Showing 78001 words to 81000 words out of 87761 words
idan da aikatau cikin gidansa ya taimaka min. Na ƙara hasko zuwan Nazifi a lokacin da kuma sanda Alhaji Fari ya ɗauko tsabar kuɗi naira dubu ɗari biyar ya damƙa su a hannuna ya ce ga shi yayi mana domin Allah. Na ƙara hasko lokacin da na juya na fuskanci Nazifi cikin tsananin murna da jin daɗi gami da fashewar kukan tsantsar farin ciki ina miƙa masa kuɗin da cewa,"Hubbi ga shi na ka ne halak malak, Allah ya amsa adu'armu Hubbi yaji kukanmu, Allah yasa ƙarshen wahalarka kenan yasa kuma silar ɗumbin arziƙinka ne mara yankewa".
Tunanin da na ke ya katse sanda Nazifi ya dawo yana cewa da ni,"me kika yanke? Ko na ƙara miki lokaci nan da anjima?. Dubu ɗari biyar Sa'ida zata iya isarki taimakawa ƴan uwanki, idan ba haka ba kuma na ƙara miki wata dubu ɗari biyar ɗin kinga har Umra za ki iya zuwa abinki".
Hannu na saka na goge hawayena da babu su, dan ban san ma sun ƙafe ba. Ina kallonsa fuskata a washe na ce,"Na amince, na baka kwanakina na tsawon wata guda bisa yardata da amincewata, ka kula da matarka yanda ya kamata, ubangiji Allah ya bata lafiya".
Murmushi yay na nuna jin daɗi ya ce,"Na gode. sannan ki nemo sabuwar me aiki don Allah saboda kinga Zahra'u ma'aikaciya ce ba zama take yi ba, kinga akwai yiwuwar a sami me tayata aiki a ranakunta".
Nayi shiru ban ce masa komai ba kaina na kan cinyata ina kallon kuɗaɗen, na dakatar da shi daga fitar da yake ƙoƙarin yi, na miƙe na isa gabansa na kama hannunsa na damƙa masa kuɗin na ce,"ba na da buƙatarsu ka ƙara a jarinka".
Kallona ya tsaya yi ya buɗe baki zai magana na ɗaga masa hannu. "Don girman Allah kar ka ce da ni komai, kaje kawai raina fess ya ke. Daidai ne dai wanda yay ya sani, haka kuma ranar tsayuwa gaban ubangiji na nan tafe".
Dogon numfashi yaja ya sauke idonsa akan kuɗin kafin ya juya ya fita ya bar ɗakin hankalinsa kwance. Hawaye ne suka shiga kwaranya a fuskata, sai na duƙe a wajen ina dukan goshina a jikin gado, kafin na ɗago kaina na kalli sama na ce,"Ya Allah dukkan abubuwan da suke wakana kana ji kuma kuna gani, ka fini sanin dalilin da yasa rayuwa ke ta ƙwallo da ni haka, na sani ba don baka sona ba ne, amma ya ubangijina ka sama min mafita nan kusa, ka sawwaƙe min wannan ƙasƙantacciyar rayuwar da na ke ciki, Ya Hayyu Ya Qayyum ka dube ni saboda tsarkakan sunayenka".
Sannu a hankali naji ina samun salama a raina, kaina har lokacin ina kallon saman ɗakin na fara tunano rayuwar baya.
*WAIWAYE, SHEKARU TARA DA SUKA GABATA.*
*MAFARI...*
Ta dabo ci gari, garin da ba kano ba dajin Allah, jalla babbar hausa, yaro ko da me kazo anfika, tabbas a duk inda kaji anyi irin wannan kirarin a kaf faɗin duniya, kasan ba da kowanne gari ake ba face garin kano da ake yiwa laƙabi da tumbin giwa, garin da ya amsa wan nan sunan, musamman idan aka yi duba da yawan al'ummar da ke cikin garin, ƴan asali da kuma zuwo daga ƙabilu daban daban, garin da ya tara manyan Malamai, ƴan kasuwa, Attajirai, ƴan siyasa, Dattawan arziƙi, Sarakai, Makarantun boko da na addini, garin da yay shura wajen haɓɓakar kasuwanci da kamfanunuwa.
