Showing 45001 words to 48000 words out of 87761 words
ba yay sha'awar ƙara zuwa gidana, kuma su ɗore a haka duniya ta ɗora laifin akaina ace saboda ba nawa ƴaƴan ba ne yasa ban basu tarbiya ba.
na samu ma da ƙyar na kashe maganar, sai bayan la'asar kafin su tafi. sai dai fa Hindatu kamar za tayi bindiga saboda haushi da takaicina, wai haƙurina ya wuce ƙa'ida.
washe gari da safe bayan Hubbi ya kai yaran makaranta ya dawo, mu ka yi breakfast sai dai tun dawowarsa naga kaman akwai matsala, don ba haka ya fita ba, na tambaye shi bai ce min komai ba, na ce Allah ya kyauta don bana so na takura masa da tabaya ya fusata, yana daga cikin mutanen da in ransu ya ɓaci to basa so kowa yay musu magana sai sun sakko, ban kawo matsalar tsakanina da shi ba don na san babu abin da ya haɗamu, lafiya lau ya fita kai su makaranta har yana tsokana ma wai na fara tumbi.
da rana bayan ya ɗauko yaran a makaranta, na zuba musu abinci suka ci, na ce musu zanje in kwanta in huta idan lokacin islamiya yayi su shirya su wuce. shigata ɗaki ba daɗewa sai ga Atika ta shigo ɗakin tana faɗin,"wai ki zo inji Abba".
bayanta na bi, ina shiga ɗakin kamin nayi yunƙurin magana ya ce,"sako hijabinki zamu fita".
yanayin yanda yay maganar kaɗai ya shaida min bafa lafiya, na fita a ɗakin kafin na sauko har sun kai mota shi da yaran, can na tarar da su ina zuwa na buɗe na shiga. magana na ke ta masa tun barowarmu gida bai ce min ƙala ba, raina ya ɓaci zuciyata ta ƙuntata, don bana so ya ke min irin haka a gaban yaran, shiru nayi ban ƙara magana ba har sanda na ɗago ido naga yay parking motar a ƙofar gidanmu.
nan kuma naji yana waya yana cewa,"Yashaik mun ƙaraso".
ya sauke wayar a kunne yana juyawa ya kalli yaran ya ce,"ku buɗe ku fita". sai bayan sun fita nima ya ce da ni,"fita mu je".
na ce,"wai lafiya?".
"za ki gani in mun shiga daga ciki".
da tarin tambayoyi fal a raina dangane da zuwanmu gidan na fito daga motar, fitowata tayi daidai da isowar Yashaik, su ka yi musabaha nima ina cewa,"Yashaik ina wuni".
wani wawan kallo ya watsa min ba tare da ya amsa ba, yaran suka gaishe shi yana musu fara'a ya amsa tare da kama hannunsu suka shiga gidan, bayan yace da Hubbi Bismillah ka shigo.
ya dube ni ya ce,"muje".
na yi gaba yana biye ni da ni a baya, jikina duk a sanyaye don ban san me ke faruwa ba, kuma ƙwaƙwalwata ta kasa haska min abin da ka iya faruwa ɗin.
Ummani na tsakar gida muka shiga, yanayin fuskarta sak na Yashaik babu annuri, karo na farko da banga farin cikin ganina ba duk sanda na zo gida a tare da ita. ta sakarwa Hubbi fuska su ka gaisa tana shi masa albarka sannan ta ce mu shiga falon Kaka.
shi ya fara shiga daga ciki, ni kuwa tsayawa ni na kasa shiga saboda tsabar tsoro, ƙirjina sai fat fat ya ke, Ummani ta zo ta wuce ni ta shiga. Kaka ya danno min zagi ba shiri na ɗaga labule na faɗa ciki.
ciki ciki duk suka amsa gaisuwata, Kaka ne da Abbaa da Yashaik da Yaya Imam sai Ummani, banga yaran ba ina ga suna ɗakin Ummani.
gefen kujerar da Ummani ke kai na zauna, a tsawace Kaka ya ce in dawo daga tsakiya, na miƙe ƙafafu na rawa na isa in da ya nuna min.
