Showing 9001 words to 12000 words out of 87761 words
dan ko da nazo ɗora tukunya ma na ɗan buge shi ban sani ba ruwan zafin ya zubar masa a hannu sannu ban ce masa ba, haka shima ɗin kallo kawai ya bini da shi.
Bayan na kammala girki na kwashi kwanukan abincinsa na kai ɗakinsa, lokacin yana zaune bisa darduma yana jan carbi, na ajiye na zauna ina faɗin,"ga abincinka".
Sai kuma na kalli hannunsa nace,"kayi haƙuri bana sane ruwan zafin ya zubar maka".
Ina jin yanda ya kalle ni, ban san tunanin me yayi ba sai kuma yaja jallabiyarsa ya lanƙwasa ƙafafu, na dire plate ɗin da na zuba masa shinkafa da miya a gabansa tare da zuba lemo a kofi shima na ajiye. Fuskata a haɗe kamar hadari, tun da ya ɗau cokalin yake ta kallona, ni kuma hannun nasa da ruwan zafin ya zuba kawai nake kallo, sai naga kamar shi ya hana shi cin abincin, a hankali nace da shi,"ba zaka iya cin abinci da hannun ba ne?".
Ya haɗiye yawun da ke maƙoshinsa yace,"abinci babu nama ba kifi?".
Nace,"ka ci abin da ya samu mana".
"Ban gane me kike nufi ba".
Na miƙe ina kwashe kayan da ya cire nace,"babu ɗaya daga cikin abin da ka tambaya a gidan".
"Kuma shi ne ba za ki iya shaida min sun ƙare ɗin ba, ban hana abu ya ɗauko ƙarewa ba aƙi sanar min".
Baki na taɓe nace,"ban ganka a gidan ba ne".
Bai ce da ni komai ba naji ya ɗauki waya, Labaran ya kira wanda yake bawa yayo cefanen gida, ya karanta masa abubuwan da zai siyo, ina jinsa yana tambayana bayan nama da kifi sai mene babu, ni kuwa na bawa iska ajiyarsa, sai da ya ɗaga murya sannan nace,"ina jin su kaɗai ne babu, sai maltina wadda ta rage iya shan yau ce".
Wankinsa da ke cikin kwando na tattara na ɗaure na ajiye a gefe, na ce masa,"ga wannan wankin".
Ta gefen ido ya kalle su yace,"Shehun bai zo ya ɗauka jiya ba?".
Nace,"ban sani ba ko ya zo ɗin".
A ƙufule yace da ni,"saboda kin je ina?".
"Saboda ina ɗakina".
Na faɗi hakan ina tsugunawa zan ɗauke plate ɗin abincin gabansa da ya gagara taɓawa har yanzu, ya barsa sai shan iska yake daga ba ya yace ba zai ci mai sanyi ba, dakatar da ni yay da cewa,"me kika taka ne wai?".
Shiru nayi ban ce masa komai ba. Ya ƙara cewa,"ba magana na ke miki ba".
Kamar ba zan tanka ba sai nace,"me kuwa na taka Hubbi wanda ya wuci abin da ka taka".
Yanayinsa naga ya sauya haka kuma muryarsa tayi sanyi wajen cewa,"asibiti na tsaya jiya, na bige wani yaro, amma da sauƙi".
Gabana naji ya faɗi, har zan yi ƙorafi kan cewa shi ne ya gagara ya sanar da ni, sai kuma kawai na bagarar nace,"Allah ya ƙara sauƙi".
Yace,"amin, ya zubar da jini da yawa yau zanje a ɗibi nawa a saka masa".
Kallonsa nayi ta ƙasan ido nace,"Allah ya taimaka".
Ina faɗar hakan na bar masa ɗakinsa na fita. Samu nayi ana ƙwanƙwasa ƙofan falo, na ƙarasa na buɗe, ganin wadda ke tsaye a gabana nace,"Hassana Tijjani".
Na faɗi sunan nata da muryar bayyana murna da jin daɗin ganinta. hanya na bata ta ƙaraso ciki tana ta nishi alamun ta gaji da yawa, jakar hannunta ta wancakalar kan kujera tare da kwance goyon bayanta, sannan tace da ni,"me gidan yana nan?"
Nace,"Yana ciki". sai ta fasa cire mayafinta tana sake cewa,"ke ƙaro gudun Acn nan, jina nake kamar a garwashi".
