Showing 36001 words to 39000 words out of 87761 words

Chapter 13 - ƘAYAR RUWA Book 1 HAUSA NOVEL

HALIMAHZ   

20 Dec 2024

6118

yi mana a ko da yaushe, duk da cewar abu ɗaya ne dai ake ta faɗa maka to amma muhimmancinsa yasa ake ta nanata maka ɗin.

Abbaa ya fito shima a lokacin tare da Ummani ta rako shi, da yake gaskiya iyayenmu da wuri wuri su ke fita kasuwa, zaka samu ƙarfe tara sun fita. Baba Tijjani ne ma ba ya fita sai kusan sha biyu na rana, da ike shi yafi su Abbaa samu sosai, don shagunan kansa ne ma da shi har guda biyu, kuma duk ya zuba yara a ciki, to ko yaje sai dai duba yanayin yacca ciniki ke tafiya, ba wai zama yake siyar da kaya ba kaman su Abbaa.
gaisawa su ka shiga yi da juna, Babanmu ya ke cewa da Abba,"ai ce na ke ka fita ma naga yau na fito a makare". Abbaa ya ce da shi,"nima haka ai, don yanzu ma maganar da Sa'adatu ke yi kenan ta ce yau mun raba tafiya".

Babanmu na murmushi ya ce,"yanayin garin ne ai na hazo ba zaka ankare ba lokaci ya tafi. muje ko".

Ummani ta shiga yi musu adu'ar a dawo lafiya da fatan nasara, yayin da su kuma ke amsawa da amin, nima nayi musu tawa, suka nufi zaure za su fita, sannan Abbaa ya dakata ya juyo yana me kiran sunana. na ɗauraye hannu na miƙe ina yarfe ruwan. cikin ladabi da girmamawa na rissina ina cewa,"Abbaa ga ni".

idonsa a kaina ya ce,"sai yaushe ɗin za ki tafi?".

murya na sarƙewa na ce,"zuwa yamma dai, zan jira Adamu ya dawo daga kasuwa maƙullin ɓangaren namu yana hannunsa shi ya bawa da zai tafi".

na shirgo ƙaryar da ban san taya akayi tazo cikin kaina ba lokaci guda. ya gyaɗa kai ya ce,"ba na son dai tafiyar dare kin sa ni ko".

"in sha Allah ba zan kai dare ba".

hannu yasa a aljihu ya zaro kuɗi ya miƙo min, dubu ɗaya ce yana cewa,"babu kuɗin a jikina da yawa, ga wannan zai ishe ku kuɗin mota?".

kaina sunkuye na ce,"Abbaa ka barshi ma ai Ummani zata ba ni".

Babanmu ya ce da Abbaa,"maida kuɗinka". sai kuma ya kallen ya ce,"ku karɓi kuɗi hannun Al'ameen in ya tashi, ki ce na ce ya baku dubu biyar".

na fara godiya maganar Abbaa ta kutso da ce masa,"dubu biyar ta musu yawa Sabi'u...".

Babanmu ya katse shi da cewa,"bata yi yawa ba in da fin haka ma ƙara musu za'ai".

nan su ka fita ni kuma na bi su da adu'a na dawo na ci gaba da aikin da na ke. sai dai gaba ɗaya ban da natsuwa sam, zuciyata fal da fargaba da taraddin abin da zai iya faruwa a yau, ɗayan ɓari na zuciyata faɗa min ya ke kawai in faɗa musu gaskiya a wuce wurin, faɗa ne dai zan sha, sai a zo gaba batun sulhu wanda na san dole ni za'a bawa rashin gaskiya, in ya amince in koma gidansa in bai yarda ba in ci gaba da zama gidan ubana, shikenan fa kawai, to duk takura kaina da ɓoye ɓoyen na mene?, dama damuwar iyayena da bakin ƴan gidan da basa son aurena na ke gudu, to na iya shanye duk baƙin cikin miji da ƴan uwansa ma balle faɗa na lokaci, ai kafin faruwar lamarin dare na raya ina roƙon Allah mafita kuma sai ga shi ya kawo min, don haka alkhairin kenan.