Kaka ne yay gyaran murya yana fuskantar Hubbi ya ce da shi,"Nazifi me yake faruwa? ka faɗi duk irin ɗibar albarkar da ƴar banzan yarinyar nan ke yi maka a gidanka ni kuma zan sa ka ɗauki matakin da ya da ce da ita don ubanta Salman da yake zaune kusa da ni, ahalinmu kaf ai babu ɗan iska to me kuma dalilin da zai sa a samu ƴar banza a gidan aure".
furucin na Kaka yasa na ɗago a ruɗe ina kallonsa, kafin in kalli Hubbi da ya fara rattabo zance tamkar ɗan jarida.
"amm Kaka dama matsalar dai akan yaran da Yayyuna su ka bani ne saboda sunga Allah bai azurtani da haihuwa ba, wannan tausayin yasa suka ɗebi yara har biyu suka bani halak malak, sun bani domin suna da yaƙinin zan riƙe su bisa gaskiya da amana haka kuma da yaƙinin ita iyalina zata kula da su. da lafiya lafiya mu ke zaune da Sa'ida Kaka ba wata matsala sai ɗan saɓani na wani lokaci da ba'a rasawa ga ma'aurata. amma tun zuwan yaran sai ta sauya gaba ɗaya, ta canja ɗabi'u, ta ɗauko wasu halaye na banza ta ɗorama kanta, ban san wa yake zugata ba ta ɗora karan tsanarta akan yaran nan, bata sonsu sam, kuma abin sai ya shafa har da ni, yanzu haka zancen da na ke tsakaninta da Yayyuna kallo ne bata ko gaishe su.
kuma da aka ce an mallaka min yaran saboda na fita hakkinta don ban san ba ko ita zata iya cutuwa tun da ba kowa ne ke iya karɓan ɗan wani ba, lokacin ta nuna farin cikinta har da hawayen murna. amma yanzu ban san mene matsalarta da yaran ba, tsakani da Allah suna mata biyayya, amma ita kenan kullu yaumin cikin muzguna musu take yi, bata da burin da ya wuce taga sun ƙuntata, tamkar marayu haka suke komawa a gidan idan ba nan.
kwanakin baya haka ta hora su da yunwa, ta hana su abincin safe kuma ta ƙi ba su na makaranta, wallahi ɗayar cikinsu Atika daga makaranta aka kaita asibiti kamar zata mutu saboda ciwon ciki, sai kirana akayi a waya aka shaida min, ina zuwa asibiti likitan yace yunwa ce a dinƙa bata abinci.
to wannan ya wuce ma. jiya nayi tafiya kaduna tasa yaran a gaba ta zane akan ta dafa abinda ba sa ci sun ce a dafa musu wani, kawai sai ta hau zaginsu har tana cewa zata saka su wani gida a saka su a ɗakin karnuka, wai har da baƙinta suma suka rufarwa yaran, haka su ka yini babu abinci sai da safen nan da zan kai su makaranta su ke faɗa min abin da ya faru, saboda a gidan kasa faɗa min suka yi saboda tsoronta ta ce zata faffasa musu baki. wallahi yanzu haka shatin waya ne a bayan ita Atikar alamar ta zanu iya zanuwa, sai da ta nuna min ma na ke jin zazzaɓi a jikinta alamun ba lafiya tabbacin dukan ne ya haifar mata da zazzaɓi, har raina ban ji daɗi ba, ina son yaran, ko ɗan wani ba zan so inga ana zaluntarsa ba wallahi balle wanda ya ke nawa, duk da bani na haifesu ba amma ko yau Allah ya bani nawa ba zan banbanta su ba.
tsakani da Allah idan iyayensu suka san abinda yake faruwa sai ta raba zumuncina da su, abin da ya faru wancan karan har yau mahaifiyata na fushi da ni, ba wanda zai ji daɗi yaga ana cutar masa da ɗa.
to Kaka ni tunda gaskiya na kasa gane kanta shi ne na ce bari na kawota gareku, aji ta bakinta mene yaran su ka mata, kuma mene matsalarta da su ƴan uwana da yanzu ma gaba ɗaya bata shiga sabgarsu don ko abu ne ya kama na gidanmu kaitsaye zata ce min ita bata son zuwa. to ayi haƙuri a mata nasiha ta gyara don ni idan nayi mata ta dinƙa botsare botsare a gidan, in kuma wani laifi na mata da yasa ta ƙullace ni ta faɗa a samu masalaha. amma gaskiya tsakani da Allah Kaka zan faɗa muku akan ƴan uwana ko ɗan da na haifa a cikina zan iya rabuwa da shi, haka akan yarana zan iya rabuwa da uwarsu ma muddin ta takura musu. ta faɗa idan ba zata iya karɓar yaran ba ne to".
