Showing 51001 words to 54000 words out of 87761 words

Chapter 18 - ƘAYAR RUWA Book 1 HAUSA NOVEL

HALIMAHZ   

20 Dec 2024

6125

sai ta kyaɓe fuska ta dube ni ta ce,"kayana fa to?".

kafin na bata amsa sai ga ɗan nata ya shigo da ƙatuwar katifa wadda ta kan gadonsa ce ya ciro, wajen biyayya kam a wajen mahaifiya ba daga nan ba, shiyasa ita kanta kaf ƴaƴan nata tafi sonsa.
na kama masa muka sanya katifar ya ba za mata sabon bedsheet me bala'in taushi, ya koma ya ɗauko sabon blanket da ya taho da shi daga saudiya ya ajiye, dama akwai sababbin fulalluka duk aka saka mata.
da yake da taimakonsa aka ƙarasa gyaran sai ta washe baki tana yabawa sai jera masa sannu take yi. sannan ne shi kuma yake cewa da ita tayi haƙuri zuwa gobe a kawo gado da wadrobe da dai sauran abubuwa buƙata.

"a'a ni hakan ma ya ishe ni Nazifi Allah yay maka albarka, abu da ba zaman dindin zan yi ba, Malam ne fa yana dawowa zan koma gida, idan na zauna can ne hankalina sam ba zai kwanta ba tun da gidan naka ya rasa macen arziƙi".

kallona yay ta gefen ido ina kallonsa, ya ja numfashi ya sauke ya ce,"duk da haka dai za'a saka komai zuwa gobe in sha Allahu, Malam ko da kwana ɗaya zai yi ai ba zan barki haka ba balle watanni da yawa zai yi".

"to ai shikenan, kaje ka kwanta ka huta sai da safe. yaran ka turo min su nan mu kwana tare".

ya juya ya fita nima na bi bayansa bayan na ce mata sai da safe, ba kuma ta tanka min ba banda tsaki da ta bini da shi. Tun daga wannan ranar na janye jikina daga shi Nazifin, Yaran da kuma Uwarsa, tsakanina da su gaisuwa ce, shine ma kawai zan samu arziƙin ya amsa min amma ita Iyam kam dama naci daraja ta amsa ciki ciki, shi kuwa idan ba maganar da ta zama dole ba ko ganinsa ma bana tsayawa na yi. ƴan uwansa kuwa sai su zo su yini ban gansu ba, don yanzu sun mayar da gidan kamar na su, tunda mahaifiyarsu na ciki a sati bai fi sau uku ne basa zuwa ba, kuma in aka zo tun safe sai a yini ana nuna iko da isa, aita bidiri ni dai bana bi ta kansu tun gaisuwa da zata haɗamu wacca za'a amsa min a wulaƙance, dama in suka zo bana girki da kansu su ke shiga kitchen su dafa son ransu, sunce suna da iko da gidan don haka ba za'ai masu iyaka ba, ni dai ko kusa bana taɓa biye musu zaman ɗakina ya fishshe min.

Ni a yanzu ba Nazifi ne kaɗai bana so ba hatta aurensa bana so, kuma har mutuwa ta naɗe ba zan manta da baƙin cikin da ya dasa min a zuciya ba, bana tuna komai da yay min, haka bana tuna duk abin da ƴan uwansa da uwarsa ke min, abu ɗaya na ke tunawa da shi kaɗai ya tsaya a raina shiga tsakanina da mahaifina da yay, har ta kai yanzu idan na kira wayar Abbaa ba ko da yaushe ya ke ɗagawa ba, idan ya ɗaga kuwa magana sama sama, wataran ma sai dai na kira Ummani in roƙeta ta haɗa ni da shi. fushi da Abbaa ke yi da ni shi ɗaya ne ciwon da ke dashe a zuciyata, ba Nazifi da abin da ya dangace shi ba, hakan ne kaɗai yanzu abin da ke saka ni zubar da hawaye a kowacce rana amma ba akan Nazifi da takaicinsa ba, haka ina ji ina gani mahaifiyata ta kwana uku babu lafiya amma Abbaa ya ce in har na zo gida babu ni babu shi, ranar ban iya runtsawa ba, ban iya shan ko da ruwa ba, amma a haka muka yi waya da mahaifiyata tana bani haƙuri da shaida min ta sami lafiya bacin na san kawai ta faɗa ne saboda in kwantar da hankalina, ƙarshe sai yaran ne su ka zo suna ce min sunje duba Ummani har ma ta basu sabuwar atamfa a ɗinka musu, suna ta murna abinsu suka bani na aje musu na ce su kaiwa Kakarsu.