A tarin unguwannin da ke cikin garin kano, unguwar yakasai na daga cikin manyan anguwanni wadda ake kira da Yakasai rabin birnin kano, idan muka tattara zuwa makarantun da suke cikin garin kano da bamu san iyaka adadin su ba, Shekara secondry school na ɗaya daga cikin makarantun sakandire ta gwamnati da ke a cikin anguwar ta yakasai, me ɗauke da ɗalibai maza da mata. Ɗaya ga watan octoba ita ce ranar da duniya ta shaida a matsayin ranar murnar samun ƴanci na ƙasa najeriya, a bisa girman ranar ga ƴan ƙasa yasa hutu ke ta'allaƙa ga dalibai, ma'aikatan gwamnati, kamfanunuwa masu zaman kansu, har ma da wasu daga cikin ƴan kasuwa.
A yau da ya kasance talatin ga watan Satumba, daga cikin harabar makarantar sakandire ta shekara, ɗalibai ne ke ta dabdalar shigewa cikin ajujuwa bayan kammala taron asambili da akayi, mafi yawanci fuskokin su ɗauke da farin ciki saboda murnar hutun da aka basu na tsawon kwanaki biyu sakamakon murnar zagayowar ranar ƴanci na ƙasa. tun bayan komawa aji kowanne ɗalibi ka kalla zaka ga zaƙuwa a fuskarsa na son a buga ƙararrawar tashi domin tafiya gida. Ƙarfe ɗaya da rabi dai-dai aka buga ƙararrawar tashi, kuma a wannan lokacin ajinmu SS2 mune muka fara fitowa.
Sunana Sa'ida Salman Madobi, shekaruna goma sha biyar a duniya, ina ɗaya daga cikin sabbin ɗaliban da aka kawo watan da ya wuce da na baro makarantar Aisami na dawo nan ta shekara. Ni ɗin ba doguwa ba ce haka kuma ba gajeriya ba ce ina da matsaikacin tsayi me kyau gami da dirarran jiki na jan hankali, ina da cikar halitta ta ko'ina, doguwar fuskata na ɗauke da dogon hanci da madaidaicin baki da kuma irin idanun da ake kira da sexy eyes, ba zan ce ni kyakykyawa ba ce can amma dai ba na cikin sahun munana ina da kyawuna daidai misali, hasken fatata ba irin hasken nan ba ne sosai kuma ba baƙa ba ce ni, sai dai na ɗauko ɗabi'ar mahaifiyata na bala'in haƙuri da sanyi. ban da yawan magana ina son shiru a rayuwata ni kam, dan ina iya zaman minti talatin a wuri ban magana ba duk kuwa irin surutun da ake yi, wannan dalilin ne yasa wasu ke cewa ina da girman kai wasu kuma su ce saboda ƴar gidan masu kuɗi ce, basu san ni ɗin ƴar masu rufin asiri ba ce, kuma ba komai yasa ake min kallon ɗiyar masu ƙumba ba sai dan zubina da irin shigata ta uniform da jakar makaranta da yanda na ke fesfes, da Yayana da ya ke kawo ni a motar uban gidansa idan ya kai yaransa makaranta, wannan yasa da yawa ke tunanin Abbaana wani Alhajin Neran ne.
Sunan Mahaifina Malam Salman, Asalinmu ƴan ƙauyen Madobi ne daga baya kuma karayar arziƙi da mahaifin su Abbaanmu ya samu yasa muka dawo nan cikin kano da zama, tun lokacin ina cikin zani. Abbaana yana kasuwancinsa anan kasuwar kurmi shi da ƙaninsa Baba Sabi'u in da su ke siyar da citta da kayan ƙamshi na abinci, yanzu haka kuma sun koma ƴan tebura anan bakin asibitin Murtala suna siyar da atamfofin leda turmi da falle falle. Mutane da yawa sun shaidi Mahaifina akan kirkinsa da dattakonsa, duk wanda ya san Malam Salman Madobi zai buɗi baki ya ce maka mutum ne na gari wanda ya san darajar ɗan Adam da kyautatawa, ba a taɓa jin kansa da kowa rayuwarsa kawai yake yi shi da iyalansa da ƴanuwansa, ga shi da ƙoƙarin taimako.
Mahaifiyata ita ɗaya ce matarsa Sa'adatu muna kiranta da Ummani, ita kanta jama'a na shaidarta da halin kirki da sanin yakamatarta, kowa kuma zai ce maka Ummani bata da wani farin ciki sama da taga ta taimaki wani da ke cikin tsananin buƙata duk da itama ɗin ba shi ne da ita ba, akwai ta da halin kawaici da kauda kai gami da masifaffan haƙuri da ka iya hallakar da ita, amma banda idan aka taɓa ƴaƴanta, duk haƙurinta da shirunta ajiye shi take a wannan fannin ko da za su samu saɓani da mahaifina, akwai soyayya me ƙarfi tsakanin iyayena da kuma fahimtar juna, kyautatawa da rufawa juna asiri.