tun fara jawabinsa na zama tamkar matacciya, da ƙyar na ke iya fidda numfashi, hawaye kuwa tsabar ruɗani da mamaki gami da baƙin ciki ya gagara sakko min, sai zuciyata da naji tana wani irin zafi. Allah ɗaya ya san irin baƙin cikin da ke narke a ƙasan zuciyata. na sani a yau kam ba ni da wani gata sai na Allah, ban da ta cewa domin a wannan dogon jawabin nasa babu mai tsayawa ya saurari nawa, za'a yanke hukunci ne kawai da iya abin da ya faɗa.
Kaka na kallonsa ya ce,"Yanzu kai haka ka zauna kana haƙurin ƙunsar baƙin cikin yarinya ƙarama, to ai ba shiru za ka yi ba Nazifi, ci gaba da zayyano shika shikan rashin mutuncin da take shuka maka, sam sam cire tausayinta a ranka ka zayyane mana komai, wannan muguwar ai tafi ƙarfin aikata ta'addacin iya haka, maza zayyano min su kaji na san akwai wasu bila adad, kai kenan tsawon shekaru takwas ɗin nan zaman haƙuri ka ke da ita baka taɓa hankaɗo mana ita nan ba an gyara mata zama".
ya ce,"Kaka ni dama cuzgunawa yaran shine dai damuwar, zan ɗauki komai banda cutar min da yara da wulaƙanta ƴan uwana, idan har aka saita haka ɗin to komai me sauƙi ne".
na ɗaga kai ina kallonsa da maɗaukakin mamaki, Namiji Ƙayar Ruwa, nama rasa wanne irin tunani zan yi akansa, amma komai LOKACI NE na (oum Mumtaz).
"Keee". Kaka ya kira sunan nawa a kausashe.
gabana ya faɗi, na ɗago kai a sanyaye ina amsawa cikin dashewar murya.
"bar sadda kai ƙasa munafuka, idona za ki kalla muguwa wadda taci amanar tarbiyar da iyayenta su ka bata, kuma ki sani ba kiyi mana adalci ba don sam babu koyarwar zalunci a ɗabi'un ahalinmu, karo na farko da naji ina danasanin wani jika nawa".
sai kuma ya juya kan Nazifin yana faɗin,"kaima lusarin namiji da ka bari mace ta rainaka har tafi ƙarfin ka hukuntata sai ka kawota gaban iyayenta, ta ya ma za'ai manyan abubuwa na faruwa irin haka ka zuba mata ido".
da faɗin haka sai jin saukar kwanon sha nayi kaf akan fuskata, da ya ke na silver ne hakan yasa naji zafi sosai, na rufe ido a razane jikina na rawa, zafin na cikin ratsa jikina sai ga ƙundumemiyar ashariya daga bakin Yaya Imam wanda ya taso a fusace zai sa ƙafa ya hamɓare ni sai shi Nazifin yay saurin dakatar da shi.
"kar ka dakar min mata Imam, ban kawota nan dan a ɗora hannu a jikinta ba, na kawota ne domin a nusar da ita daidai".
"rabu da ni Nazifi in saukewa azzaluma mara mutunci iskancin da ya ke kanta...".
Yaya Imam ɗin ya faɗa a zafafe cikin hasala.
yana shiru Yashaik ya ce,"da ya ke butulu ce ke wadda bata san alkhairi ba, har a ɗauki ƴaƴa a baku abun da ba kowa zai iya ba, ko mu nan ƴan uwanki bamu yi tunanin hakan ba amma ki kasa godiya garesu da ubangijin da ya ba ki ta wata hanyar, sai rama khairi da sharri? to zatonki za ki ga daidai a rayuwa?".
Yaya Imam dai so kawai yake ya dake ni, don kaɗa ƙafa yake ta aikin yi yana dunƙule hannu ya yarfar.
