Showing 57001 words to 60000 words out of 87761 words
ba balle sanin darajar girmama miji. to kije tsinuwar mala'ikun Allah ma kaɗai ta isheki".
Turo ƙofar ɗakin yasa mu kallon ƙofar duka. Iyam ce ta shigo tana faɗin,"lafiya Nazifi? muryarka duk ta karaɗe gidan nan, da alama ɓata maka rai aka yi".
Gefe ya juya yana cewa,"Don Allah Iyam ki ce da ita ta bar ɗakin nan".
Ta dube ni tana cewa,"yau naga jaraba ni Jummai, to ana dole haka dama? ki bar masa ɗaki mana tunda ya ce ki fita, kinga tashi don Allah yi waje tunda dai kina da ɗakin kwanan ni bana son abunda zai ɗaga hankalin ɗana nima nawa hankalin ya ɗaga, dare mahutar bawa amma ke sai lokacin za ki tashi neman bala'i".
kasa tashi na yi hakan yasa ta ɗaga murya da cewa,"natacciya ba za ki ta shi ba ne wai". so na ke na tashi ɗin amma ina jin kunyar miƙewa a gabanta da rigar da ke jikina. rigar gaba ɗaya iyaka gwiwa ce haka kuma shara shara ce ana ganin komai na jikina. nayi ƙasa da kaina hawaye na zuba a idanuna, saukar abu naji akaina hakan yasa na ɗago, shi ne ya jefo min babbar rigarsa, daga tsugunen na ɗaura kana na miƙe na fita da sauri. ina shiga ɗaki na faɗa kan gado ina kuka me shiga jiki, wani irin kuka da ke fitowa daga can ƙarƙashin zuciya tare da bayyanar da labarin da ke cikinta, ban taɓa tunanin matakin share Nazifi zai janyo min matsala haka ba, da na san hakan zata faru tabbas da ban aikata ba na bari mun ci gaba da tafiya a yanda mu ke, ga yanzu har yana tunasar da ni tsinuwar mala'ikun Allah, rumtse ido nayi ina faɗin Allah ka yafe min Allah ka yafe min.
Bayan sati biyu na dawo daga unguwa, da yake azumi ya gabato na ce bari na jajje wuraren da zuwa ya kamani banje ba, in aka fara azumi fitar na zama da wahala. to sai ma kuma ya bani kayan sadaƙa da ya fitar na azumi ya ce in kakkai wurin da naga ya dace.
a matuƙar gajiye na dawo duk da ba wani jimawa nayi ba na dai fita da sassafe ne saboda gidan rasuwa muka fara zuwa ni da Ummani, tun daga compound na bawa Rumana jakata hijabin ma na cire shi da zummar ina shigowa falo zan rashe akan kujera, ni yanzu kam kullum cikin ciwon jiki na ke saboda bautuwar aikin da na ke sha, me shara da wanke wanken ma Iyam tasa tayi gaba, Fati kuwa ko tsinke bata taya ni ɗaukewa, za dai a ɓata da ita amma gyara ba nata ba ne, ko ɗakin Iyam ɗin da su ke kwana tare bata san ta gyara ba dole ni ke shiga in gyara musu.
Da shigowata nayi turus jiyo muryar su Yaya a ɗakin Iyam, ga ƙanan yaransu a falo suna ta dabdalarsu duk sun yi kaca kaca da wurin. ɗakin Iyam ɗin na shiga don shaida mata na dawo, ina shiga naga kusan duka ƴaƴan mata masu auren ne ma su ka zo, ban san dalili ba naji gabana ya faɗi, tsoron da ya dirar min lokaci ɗaya na kawar na ƙarasa shiga ɗakin, na gaida Iyam ɗin na ce mata na dawo ta ce to har da min sannu da zuwa, su kuwa ƴaƴan nata banda Lubabatu babu wanda ya amsa mini sai kallo da su ka ƙare min kafin daga bisani kowacce ta ɗauke ido tana faman yatsine fuska kamar sunga kashi.
maganar da na riskesu suna yi naji sun koma yi ƙasaƙasa, dama can banji me suke cewa ba balle na buƙaci jin sauran zantukan. to kan me ma suke tsammanin zan damu ba yan ba dani ake maganar ba? Ni ɗin kuma ba munafuka ba?.