Yashaik kusan duk sati biyu sai ya zo gidana, ko in bai zo ba ya kirani a waya ya ce in ba su, da kansa zai saka yaran a gaba da tambayar ina yi musu wani abun ne, wannan kuma na san sawar Kaka ne, to da yake dai ƴan sharrin basa kansu sai suce masa bana musu komai, ban sani ba ko da na fita a sabgarsu ne yasa su ka fara sanyi da makircinsu oho, ni yanzu abu ma idan ina da buƙata Ummani na ke kira, ita ke tura min kuɗi in kashe sabgar gabana da yake yaga idan na tambayi fita yana bari.
kuma dalilin rashin zuwana gida duba Ummani Maman Yasmin ta kira ni a waya, na zayyana mata duk abin da ya faru tace ashe shiyasa Yashaik yaƙi haɗa kayan sallah da ni wannan karan, ta tuna ranar har itama sai da yay mata masifa, nan fa ta hau min faɗa da ke jarababba ce itama shiyasa ita ɗaya ke iyawa da jarabar mijinta, kafin ta shiga roƙona akan in aje haƙurina da sanyina a gefe na ɗan wani lokaci in fara rama abin da ake min hakan zai saka duk su saduda, amma wannan haƙurin da na ke shi ke basu lasisin ci min fuska har shi mijin. saboda haka na aro rigar rashin mutunci da masifa da bala'i in saka in zama kamar wuta saboda zafin rai, in ci kutumar uban duk ɗan iskan da yay min ko da kallon banza ne balle ya nemi ya gaya min magana, ta ce harta uwarsa kar in raga mata, ƙarƙari in koyi kissa in yi kaman zan mata sujjada a gabansa amma a bayan idonsa in nuna mata karrr na ke bani da mutunci ko ƙwas, idan na fara hakan za su rabu da ni su kama abun da yake gabansu nima in huta.