"banza kawai, duk irin halaccin da mutumin nan yay miki shashasha idonki ya ƙeƙashe saboda kina da baƙar zuciya za ki saka yara a gaba kina cutarwa".
Yashaik ya amshe,"yo ina ta san zafin rainon ciki da haife shi da zata san darajar ɗa, tunda Allah bai bata ba ai bari ta kassara na wasu saboda tana baƙin ciki, to kuwa ina za'a ba ki haihuwa Sa'ida a wannan matacciyar zuciyar ta ki, ai ubangiji ma kyawun zuciyar mutum ya ke kallo yay masa ni'ima. ni wallah ban taɓa tunanin ba ki da hankali da tunani ba sai yau, ashe daƙiƙiya ce ke me amfani da ƙwaƙwalwar jahilan farko".
ya numfasa saboda yacca amon muryasa ya tsananta nuna ɓacin ransa, ni kuma sai lokacin hawaye yay nasarar sauka daga idona, na ɗora hannu bisa goshina kaina kife ƙasa ina jin wani azaba daga zuciyata tamkar an cirota ana babbakata, ai dama ni na san kam yau sai abinda naji na gani, haka ahalina su ke idan ransu ya ɓaci komai faɗa maka su ke yi, don ma dai shi ɗin ya hana a dukeni da ba za su tsaya doguwar magana haka ba, kawo yanzu ina nan da fasashshen jiki.
zan buɗi baki nayi magana Kaka ya dakatar da ni a tsawace,"kika yi magana a wurin nan sai na faffasa miki baki don uwarki da ubanki mara mutunci. idan auren kika gaji da shi yasa kika tsiri wannan iskancin yanzu zansa ya sake ki ya huta da masifa, daga nan sai inga a inda za ki zauna kiyi zaman zawarcin don ba'a gidan nan ba".
ya kalli Nazifin ya ce,"maza rattaba mata kalaman da za su rabaka da ita har abada, in ya so kaje ka auro mai mutunci da tarbiya da ilimi me imani a zuciya ka zauna da ita wadda zata riƙe maka yaranka tsakani da Allah. ni bana goyon bayan kaci gaba da zama da wannan ƴar banzar yarinyar, ba sonka take ba, gwara ka sakota ko bara ne ta koma yi don babu wanda zai kuma ɗaura mata aure, ba mutanen banza ba ne mu da zata je ta wulaƙanta mana ahali, uban da yake zugata taje taci gaba da zama da shi".
kuka na fashe da shi sosai ina girgiza kai na ce,"Kaka wallahi duk ba haka ba ne, ba haka ba ne Ka...".
Nazifin yay caraf ya ce,"Kaka ayi haƙuri ai mata nasiha kawai...".
sandar da Kaka ke doragawa wani lokacin ita ya ɗauko ya buga min a ƙashin baya.
"bar ni da ƴar banza Nazifi da ina magana zata sako min baki tana ƙaryata mijinta saboda ta cika wadda bata san darajan manyanta ba. nasihar me za'a mata bayan ta san daidai da ba daidai ba, to billahillazi Sa'ida ba ki fi ƙarfin duka ba a wurina, in kina tunanin ni da kaina ba zan iya lallasaki ba zan sa Imamu yayi miki matsiyacin dukan da za ki dawo hayyacinki. don ubanki ba'a riƙe ɗan wani ita uwarki aka riƙeta, ba a haƙuri da halin yaro aka yi haƙuri da na uwarki, wa ya san kalar haƙurin da aka yi da ita, sai ke kin samu yara masu tarbiya da miji na rufin asiri shine za kike cutar da su gaba ɗaya".
yay shiru na ƴan sakanni sannan ya kira sunana da cewar kina jina. na ce "ehh Kaka".
"na rantse da tsarkin mulkin Allah kika janyo abun da zai rabaki da igiyar aurenki idan kin zauna a gidan nan Allah ya ɗauki raina a ranar, kuma sai nasa Salman ya sallamaki a ƴaƴansa. saboda haka ki shiga taitayinki, daga yau kuma wannan lokacin ki aje duk wani rashin mutunci da yake ranki ki kula masa da yaransa, kar na ƙara jin ƙorafi irin haka, bautar aure kika je yi ba zalunci da rashin mutunci ba".