Mu biyar ne a wurin iyayenmu, maza huɗu sai ni ƴar autarsu mace, Sa'id shine Babba wanda mu ke kira da Yashaik saboda tsantsar uztazancinsa amma mutum ne me zafi don shi ya gaji Kakanmu Zakariyya mahaifin Abbaanmu da mu ke kira Kaka, sai Yaya Imam da ke bi masa shima ɗin yana da zafi kamar Yashaik, sai Yaya Al'ameen shi kuma irin Abbaa ne kaifi ɗaya mara magana sosai, Yaya Salman me sunan Abbaa shine na huɗu muna ce masa Abbayo, shi kuma ba gidanmu yake zaune ba a gidan babban wan su Ummani yake, sai ni Autarsu wadda tazararmu da Yaya Abbayo shekaru bakwai ne.
Ba masu kuɗi ba ne mu sai dai muna da rufin asiri, Mahaifinmu jajirtaccen uba ne wajen ganin ya tsaya akan dukkan buƙatun iyalansa da kuma ganin ya gina ƴaƴansa kan tarbiya me kyau da kuma basu ilimin arabi da boko gwargwadon iyawarsa, mahaifina bai boko ba amma mutum ne shi me son ganin ɗa na karatun boko shiyasa ya tsaya mana tsayin dka a wannan ɓangaren. Duk Yayyuna maza sun kammala makarantarsu, Yashaik shine me degree da ya kammala BUK in da ya karanci law, sai sauran masu diploma duk polytechnic suka yi, Ya Imam pharmcy Ya Al'amin Science lab, sai dai cikinsu har yanzu babu wanda ya sami aiki.
Ya shaik driver ne a wani gida yana kai yara makaranta da kai iyalan gidan unguwa, Yaya Imam kuma ɗinki ya ke yi kuma yana samu sosai, Yaya Al'amin kuma su Abbaa yake bi kasuwa, sai ni yanzu da nake kan karatuna wacca iyaye suka ci burin karatun akaina kamar ni ɗaya ce na fara boko a gidan, duk wani gata ina samu, duk abin da nace ayi min sai an yi min shi duk domin ƙarfafa min gwiwa nayi karatu sosai, domin fatansu da burinsu shine na karanci aikin likita dan tun yanzu mafi yawan lokuta Abbaana da likita yake kirana, ni kuma domin farin cikin mahaifana nasa a raina cewar in sha Allahu zan yi duk iya ƙoƙarina na dage nayi karatu don wanzar da farin ciki bisa fuskar iyayena wanda kuma nasan ta hakanne zan biyasu da kaso babu cikin kaso ɗari na ɗawainiyar da suka yi da ni. Yanzu haka duk wata jarabawa da za'ai ni ke zuwa ta biyu bayan ƙawata Safiyya da ke ɗaukan ta ɗaya. Ina maida hankali sosai a karatuna matsalata ɗaya yaren turanci wato english bai zama akaina balle bakina, ƙila don Malamai ba da turancin suke mana karatu ba ne ko da zasu yi magana da mu, hakan na ɗaya daga dalilin da yasa turanci yay min ƙaranci, kuma shine kawai matsalata a karatun boko, iyayena duk ba su yi karatun boko ba balle na sami taimakonsu, Yayyuna ba zaman gidan suke ba, amma a hakan ma ina ɗan ƙoƙartawa wajen kwaɓawa. Ɓangaren islamifa kuwa nayi saukar ƙur'ani na makarantar allo tun ina shekara tara, yanzu haka kuma na kusa yin sabuwar sauka a islamiyarmu, banda tarin littafan addini da na sauke na haddace su, fagen larabci a bakina kuwa ba'a magana.
"Wallahi nayi mugun jin daɗin hutun nan".
Safiyya ɗaya daga cikin ƴan mata mu ukun ƙarshe da muka fito daga aji ta faɗa tana gyara goyon jakarta. Maimuna da ke daga gefen hannun hagunta ta ce,"ba ki kai ni jin daɗi ba, saboda dama duk na rasa yanda zanyi da bikin Anty Samira, Baba yace ba za'a je da mu Kaduna ba, kinga yanzu na sami dama tun da dai monday ba makaranta".