Sai da zan fita a ɗakin kuma naga Ummaa ta fito daga banɗaki, da murmushina na tsuguna ina gaida ita amma itama sai naga tayi min yanda su Yaya suka min, wato dai amsawa a daƙile ba don ta so ba.
kawai sai naji kaina ya ɗaure, na farko zuwansu gidan kaf ɗinsu kamar za'ai wani taro? na biyu Ummaa ba haka ta saba min ba dan ko satin da ya wuce naje gidan kuma fuskarta sake ba alamun kwai matsala tsakanina da ita.
fita nayi daga ɗakin cikin sanyin gwiwa, karo muka yi da su Fati ita da matar ƙanin Hubbi Sulaiman, yanda su ka kalleni su ka watsar haka nima na kallesu na watsar, dama ita Zalihan cikin facalolina da ita ne bama wani ɗasawa tun can da.
Da sauri nayi gaba dan jikina bani ya ke wannan taron na su kaman da wata a ƙasa, ga kuma kallon banzan da na lura duk suna bina dashi, kaman sun yo zuga ne don cin mutuncina yacca aka saba. ina shiga ɗaki kawai nayi wankana na shirya na fita, kasa sauka nayi don sam bana so na sauka mu kuma haɗuwa da wani cikinsu, ga dole ma sai na sauka naje na sameshi tunda na ga motarsa tabbacin ya dawo kenan, Allah yasa sun yi girki sun ba shi su hutar da ni.
ni dai addu'ata Allah yasa zuwan na su ba shi da alaƙa da ni dan gaskiya tuni na gama gajiya da wannan tashe tashen hankulan da komai yaƙi ci yaƙi cinyewa, kwanciyar hankali na ke buƙata a yanzu kam. kawai dai na sa a raina yau duk wacca tayi min a cikinsu tabbas zan rama ba zan ƙyale ba ko a gaban uwarta ko a gaban ƙanin na su.
ko da na shiga ɗakinsa yana banɗaki, na zauna jiransa sai ga yara sun shigo suna faɗin za su tafi islamiya. jiran fitowarsa su ka yi saboda kuɗin littafan da za su karɓa. bayan ya fito ya ce na ɗauka rigarsa na ɗau kuɗin na ba su, sai dai ko da na duba babu hakan yasa shi cewa na ɗauka maƙullin motarsa,"cikin wajen da na ke zuba takardu akwai kuɗi ki ba su".
na ce,"nawa?"
su ka ce,"kowa dubu biyu aka ce Abba".
Na miƙe muka fita tare da su, bayan na basu kuɗin na raka su bakin gate su ka wuce kana na dawo motar don ɗauko hulunansa da ya ce za'a kai wanki. dama a kujerar baya ya ke ajiye su, na tattaro su gaba ɗaya don kusan ya saka su dukka. sai dai ina shirin fitowa daga motar wani abu ya ɗauki hankalina da yasa ni ware idona akai gaba ɗaya. lokaci guda idanuwana su ka disashe, ganina ya fara ƙoƙarin ɗaukewa, haka na daina jin sautin komai a kunnuwana, lokaci guda ƙwaƙwalwata ta tsaya cak da aiki, ganin ina neman gaza shaƙar iska da fitar numfashi nayi saurin fito da kaina daga cikin motar. Sai dai ba ni da wani iko da motsa jikina domin kuwa jini ya tsaya da gudanar da aikinsa balle na sami damar ɗaga ƙafa na bar wurin saboda tsantsar tashin hankalin da na shiga.
Yanda jikina ke karkarwa daidai yake da kaɗawar guguwa a tsakiyar rana, haka yanda na ke jin dummm a cikin ƙoƙon kaina tamkar saukar tsawa a tsakiyar duhun dare ne, allon ƙirjina kuwa girgiza ya ke yana neman barin ƙirjina ya tarwatse a ƙasa wanwar, ban san ta ya ba, ban san ya za'ai ba, amma tabbas bana tunanin zan iya gasgata abin da ƙwaƙwalwata ta karanta a jikin katin ɗaurin auren hannuna, balle kuma har zuciya da gangar jiki su iya ɗaukan lamarin.