haka na dawo tamkar mara lafiya, har Ummani na tambayata ko ban da lafiya ne ganin yanayina duk ya sauya. ina murmushin yaƙe na ce babu komai, kawai na shirya na fita gidan Maman Yasmin, da ke tsakaninmu babu nisa, can nayi zamana muna ta hirarmu wacca itama har sai da ta fuskanci akwai matsala, tun da ta takurani da tambaya kuma na baro gidanta na dawo gida.
dawowata na tarar Ummani har ta gama girkin da na ke cewa zan dawo in ɗora, a plate ɗaya ta zuba mana ni da ita, amma sam duk bala'in sona da dambu wallahi ɗanɗane ma sai na kasa, zoɓon da na sha kuwa sai naji yana min ɗaci. idan ina tare da uwata hira mu ke sha tamkar wasu ƙawaye, amma ina yau babu hirar don ita ɗaya na bari tana ta maganarta ni hankalina yana can neman mafitar da zata hana ni tafiya a yau ba tare da fallasuwar lamarin da na rufe ba. har sai da ta gaji itama da ta fuskanci akwai matsala, ta dinƙa min tambayoyi ina basarwa, ƙarshe a dabarance cikin hikima kuma ta fara bugun cikina har ban ankare ba na bayyana mata mun sami saɓani tsakanina da mijina.

kuma cikin ƙunci da ɓacin ran da na ke ciki ina turo baki gaba ba tare da sani ba na furta,"ni aurenma duk ya fita a raina, a barni kawai nayi zamana a gidan ubana inda ba me cin mutuncinka ya ɓata maka rai, da za'a sakeka ma da ka huta".

baki sake ido a waje Ummani ke kallona da tsantsar mamaki, don ko kusa aka ce mata zan yi furuci irin haka ba zata taɓa yarda ba, sai ga shi na furta hakan a gabanta.
ta tsura min ido tana faɗin,"kike cewa auren ya fita a ranki gwara zaman gidan ubanki, Sa'ida wa kike nufin yana cin mutuncinki har kike wannan furucin mara daɗi? hankalinki ɗaya kuwa?".

sai lokacin na ankare da baragadar da nayi, ai sai na koma tamkar wadda ta yiwa sarki ƙarya, na shiga raba idanuwa ina so na musanta abin da na faɗa duba da yanda ta rikiɗe min tamkar ba uwar da ta haife ni ba. ta ɗaga murya wajen sake faɗin,"magana nayi kika mayar da ni allon kallonki".

"Ummani ba yanda kika ɗauka na ke nufi ba fa, kawai...".

a fusace ta ce,"mayar ni shashashar Uwa kinji ko, saboda ba ki da hankali za kike irin furucin marasa tunani. tun da kike da ni kin taɓa jin na yi magana makamanciyar haka akan aurena?".

na shiga girgiza kai da sauri alamun a'a. nan kuma na shiga bata haƙuri da roƙonta cewa tayi shiru ta bar maganar haka kuskure ne na riga na yi, na san Ummani da mita kuma ga Yaya Imam na gidan yana jiyo abin da ke faruwa zai fito yay min lilis, shi ba irin Yashaik ba ne me tsayawa nazari da duba akan batu. aifa kamar na turata faɗa take yi har sai da na fara hawaye, don idan akwai abin da na tsana bai wuci ɓacin ran mahaifiyata ba musamman ace ni ce sila. ni dai ina ga tun da ta haife ni ban taɓa shan faɗa a wurinta ba irin yau, haƙurina ba shi yasa ta haƙura ba sai don karan kanta.

"ni dama tun ranar da kika zo na kalle ki na kasa yarda da yanayinki, shiru kawai nayi miki. don haka buɗe ba ki ki faɗa min haƙiƙanin matsalar da ke faruwa har kike ikirarin a sakeki ki huta".

ina kuka na ce,"Ummani babu komai, kawai ji nayi na gaji da zaman auren, gaba ɗaya na daina farin ciki sai tarin damuwa, maimakon dariya kullum cikin kuka na ke, ni har son Nazifin ma na daina, kuma ban san dalili ba".