na ji shawarartata na ɗan hau kan wata, tun da lallaɓawa na ke kar na zaƙe da yawa ya kuma kai ƙarata gidanmu in shiga uku. yanzun dai yadda nake haɗe rai idan na gansa har shakkar yi min magana yake, na fita harkarsa gaba ɗaya na cire tsoro sai ya fara mamakina hakan kuma ya dame shi, ya fara neman shishshige min yana neman shiri, ni kuwa sam naƙi basa fuska na nuna masa nima mutum ce me zuciya a ƙirji. ko fita zai yi bana damuwa da in bisa in masa a dawo lafiya, sai ga shi in yaga dama wani lokacin idan zai fita ya zo yace min zai fita, ba kuwa na ɗaga ko gashin gira na kalli inda ya ke, hatta ɗakinsa yanzu tsakanina da shi in kai masa abinci da na gama gyara kuma sai washegari, karatu ma sai na so nake zama yay min, ranar nan babu yanda bai da ni ba akan in zo ɗakinsa cikin dare nayi mursisi naƙi zuwa, domin na ƙudurci ni da zuwa ɗakinsa sai ranar da ya san darajata.
To haka dai na ke ta zaman babu daɗi, duk wani nawa da ya kamata ya zo gidan in gansa inji daɗi Abbaa ya hana domin da kansa yasa aka kira masa me gadi da shi Nazifin ya faɗawa me gadin duk baƙon da aka yi ya tambaye shi wurin wa ya zo, in dai wurina aka zo to kar ya bari a shiga. to Yashaik ɗin ma da yake zuwa ya daina, in ya zo dai faɗa ne ke kawo shi to amma a haka na ke farin ciki.
ta ɓangarensa yanzu ba na da wata matsala tunda babu abunda ke haɗamu, daga wajen Iyam ne dai da kuma ƴan uwan nasa abun babu sauƙi matsalar ta tsananta har tafi da, sun matsa min sosai cin mutuncina su ke yanda suka so. duk abunda su ke min haka nake shanyewa in hana kaina damuwa tun da dai haihuwar ba ni zan bawa kaina ba, haka kuma shi da su ke yi akansa ɗin ba ya yi min, tunda ba shi su Atika ya rage nuna damuwa akan rashin haihuwar.
Maman Yasmin kuwa ranar ta saci hanya tazo ta dinƙa faɗan maita da rashin zuciya irin nawa ne yasa na ke zaune a gidan, in bar musu gidan mana rabuwa da Nazifi ai ba shi zai hana ni ƙara yin aure ba. na ce mata sam ba rashin zuciya ba ne ina gudun bakin mutane ne da kuma ɓacin ran iyaye, domin duk ranar da Abbaa ya tashi zai ce min babbar biyayyar da zan masa ita ce na zauna gidan mijina, Ummani kuwa da ta tashi yi min nasiha zata fara ne da haƙuri sannan ta tafi ga batun babbar suturar Ƴa mace shine aure, kuma gidan miji shine mafi daraja wajen ƴa mace.
Yau ya kama lahadi, na tashi da sha'awar yin jan lalle, dama zan je kitso in sha Allah daga can zan wuce ayi min ko iya hannaye ne, da yake muna da taron suna ranar laraba jiya Ummani ta kirani take faɗa min Asiya ta haihu ƴar ƙanwar su Abbaa wacce su ke uba ɗaya, haihuwar sosai ta sakani farin ciki kuma a sannan nima na cire tsammani akan ba zan taɓa haihuwa ba, domin kuwa Asiya ta riga ni aure ita shekara goma kenan sai yanzu Allah ya kawo haihuwar, babu irin tsangwamar da bata sha ba don zan iya cewa har gwara ni, tunda ita sau biyu mijin na sakinta, ga kishiya da ta sanyota gaba, da yake Allah ne mai bayarwa komai kuma Lokaci ne sai ga shi yanzu Allah ya bata, ni ma Allah yasa ina da rabo, ya bani ko don masu goranta min da ganin ni na gaza.
bayan na shirya na fito domin naje na yi ayyukan da zan yi, a falo na tarar da su gaba ɗaya a zaune, dama tun zuwan Iyam gidan duk ranar Lahadi yini su ke a falo gaba ɗayansu, in ba yaran ne za su wuce islamiya ba, shi kuwa tun can asali lahadi ranar hutawarsa ce da lokacin iyalinsa balle yanzu da mahaifiyarsa ke gidan, in ba masallaci ba ko ƙofar gida ba ya leƙawa. ni dai in ka ganni a falon to zirga zirgar aiki ce don ba na zama balle raina ya ɓaci, idan tana zaune na zo na zauna don tayata hira in ba ya nan sai ta kama faɗin kana zama tare da surukarka waje ɗaya saboda rashin ɗa'a, idan kuma shine zaune a falon babu ita na zo na zauna sai ta kama bambamin ai bani da kunya ba ni da tarbiya dole sai na nuna mata ƴar zamani ce ni, ina faman liƙewa miji alhalin na san tana zaune cikin gidan saboda dai ba na son zamanta so na ke ta bar gidan. ranar har ce tayi da shi ita akan lamarina na ƴan iskan mata sai ta iya tattarawa ta tafi, banda tana ganinsa kusa da ita kullum hankalinta na kwanciya ai tuni ta kama gabanta, yay ta bata haƙuri ni kuma ya sameni yace ko magana na ke son yi da shi in ke iske shi ɗakinsa kar in ƙara zuwa gareshi idan suna tare da mahaifiyarsa.