Na wuce wajen makunnin AC na ƙaro ina cewa da ita,"daga ina kike haka ne?, Naga sai zufa kike haɗawa...bari na kawo miki ruwa".
Kitchen na wuce ina jiyota tana faɗin,"ke dai bari tafiyayya nayi tun daga Shanono, naje gidan wan Mamarmu gaisuwar ɗansa, muna shigowa kano kuma muka wuce gidan ƙanwata Saratu anyi mata tiyata an ciro yaro babu rai, nace dai to yau tun da Allah yasa nayi kusa da unguwar su Sa'ida in sha Allahu sai na zo mun gaisa".
Ina ta murmushi na ajiye babban farantin hannuna da na sako ruwan sanyi da lemun ɓawo da ayaba,"sannu da hanya, to ya aka yi kika gane gidan?".
Tana goge zufa tace,"na kira wayanki ban samu ba sai kawai na kira Ummani ta min kwatance".
Nace,"kar ki ce min sai da kika je gidanmu".
"Wallahi sai da naje, ai ba zan iya zuwa kano dai in yawace yawace ban je na gaida Ummani ba, tace ma in gaida ke".
Na kuwa ji daɗi matuka da cewarta, fuskata ta washe da annuri ina cewa,"Maimuna ina godiya da yanda kike girmama mahaifiyata, Allah ya bar zumunci". Ta amsa da amin, ni kuma na ƙara cewa,"ya ƙarin haƙuri?".
"haƙuri mun gode Allah, kwanakin nan anata rasuwa wallahi, rasuwar ma ta matasa".
Nima cikin jajantawa nace,"wallahi kuwa sai fatan Allah yasa muyi kyakykyawan ƙarshe. Dama Saratu lokacin haihuwarta yayi?".
"Ina fa bakwaini ne, to ɗan ma sai yazo babu rai".
Nace,"Allah sarki Allah ya bada rayayya".
Naje na ɗauki yaronta da ke bacci na kwantar da shi kan wata ƙaramar katifa da na ɗauko gudun kar yay fitsari akan kujerar. Ni dai har raina naji daɗin ganinta, rabona da ita tun kafin mu dawo gidan nan, ƴar ajinmu ce tare muka yi sakandire, tana cikin abokan arziƙin da aka yi zaman mutunci da su, ƴan gidanmu kaf babu wanda bai san Hassana Tijjani ba, kafin muyi aure yawan lokuta ta kan zo gidanmu, bini bini ta kira Ummani su gaisa, saboda tana sonta sosai, ko ina ta shiga ta yabi mahaifiyata taita bada labarin mutuncinta. duk da ni ina ɗan shashshareta saboda ban cika son ƙawaye ba, amma hakan bai sa ta ja baya da ni ba, ko da bikina tun daga Zariya ta zo sai da ta kwana uku, haka da su ka dawo zama kano ta jajje gidana ba zai ƙirgu ba, amma ni kuwa tsabar kirkina zuwana gidanta bai fi sau uku ba.
"Sa'ida ban fa yi sallah ba. In fara yi kafin mu zauna wannan hirar tamu ta yaushe gamo". Ta ce bayan ta ajiye jarkar ruwan da tun da ta kafa kai bata sauke ba sai da ta kusa shanyewa.
Na kalleta murmushin fuskata bai ɗauke ba na ce,"to ko sama zamu hau, kyama yi wanka kiji daɗin jikinki".
Tana dariya tace,"wanka Sa'ida kamar wacca ta zo kwana, raba ni, na dai yi sallar kawai. Sallar ce in baka yita ba babu natsuwa kwata kwata".
Tashi nayi na ɗauki yaron nata da na ke ta jin kunyar in tambayeta sunansa, lokacin da ta haihu har hotonsa ta turo min da sunansa, haihuwanta biyu duk babu wacca naje mata barka, amma hakan baisa ko kaɗan Hassana ta nuna min rashin jin daɗinta ba ko ƙorafi, ita ce ma mai yawan nemana a waya taji ya nake.
Ina nufar sama ta ce da ni,"Sa'ida ku fa gidan nan na ku na ƴan gayu ba a rasa ku da banɗakuna a ƙasa, saboda haka ki taimaka ki rabani da hawa dogon benen da idanuwana ke gani, ba za ki gane yanda ƙafafuna su ke a gajiye ba".