"ehh lalataccen lamarin babba ne tun da har da kanki yau kike buɗar baki ki faɗi sunan mijinki gatsal abinda ba ki taɓa ba, auren ma kin gaji da shi la gaira wala dalil, to ko dai aljanu sun shigeki bamu sani ba Sa'ida".

"aljanu kuma Ummani!".
"to in ba aljanu ba haka kawai ki ce kin gaji da gidan aure kin daina son miji duk babu dalili".

nayi shiru ban ce komai ba. ita ɗin ma shiru tayi tare da tsura min ido, kallona take cike da zurfin nazarin son gano gaskiyar lamarin. a gefe guda kuma itama damuwa ta bayyana ƙiri ƙiri a fuskarta, tabbas uwa dabance.

"zan iya cewa ba ki taɓa min ƙarya ba Sa'ida, fito ki faɗa min gaskiyar abin da yake faruwa kar ki ɓoye min. ba akan kowacce matsala ta gidan aure ake shiru a ɓoye ba, in ta girmama faɗarta ake don a san hanyar da za'a bi a magance, balle ke da kika yi irin wannan furucin kowa yaji ya san lamarin ba ƙarami ba ne".

ajiyar zuciya na sauke ina tunanin abin da zance mata, bana so na faɗa mata abunda zai ɗaga hankalinta ya sakata a tsananin damuwa, to amma kuma idan ban faɗa mata ba bayan ita ɗin wa na ke da shi?, idan na ce zanci gaba da ɓoye komai a raina ina barinsa ni kaɗai cutuwa zan ta yi, don haka gwara na faɗa mata ɗin, ita uwa ce, wacca ta shekara kusan arba'in a gidan aure, don haka fahimtar matsalar gidan aure ita ɗin ce kawai, har ta kwantar min da hankali cikin salama.
takaicin da ke ƙasan zuciyata shi ya riƙe zubar hawaye na, tiryan tiryan na shiga zayyano mata halin da na ke ciki kusan shekara guda, sai dai haka dole na ɓoye mata zancen dukan da da su Yaya suka min da kuma shi da yace in dawo gida sai ranar da ya neme ni.

ta dinƙa kallona da matuƙar mamaki. muryarta a sanyaye ta ce,"yanzu tsawon wannan lokacin kika kasa samuna ki sanar da ni matsalar nan. ai shikenan komai yayi zafi maganinsa Allah, kuma komai yayi farko zai yi ƙarshe, Allah ya magance. hakan kaɗan kenan daga jarabawar gidan aure, sai dai ba kowacce mace ke iya cinyewa ba, a zamanin nan wadda zata yi irin haƙurinki da wuya. kema tun da kika faɗa ba kya jin daɗin zaman tabbas kin gaji da abubuwa ne, to amma ki sani ba ke kaɗai ke cikin irin wannan yanayin ba, mata da yawa basa jin daɗin zaman haƙuri kawai ake ana shanyewa, da za kiji matsalar wasu sai ki ce naki ba komi ba ne, akwai case ɗin auren da naji a radiyo ce nayi idan ni ce sai dai auren ya mutu, to amma ba yanda ka iya, mutuncin mace da darajarta na ga gidan miji, idan ka fito ma zaman zawarcin kansa ƙalubale ne babba. saboda haka ki ƙara haƙuri akan wanda kike yi Allah ba zai barki dawwama a haka ba. daidai da rana ɗaya karki ce za ki ɗauki huɗubar shaiɗan domin zai kai ki ya baroki, a ƙarshe ya barki da faɗawa kogon danasani. kuma ki godewa Allah Sa'ida domin masu matsalar rashin haihuwa da yawa suna gidan iyayensu auren ya mutu saboda ba za'a iya zama da su a haka ba, kuma sun fito an rasa me aurensu. Tabbas mijinki yay ƙoƙari kuma yay haƙuri, in wani ne tuni ya ƙaro aure, kuma matar ta zo da zarar ta haihu ya samu ƙofar wulaƙantaki, don ƙarara zai nuna miki banbancinku. to amma kinga bai auren ba bai kuma da niyya, ba don ba ya so ba sai dan ganin in yay hakan bai kyauta miki ba. babbar matsalarki ƴan uwansa masu shiga hurumin da bana su ba, don haka ki ɗauke ji da ganinki akansu da ita kanta mahaifiyar tasa, in kika nuna musu damuwarki kin ƙara basu gudunmawar cin mutuncin goranta miki ne. ke dai in har kina riƙe da addu'a, nafilfili da karatun ƙur'ani kin gama wallahi, nasara sai dai ta fuskanceki ba dai ta juya miki baya ba, kuma komai sai ya juye miki shi zuwa alkhairi, haihuwa Allahn da ya basu har su ke goranta miki akan ke ba ki samu ba, in sha Allahu kema kafin gushewarsu a duniya Allah zai dube ki ya azurtaki da haihuwar nan su ga ƴaƴanki, amma sam ki daina damuwa da kalmar juya duk da kalmar akwai ciwo, Allah ya saita lamuranki".