Na haɗiye yawu da ƙyar na ce,"insha Allahu Kaka, insha Allahu kawo ƙarata ba zai kuma zuwa gabanka ba, kuma don girman Allah kuyi haƙuri zan gyara nayi alƙawari".
tun ɗazu Abbaana bai ce komai ba, kuma naji daɗin hakan domin ban san me nasa ɓacin ran zai sa ya gaggaya min ba, duka ne kawai Allah ya riƙi hannunsa darajar aurena, sai kuma takaici abun da Nazifi ya karanta musu akaina ya hanasa magana.
gyaran murya yayi ya kira sunansa sannan ya ce da shi,"Nazifi wanne mataki zuciyarka ke faɗa maka ka ɗauka akanta? Kar ka ji nauyinmu".
kansa ƙasa ya ce,"Abbaa nasiharku gareta kawai na ke roƙo".
Abbaa ya sauke numfashi ya ce,"Bisa umarnina Nazifi, duk ranar da ta ƙara yunƙurin cutar maka da ƴaƴa ko ta nemi ta wulaƙanta ƴan uwanka don Allah kaima ka wulaƙantata, ka ƙuntata mata, ka ɗauki duk kalar hukuncin da zuciyarka ta yanke akanta kar ma ka kawota gabanmu...sannan bisa umarnina in har zanci alfarmar zama mahaifi gareka, ina so daga ranar yau ka datse alaƙarta da duk wasu mutane da take mu'amala da su idan ba ƴan uwanka ba ko nata, na tan ma sai wanda ka yarda tayi mu'amala da su in ba su maka ba ina goyon bayanka ka ci mutuncin duk wadda ka gani cikin gidanka".
sai kuma ya juyo gareni ya ce,"ke kuma ki buɗe kunnuwa da kyau ki jini, idan ƴaƴan Sa'id ko na Imam aka ɗauka aka baki haka za ki cutar da su?".
"a'a Abbaa".
"to don me akan ƴaƴan ƴan uwan mijinki, baku fa akai saboda tausaya muku an san cewa rashin haihuwa da raɗaɗi, amma saboda rashin tausayi da imani sai ki ɓige da mugunta da zalunci Sa'ida, kuma akan ƙanan yara, haka ake yi dama? silar haka yanzu ba sai ki raba shi da yayunsa ba. yanzu can sun ba ki kin kasa riƙesu, kina tsammani cikin ƴan uwanki yanzu akwai wanda zai sha'awar ɗaukar ɗansa ya ba ki? in Allah ya ba ki ki mutu kika barsu wa zai ji tausayinsu ya ɗauka tun da an san uwarsu ba mutuniyar kirki ba ce".
ya nunfasa,"to daga yau bisa kashedi me girma kar ki kuskura mijinki ya ƙara kawo ƙorafi akanki idan ba haka ba za ki shiga uku a hannuna, zan mugun saɓa miki ne, ki cirewa kanki duk wani mugun ƙuduri, zuciyarki ki ta so yaran kamar ke kika haifa, yanda ba'aji ƙyashin ɗauka a baku ba bai kamata ke kiji ƙyashin kula da su ba".
"nayi alƙawarin gyarawa Abba, laifina ba zai ƙara zuwa gareka ba da yardar Allah, ka yi haƙuri ka yafe min".
na faɗa cikin kuka me taɓa zuciyar me saurare ina haɗa hannayena wuri ɗaya alamar roƙo.
ya ɗauke ido akaina ya mayar kansa ya ce,"kayi haƙuri Nazifi da duk rashin mutuncinta, na kuma gode da ka kawota muka san halin da kuke ciki. sannan abu na gaba da zan faɗa maka shine; yau ta zama rana ta ƙarshe da zan kuma ganin Sa'ida a cikin gidan nan har sai nan da tsawon shekara guda".
ya faɗa yana juyawa ya kalli Yashaik yace,"Sa'id ka rubuta min kwanan watan yau". kana nima ya kalle ni ya ce,"kin ji me nace ai, kar na ƙara ganin ƙafarki cikin gidan nan har tsawon shekara guda cif, saɓa hakan kuma zai ja miki samun saɓani da ni ki kuma