Gajeriyar dariya nayi na maida yaron na kwantar, bedroom ɗina na ƙasa na rakata, sai da na takurata akan tayi wanka. Na fito na barta a ciki na wuce kitchen na haɗo mata kayan abinci, lokacin yaronta ya tashi na ɗauke shi ina ta masa wasa, yaron tubarkallah ɗan kuɓulɓul da shi ga shi tsab tsab, babu ko irin ƙarnin tumbuɗi a jikinsa sai ƙamshi yake yi, daɗina da Hassana kenan tsabta gaba ta bata ba baya ba.
Dawowarta tana murmushin jin daɗin da ya kasa ɓoyuwa a fuskarta take cewa,"au Jamil tashi ya yi?".
Aiko nan naji daɗin faɗar sunan da tayi, ina murmushin nima nace,"ai yanzu na ke cewa Jamil har haka yayi wayo sai dariya yake yi abinsa, ga shi babu ruwansa da rigima".
Haka ta zauna ta shiga cin abinci, tana ci muna ta hira abinmu, sai zuba santin gidana take yi, faɗi take wannan ai shi ake kira da aljannar duniya, dama gata ƴar barkwanci duk in da na zagaya da ita sai tace wannan kuma ni Hassy menene shi, haka fitilun falo ma wai ai ita ba zata iya kwana ba gani zata yi kamar zasu faɗo kanta taga haka ake yi a film ɗin indiya...cikin hirarmu take bani labarin mutuwar mijin Firdausi itama ƴar group ɗinmu ce a makaranta, na ke ce mata wallahi ban sani ba amma zan samu in shiga a satin nan in mata ta'aziyya. Hirar tamu kuma ta juya kan kasuwancin da uwar bari tasa mata su ka durfafa, har take neman shawarata akan sana'ar da take so ta fara na kiwon kifi, ai kuwa nan na ƙarfafa mata gwiwa akan tayi ɗin na kuma daɗa nuna mata muhimmancin sana'a a wajen mace. Taji daɗin shawarwarina sosai, mu ne har la'asar anata zuba ana shewa, sai lokacin ne tayi ɗan jim ta kalle ni tace,"don Allah kiyi haƙuri da tambayar da zan yi miki".
Nace mata,"tambayan me Hassana?".
Ta numfasa tace,"kiyi haƙuri ba sa ido ba ne, damuwa da ke ne wallahi, ke dai kin san yanda Allah ya jarabce ni da sonki, domin ni ba matsayin ƙawa kike garen ba, ganinki na ke tamkar Hussaina da na saki Nono ta kama".
Na murmusa kuncina na ce,"na sani Hassana kar ki damu faɗi abin da yake cikinki".
"Me yake damunki naga kinyi uwar rama haka?".
"Wai da gaske ramewa nayi?, Sai aita na rame ni kuwa banga ramar da nayi ba, Hubbi ma ce yay nayi ƙiba".
Galla min harara tayi tana faɗin,"ban sani ba ƴar rainin hankali, ga fa ƙashin da ke wuyanki Sa'ida abin da babu a da".
Dariyar da ta bayyanar da haƙorana na yi nace mata,"kar ki damu ba wata damuwa ba ce, jinya na sha kwana biyun nan, watana biyu a kwance".
Aikuwa ranta ya ɓaci ta nuna min rashin jin daɗin hakan. ta fara mita akan me yasa ban taɓa faɗa mata ba, ta ya za'ai ace har na sha jinya irin haka bata sani ba, ko bata zo duba ni ba adu'a da sannu ai suna da daɗi. Ni dai haka nayi ta bata haƙuri, ta gama mitar sai kuma can ta doka tsalle ta rungumoni tana murmushi cikin fara'a tace,"kinga ki bani wanga albishir kawai kar ki ja min rai".
Nayi lakato ina kallonta domin na san in da zancen nata ya dosa, ta zame a jikina tana daɗa cewa,"wata nawa?".
Na waro ido na ce,"keee mene wata nawa?".
Tayi min wani kallo na kar ki raina min hankali. Na ce,"Allah kuwa, idan shi ne ai tun a waya zan sanar miki, wallahi bani da komai Hassana har yanzu shiru, sai dai a ci gaba da samu cikin adu'a".
Jikinta a sanyaye tace,"to Allah yasa jinkirin Alkhairi ne. Amma dai ai ba kya fuskantar wata matsala ko, kin san sha'ani na dangin miji".
Murmushi nayi na ce,"ko ɗaya fa, ai kin fi kowa sanin surukai na. Ita Iyam ma da kanta take nema mana magani".