"Ameen Ummani na gode sosai Allah ƙara lafiya da tsawoncin kwana".

ta numfasa kafin ta ƙara cewa,"kuma ina so na ankarar da ke Sa'ida, duk fushin namiji duk wulaƙancinsa akan matarsa ba ya fasa nemanta ya karɓi hakkinsa duk da suna iya jurewa amma akwai cutuwa a hakan daga ke har shi. ban ce kisa shakku akan mijinki ba ban kuma ce ki fara zarginsa ba, amma dai kin yi shashashanci da sakarci, na san kin sani tunda kina da ilimin da ni kaina za ki bani, amma ko a addini wannan ƙauracewa junan bai halatta ba. naji kin yi iyakar yinki wajen ba shi haƙuri amma bai haƙura ba, to kin manta ke macece cikin ruwan sanyi da dabararki ba tare da tashin hankali ba za ki dawo da hankalin mijinki gareki, amma ta irin hanyar ko in kula da kika bi ai hauka ne, sai ya fara sha'awar wata macen can daban, ga ƴan uwansa kusa da ke da su ke jiran kowacce dama dan shiga tsakaninki da shi amma ba ki fahimta ba. duk wannan abin da suke aure su ke son saka shi yayi ko ya sallameki, amma in sha Allahu ba zasu yi nasara ba. gwara ki zauna ku fahimci juna, da kalar na ki salon ki faɗa masa idan har akan rashin haihuwa ya sauya miki to kin amince masa ya auro wata ke ba ki da matsala da kishiya".

Haka mahaifiyata ta saka ni gaba da tarin nasihohi akan biyayya da haƙuri a zamantakewar aure, ta bani shawarwari wajen kulawa da mijina, da hanyoyin da zan bi wajen karkato da hankalinsa kacokam gare ni. numfashi na sauke bayan gama jin duk kalamanta, cikin raina ina alƙawarin cigaba da haƙuri da kau da kai fiye ma da wanda ni a baya. nan ta umarce ni da in tashi in fara shiryawa la'asar na yi magriba zata kawo kai, bacin haka ma in yamma tayi masu mota sun fi cika kuɗi.

A sanyaye na miƙe ina wucewa ɗakina, ina shiga kuma na fashe da kuka don har ga Allah ni dai bana so na koma gidan Nazifi a yanzu, ina so zuciyata ta huta na lokaci mai yawa in dawo hayyacina. to na rasa ta yanda zan buɗi baki in bayyana musu cewa shi da kansa ya sallamo ni, ina hasko yanda zasu ƙuntata ne shiyasa na zaɓi in ɓoye ɗin, gwara kawai in haɗa kayan in koma can ƙauye nayi zamana in ya so in nemi ɓangaren da kwata kwata bamu kai musu ziyara ba, ko in koma gidan nasa in yaso duk wulaƙancin da zai min yayi na shirya ɗauka, da wannan shawarar da zuciyata ta bani na shiga kimtsa kayana cikin ƙwarin gwiwa.
motarsa ta faka a ma'adanar motoci, ya fito daga cikin motar hannunsa riƙe da leda fara me ɗauke da tambarin gidan abinci. me gadi yay masa sannu zuwa shi kuma ya shige bayan gaisawarsu. da shigarsa falo ya aje ledar akan kujera, ƙarasawa yay ya kunna tv ya dawo ya zauna, can kuma ya miƙe tare da ɗaukar ledar ya shiga kitchen, abincin da ke cikin takeaway ɗin ya juye a plate, duk abin da yake yana yi yana bin kitchen ɗin da kallo, gani yake kamar zai ga Sa'ida ta bayyana da wannan annurin a fuskarta, fuskar da kana gani zaka tsinci zallar so da ƙaunar kyautatawa mijinta, fuskar da bata nuna fushi ko da tana cikin damuwa, ko da ta gaji zaka ga akwai murmushi a fuskarta.