Tayi maganar cike da farin ciki.
Haka suka yi ta maganganunsu har sanda muka fito bakin gate. Maimuna na kallona tace,"Yau me zamu siya?".
Sanyayyan murmushi me faɗi nayi kafin na ce,"abin da aka saba mana".
"Mayyar rake, to ni kam yau siyan rake ba da kuɗina ba, sai dai kowa ya siya abin da ransa ke so". cewar Safiyya tana min harar wasa.
Na harareta da manyan fararen idanuwana, ban ce mata komai ba naja hannunta muka nufi titi muka tsallaka. Sai da muka je daidai wajen me rake tukunna muka tsaya, sallama muka masa ya amsa mana, daga yanayin yanda mu ke gaisawa da shi zaka fahimci mun saba da cinikayyar yau da gobe, yana zuba mana raken a leda Safiyya na ta zuba masa zance, shi kuma yana ta biyeta da yake yana da baki kamarta, irin hirar ta su ba zaka ce a wajen siyan raken suka saba ba, Ni da Maimuna dai sai um da um da ke itama irina ce wajen rashin son magana.
"Ka biyewa zancenta kana ta zuba raken da yafi ƙarfin na kuɗin da aka baka".
Maimuna tayi maganar tana ɗora hannunta a kafaɗata.
"Ƙila sai ya kwashe raken gaba ɗaya kafin ya ankare". cewata wadda nayi maganar da zolaya kuma lokacin ya ɗago ya kalle ni.
Dariyar da Safiyya ta saki yasa muka zuba mata ido, raken ne a hannunta tana kaiwa baki tana ce masa,"Yaya Nazifi kaga waɗannan ƙawayen nawa haushi su ke ji saboda ina sha su basa sha, kuma fa daga yau kafin na ƙara samun rake me kyau da zaƙinsa har sai nan da kwana huɗu. Don haka Yaya Nazifi rabu da su ka cika mana leda".
Na girgiza kai nace da ita,"ke dai ba ki da tausayi"..
Kallona tayi tana ɗaga gira irin eehh taji ɗin. Maimuna tace da me raken,"Yaya Nazifi to kaji mara ƙaunarka da rashin tausayinka".
Ba tare da ya ɗago ya kalle mu ba yaci gaba da zuba raken fuskarsa na washewa da murmushi. gaba ɗaya yaran jinsu yake tamkar ƙannensa, shiyasa sau tari idan sun zo siya baya basu da wuri sai yay ta laƙai-laƙai don yana jin daɗin hira da su, akwai tarbiya, kama kai da girmama manya. Sai bayan ya ɗaure ledar tukunna ya ɗago duk ya kalle mu kana yace,"ga shi ƙannena asha rake lafiya, yau na san har dalalar yawu za'ai saboda zaƙinsa na daban ne, ai dai sha a hankali kar zaƙin yaywa haƙori illa".
Yay maganar da ƙawataccen murmushi kuma cike da zolaya.
Ina kallonsa sosai na ɗan waro ido waje na ce,"Naira sittin fa muka baka, wannan kuma ai ya kusan na dubu ko ma yafi".
Maimuna ta ce,"wannan sudar ce ai duk taja, ka rage don Allah".
Annuri ya ƙara wadatuwa a saman fuskarsa sannan yace,"kar ku damu ƙannena, idan ban baku ba zai zama asara ne, saboda dama da makarantar taku na ke ciniki, ga shi kuma kunyi hutu, kuna ta murna abinku ni kam ina ta fargaba domin zan rasa kasuwa, ko cinikin kwana guda bana so na rasa".
Tausayinsa yay matuƙar kama mu, tun ma daga yanayin yanda maganar tasa da ke tattare da damuwa tsantsa. Safiyya tasa hannu ta karɓi ledar tana ta zuba masa godiya. Maimuna ta warce ledan daga hannunta tana faɗin,"ke ba ki da tausayi sam wallahi, hankalin ma ba shi ne da ke ba".
Sannan ta dubi me raken ta ƙara cewa,"gaskiya ba za'a yi haka ba, idan ka barsa za'a samu masu siya ko ba'a nan ba".