Idanuwana na rumtse gam na ƴan sakanni kafin na shiga buɗe su a hankali, har yanzun dai a disashe su ke bana gani sosai, don haka kawai sai na ke kallon invitation card ɗin ina ƙara kallonsa, na kasa sakinsa ya kuma ƙi faɗuwa daga hannuna duk da irin karkarwar da hannayen nawa ke yi. ta cikin ruwan hawayen da su ka ɗan taru a idona na ke ƙara bin rubutun jiki da kallo, so na ke na aro hankali a wani wajen tukunna in ƙara karanta abin da ke jiki, bana tsammani a yanzu akwai hankali a tattare da ni kam, don in akwai ba zan karantowa kaina wannan baƙar musibar ba, Aure fa, Aure guda ba abin wasa ba, auren da ban san da batunsa ba, inaa da sake, ko da mijina zai ƙara aure to ba ta wannan hanyar wulaƙantawar ba, rashin darajtawa har ina haka?.
_hasbunallahu wani'imal wakil._, zuciyata ta ambata, tabbas babu ƙarya a rubutun da na gani, Aure Hubbi zai ƙara, saura kwana biyu ɗaurin aurensa, amma ban sani ba, wadda na ke da hakki akan sanin hakan.
wani wahaltaccen yawu ya wuce ta maƙoshina da ƙyar, ya sauka a cikina da babu komai face baƙar yunwar da ke ƙwaƙulata tun ranar jiya, kayan cikin nawa suka amsa, na rumtse ido saboda raɗaɗin wahala. wucewar sakan ɗaya, biyu, ubangiji ya bani aron ƙwari na samu damar ɗaga ƙafata na bar bakin motar ba tare da ko na maida murfin na rufe ba, haka na bar compound na tafi bana iya ganin gabana sosai, cikin matsanancin tashin hankali da kaɗuwa na faɗa ɗakinsa.
Zaune na same shi akan cushion ya miƙe ƙafafu kamar ba wanda na fita na bari ya fito a wanka ba, rediyo na kusa da shi yana sauraren tafsir a freedom radio, hannunsa kuma riƙe yake da littafin Muwaɗɗa yana karantawa. A hankali na ƙarasa gabansa na tsaya, kallonsa nake yi tun daga tsakiyan kai har tafin ƙafarsa, nafi ƙarfin minti biyu tsaye a gabansa amma tamkar bai san da shigowar tawa ba, ƙafafuna suka gaza ci gaba da ɗaukar tsayuwata, na duƙe a gabansa ina dire gwiwoyina a bisa carpet. Sai a sannan ya ɗago ido yay min kallo ɗaya ya ɗauke, can kuma sai ya ƙara dubana da kyau sannan ya buɗi baki yace,"lafiya?".
kai na shiga girgiza masa na gaza furta komai. tsaki yaja na takaici yana sakko da ƙafafunsa ƙasa fuska a ɗaure ya ce,"sarai kin san bana son wannan halin ko, mene ya faru?".
Hannuna da ke aikin karkarwa na ɗago na miƙa masa katin ɗaurin auren ina cewa,"tabbacin wannan na ke son sani Hubbi".
Bai karɓa ba bacin ƙwayar idonsa da ya tsayar akan fuskata, kallona yake yi tamkar yau ne ya fara ganina a duniyarsa, kukan da nake ta dauriyar riƙewa ya ƙwace min ina haɗa hannayena wajen cewa,"Don Allah, don Allah don Annabi Hubbi ka ƙaryata abin da nake gani, don Allah kar ka bar kunnuwana su jiye abin da zuciyata ba zata iya ɗauka ba...".
Katin ya karɓa a hannuna ya ajiye a gefensa, ya tari numfashina da faɗin,"raya sunnar ma'aikin shi ne zuciyarki ba zata iya ɗauka ba?, Jayayya za ki da lamarin da ubangiji ya rubuta?".
Na zuƙi numfashi ina jujjuya kaina na ce,"ban isa ba, ban kai ba, baiwarsa ce ni ban isa nayi jayayya da lamarinsa ba, kawai ni dai ina so ka tabbatar min ne".