cikin sanyin jiki ya fito daga kitchen ɗin ɗauke da plate a hannunsa, duk cikin kwanaki shida da suka wuce yaune ranar da ya fi jin gidan ya masa mugun girma, haka kuma yau yafi jin yana matuƙar kewar matar gidan. zama yay yana cin abinci sai dai cinsa yake yana jin kamar magani, bai sani ba rashin daɗin daga bakinsa ne ko kuma daga abincin ne, duk da dai yana ɗora hakan ma akan damuwar da yake ciki, don faruwar lamarin su Atika yasa Iyam ta ɗauki fushi da shi, tana faɗa masa lallai sai dai ya zaɓa ko yaran ko kuma muguwar matarsa juya wadda bata san darajar ɗa ba.

shi bai taɓa sanin Sa'ida ce gidan nan ba sai bayan tafiyarta, don ranar da ya dawo jin gidan yay ya zama tamkar kango, ga dai shi ba wai suna good time da ita ba ne, haka ba wuri guda su ke kwanciya ba, amma sai yaji ashe motsinta ma a gidan rahama ne, a washegari kuwa da safiya tayi babu abincin safe babu na rana sai yaji duk kewarta ta cika shi, duk da ko kusa bai nadamar turata gida, haka ya gangara ya tafi gidansu zai ci abinci saboda shi ba mai son na siyarwa ba ne, sai dai yana zuwa Iyam tayi masa gate tace ai yanda ba'a bawa yara abinci a gidansa haka itama abincin gidanta ya daina ci duk da gidan ubansa ne, dole yana ji yana ganin abincin da yake so ya tafi ya barshi, sai ƙanwarsa Basira ya kira ta kai masa office da yake bassu nisa da gidanta.

kasa cin abincin yayi ya ajiye ya kwantar da kansa a jikin kujera, idanuwansa a rufe tamkar mai bacci, ya jima a haka kafin ya buɗe ido yasa hannu a aljihu ya ɗauko wayarsa. lambarta ya danna sai dai bai latsa kira ya tafi ba, sunan da ke kan screen ɗin kawai yake kallo, shi kam har ga Allah ko da yace ta tafi bai taɓa tsammanin zata yi zuciyar tafiya ba, kamar yanda bai taɓa tsammanin za'a yi kwanaki har bakwai babu kiranta babu saƙonta, saboda shi ya san wace ita akan haƙuri, kuma shi ya san wace Sa'ida akan son Nazifi.

Numfashi ya sauke ya ajiye wayar a gefe yana so ya daure kar ya kirata ɗin amma ya kasa daurewa saboda mugun kewarta da ke addabar zuciyarsa, sai dai yana kira aka shaida masa wayar a kashe. wannan hakan kuma ya taɓa zuciyarsa, kallon agogon falon yayi wanda yake ɗauke da hotonsa da nata, hoton tun na ɗaurin aurensu ne, kuma agogon Yaya ce ta basu gudunmawarsa. ƙarfe huɗu da rabi na yamma, ya sauke numfashi ya rumtse ido gam tare da riƙe kansa, anya yau zai iya kwana shi ɗaya a gidan nan? anya zai iya kwana a koma ina ne babu motsin Sa'ida?

miƙewa yay tamkar wanda aka tsikara yana isa gaban TV ya kashe, sannan ya dawo ya ɗauki maƙullan mota ya fita ba tare da tunanin ina za shi ba, shi dai kawai zai fita ɗin ne don neman mafitar da zuciyarsa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login