wasu tv, hirar uwa da ƴaƴanta ai akwai sirri".

Furucin nata ya taɓa ni, na miƙe jiki a saɓule na fita idona duk ya cika da ruwan hawaye, yaran dai har yanzu suna wajen Malam don ina jiyo ƴar hayaniyarsu, ƴan matan kuma suna ɗakunansu sai dai ba na je ba su tsammaci faruwar wani abun, idan na zo na saba a ɗakin Iyam na ke yini, duk mai son hira da ni sai dai ya sameni acan. ni kaɗai na zauna nayi jugum kamar wata marainiya wacce bata da uwa bata da uba. damuwar da na ke ciki sam ba zata barni ɗauko waya in daddana ba don ɗebe min kewa, ga tarin tambayoyi sun cika ƙwaƙwalwata, ko canjin Hubbi bai girgiza ni ba kamar canjawar Iyam a gare ni.

kusan tsawon minti biyar Ummaa ta fito daga ɗakinta, ganina zaune ta saki baki tana kallona da mamaki.

"Sa'ida zuwan yaushe?".

Ina murmusawa na ce,"zuwanmu babu daɗewa kenan Ummaa, Ina yini".

"Lafiya lau, to kuma kika zauna ke ɗaya anan kamar wata baƙuwa, ruwan da aka yi da magribar nan ne yasa duk muka wuce ɗaki da wuri, ke ɗaya ce ne?".

Nace,"aa tare da shi muke".

"to ƙalau dai ko?".

Na amsa da,"ƙalau Ummaa, mun fita ne dama sai muka biyo ta nan ɗin mu gaishe ku".

"Allah sarki, Nazifin bai shigo ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login