Tace,"Allah sarki. To Allah yasa a dace, ke kam Sa'ida ai kinyi dacen suruka wallahi, ga dangi miji kamar kece ƴar tasu".
Ni dai murmushi kawai nayi na kuma san yanda nayi na katse maganar haka. ta miƙe tana faɗin,"bari nayo fitsari in zo in ɗauki hanya yanzu za kiga magriba tayi".
Tashinta ba daɗewa naji Maganar Hubbi akaina yana cewa,"ina jiranki".
Bayansa na bi da kallo wanda tuni ya wuce yay komawarsa ɗaki, nayi godiya ga Allah da yasa Hassana bata nan, da haka zai fallasa lamarin da na ke ɓoyewa. Kaina na girgiza cike da takaici da baƙin ciki na tashi, na ɗauki Jamil na tafi da shi. A ɗakin na same shi yana kaiwa da komowa, na tsaya daga gefe na ce,"gani".
Tsaye yayi yana ƙarewa Jamil kallo, ban sani ba burge shi yaron yay kome masa ne oho, yana dai ta kallonsa kamar ma zai miƙo hannu ya karɓe shi. shirunsa yay min yawa na ɗago kaina na kalle shi naga bai ɗauke ido daga kallon Jamil ɗin ba, muryata a hankali na ce masa,"ɗan gidan Hassana ne".
Sai sannan ya ɗauke idonsa akan yaron yana cewa,"wace hakan?".
Na kalle shi nayi guntun murmushi na ce,"Hassana Tijjani dai ƴar ajinmu".
"Ohhh, haihuwa ta ƙara yi?".
"Ehhh shi ne wanda aka haifa ranar da zaka tafi Hajji ban samu zuwa barka ba".
Ya sake cewa,"ohh Allah ya raya". Na amsa da,"amin". jimm na ƴan sakanni kuma sai ya sake cewa,"ashe Yaya ta zo jiya".
Furucin nasa yasa gabana ya faɗi ras, duk sai na nemi na daburce da yay maganar wacca ta fama ciwon jiya na cin mutunci da Yaya ta yi min. Idona na rumtse gam nace,"ehh na manta ne ma ban faɗa maka ba".
Cikin fusata ya ce,"wai ke mene matsalarki ne, iskanci ko kuma rashin mutunci?, Yayan ta zo jiya, jiyan ma da daddare amma saboda rainin wayo za ki buɗi baki kice kin manta da zuwanta. dama har haka kika fara raina min ƴan uwa?, Ashe maganar da na ke ji na cewan kina wulaƙanta su gaskiya ne ba ƙarya ba, to bari kiji na faɗa miki, zan iya ɗaukan komai amma ban da cin zarafin ƴan uwana, ba zan ɗauki hakan ba Sa'ida ke kin san waye ni, akan ƴan uwana ina iya rabuwa da kowa ko da ace ɗan cikina ne...".
Furucinsa na ƙarshe yasa na kalle shi babu shiri, ɓoye raunina nayi na tari numfashinsa ina basa haƙuri, saboda yacca yake ɗaga murya tsab Hassana da ke falo zata iya juyo komai.
Daka min tsawa yay wacca har ta firgita Jamil, nan kuwa ya tsanyare da kuka, na furta na shiga uku ina jijjiga yaron a kafaɗata, na kalli Hubbi da idanuwansa ke a warwaje nace,"don Allah kayi haƙuri".
Ya watsa min banzan kallo da ya saka yanayina sanyi, na sadda kai ƙasa ina mayar da ruwan hawayen da ke shirin sakkowa. A hankali nace da shi,"don Allah kayi haƙuri kayi ƙasa da muryarka kaga bamu kaɗai ba ne a gidan...".
Ni dai ban iya ƙarasa maganar ba kuka ya ƙwace min, ƙafafuna na rawa na nemi kujera na zauna don sam bana so in fita a haka Hassana ta fuskanci matsalar da ke tsakanina da mijina. Ganin na zauna takaici ya kama shi ya kuma doka min tsawa da cewa,"dukanki nayi ko zaginki nayi da za ki sakar min kuka?". Sai kuma yaja tsaki yace,"ki wuce kije ki sallameta ta bar min gida, minti biyar na ba ki ki shirya zamu fita".