"Rubutun da kika gani a jiki bai ishe ki shaida ba?".
"Bai ishe ni ba Hubbi, sai naji daga bakinka tukunna, sai naji daga bakin da bai taɓa min ƙarya ba balle yaudara".
Ɗakin ya ɗauki shiru, bakinsa ya furzar da iska, sautin muryarsa ya fito a hankali da cewa,"ƙwarai aure zan yi, zan kawo miki abokiyar zama, na kuma zaɓi ɓoye miki ne saboda tsarina ne hakan, dama na faɗa miki ai zan tabbatar da na ba ki mamaki".
Furucin nasa yasa na zabura na miƙe da sauri wanda har ban san yanda aka yi na tsinci hannuna a ƙirjinsa ba. Ƙirjina ya shiga dukan tara tara ina jin zuciyata tamkar ana soyata da dalma, cikin raina ina nanata kalmar AURE da ABOKIYAR ZAMA.
Muryata ta fito cikin sanyi da rauni ina cewa,"da gaske aure za ka ƙara?, Hubbi aure ba tare da na sani ba?, ace ban da masaniyar mijina zai aure sai da ya rage saura kwana biyu?, yanzun ma da ban gani ba shikenan sai dai inga ana shigo da amarya?, dama ana haka da gaske?, Hubbi komai nayi maka ban cancanci hukunci ta irin wannan sigar ba, ko ɗaya ban cancanta ba, me yasa zaka ƙara aure?, biyayyar me na gaza yi maka? duk irin haƙurin da na ke, duk irin kauda kan da na ke yi".
Na ƙarasa maganar ina girgiza kaina cikin matsanancin ƙunar rai tare da binsa da kallon mamaki matuƙa. Na ƙara faɗin,"Don Allah in wani laifi nayi maka ka faɗa min wallahi na ɗauka alƙawarin zan gyara amma kar ka hukunta ni ta hanyar yi min kishiya".
Maganar tawa ta katse, na duƙar da kaina ƙasa tare da damƙar gaban rigarsa da kyau. "Kayi haƙuri Hubbi, ka yafe min laifin da na aikata maka bisa rashin sani, in ka ƙara aure ka zalunce ni, haƙiƙa ka zalunce ni...".
Ya katse ni a tsawa ce,"Dakata!, ƙarin aure ba yana nufin lallai sai kin min laifi tukunna zan yi ba, ra'ayina ne in zauna da adadin matan da na ke so, ba'a ce lallai da ke kaɗai zan zauna ba, don haka ka da ki nemi ki haramta abin da Allah ya halasta min...kuma da kike maganar na zalunce ki ta ina na zalunce ki ɗin?, ke idan ma ba ki gode min kin ce nayi adalci ba ai kin zama butulu, duk irin haƙurin da nayi na zama da ke a haka tsawon shekaru masu yawa?, amma ba ki ko ji kunyar kallona kina tambayar akan me yasa zan ƙara aure ba, to dama ta ya kike tunanin zanci gaba da zama da ke ke ɗaya alhalin ina so naga jinina, ke in da na san ma ba kya haihuwa zan aureki ne?, kin zo kawai kin zauna daɓas ban da ci da kasayarwa babu abin da kika sani, komai sai dai ayi miki, sai aukin a baki a baki ko kunya ba kya ji, wallahi tallahi Sa'ida ban da wata darajar ko kaɗan zama da ke ya sire min, shekaru da yawa kin kasa wayewa, kin kasa zama ƴar gari ki koyi soyayyar zamani, cikin kanki empty babu turanci, duk da dama ba wani karatun arziƙi kika yi ba...ga matan abokaina nan duk ƴan boko ko ina shiga su ke da su, amma ni har kunya na ke yi idan na tuna tawa matar satifiket ɗin sakandire ne da ita, ɗan aikin zamanin nan na zaman office babu sai shiga kitchen ɗin banza da wofi, ciki ya iya ɗaukar abinci amma ya kasa ɗaukar ɗa balle har a haife, to ni ba zan iya ci gaba da zama da wadda bata haihuwa ba, ba ɗan iska ba ne ni wanda bai san ciwon kansa ba, ba zan mutu a haka ba bayan nayi aure tun da ƙuruciyata, ina son ganin jinina ɗa na cikina".