Yanzunma kallo su ke yi sai dai ita da shi suna hira jefi jefi, yaran ne hankalinsu ya tattara ga tv, nayi sallama su ka ɗago su ka kalleni, a daƙile Iyam ta amsa shi kuwa sai tsareni da ido yay, sannu da hutawa nayi mata domin mun rigada mun gaisa tun ɗazu, na tambayeta abinda take so a dafa da rana tace faten tsaki amma yaji gyaɗa da ganye na ce to, miƙewa nayi na wucewata kitchen ban bi ta kansa ba da bakinsa da naga yana son magantuwa da alama. tun zuwanta na daina dafa son ran kowa sai na tambayeta me take so a girka, har ga Allah jinta na ke yi kamar uwata, kullum ƙoƙarina in kyautata mata amma sam ba na tsira, komai na yi bana burgeta balle yay mata daɗi, burinta ta kushe ni kawai, ku san kullum sai ta faɗa min bata sona bata son zamana da ɗanta, maganar tun tana damuna ma har na daina jinta, takurawar da baiwar Allah nan ke min yayi yawa, ta hana ni shan iska kwata kwata, ta hana na huta na sake, magana tsakaninta da ni daga gori sai cin mutunci da zarafi, kuma duk wannan abubuwan da take min daidai da rana guda ban ji ina so na mata rashin kunya ba ko na ƙi bin umarninta, uwa ce ita ko bata haife ni ba ta haifi mijina.

ina tsaka da aiki sai ga shi ya shigo kitchen ɗin, tun kallo ɗaya da na masa na watsar, ya shiga dube duben da zai yi, ni na san babu abinda ya shigo da shi sai don dai yay min magana kawai.
kusan minti ɗaya yana faman bulayin iska ganin na basar da shi sai ce yayi,"babu abunda ake buƙata?".

kamar bazan amsa shi ba sai can na ce,"babu".
"komai akwai?".

na ce,"ummm".

shiru yayi na ƴan sakanni sannan ya sake cewa,"ki saka daddawa da yawa a ciki bata son fate babu daddawa".

na ce,"na sani ai".

ina jin kallonsa a jikina har ya fice a kitchen ɗin. bayan na kammala girkin Iyam na fara zubawa na kai mata ɗakinta, na zo ina zubawa yaran nasu sai ƙwala kiranta naji, naje da hanzari gareta cike da ladabi da girmamawa. flask ɗin abincin ta turo gabana tana cewa,"wannan abincin na ki ai kin cika tafarnuwa tayi wani bauuu, ni kuwa kin san idan tayi yawa bana iya ci. ɗauki kije kawai idan anyi na dare na ci".

shiru nayi na kasa motsi, wai tafarnuwa! ni da rabon da nayi girki ma da tafarnuwa har na manta, tun farkon zuwan su Atika na daina amfani da ita saboda Rumana bata ci, kawai dai saboda ta janyo min faɗa wurin ɗanta, kuma yanzu na san ba komai yasa ta yin hakan ba sai ganin zan fita ne, tunda a gabanta na tambaye shi ya ce naje amma kar nayi yamma, to fitar ce bata so idan na ɓata lokaci sai yace in fasa ranta yay fari.
na sauke numfashi na ce,"to me zan ƙara dafa miki?".

"a'a ke da kike sauri za ki fita ai bana ƙara sa ki wahala ba".

nayi murmushi na ce,"fitar ba ta fiki muhimmanci ba, in dai fita ce kam sai na haƙura da ita akanki. don Allah ki faɗa min me zan dafa miki babu wahala ga aikin uwa".