Haka muka yi ta fama da shi akan ko yane ya rage amma sam yaƙi, dole muka haƙura muna zuba masa adu'a da godiya. san da muka juya za mu tafi muka ce ya gaida Antin mu ya amsa mana da tabbacin zai isar da saƙonmu. Tare da ƙara cewa,"Mahaifiyata bata da lafiya don Allah ku sakata a adu'arku ta kullum".
"Subhanallah Allah ya bata lafiya yasa kaffara, Allah ya tashi kafaɗunta nan kusa, Allah yasa zakkar jiki ne".
Muka haɗa baki wajen faɗar hakan, yaji daɗin adu'ar na mu sosai, ni dai sarkin tausayi har da ƙwalla ta taru a idona, muka masa sallama muka wuce, yayin da shi kuma ya ɗaga bindi(jelar saniya da ake kore ƙuda) yana kore ƙudajen da ke neman kawowa raken hari, gefe guda kuma yana ƙara ɗaga murya da faɗin,"Asai rake, azo a siya rake me zaƙi, ga arha ga daɗi".
Cikin waƙa yake ta faɗin hakan domin janyo hankalin abokan ciniki.
Ai kuwa abin kamar almara, nan da nan sai ga sauran ƴan makaranta sun zo sun siye shi tas, a lokacin babu abin da ya tuna sai maganar Sa'ida da tace za'a siya insha'Allah, murya a hankali ya ce,"Na gode da adu'arki". Ya faɗa kamar a gabanta, bayan ya gama tattara kuɗin cinikinsa ya tura baron raken ya tafi.
*MANDAWARI ROAD, KANO.*
Daga cikin baƙar mota ƙirar Rolls-Royce, wata dattijuwar mata ce fara ƙal zaune a bayan kujera yayin da driver ke tuƙata, kallo ɗaya zaka yi mata ka gano tsantsar hutu, natsuwa, kwanciyar hankali da jin daɗi a jikinta, ka kuma san lallai naira ta samu wuri ta zauna. kunnenta zuwa wuyanta da tsintsiyar hannunta da ƙafarta sanye su ke da gwalagwalai na gasken gaske, ga walwalin adon stones na tsadadden less ɗin jikinta na matuƙar ɗaukar ido.
Waya ce kare a kunnenta ƙirar Iphone 6plus a lokacin ita ake ganiyar tashe, hankalinta ya tattara gaba ɗaya ga maganar da ake yi ta cikin wayar, da dukkan alama waya ce take yi da mutum me muhimmanci a rayuwarta, saboda yanayin tsantsar farin cikin da ya nuna a tare da ita, tun fara wayar bata furta komai ba, sauraren shi kawai take yi cike da annashuwa, a karo na barkatai fuskarta ta ƙara washewa da sanyayyan murmushi me faɗin gaske, take kuwa haƙoran makka guda huɗu dake a bakinta sama da ƙasa suka bayyana, inda asalin kyawun fuskarta ya ƙara fitowa.
"Tom shikenan, amma ka sani ina kewarka sosai ya kamata kaji tausayina ka dawo haka".
Shiru ya gimla na ƴan sakanni tana ci gaba da sauraron maganar cikin wayar kafin ta sake cewa,"ni dai ba na son wayo".
Siririyar dariya ta maye gurbin murmushin da take yi sannan ta ƙara cewa,"To ya zanyi da kai, yanda kaso haka zan so, fatana shi ne ka dinƙa kulawa kaji ko, a tsare mutunci ka kuma ji tsoron Allah a duk inda kake".
Ta numfasa tana lumshe idanuwanta tare da cewa,"Allah yay maka albarka, Allah ya kiyaye min kai. Ka kira Madam ku gaisa tana ta min sababi baka ganinta da gashin ido".
"Oak to bye bye, i love you so much my son".
Wayar ta yanke sa'ilin da take sauke gwauron numfashi tare da kwantar da kanta jikin kujera still idanunta a rufe, yanayinta kuma na canjawa, kamar dai tana ɗauke da wata ɓoyayyar damuwa da ke maƙale can ƙasan zuciyarta, yayinda a gefe ɗaya ta ɗan takure hannunta cikin mayafi kamar me jin sanyi. Kuma kamar a mafarki Mrs Abubakar Jadda taji tayar motar su ta bada sautin ƙara ƙuuuuuuu, ƙarar da ta shiga har can cikin dodon kunnenta, lumsassun idanuwanta suka buɗe a sanda Driver ke furta kalmar Innalillahi wa'inna ilihi raji'un.
"Me ya faru Muntaƙa?". tayi tambayar a ruɗe idanuwanta