Ya ƙarasa maganar yana jifana da wani irin kallo na wulaƙanci da nuna tsana. Sosai maganganunsa suka sosa zuciyata, ashe har akwai ranar da Nazifi zai wanke ni da irin munanan kalamai haka?, ashe har Nazifi zai iya ci min mutunci haka?, duk irin tarin sadaukarwar da na yi akansa a baya?, kuma har yana da bakin cewa banyi karatun arziƙi ba?, har yana da bakin ce mini ban da aiki sai in miƙa hannu a bani a bani?.
Tunanina ya katse dalilin jin maganarsa a tsakar kaina yana sake cewa,"shekaru da yawa ba ki tsinana min komai ba, sannan ki sawa ranki cewar da ke kaɗai zan zauna tsabagen son kai irin na ki, wacece ke da har za ki ce ba za'ai miki kishiya ba, marar haihuwa ko wacca mijinta ke kunyar shiga da ita manyan wurare?, to ki sani dole zan auro mace ƴar boko, wacce ta waye, wacce zata haifa min yara, wacce zata taimaka min ba wai ni in ƙare a ɗaukar nauyinta da na ƴan uwanta ba...".
"Kai Nazifi!". Na katse shi ta hanyar kiran sunansa kai tsaye, abin da ban taɓa ba. idauwana suka firfito waje cikin ɗaga murya na ce,"na gaji da cin fuska da rashin mutunci da gorin da ku ke min kai da ƴan uwanka a cikin gidan nan, ba kuma zan ci gaba da ɗauka ba, an kawo gejin da haƙurina ya ƙare, nima zan fito in ɗaga murya tamkar kowacce mace mai ƴanci, dama na sani ba don komai aka ƙulla munaƙisar wannan auren ba sai don a ƙara samun hanyar cin zarafina, to kuwa kun yi kaɗan gaba ɗayanku, kawai! akan ban haihu ba?, akan bani da aikin yi?, akan ka taimaki ƴan uwana?...ehen haihuwa ni ce zan bawa kaina?, karatun kuma ta silar wa nayi asararsa?, to idan ka manta bari na tuna maka, ban da ƙaddarar da ta haɗa aurena da kai sanin kanka ne da yanzu na zama abar kwatance fiye da kai ɗin nan. kuma har kana faɗin ban da wayewa, kai ɗin yaushe ka waye Nazifi?, sanin kanka ne ko a shiga aji na fika, kai ina naka satifiket ɗin da ka ke da zarafin raina na wani?, har yaushe ka fara jin turancin?, Ohhh laifina shi ne kawo maka ƴan uwana da nayi akan ka taimaka musu da jari?, Ko kuma fifita aurenka da nayi akan ilimin bokona?, karatun da iyayena suka ci burinsa akaina, amma nasa ƙafa na shure duk don saboda kai da farin cikinka, har yanzu akwai ciwon rashin karatuna a zuciyar mahaifina, ka sani ba wai baka sani ba, taimakon mene ban maka ba a sanda ƴan uwanka suka kasa taimaka maka, amma daga ƙarshe in rasa sakamakon da zan samu daga wurinka sai na tozarci da gori? In kasa sanin za ka ƙara aure tsabar bana da mutunci a idonka...to Nazifi ka ƙara aura, ka kawo duk wacce za ka kawo, kuma ba zaka taɓa burgeni ba sai ka auro ɗiyar mangofak, sai ka auro ɗiyar masu kuɗin duk duniya, sai ka auro wacce zata cika maka gidan nan da ƴaƴa, sai ka auro wacce ita take rabawa dukka ma'aikatan duniyar nan office tukunna in san da gaske kayi aure".
na ƙyasta yatsuna na ce,"amma ka rubuta ka ce na faɗa maka wataran, wallahi da sannu za ka girbi abunda ka shuka, domin sai na kai ƙararka wurin Allah".
Hankalinsa kwance, a nutse ya ke kallona yace,"kin gama haukar taki?". yay dakiyar faɗa don shi kansa ya san baida gaskiya ya kuma matuƙar mamakina ayau kamar yanda ni kaina nayi mamakin kaina.