Saboda yanayin yanda na ga ya rikiɗe nayi saurin miƙewa jiki na ɓari, Allah yasa ta cikin ɗakinsa akwai ƙofar da zata sadaka da saman bene, don haka nabi ta nan gudun kar in fito in haɗu da Hassana. Har na shiga ɗakina Jamil na ta kuka ina aikin jijjiga shi, wanka na yiwa yaron na saka masa wasu sabbin kaya da na siya nacl ce zan kaiwa Maman Amatu kayan barka. ai kuwa kamar jiran wankan yake ina gama shirya shi yay bacci, nima shiga nayi na ɗaurayo jikina na zo na ƙara shiryawa cikin dogowar riga coffee colour, na ɗauko hijab ɗina yadi uku da rabi na saka sannan na ɗauki liƙab na zura a jakata.
Ko da na sakko na sami Hassana tana jirana, galala tana kallona ta ce,"wai bacci yaron nan yayi?".
Ina murmushi na ce,"bawan Allah shima ya gaji, kuka ya saka ina masa wanka kuma sai bacci".
Ta karɓe shi fuskarta sai ƙara fidda annuri take yi tana ta godiya da yaba kayan da na saka masa. Tana ce mun za ta tafi nayi shahadar ce mata,"a'a ai ki tsaya kawai mu fita tare sai mu rage miki hanya, kema ai sauƙin ki ne".
Bata ƙi ta tawa ba cikin jin daɗi ta ce,"aikuwa na gode sosai, dama yanda yamman nan tayi sai kayi ta fama da masu ɗan sahu".
Na juya ina ce mata ta jira ni gamu nan fitowa, haka na wuce gabana sai dukan tara tara yake, tsorona bai wuci inje in ce masa zamu ragewa Maimuna hanya ba ya yarfani, yazo yay ta ɗaga murya yana hayagagar faɗa har mata ta jiyo mu, ni ban ma san shegen karambanin da ya kaini ce mata ta tsaya ɗin ba.
Yana ɗaura agogo na same shi, yayi kyau sosai a baƙin yadin da ya saka, lokaci ɗaya sai naji tarin tsoro da shakkar da su ke manne a zuciyata sun bi iska sun tafi, na taka na isa gabansa, ba tare da sanin ma shigowar tawa ba sai ji yay na kama hannunsa ina karɓan agogon in ƙarasa saka masa, haka maɓallin gabar rigarsa ma na saka masa sannan na miƙo masa hularsa ya saka da kansa, don ita duk san da zan saka masa sai yay min tsiyar Habibty in kika sa min hula sai ki mayar da ni kamar wani tsolon rake, ga shi kin kasa ɗaukan darasin da na ke miki akan yanda ake sakata.
To yau dai bai tanka min ba, kallona kawai yay na ƴan sakanni ya ɗauke ido yana wucewa ya ɗauko maƙullin mota. Sai a sannan na sami zarafin ce masa,"Hubbi don Allah zamu wuce tare da Maimuna mu sauketa a hanya". Na faɗi hakan ƙirjina sai bugawa yake yi.
"to".
gaba nayi yana bayana, sai da zamu fita a ɗakin naji yana cewa,"wannan hijabin ne kawai da ke?".
Na juyo na kallesa na kalli ƙasan rigata da yake kallo wacca adon stones ɗinta su kai bajau, in dai mai idanu ya kalla sai sun ɗauki hankalinsa, dalilin hana ni saka ƙaramin hijab kenan idan na saka kayan da adonsu ke bayyana har can ƙasa wanda zai ɗauki hankali da ban sha'awa. Muryata sanyi ƙalau na ce da shi,"wai bai wanke sauran ba sai waɗannan kawai ya kawo min, ina ta jiransa ma jiya shiru bai zo ba ban san uzurin da ya riƙe shi ba, ko na makaranta ma bai kawo min ba".
Wayarsa ya zaro ya danna kiran lambar me wankinmu, yana ɗagawa ya ce da shi,"kana ina?".
Ban san me Shehun ya ce masa naga ya sauke wayar yana tsaki. Kuma duk yanda aka yi uzurin da ba zai iya da shi ba ne shiyasa ya haƙura dole, banda haka ce zai yi da shi a ko'ina yake ya kawo kayan yanzu, fitar ma naga ya ɗaukaketa ne amma banda haka akan na fita da wannan hijab ɗin na jikina gwara mu fasa zuwa, ko kuma mu jira ko ƙarfe ɗayan dare ne Shehun ya kawo