"soya min wainar fulawa, amma kar kisa taruhu me yawa kuma albasa taji sosai".

na ce,"tou". kana na miƙe na tashi na fita. har na sa a raina na haƙura da fitar sai ga shi kuma na gama suyar da wuri. na kawo mata fuska babu yabo babu fallasa tace an gode Allah yay albarka, naji daɗin adu'ar da tayi min karon farko tun zuwanta gidan. na fita na koma kitchen ɗin na kwaso nasa kayan abincin sannan na wuce zuwa ɗakinsa. yana shirin fitowa muka yi kiciɓis tray ɗin hannuna ya kusa faɗuwa yay saurin tareni. bai bani hanya na wuce ba ni kuma ban ce masa kanzil ba tunda dai ai yana da ido, hannuna ne dai ya ƙage saboda nauyin kwanukan cikin tray ɗin, yay tsaye akaina kaman wani sanda, ganin tsayuwar tasa ba me ƙarewa ba ce na raɓa ta ɗan tsukukun gefensa na wuce, na shimfiɗa carpet ɗin da yake cin abinci akai tukunna na ɗora masa kayan abincin.
Shi kuwa baki buɗe ya ke kallonta, ta raɓa shi ta wuce har tana noƙe jikinta saboda wulaƙanci, bai san nufinta ba da wannan zaman da ta tsira tsakaninsu, tana ta wani shareshi tsabar raini, ga dai shi tana sakin jiki da mahaifiyarsa wani sa'in ma da yaran, amma shi sai wani nuna halin ko in kula take masa, da sun haɗa ido sai ta haɗe rai tana faman ciccin magani, ta mayar da shi kamar wani ɗan iska sai yake magana tana amsa masa a daƙile, shiyasa yake ganin kaman ba ita ba an sauyata, don mamakinya ke sosai akan canjawarta, kuma ya ɗaga mata ƙafa ne kawai don yaga iya gudun ruwanta, sai dai ya lura idan bai yiwa tufkar hanci ba haka za'a ci gaba da tafiya, zata mayar da shi shashashan miji ta bakin Iyam, kusan satika nawa ko ta hakkinsa ma ba ta bi, ko so take har sai ya nuna mata cewa ya gaji yana da buƙatar kasancewa da ita ne, yanayinta sam ma ba ya nuna tana da damuwa yanzu da shi, tayi wani haske ƙirjinta ya cika, ko faɗa yay mata yanzu sai ta ɗau fushi da shi saɓanin da da hankalinta zai ta shi ta rasa sukuni, lallai yay sake ta yawa.

ina sauke ajiyar zuciya ta gajiya na dubi inda yake na ce,"ga abincinka in zuba yanzu ko sai anjima zaka ci?".

bai ce da ni komai ba, na kuwa miƙe na shiga gyara abunda zan gyara a ɗakin ban ƙara kula shi ba har ya gaji da tsayuwar da yake ya zo ya zauna gefen gado.
sai da na kammala kana na ce masa,"zan wuce gidan kitson".

agogo ya kalla kana ya ce,"ok to nawa zai ishe ki?".

wani kallo nayi masa sannan na ce,"abun da ya samu".

yasa hannu a aljihu ya ɗauko kuɗi, dubu biyu ya zaro ya bani yana ce min wai babu cash a wajensa, kuma na san akwai kawai yanzu ba ya son bani kuɗinsa, tunda Iyam ta ƙyalla ido akan yana ban na cefane bayan yana ajiye komai sai ta fara ƙorafi akan hakan, tun daga haka kam na ce in anyi duniya don manzon Allah ban ƙara tambayarsa kuɗi, in ya bani falillahil hamd in bai bani ba Ummani na tura min kuɗi yanzu.
na fita na bar ɗakin bayan na ce masa na tafi. Allah ya gani ba ƙaramin juriya da ƙarfin hali na ke yi ba akan sharesa, yanda ya ke nuna kaman ya damu haka ni to nayi muguwar damuwa, faɗin na daina sonsa sai na tuna shiga tsakanina da Abbaa ne duk da yanzu Abbaan ya ɗan sakko yana kirana ma wani lokacin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login